Haraji wani nau’i ne na karɓar kuɗi na wajibi wanda wata hukuma ke tsarawa da karɓa a hannun ɗaiɗaikun al’umma ko masana’antu ko kamfanoni, don aikin da suke yi ko wata sana’a da suke aiwatarwa. An ƙirƙiri haraji ne don tallafa wa gwamnati ta fuskoki daban-daban. Haraji na iya zama kai tsaye ko kuma na kaikaice. Ana iya biyan haraji ta fuskoki da dama walau ta hanyar amfani da kuɗi ko kuma yin wani aiki ko bayar da wasu abubuwan, kamar amfanin gona da makamantansu. Wasu ƙasashen suna da kyakkyawan tsarin haraji wanda ke taimaka musu ta fuskoki da dama ciki har da bunƙasar tattalin arziki da ci gaba, yayin da wasu kuma ba su da kyakkyawan tsari, wanda hakan kan haifar da koma baya da taɓarɓarewar tattalin arziki.
Amfanin haraji ga gwamnati da al’umma
Masana tattalin arzikin sun ce zai yi wuya a iya rarrabe amfanin haraji ga mutane da kuma gwamnati saboda kamar gwamnatin ita ce mutane. Ga wasu muhimman alfanun haraji kamar haka:
Samar da abubuwan more rayuwa
Ana karɓar haraji ne domin ba wa gwamnati damar gudanar da ayyukan more rayuwa ga al’ummarta kamar samar da makarantu da asibitoci da ruwan sha da wutar lantarki da tituna da tallafin da gwamnati ke bayarwa lokacin da aka shiga cikin wasu matsaloli.
Taƙaita amfani da abubuwa masu cutarwa
Baya ga samar da abubuwan more rayuwa da cigaban ƙasa, haraji yana da amfani saboda yana rage amfani da abubuwa masu cutarwa, misali kamfanonin giya da taba a Najeriya, waɗanda suke biyan haraji mai nauyi wanda ya kai kusan kashi 20 cikin ɗari na kayan da suke samarwa, saɓanin kashi bakwai da rabi na sauran kayan masarufi. An yi hakan ne domin rage yawan shan barasa da kuma taba sigari a ƙasa. Idan aka sa wa kaya haraji suka yi tsada sosai, lalle mutane za su kaurace wa ta’ammali da su.
Inganta muhalli
Ana amfani da haraji wajen gyara muhalli, duk inda masana’antu suke suna taimaka wa wajen lalacewar muhalli, misali gurɓata ruwan sha da iska da sauransu. Idan ana ɗora haraji mai nauyi kan irin waɗannan dagwalon da masana’antu ke zubarwa, su masana’antun suna ƙoƙarin rage abin da suke zubarwa na dagwalon wanda wannan yana taimakawa ƙwarai da gaske.
Taƙaita amfani da kayan ƙasashen waje
Haraji yana rage shigo da kaya daga ƙasashen waje domin bunƙasa kamfanonin cikin gida. Misali, kayan da gwamnati ba ta so a shigo da su waɗanda take ganin za a iya samar da su a cikin gida sai ta ɗora musu haraji mai tsaurin gaske, waɗanda idan an kawo su cikin gida ba za su sayu ba sai dai na cikin gidan.
Haɓaka tattalin arziki
Ana amfani da haraji wajen bunƙasa tattalin arziki, lokacin da hauhawar farashi ta yi yawa cikin ƙasa mafi yawa abin da yake faruwa kuɗi ne suke yawa a hannun jama’a, sai gwamnati ta ɗora haraji a kan mutane ta rage yawan kuɗin da suke hannun mutane, ta yadda mutane ba za su iya sayan abubuwan da suke so ba, wannan zai rage yawan buƙatar abubuwa a kasuwa. Idan kuwa aka samu raguwar buƙatar abubuwan da mutane suke so a kasuwa hakan yana sa farashi ya sauka.
