Skip to content

Fasahar kariya (Cyber security)

Share |

Fasahar kariya (Cyber security)

Cyber security kalmomi biyu ne su ka haɗu suka samar da ita. Wato cyber da kuma security.

Kalmar cyber a taƙaice na nufin duk wata hada-hada da zirga-zirgar bayanai a yanar gizo hakan na nufin duk wani abu gudanar shi ke da nasaba da yanar gizo.

Security kuma na nufin tsaro ko kuma ba da kariya. Idan muka haɗa ma’anonin waɗannan kalmomin guda biyu, za mu fahimci ma’anar cyber security a sauƙaƙe.

Fasahar tsaro ga bayanai a yanar gizo

Cyber security ilimi ne da yake samar da tsaro ya kuma bayar da kariya ga bayanai, (data) hanyar sadarwa,(network) manhajoji (Applications) da na’urori (devices) domin daƙila ɓata garin yanar gizo (Cyber criminals) daga aiwatar da hari ko kutse. (Hacking).

Fasahar cyber security tamkar wani garkuwa ne da yake ba da kariya tsakanin ɓata garin yanar gizo da ɗaiɗaikun jama’a, kamfanoni da ma gwamnati, ta hanyar samar da tsaro ga na’urori, bayanai da kuma mahaɗar sadarwa. Domin kawar da barazanar masu kutse da satar bayanai a yanar gizo.

Waɗanda suke yin amfani da hanyoyi da dabaru daban daban wajen cimma mummunar manufarsu..Daga cikin hanyoyin da masu kutsen yanar gizon suke bi akwai hanyar yaɗa malware wato malicious codes, shi wannan malicious code ɗin manhaja ce da aka kirkice ta don kawai ta cutar da na’ura. Ire iren waɗannan malwares ɗin sun haɗa da spyware, adware, ransomeware, virus, trojan, keylogger da sauran su.

Suna kuma amfani da hanyar social engineering attacks domin kutse ko satar bayanan mutum na sirri. Shi social engineering attacks ɗin dabara ce da take amfani da gazawar mutum ba ta na’ura ba. Saboda na’ura ba ta jin farinciki, baƙin ciki, tsoro, fargaba, son kai ko zumufi. Ita na’ura kawai umarni take amsa daga wanda yake iya jin duk waɗannan yanayin wato Ɗan Adam. Shi ya sa suke amfani da gazawar mutum na dangane da abin da yake ji, su yaudare shi da wani albishir din da zai sa ya yi hanzarin zartar da duk abin da suka umarce shi.

Misali, irin waɗannan saƙonni da ake turawa a ce idan ka danna wani link ka cike form za ka samu tallafi na zunzurutun kuɗi, ta wannan hanyar suke iya satar bayananka ko su siyarwa da wasu kamfanoni ko su a karan-kansu su yi amfani da bayanan da suka samu su kutsa asusun ajiyarka su kwashe tattalin da mutum ya yi shekara da shekaru yana alkintawa.

Fasahar tsare sirri

Wani lokacin kuma suna aiko da saƙon da zai ɗarsa wa mutum fargaba har ya yi gaggawar ɗaukar mataki ba tare da sani cewa gadar zare aka shirya masa ba.

Misali:
Za a turo maka cewa an yi hacking ɗin wayarka ko kuma virus ya kama wayar ka yi sauri ka danna wani liƙau dan goge wannan virus ɗin, da mutum ya danna to ya gayyato wa kansa matsala a maimakon magance matsala. Domin wannan liƙau ɗin da ake turawa shi ake kira da phishing attacks.

Shi ma phishing attacks ɗin hanya uku ce zuwa huɗu. Idan aka turo maka liƙau ko wani kundi mai ƙunshe da liƙau ta email to wannan shi ne phishing.

Idan kuma ta hanyar rubutaccen saƙo wato SMS ko ta chat aka turo shi kuma ana kiranshi Smishing.

Idan kiran waya ne na kar ta kwana misali wani ya kira ka yana iƙirarin cewa daga bankinka ne ko wani kamfani, yana buƙatar bayananka na sirri waɗanda suka haɗa da bayanan asusun ajiyarka to shi ake kira da vishing.

