Cutar farfaɗiya cuta ce ta jijiyoyi da ke shafar Kwakwalwa wacce ke rikita saitin jijiyoyin da cikin ƙwaƙwalwar. Wannan rikita saitin na iya bambanta ta fuskar tsanani, yawan faruwa, da kuma tasirinsa ga rayuwar yau da kullum.
Cuta ce da take shafar kwakwalwar mutum ta yadda take wargaza wani saiti mai kama da wayoyin lantarki da ke cikin kwakwalwa. Hakan kan sa wanda yake fama da cutar yin wasu dabi’u na daban ko fita daga cehayyacinsa. Shi ya sa da zarar cutar ta buge wanda ya kamu da ita, takan jefa shi cikin barazanar fadawa cikin hadura idan babu wani a kusa. Sannan faduwar kan zo wa mutum ne ɓakatatan.
Alamomin cutar farfadiya
Akwai bayanai da suka fito daga binciken masana daban-daban a fadin duniya game da alamomin cutar ta farfadiya da suka hada da:
- Jijjiga musamman daga hannaye da kafafuwa.
- Kafewar idanuwa zuwa kallon sama.
- Gushewar hankali ko rikicewa na dan kankanen lokaci.
- Alamomin razana da firgici.
- Jin jiri da hajijiya.
- Ganin haske kamar walkiya yayin farfadiya
- Tashin zuciya da yin amai, da fitsari da ba haya lokacin farfadiya.
Abin da ke janyo farfaɗiya
Likitoci da sauran masana kan cututtukan da suka shafi kwakwalwa a duniya da dama sun yi ittifakin cewa abubuwan da suke haifar da cutar farfadiya na da sigogi daban-daban, kuma sun danganta ga yanayin yadda mutum ya samu kansa a fannin tafiyar da rayuwa.
1. Lokacin haihuwa: Cutar farfadiyar na iya faruwa tun daga lokacin haihuwa idan ta zo da gardama idan jaririn ya fito bai yi kukan farko ba.
2. Yin rauni: Farfaɗiya kan faru idan yaro ya samu rauni, misali ko ya faɗo daga sama ko kan gado kansa ya bugu.
3. Cutar sanƙarau: Cutar sankarau idan ba a samu an yi magani da wuri ba takan shafi kwakwalwa, wanda hakan kan haifar da cutar ta farfadiya.
4. Aukuwar haɗari: A wasu lokutan mutum yakan kamu da cutar farfadiya sakamakon aukuwar hadarin mota idan kai ya bugu, mutum ya fita daga hayyacinsa har na tsawon kwanaki.
5. Tiyata: A yayin tiyata don ciro jariri yakan sha wahala, ko wata cuta ta shige shi ko taruwar jini da ruwa a cikin ƙwaƙwalwa ko kuma a ji wa jaririn ciwo a kai yayin ƙoƙarin tiyatar fito da shi daga ciki.
6. Zazzaɓin cizon sauro: Wasu masanan sun bayyana cewa cutar zazzaɓin cizon sauro ma idan ya tsananta yakan taɓa kwakwalwa har ya haifar da cutar farfaɗiya.
7. Shanyewar ɓarin jiki: Har ila yau, masana sun tabbatar da cewa cutar barin jiki ita ce kan gaba wajen jawo cutar farfadiya ga mutane ‘yan sama da shekara 35.
8. Cutukan kai masu haifar da farfadiya
- Lalacewar ƙwayoyin halitta: Tasirin Lalacewarsu na iya cutar da ƙwayoyin kwakwalwa (brain cells), wanda ke haifar da ƙarancin aikin jijiyoyi da ke da tsarin lantarki.
- Zubar jini ko daskarewar jini: Zubar jini ko gudan jini na iya sanya matsi a kan nama a kwakwalwa, wanda hakan zai haifar da farfadiya.
- Cutar ƙwaƙwalwa: Budadden rauni a kai na iya haifar da shigar kwayoyin cuta, wanda kan janyo cututtuka irin su sanƙarau ko kuma encephalitis, wanda zai iya haifar da farfadiya.
Yana da mahimmanci a nemi kulawar likita nan da nan bayan rauni a kai, saboda gaggawar magani na iya rage haɗarin kamuwa da farfadiya.
A gagaguta kai mai farfadiya asibiti
Ya kamata wadanda ke tare da mai cutar farfaɗiya su riƙa lura sosai da yanayi da alamomin da yake ciki, domin sanin lokacin da ya dace a ɗauki matakin gaggawa na ganin likita.
Alamomin dai in ji kwararru sun hada da:
- Jijjiga ko bugewar farfadiyar da ta wuce minti biyar.
- Daukewar numfashi da kuma fita daga hayyaci bayan farfadiyar ta saki marar lafiya.
- Bugun farfadiyar da ta wuce sau daya a rana ko lokaci guda.
- Marar lafiyan da ya ji rauni ko ya bugu sosai bayan farfadiyar ta sake shi.
- Sai kuma zazzabi me zafi da kan dade bai sauka ba.
- Mace mai juna biyun da farfadiya ta buge ta da ta.
Magunguna
Idan aka gano anihin abin da ke kawo cutar farfadiya sannan aka warware shi to za a iya warkewa.
- Yawanci idan kamar rauni ne aka samu ko kuma lokacin haihuwa ne ba a cika warkewa ba, sai dai a rika yawan shan magani don rage yawan samun buguwa.
- Akwai magani da ake kira ‘Anti-convulsants’ a turance yakan hana yawan aukuwar farfadiyar, akan bai wa masu ɗauke da ita.
- Tiyata (a wasu lokuta)
- Gyaran salon rayuwa (misali, rage damuwa, barci na yau da kullun)
- Wasu hanyoyin kwantar da hankali
Me ya kamata a yiwa wanda fardadiya ta buge?
Masu dauke da cutar farfadiya na matukar bukatar taimako a koda yaushe, saboda irin halin da sukan samu kan su a lokacin da ta buge su.
Haka ya sa kwararru ke fadakar da mutane, musamman makusantan masu dauke da cutar cewa kada su rika kasancewa cikin duhu kan matakan da suka kamata su dauka na kai daukin gaggawa ga wadanda ke dauke da cutar.
• Kawar da duk wani abu da aka san zai yi wa marar lafiya barazana kamar wuta, ko kujera, teburi ko wani karfe a lokacin da cutar ta buge shi.
• Kada a taru a kan maras lafiya don yana bukatar iska sosai, a kyale shi ya numfasa kafin nan a garzaya da shi asibiti.
• Kada a ɗura masa magani ko manja a baki, hakan zai iya shake shi ya hana shi numfashi, ko a saka masa cokali ko wani abu a baki ba don zai iya kawo masa matsala.
Manazarta
BBC News Hausa. (2021a, February 21). Abin da ke haifar da cutar farfaɗiya da yadda ake magance ta. . BBC News Hausa.
Hussain, A., Oves, M., Alajmi, M. F., Hussain, I., Amir, S., Ahmed, J., Rehman, M. T., El-Seedi, H. R., & Ali, I. (2019). Biogenesis of ZnO nanoparticles using Pandanus odorifer leaf extract: anticancer and antimicrobial activities. RSC Advances, 9(27), 15357–15369. World Health Organization