Samar da ayyuka
Karɓar haraji na taimakawa wajen samar da ayyukan yi, idan gwamnati ta rage yawan haraji a kan mutane domin su samu kuɗaɗe da yawa a hannunsu da za su kashe a kasuwanni, idan sun kashe kuɗi da yawa a kasuwanni, masana’antu za su samu damar yin kayayyaki da yawa saboda akwai ciniki a kasuwa. Wannan zai taimaka su ɗebi ma’aikata da yawa.
Daidaito tsakanin ‘yan kasa
Ana kuma amfani da haraji wajen daidaita tsakanin ‘yan ƙasa ta fuskar tattalin arziki saboda masu wadata sun fi biyan haraji mai yawa yayin da talakawa suke biyan haraji ɗan kaɗan ko ma ba sa biya.
Matsalolin ƙin biyan haraji
Shiga wahala
Babbar matsalar rashin biyan haraji ita ce gwamnati za ta koma dogaro ne da kuɗaɗen da take samu daga wasu hanyoyi wanda ba za su wadatar ba, misali sayar da mai da sauran ma’adanai. Idan farashin ma’adanan ko man ya faɗi a kasuwar duniya, ƙasa tana shiga wani hali saboda mutane ba sa biyan harajin da ya kamata. Kowa a ƙasar sai ya shiga wahala, tsadar rayuwa da talauci da rashin aikin yi.
Karɓo bashi daga waje
Haka nan dole a samu yawan basussukan da gwamnati take ciyowa domin ta samu ta yi ayyukan da suka zama wajibi ko kuma take son yin su. Idan har gwamnati tana samun isassun kuɗaɗen haraji, wataƙila da ba sai ta riƙa karɓo bashi ba.
Kyawawan siffofin haraji mai tsari
Akwai siffofi da ƙa’idoji da ingantaccen haraji ya kamata ya siffantu da su, suna da matuƙar mahimmanci a cikin kowane tsarin haraji a dukkan matakan karɓar haraji. Waɗannan siffofi sun haɗa da:
1. Mai sauƙi, tabbatacce kuma bayyananne
Tsarin haraji mai kyau dole ne ya zama mai sauƙi kuma mai sauƙin fahimta ga al’umma, ya kasance daidai da dokokinsa da kuma hanyar gudanar shi. Kuma ya zama mai ɗorewa, ya zama an fahimce ta kowace fuska.
2. Sassauci
Haraji ya kamata ya zama da sassauci ba da tsauri ba, kuma ya kasance mai canjawa. Har ila yau, tsarin gudanar da harajin da kuma adadin kuɗaɗen da za a karɓa ba za su zama masu wahalar sauyawa ba ko kuma wasu matsaloli masu yawa. Tsarin haraji mai kyau tilas ya kasance mai ƙunshe da tanade-tanaden sauye-sauyen da za su dace da yanayi.
3. Tsaka-tsaki
Adadin kuɗaɗen harajin da za a biya ya kamata su kasance cikin rahusa domin samun amincewar masu biya. Wato kuɗin harajin su kasance a sauƙaƙe babu tsawwalawa. Wannan yana da mahimmanci saboda lokacin da kuɗi suka yi yawa masu biyan haraji za su nuna gazawa ko yin bore.
4. Ingancin gudanarwa
Kuɗin da ake kashewa a hanyar gudanar da tsarin haraji dole ne su zama daidai misali idan aka kwatanta da kuɗaɗen shigar da aka tattara. Manufar haraji ta ƙasa wato (The National Tax Policy) ta ba da damar yin cikakken bincike a kan adadin kuɗin da ya kamata a tsayar ko a ayyana a matsayin haraji da kuma fa’idojinsa kafin a sanya kowane irin haraji a Najeriya.
5. Gaskiya da riƙon-amana
Tabbatar da gaskiya da rikon amana su ne tushen alamar kowane kyakkyawan tsarin haraji. Wajibi ne a yi amfani da kuɗaɗen haraji yadda ya kamata ta hanyar lura da dalilan da aka suka sa aka sanya harajin. Jami’an gwamnati ya kamata su kasance masu gaskiya da rikon-amana kuma kada su yi almubazzaranci da kuɗaɗen haraji.
6. Daidaito da adalci
Ingantaccen tsarin haraji ya kamata ya kasance cikin adalci da kuma kulawa da duk masu biyan haraji daidai da daidai, ba tare da nuna bambanci ko sanayya ba. Bai kamata tsarin haraji ya yi watsi da batun adalci ga masu biya ba. Hukumomin haraji da masu biya kowa adalci yake nema, dukkansu kowa na bukatar daidaito, wannan siffa ce ta kowane kyakkyawan tsarin haraji. Daidaito a nan yana nufin a lura da yanayin da mutane suke ciki, wato waɗanda suke cikin yanayin wadata za a kwatanta yanayin harajinsu da wadatarsu. Haka nan mutanen da ba sa cikin wadata ba ya halatta a sanya su mataki bai-ɗaya.
7. Ingantaccen tattalin arziki
Ba a tsammanin tsarin harajin Najeriya zai kasance cike da cikas ba ta fuskar bunƙasar tattalin arziki a kowane lokaci, duba da arzikin ƙasar. Tsarin harajin ya kamata ya kasance bisa manufar tabbatar da cewa yawan harajin ba zai hana masu biya samun damar tanadi da zuba jari ba. Wato ko yaya, mai biyan haraji zai iya yin tanadi kuma zai yi harkokin kasuwancinsa.
Harajin VAT da yadda ake raba shi
Value Added Tax (VAT), wannan ba wani nau’in harajin kai tsaye ne da ake ƙagawa a kayayyaki da ayyuka. Haraji ne kusan kowa yake biya, da zarar mutane sayi kayayyakin masarufi ko wasu ayyuka, to mai sayarwar yana sayarwa ne haɗe da cajin harajin da aka yi wa kayayyakin ko ayyukan tun daga tushe.
Wannan haraji na VAT yana taimakawa da akalla kashi 16% na abin da ƙasa ke samu wanda hukumar FIRS ke tattarawa tana sakawa a asusun gwamnatin tarayya watau. Ana lura ƙwazon da jihohi da kananan hukumomi suka yi wajen tara kuɗaɗen harajin da kuma yawan abin da suka samar. Hukumar FIRS tana fitar da kashi 4% na abin da aka samu daga VAT sannan sauran abin da ya rage ana rarraba shi ga matakai uku na gwamnati kamar haka:
- Gwamnatin tarayya na samun kashi 15%
- Jihohi gabaɗaya suna samun kashi 35% su raba a tsakaninsu
- Kananan hukumomi su kuwa kashi 50% suke karɓa.
Hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya
Harajin ɗaiɗaikun mutane (Individuals Income Tax)
Wannan harajin ya kasance mafi girma a a dukkan hanyoyin samun kudaden shiga na tarayya tun shekarar 1944, kuma a cikin shekarar 2022, ya ƙunshi kashi 54 na jimullar kuɗaɗen shiga da kashi 10.5 na GDP a cikin 2022. Wannan kudaden haraji a cikin 2022 su ne mafi yawan da aka taba samu.
Harajin kamfani (Corporate Income Tax)
Harajin da kamfanoni ke biya ya samar da kashi 9 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na gwamnatin tarayya a shekarar 2022. Harajin da ake samu ya ragu sosai daga matsakaicin kashi 3.7 na GDP a karshen shekarun 1960 zuwa matsakaicin kashi 1.5 bisa dari na GDP a cikin shekaru goma da suka gabata, tare da yin ƙasa da kashi 1.5 na GDP a cikin shekaru goma da suka gabata.
