Gasar Arc. Ahmad Musa Dangiwa, wato Gasar Rubutattun Gajerun Labaran Hausa, gasa ce da Gidauniyar Adabi ta Arc. Ahmad Musa Ɗangiwa ke shiryawa domin bunƙasa adabin Hausa da baiwa marubuta damar bayyana matsalolin al’umma ta hanyar rubuce-rubucensu. Gasar na daga cikin matakan da ya ɗauka domin bunƙasa adabin Hausa da kuma ƙarfafa marubuta wajen amfani da basirarsu don magance matsalolin al’umma.
Yaushe ake yin gasar Ɗangiwa?
Gasa ce da ake gudanar da ita duk bayan shekaru biyu, tun daga kan shekara ta 2020 zuwa shekara ta 2024. An soma gudanar da wannan gasa ne a shakerar 2020. Wadda ta ƙunshi manufofi da dama.
Manufar gasar
Bunƙasa adabin Hausa
Gasar na ƙarfafa rubuce-rubucen Hausa da kuma haɓaka sha’awar karatu da rubutu a tsakanin marubuta.
Ƙarfafawa marubuta guiwa
Ta hanyar ba su damar nuna basirarsu da samun horo domin inganta rubuce-rubucensu.
Bayyana matsalolin al’umma
Ana amfani da labarai don tattauna matsaloli da damuwar al’umma, tare da samar da mafita.
Samar da ƙwararrun marubuta
Gasar na bai wa marubuta damar samun gogewa da ci gaba a sana’ar rubutu.
Haɓaka al’adun karatu
Ta hanyar samar da ƙayatattun labarai, ana ƙarfafa sha’awar karatu a tsakanin masu karantu a fanin adabin Hausa.
Su waye suke ɗaukar nauyin gasar?
Arc. Ahmad Musa Dangiwa, fitacen ɗan siyasa ne wanda aka haifa a ranar 10 ga Fabrairu, 1963, ƙwararren mai tsara birane ne kuma ɗan siyasa. Ya rike muƙamin Manajan Darakta na Bankin Lamuni na Gidaje na Najeriya daga 2015 zuwa 2022. Haka kuma tun daga watan Agusta na 2023, yake riƙe da muƙamin Ministan Gidaje da Cigaban Birane na Najeriya. Mutum ne mai tausayi da ƙoƙarin taimakawa na kasa da shi wanda dalilin haka ne ya samar da wata gasa ga marubuta.
Gidauniyar Arc. Ahmad Musa Dangiwa ce take ɗaukar nauyin gasar, tare da tallafawa marubutan da suka fi ƙwazo. Ta hanyar ba su kyaututtuka masu tsoka tare kuma da bayar da ɗan hasafin gyaran alƙalami ga wasu daga cikin marubutan da ba su samu damar kaiwa ƙololuwar mataki ba.
Waɗanda suke shiga gasar
Gasar Arc. Ahmad Musa Dangiwa tana buɗe wa duk wani marubuci ƙofar shiga gasar, musamman marubutan da ke da sha’awar rubutu da kuma iya rubutu da kyakkyawan salo a harshen Hausa.
- Masu sha’awar rubutu: Waɗanda ke son inganta fasahar rubutunsu na iya shiga gasar
- Marubutan Hausa: Sun haɗar da maza da mata, haka kuma matasa masu tasowa da waɗanda suka jima a duniyar rubutu
- Ɗalibai: Musamman waɗanda ke da sha’awa da ƙwarewa a fannin rubutu.
- Masu kishin Adabin Hausa: Ko da ba marubuta ba ne kai tsaye, amma suna da sha’awar rubuce-rubuce.
Yadda tsarin gasar yake
Ana buƙata marubuta su turo tsakuren labaransu, wasu lokutan ana buƙatar tsakuren kalmomi 500/1000/ 1500/2000 ya danganta da yadda tsarin shekarar ya kasance. Bayan tantancewa ana fitar da adadin marubutan da suka haye zagayen farko, daga nan sai ayi musu bisa mai zaman kanta. Inda ake gayyatar manazarta da malaman adabi su yi musu bita kan yadda ake son labaran su kasance zuwa mataki na gaba.
Daga nan za a buƙaci kowa ne marubuci da ya ciko ƙarashen kalmomin labarinsa, a wannan matakin ake cire na daya zuwa matakin na goma 15. Daga bisani akan ware lokacin karramasu tare da ba su kyaututtukan da aka alƙawarta.
Zaɓar jigo a gasar Ɗangiwa?
A gasar Ɗangiwa masu alhakin gasar su ne suke samar da jigo saɓanin sauran gassani irin su, Gasar Gusau, BBC Hikayata Hiafest da sauran su.
Da, ba sa ba da jigo, sai dai kuma ana iƙirarin akwai abin da suka fi buƙata duba da waɗanda suka kai matakan nasarorin da suka gabata.
