Skip to content

Gatse

Gatse, na nufin fasahar sarrafa harshe mai cike tarin hikima wajen nuna gwanintar iya magana da zance. Fasahar magana ce wacce ke bayyana saɓanin abin da aka faɗa. Wato salon magana ne da take zuwa a matsayin a’antawa, wato hani ke nan ko kuma a’a, ko kuma umarnin yi. Gatse na nufin dukkan abin da aka faɗa ba shi ake nufi ba, saɓanin shi ake nufi.

Samuwar gatse

Ba a hakikance lokaci ko wuri ko wasu mutane da suka keɓanta da yin gatse. Amma an fi yin shi ko dai a lokacin da mutum yake fushi ko kuma yake kusa da yin fushin. Misali, idan aka ce da mutum ya aikata wani aiki mummuna, wanda shi kuma yana ganin kamar sa a ce ya aikata wannan aikin, ya wuce nan. To, idan aka ce wane kai ka aikata ka za? Sai shi kuma ya ce e, ni ɗin ne. A wannan gaɓar za a gane cewa gatse yake yi idan aka lura da yanayin fuskarsa da kuma sigar da ya faɗi maganar. Saboda duk lokacin da za a yi gatse, da wahala a ga fuskar mai yin gatsen ba a ɗaure ba. Sannan kuma sigar fitar maganar ita ma za a ga da alamar zafi a ciki.

Sannan kuma a wasu lokutan da yara kan tambayi izinin aikata wani aikin da bai kamata ba, akan yi musu gatse. To ko a nan ɗin ma jin haushin tambayar shi ke saka wa a yi gatsen. Misali, kamar a ce an kawo wani abin amfani a gida da ya kamata a ce kowa a gidan ya samu wani adadi, to wani daga cikin yara bayan ya ɗauki nasa sai kuma ya ce na ƙara wani? Sai a ce da shi I, ƙara mu gani.

Haka nan a wasu lokutan akan bibiyi gatse da ƙwafa, gyaɗa kai, cizon fatar baki, harara, da sauran su. Duk waɗannan idan suka biyo bayan magana suna tabbatar da cewa wannan magana gatse ce.

Bugu da ƙari, gatse yana iya zama wata hanyar isar da saƙo mai cike da gargaɗi ko hani a fakaice, kuma salon magana ne da ake yi a fakaice da wasu kalmomin da suka zamo kishiyoyin waɗanda ake son faɗa domin isar da wani sako ko binciko wani abu.

Misali, mutum ne ya je kasuwa zai sayi wani kaya, sai mai kaya ya zuba wa kayan kuɗi, to a nan mai saye zai iya gaya wa mai sayarwa baƙar magana a fakaice. Kamar a ce ya kamata a sayar da kayan naira dubu, sai shi mai kayan ya ce a’a sai dai a saya naira dubu uku, to a nan mai saye zai iya faɗa wa mai sayar da kayan baƙar mata ta cikin gatse ya ce, a’a, naira dubu goma zan saya.

Haka ma mutum zai yi tambaya wani ya faɗa masa amsa cikin gatse, irin maganar da ya san ba haka take ba.

Misali.

  • “Wannan ramin idan na shiga ba shi da zurfi?”
  • Kai tsaye za a ba shi amsa cikin gatse a ce,
  • “Guntu ne shiga.”
  • “Mama na tafi wurin bikin?”
  • Amsa:
  • “Tafi tun da kin isa da kanki.”
  • “Abincin nan duka nawa ne na cinye?”
  • Amsa:
  • “Cinye tun da kai kaɗai ne a cikin gidan.”
  • “Na zube miyar?”
  • Amsa:
  • “Har naman ka cinye.”
  • “Umma na yi wankan?”
  • Amsa:
  • “A’a ki yi zamanki cikin bayin har ruwan zafin ya huce.”

Ko kuma a yi tambayar wani abu fari sai a ce baƙi ne. Kenan dai gatse salon magana ne da yake faɗar akasin abin da aka faɗa. Idan mutum yana da hankali zai iya hankalta ya gano gatse ne aka yi masa don ya kiyaye yin abin da ake yi masa gatsen a kansa. Idan kuma bai da cikakkiyar Hausa zai iya yin abin sai daga baya ya fahimci ashe ba da gaske aka yi masa maganar ba.

Saboda gatse ga wawa ba ya wani tasiri illa ma ya tunzura shi yin abin da zai zo daga baya yana danasani. Mai fahimta kuma zai kiyaye saboda gudun ya rufta komar danasani wadda aka ce ƙeya ce tana zuwa daga baya.

Abin lura, wanda ya ga dogon rami ya yi tambayar babu zurfi ya shiga, kuma aka ba shi amsar guntu ne ya shiga. Idan wawa ne shiga zai yi sai dai wurin fita a yi tataɓurza.

Haka mai son tafiya wurin biki, Mamarta ta ce ta tafi tun da ta isa da kanta. Idan wawuya ce tafiya za ta yi sai idan ta dawo a yi wadda za a yi don za ta yi tsammanin umarni ne aka ba ta.

Mai tambayar abinci nasa ne aka ce ya cinye tun da shi kaɗai ne a gidan. Idan bai fahimci gatsen ba zai cinye abincin tas, saboda zai yi tunanin wataƙila babu kowa duka sun fita shi kaɗai ne a cikin gidan nasu. Ko kuma idan ya ga mutane a gidan ya yi tunanin ya aka yi aka ce ya cinye tun da shi kaɗai ne bayan kowa yana nan a cikin gidan ba su tafi ko’ina ba.

Mai zuba miya ma zai iya zube ta gabaɗaya har da naman duka ya cinye idan bai fahimci gatsen da aka yi masa ba cikin sauƙi.

Wadda za ta yi wanka ma za ta iya jira har ruwan ya huce tana cikin bayin cike da tunanin ai haka ake so ta yi idan ba ta fahimci salon maganar da aka yi amfani da ita wurin yi mata gatse don a hana ta yin jinkiri a bayin ba, saboda ta gama wankan da wuri tun kafin ruwan ya huce ta fito.

Abin lura

Gatse ba zai taɓa zama daidai da abin da ake tambaya ko maganar da ke buƙatar miƙaƙƙiyar amsa ba. Saboda zance zai yi gabas amsa mai ɗauke da salon gatse ta yi yamma. Amma ga mai hankali da fahimta zai iya gano abin da ake son nusar da shi domin kauce wa matsala ko kuma zama a kan daidai idan an yi mutum nuni a cikin gatse.

Manazarta

Aminiya. (2019, September 13). Yadda Hausawa ke sarrafa harshe. Aminya

Sarrafa Harshe. (n.d.). Sarrafa harshe

Hausa baƙar magana. (n.d.). Hausa baƙar magana Rumbun Ilimi

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×