Gizo-gizo ƙwari ne nau’in arachnids masu kafa takwas waɗanda ke rayuwa a kusan dukkanin sassan duniya in ban da Antarctica. Kawo shekarar 2022, akwai kusan nau’ikan gizo-gizo 50,000 da ke rayuwa a kusan kowane babban biome. Gizo-gizo suna da girma daban-daban, mafi ƙanƙantar gizo-gizo ɗan guntu ne mai girman da bai fi kai ba, akwai kuma manyan gizo-gizo waɗanda za su iya kaiwa tsayin ƙafa.
Sunan gizo-gizo a kimiyyance shi ne Araneae, kuma su ne ƙwarin arthropods masu shakar iska da ke da ƙafafu takwas, da harshen da suke fitar da sauran sassan jiki. Wannan nau’i na arachnids yana ɗaya daga cikin mafi bambance-bambance a tsakanin dukkanin halittu kuma suna iya samuwa a kowace nahiya ban da Antarctica. Kawo yanzu, an ƙiyasta nau’ikan gizo-gizo har guda 50,356 kuma an rarraba su zuwa rukuni 132, kodayake akwai muhawara tsakanin masana kimiyya game da yadda ya kamata a rarraba su, tare da rabe-rabe sama da 20 daban-daban.
Gizo-gizo mafi girma a duniya shi ne wanda akewa huntsman spider. An gano wannan gizo-gizo ne a wannan ƙarni da muke ciki, a cikin wani kogo a cikin ƙasar Laos. Babban sanannen gizo-gizo mafi daɗewa a duniya ya rayu yana da shekaru 43. Ya kasance gizo-gizo mai tsaron kofa a Ostiraliya kuma bai mutu ba saboda tsufa, a maimakon haka, wani babban gizo-gizon ne ya kashe shi wanda ya sanya ƙwai a cikin gizo-gizon.
Fiye da nau’ikan nau’ikan 300 ne suka sanya kafafunsu na gaba a saman kawunansu don yin kama da tururuwa. Wannan hali yana taimaka musu su guje wa harin tururuwa.
Siffar gizo-gizo da halayensa
Tsarin jikin gizo-gizo ya bambanta da sauran halittun arthropods ta yadda sassan jikinsu na yau da kullum ke haɗuwa zuwa sassa biyu, kai da gangar jiki, wanda aka haɗa ta hanyar siririn bututu. Cikin kowane gizo-gizo ya ƙunshi zuciya da bangarorin numfashi. Dukkan gizo-gizo suna da ƙafafu takwas. Da yawa daga cikinsu suna da wasu irin haƙora waɗanda suke iya fitar da wani abu guba ko dafi.
Gizo-gizo suna da gabobin da ɗauke wani ruwa nau’in siliki da ake kira a kan ƙafafunsu na gaba ko ƙarƙashin ciki. Wasu gizo-gizo suna da wadannan gaɓoɓi da ake kira spinnerets guda shida, ko guda biyu, ko guda huɗu, ko kuma guda takwas waɗanda suke yin tafiya da su tare ko daban-daban kamar yadda suke so. Ƙafafun bayansu ba kawai zaren siliki ɗaya suke saki ba, suna da rikitarwa kuma suna ɗauke da ɓangaren takaita fitar silikin da yawa waɗanda kowannensu ke sakin zaren siliki mai kyau. Haka nan gizo-gizo na iya samar da nau’ikan siliki daban-daban.
Gizo-gizo suna amfani da siliki don yin abubuwa daban-daban, kamar gina gidajensu zamansu, saka gidajen yanar gizo don kama abinci, yin wuraren saka kwai, canja wurin maniyyi, kama ƙwari, ƙirƙirar saƙa don kare kansu daga mafarauta da dai sauransu.
Gizo-gizo sun bambanta da ƙwari saboda ba su da antenna. Yawancin gizo-gizo suna da tsarin jiki mai tushe daya a tsakiya, wato dukkanin jijiyoyin jikinsu suna haɗuwa tare a cikin ɓangaren kai. Bugu da ƙari, gizo-gizo ba sa amfani da tsokoki don tsawaita gaɓoɓinsu.