Jigogin da gasar ta yi amfani da su
Gasar farko ta yi tsokaci je a kan matsalolin muhali, da kuma hanyoyin da za a bi domin magance su. Tare da aiyukan bankin lamunin bayar da gina gidaje na ƙasa, tare da fito da hanyoyin da ake bi a amfana.
Gasar ta biyu ta yi magana ne akan abin da ya shafi wayar da kan matasa a cikin al’umma. Gudunmuwarsu wurin ci gaban ƙasa. Fito da yadda barin su kara zube suna rayuwa zai iya haifar da matsala.
Gasar ta uku ta yi tsokaci ne akan abin da ya shafi buri, wadda abin da ɗan Adam yake da shi a kansa da kuma hanyoyin cika wannan buri tun daga kan matakin ƙuruciya. Ƙalubalan da ake fuskanta wurin cimma buri a rayuwa.
Sunayen litattafan da aka buga a dalilin gasar
- 2020 Muhali Sutura
- 2022 Ɗaukar Jinka
- 2024 Burina
Gwarazan da suka yi nasara tun fara gasar
Shekarar 2020
- Bishir Adamu daga jihar Katsina shi ne ya zo matakin na ɗaya. Da labarinsa mai suna,
- Bilkisu Muhd Garkuwa ita ce ta zo matakin na biyu da labarinta mai suna, Laifin Wa?
- Aliyu Rabi’u Aliyu daga jihar Katsina ne ya zo na uku. Da labarinsa mai suna,
Shekarar 2022
- Amrah Auwal Mashi daga jihar Katsina ita ce ta zo matakin ta ɗaya. Da labarinta mai suna, Tun Ran Gini.
- Rufaida Umar daga jihar Kano da labarinta mai suna, Son Zuciya ta zo ta biyu.
- Haka kuma Jibrin Adamu Rano daga jihar Kano shi ma ya zo matakin na uku da labarinsa mai suna, Kafi Ɗan Uwa.
Akwai Zahra Bala da labarinta shi ma ya zo na uku mai taken, Sara Suka. A shekarar mutum biyu ne suka yi kunnen doki a matakin na uku.
Shekarar 2024
- Abu Ubaida da Aisha Muhammad waɗanda suka kasance mata da miji daga jihar Gombe su ne suka karɓin kambun na ɗaya da labarinsu mai suna, Kabarin Burina.
- Fiddausi Muhammad Sodangi daga jihar Katsina ita ta lashe mataki na biyu da labarinta mai taken, Tarnaƙi.
- Sai Muhammad Lawan PRP da ya karɓi matakin na uku da labarinsa mai taken, Sauyin Tunani
Alfanun gasar
Gasar ta taimaka ta ɓangarori da dama, kamar haka:
Cicciɓa marubuta zuwa wasu matakai a duniyar rubutu.
Samar da litattafai a tsakanin makarantun sakandire da kuma jam’o’i.
Samar da abubuwan da za su kawo cigab ƙasa da kuma marubuta a faɗin duniya.
Samar da yawaitar faɗaɗa ilmi a fanin masu nazari da ma kansu malaman. Duba da yadda ake haɗa malamai lokaci zuwa lokaci domin yin bita.
Ƙarfafa zumunci tsakanin marubuta da manazarta.
Abubuwan da aka cim ma a dalilin gasar
Wayar da kan al’umma musamman na arewa akan aikin bayar da lamunin gina muhali.
Samar da litattafan karatu masu ƙunshe da labaran gasar domin haɓaka ci gaban adabi. Wanda sai da aka raba littafin gasar farko kusan kwafi 600 a makarantu.
Rangadi tsakanin wasu jahohin Najeriya domin tattaunawa da marubuta kan yadda gasar za ta kaya tare da kawo ci gaba mai amfani.
Bambamcin gasar Ɗangiwa da sauran gassani
Gasar tana da bambanci da sauran takwarorinta gassani ta fuskoki da dama.
Gasar Ɗangiwa su suke zaɓar jigo da kan su su sanya shi tsakanin marubuta daga bisani su ba su damar tattaunawa.
A gasar Ɗangiwa ana yi aa marubuta bitar yadda za a gina labaran zuwa matakin gaba saɓanin sauran gassani da idan ta kama an yi bitar ba a bayar da yadda ake buƙatar tsarin labaran su kasance.
Gasar Ɗangiwa ita ce gasa mafi ƙoƙololuwa dake karama gwaraza, akan gasar censorship ne kaɗai aka samu gasar da ta karama gwaraza sama da gasar ko kuma ace kwatankwacinta.
Akwai bambancin yadda ake rabon kuɗi ko kuma kyaututaka tsakanin gasar da sauran gassani, domin a gasar farko har da wayoyin hannu aka rabawa marubutan da sauran abubuwa masu armashi da ƙara karsashi.
Ko da ba su yi kafaɗa da kafaɗa da gasar BBC ba za a iya cewa sun yi kusan kunnen doki duba da yadda gasar take yin abin da BBC ma ba ta yi.
Manazarta
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.