Harajin inshora (Social Security (Payroll Tax))
Harajin a kan albashi da harajin da ke samar da kuɗaɗen ‘Social Security’ da ɓangaren inshorar lafiya shi ne babban kaso na wannan haraji na ‘Social Security’. Sauran hanyoyin sun haɗa da harajin layin dogo da shirin inshorar rashin aikin yi, da kuma gudunmawar fansho na ma’aikatan tarayya. Jimullar harajin social security shi ne kashi 30 na kuɗaɗen shiga na tarayya a cikin 2022.
Federal Execise Tax
Shi ne haraji kayayyaki da ayyuka, galibi daga man fetur, sigari, barasa, da tafiye-tafiyen jiragen sama, wannan ya samar da kashi 1.8 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na tarayya a shekarar 2022. Wannan kuɗaɗen harajin sun ragu daga matsakaicin matsakaicin kashi na 1.7 na GDP a ƙarshen shekarun 1960 zuwa matsakaicin kashi 0.5 cikin ɗari a cikin shekaru goma da suka wuce, kwanan nan kashi 0.4 bisa dari ne na GDP a cikin 2022.
Sauran hanyoyi (Other revenues)
Har ila yau gwamnatin tarayya na karbar kuɗaɗen shiga daga harajin gidaje da na kyautuka da harajin kwastam da kudaden da ake samu daga rarar asusun tarayya, da kuma kuɗaɗen caje-caje daban-daban. Jimullar waɗannan hanyoyin sun samar da kashi 5.0 na kuɗaɗen shiga na tarayya a cikin 2022.
Jimullar harajin da gwamnatin tarayya ta samu
Gwamnatin tarayya ta tara kuɗaɗen shiga da suka kai dalar Amurka tiriliyan 4.9 a shekarar 2022, daidai da kashi 19.6 na (GDP). A cikin shekaru 50 da suka gabata, kuɗaɗen shiga na tarayya sun kai kashi 17.4 bisa dari na GDP, daga kashi 20.0 a cikin shekarar 2000 zuwa kashi 14.5 a cikin shekarar 2009 da 2010.
Rabon harijin a takaice
Harajin samun kudin shiga na Individuals Tax (harajin ɗaiɗaikun mutane) ya samar da kusan ninkin jimlar kuɗaɗen shiga na tarayya tun daga 1950, yayin da sauran hanyoyin samun kuɗaɗen shiga suka ragu. Harajin ya kawo kashi 19 cikin 100 na jimlar kuɗaɗen shiga a shekarar 1950, amma kusan kashi 2 cikin 100 ne kawai a shekarun baya-bayan nan.
Rabon kuɗaɗen shiga da ke fitowa daga harajin kamfanoni ya ragu daga kusan kashi ɗaya bisa uku na jimullar su a farkon shekarun 1950 zuwa ƙasa da kashi 10 cikin ɗari a mafi yawan shekaru tun farkon shekarun 1980. Saɓanin haka, harajin albashi ya ba da kusan kashi ɗaya bisa uku na kuɗaɗen shiga tun farkon shekarun 1990, idan aka kwatanta da ƙasa da kashi 15 cikin ɗari a cikin shekarun 1950.
Haraji wasu caje-caje ne da gwamnati kan ɗora a kan ayyuka da kayayyakin sayarwa, ga ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni. Akwai tsare-tsare masu kyau da haraji ke siffanta da su, haka nan akwai ƙalubale da tsarin haraji ke fuskanta. Najeriya da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da dama, ciki har da harajin VAT da yadda ake raba shi ga matakai uku na gwamnati a Najeriya.
Manazarta
GeeksforGeeks. (2023, July 28). Characteristics of a good tax system. GeeksforGeeks.
Haruna, D. (2024, May 20). Harajin VAT Bakandamiya.
Team, T. (2024, December 20). Sabon tsarin karba da rabon harajin VAT a Nigeria. Tambayoyi.
Tax Policy Center (n.d.): What are the sources of revenue for the federal government? Tax Policy Center.