Tsarin halitta da asalin wanzuwar gizo-gizo
Waɗannan ƙwari dai wataƙila sun samo asali ne kusan shekaru miliyan 400 da suka wuce. Mai yiwuwa nau’in gizo-gizo na farko sun fito ne daga tsatson arachnids waɗanda kwanan nan suka bar muhallansu na ruwa. Kasusuwan burbushin gizo-gizo na farko sun kasance na nau’in Mesothelae, waɗanda ke da ƙafafun da aka sanya a tsakiyar cikinsu maimakon a karshen, kamar gizo-gizo na wannan zamani. Ana tsammanin su ne mafarauta a ƙasa, suna zaune a wuraren gansakuka. Mai yiyuwa ne waɗannan gizo-gizo sun yi amfani da siliki don kariya ga ƙwayayensu.
Kamar yadda tsirrai da kwari suke girma tare da sauyawa, haka gizo-gizo ke amfani da siliki wajen sauyawa da kuma girma. Gizo-gizo masu ƙafafu a jikin cikinsu (wato Opisthothelae) sun bayyana sama da shekaru miliyan 250 da suka wuce, wanda hakan ya ƙarfafa samar da ƙarin hadaddun sakar yanar gizo don kama abinci a ƙasa da kuma bishiyoyi. A lokacin Jurassic, gizo-gizo masu saƙa sun haɓaka yanar gizo don kama nau’ikan ƙwari masu tashi.
Rubuce-rubucen tarihin gizo-gizo ba su da yawa sosai. Duk da haka, burbushin launukan gizo-gizo, waɗanda cikakkun gizo-gizo ne da ke maƙale a cikin rassan bishiya, sun nuna cewa yawan gizo-gizo kamar na wannan zamani ya wanzu shekaru miliyan 30 da suka wuce. Bugu da ƙari, ɓangarorin gizo-gizo sun rayu a Gabashin Asiya tun daga ƙarshen lokacin Palaeozoic har zuwa yanzu. Suna zaune a cikin kogo.
Muhallin da gizo-gizo ke zama
Akwai wuraren zama iri-iri inda ake samun gizo-gizo. Yawancin nau’in gizo-gizo sun fi son zama a sarari, inda suke saka yanar gizo ko farautar abinci a ƙasa ko tsakanin ciyayi. Mazaunan waje gama gari sun haɗa da dazuzzuka, filaye, lambuna, da yankin hamada.
Haka kuma gizo-gizo na iya zama a cikin gidaje, musamman a wurare irin su ginshiƙai da ɗakuna masu duhu da mutane ba sa yawan kai komo. Bugu da ƙari, yawancin nau’in gizo-gizo suna yin gidajensu kusa da maɓuɓɓugar ruwa kamar tafkuna da koguna don samun sauƙin hanyoyin abinci kamar ƙwari da ke taruwa a kusa da ruwa.
Wasu nau’in gizo-gizo na ruwa suna zaune a cikin koguna da tafkuna, inda suke rataye a ƙarƙashin ruwa ta hanyar saƙa kumfa ta iska zuwa cikin gidajen sakar siliki wanda daga ciki suke shakar iskar oxygen yayin da suke nutsewa a ƙarƙashin ƙasa.
Baƙaken gizo-gizo ba sa rayuwa mai tsawo. Maza yawanci suna mutuwa a cikin watanni, yayin da mata masu sa’a ne kawai ke kaiwa ga cikar shekaru uku. Duk da ƙanƙantarsa, baƙin gizo-gizo yana da dafin da kan iya haifar da mutuwa. Cizonsa yana fitar da wani dafi wanda zai iya haifar da matsanancin zafi, taurin tsoka, amai, da zufa sosai.
Abincin gizo-gizo
Gizo-gizon da ke cikin lambu ba su da ƙarfin gani ta hanyar amfani da idanunsu, don haka dole ne su dogara da wasu gaɓoɓin don farautar abinci. Idan za su kama abinci, suna jira ne a kusa da gefan yanarsu ko a cikin ko a bayanta.
Gizo-gizo dabbobi ne masu cin nama kuma suna cin ƙwari, yawanci su ne abincinsu. Dangane da nau’ikansu, suna iya cinye wasu gizo-gizon, ƙananan dabbobi masu shayarwa, da dabbobi masu rarrafe. Duk da haka, manyan hanyoyin abinci su ne ƙwari masu tashi ko rarrafe kamar kiyashi da tururuwa. Wasu nau’in gizo-gizon ma sukan cin ‘ya’yan kwaɗi ko kifi idan sun ci karo da su.
Nau’in abinci ga wani nau’in gizo-gizo na musamman ya dogara da girmansa; manyan gizo-gizo suna da ƙarin hanyoyin abinci idan ana batun abubuwan da suke iya kamawa fiye da waɗanda ƙanana suke samu. Wasu nau’ikan gizo-gizo suna rayuwa ta hanyar cin matattun dabbobin daji maimakon ƙwari. Baya ga irin waɗannan halaye na cin abinci, wasu gizo-gizo na amfani da dafinsu wajen sauƙaƙa narkar da abin farautar da suka kama kafin su cinye gabaɗaya.
Maharan gizo-gizo
Tsuntsaye, tururuwa, da ƙadangaru duk maharan gizo-gizo ne, suna kalaci da gizo-gizo. Dukkan dabbobin da suke cin ƙananan ƙwari za su ci gizo-gizo. Dabbobi kamar kwaɗi, tsuntsaye, da kadangaru su ne manyan mafarautan gizo-gizo.
A wani tsibirin, masu bincike sun gwada yawan gizo-gizo tare da kadangaru, sannan kuma suka gwada ba tare ƙadangaru ba. Sun gano cewa bayan kwanaki huɗu ba tare da kadangaru ba, kashi 65% na gizo-gizo sun ci gaba da rayuwa. A yayin da aka kawo kadangaru wajen, kashi 40% na gizo-gizo ne kawai suka rage a ƙarshen binciken. Wannan shi ke nuna cewa ƙadangaru na iya rage yawan gizo-gizo cikin sauri.
Sauran dabbobin da suke cin gizo-gizo su ne kifi, macizai, tururuwa, manyan gizo-gizo, kunamu, jemagu, da ƙananan dabbobi masu shayarwa kamar shrew. Yana da kyau a san cewa duk da gizo-gizo na cikin abincin macizai, akwai wasu nau’in gizo-gizo da ke cin maciji.
Tsarin haihuwa da rayuwar gizo-gizo
Gizo-gizo suna haifuwa ta hanyoyi daban-daban, dangane da nau’ikansu. Yawancin gizo-gizo suna yin ƙwai su ajiye su a cikin gidaje na musamman ko waɗanda ke a makale a gidan yanar gizonsu ko kuma mace ta ɗauke su har sai sun ƙyanƙyashe. Macen gizo-gizo kuma na iya samar da matasan gizo-gizo masu rai ba tare da saduwa ba, wannan hanya ta fi shahara a wasu nau’ikan fiye da sauran.
Da zarar ƙwayayen sun ƙyanƙyashe, jariran gizo-gizo kan bayyana kuma su bi matakai da yawa na girma kafin su zama manya. A lokacin waɗannan matakan girma, suna zubar da saɓar fata su sau da yawa yayin da suke girma da kuma yin ƙarfi. Bayan sun girma, yawancin gizo-gizo za su rayu ne kawai na shekara ɗaya ko biyu kafin su mutu a dabi’a saboda tsufa ko harin wasu dabbobi.
Haɗarin da gizo-gizo ke fuskanta
Akwai barazana iri-iri da suka kai ga halaka nau’ikan gizo-gizo har guda 27. Waɗannan sun haɗa da asarar wurin zama ko rarrabuwa saboda yawaitar ɗan adam, ssuyin yanayi da gurɓatacewarsa, da cututtuka. Asara ko lalacewar wuraren zama na iya haifar da raguwar yawan gizo-gizo yayin da suke gwagwarmayar rayuwa a cikin sabon yanayi. Magungunan kashe ƙwari da ake amfani da su a kayan amfanin gona na iya zama mai guba ga gizo-gizo, suna rage yawansu har ma suna haifar da bacewa a wasu lokuta.
Misalai biyu na nau’in gizo-gizo da ke cikin haɗari su ne (Phidippus regius) da (Neoscona crucifera). Na farko ya fito ne daga Arewacin Amurka kuma yana fuskantar barazanar lalacewa ko sauya yanayin muhallinta saboda ci gaban birane. Na biyun kuma ana samun shi da farko a kudu maso gabashin Amurka kuma yana fuskantar irin wannan barazana daga sauye-sauyen amfani da kasa da mutane ke yi, kamar sare itatuwa don kiwo da kuma bazuwar birane.
Manazarta
PestWorld. (2024, November 18). Spiders 101. PestWorld
Raid®. (n.d.). Types of spiders: 40,000 species . . . and counting – Raid®.
Resorts. (n.d.). Spiders Facts and Information | United Parks & Resorts.