Smishing wata dabarar kutse ce da ‘yan madatsa, waɗanda aka fi sani da hackers su ke amfani da ita wajen yaudarar mutane. Suna amfani da wannan dabarar ne wajen yaudarar mutane ta hanyar tura musu saƙonni ana tambayarsu game da waɗansu bayanansu na sirri.

Irin wannan kutsen yana daga cikin ire-iren kutsen Social Engineering da ya addabi mutane. Don haka mutane da dama suna yawan ƙorafe-ƙorafe a kan yadda ake musu kutse ta hanyar shiga asusansu ba tare da saninsu ba.
Sai dai duk da haka, abin da ba a sani ba shi ne, mutanen ne da kansu ke bayar da bayanansu da hannunsu.

Hanya mafi sauƙi da madatsan kan bi wajen rudar mutane ita ce tura musu saƙonni, musamman zuwa asusun saƙonninsu (inbod) na waya da ke nuna kamar saKon yana da inganci, misali; saƙo daga 500, ko 424 ko makamancin haka. Wato dai wani code, wanda ke nuna cewa ba daga lambar waya bane, don kar a gane su.

Irin waɗannan saƙonnin suna tunzura mutum ya bayar da bayanansa na sirri, musamman idan aka dubi lambobin da aka yi amfani da su wajen tura saKonnin. Ta wannan hanyar mutum zai yi tunanin daga wani kamfani ne ake neman bayanansa.

Masu kutse don satar bayanai a yanar gizo

Akwai wasu kalmomi da suke kamanceceniya da smishing, waɗanda duk suka kasance ire-iren dabarar kutse Social Engineering kamar haka:

1. Smishing: Tura saƙonni zuwa asusun saKonnin waya don rudar da mutane tura bayanansu na sirri zuwa ga madațsa.

2. Phishing: Tura wa mutane liƙau, manhajoji ko saƙonnin email don karbar wasu muhimman bayanansu na sirri.

3. Bishing: Kiran mutane a waya ta hanyar bi da lallami da kalaman yaudara don damfarar su, musamman don samu bayanan su na sirri.

Shi ya sa ake yawan jan hankalin mutane a su daina danna kowani irin link da suka gani matsawar ba daga amintaccen waje suka same shi ba. Don bin wannan ƙa’idar zai taimakawa sirrinka wajen tabbata a sirri, zai taimakawa dukiyarka wajen tabbata a takan ba tare da ka raba da kowa ba.Zai taimakawa mutuncinka wajen dawwama a yanar ba tare da ya tankwabe ba, ya ba ka damar watayawa a yanar gizo cikin aminci.

Sai dai kuma ba dukkannin masu kutse ba ne ɓata garin yanar gizo akwai waɗanda suke da lasisi su ake kira da ethical hackers ko a ce musu white hat hackers.

Su waɗanan rukunin suna yin kutse ne don su nemo wata gazawar na’ura su gyara ta tun kafin ɓata garin su kai nasu harin. Kutsen su don gyara suke yi ba domin ɓarna ba.

Hanyoyin kariya

1. Kada a danna liƙau ko shafin yanar gizon da ba a yarda da su ba.

2. Kada a mayar da martani ga saƙon imel ɗin da ba a yarda da shi kuma ba a san wanda ya turo shi ba.

3. Kada a kula da Kiraye-Kirayen wayoyin da ba a san su ba.

4. A dings kula da shafukan da ake ziyarta da tabbatar da sahihancinsu.

5. Kada a sanya manhajar da ba a tabbatar da sahihancinta cikin na’ura ba.

6. A kula da saƙonni a cikin waya kuma kada a mayar da martani gare su.

Tabbas ya zama wajibi a kula da waɗannan shawarwari don kada a yi nadama nan gaba, domin yanzu kutse ya zama ruwan dare a wannan zamanin.

Bugu da ƙari, a rinƙa kula da saƙonnin da ake samu daga banki haƙiƙa ba kowane saƙo ba ne daga asusun banki, sau tari ana iya amfani da wasu dabaru don kutse cikin na’urori don tura wa mutane saƙonnin bogi.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading