A ranar 9 ga watan Agusta na 2021 ne wata babbar kotun tarayya da ke birnin Fatakwal ta zartar da hukuncin cewar kuɗin harajin VAT na kayayyaki ba hurumin gwamnatin tarayya ba ne. Dalilin da ta dogara da shi kuwa shi ne, babu wata ayar doka da aka ambaci wannan haraji a ƙarƙashin kundin tsarin mulki. Don haka kowacce jiha na da hurumin samar da dokokin da za ta bi wajen karbar harajin na VAT.
Shi dai VAT haraji ne da ake ƙarawa kayayyakin masarufi wanda jidalin yake ƙarewa akan masu amfani na ƙarshe watau ‘final consumer’. Harajin VAT iri biyu ne, na farko shi ne wanda ake kira ‘Input’ watau idan ɗan kasuwa ya je ya sayo kayayyaki daga kamfani ko ya shigo da su daga ƙasashen waje, za a yi masa lissafi har da harajin VAT. Wannan shi ne ‘input VAT’. A yayin da ɗan kasuwar ya sayar da kayayyakin, zai ƙara kuɗin harajin VAT akai gwargwadon farashin da ya saka. Wannan shi ake kira ‘output VAT’. Wajibi ne ɗan kasuwa ya biya kuɗin da ya caja na VAT ga hukumar FIRS bayan ya lissafa abin da tattarawa gwamnati. Ana ɗebe output daga input (output minus input).
Samuwar harajin VAT a Nijeriya
Asalin VAT a Nijeriya ya samu ne daga dokar soja mai lamba 102 ta shekarar 1993. Ita wannan dokar ta shafe dokar soja ta 1986 mai lamba 7. An yi wa dokar kwaskwarima a shekarun 1996 da 1998 da 2007 da kuma 2019. Duka gyararrakin sun yi duba ne daga kayayyaki da hurumi da kuma lokacin da ya dace a karɓa da tattara harajin na VAT. Sai a 2019 ne shugaba Muhammadu Buhari ya ƙara adadin harajin da kimanin kashi 50%, alhali a baya gwamnatin Obasanjo da ta Jonathan sun yi yunƙurin ƙarin kashi 100% da kuma 40% amma da ‘yan ƙasa suka yi ƙorafi sai suka janye aniyarsu.
Kafin dokar harajin VAT, kowacce jiha na iya tsara yadda za ta caji harajin ciniki ne yadda duk abin da aka sayar a faɗin jihar za a miƙa mata wani abu da suna ‘Sales Tax’. Wannan ya jawo ruɗani da rashin sanin takamaiman wuri da lokacin da ya dace a biya harajin.
Gudumawar harajin VAT a asusun gwamnatin tarayya
A halin yanzu harajin VAT na ba da gundumawar akalla kaso 16% na abin da ƙasa ke samu wanda hukumar FIRS ke tattarawa tana miƙawa a asusun gwamnatin tarayya watau ‘Federation Account’. Hukumar FIRS na cire 4% na abin da ta tara na VAT sannan sauran abin da ya rage ana rarrabawa kamar haka:
- Gwamnatin tarayya ta ɗau 15%
- Ƙananan hukumomi a ba su 50%
- Jihohin Nijeriya a rarraba musu 35%
A cikin kason jihohi da ƙananan hukumomi ana la’akari da hoɓɓasar da jiha ta yi wajen tara harajin da kuma abin da ya fito daga cikinta.
Taƙaddama tsakanin jihohi game da harajin VAT
Kasancewar wasu jihohin na yi wa wasu jihohin kallon hadarin kaji da ganin cewar da dama ba sa taɓuka komai, tun da jimawa jihar Legas ke ganin ta zama rumfa sha shirgi, shi ya sa suka jima suna ƙorafi tare da neman yadda za su yi awon gaba na ƙarawa kansu haraji. Don haka a suka samar da doka ta ƙashin kansu a shekarar 2002 domin tattara kuɗin haraji na Sales Tax a otal da sauran wuraren sayar da abinci. Masana sun yi ta kai kawo tsakanin kotuna, an yi musayar yawu da gwama numfashi har sai da aka dangana da kotun ƙoli (Daga ke sai Allah ya isa), wadda a shekarar 2018 ta sa ƙafa ta hamɓare wannan doka ta jihar Legas.
Haka nan jihar Kano a 2017 ta yi yunƙurin gabatar da wata doka akan kayayyakin masarufi wadda suka kira da ‘Consumption Tax.’ Ita ma a shekarar 2018 wata babbar kotu ta hana aiwatar da ita bisa hujjar cewar dokar VAT ra riga ta samu albakacin majalisar dokoki ta ƙasa.
Dokar haraji na cike da sarƙaƙiyar lissafi da murɗaɗɗun dokoki. Don haka ake ta faɗi tashi tsakanin masana haraji da masana doka wajen ƙididdige abubuwan hurumi da adadi watau ‘jurisdiction and residency’. Wannan ta da jijiyar wuya dai shi ya jawo jihar Ribas ta samu nasara a karon farko bisa hujjojin da ta gabatar gaban kotu. Kodayake wata kotun kuma, ta yi umarnin a dakatar da aiwatar da dokar VAT da gwamnatin jihar ta Ribas ta rattabawa hannu.
Wasu za su yi mamakin cewar wannan taƙaddama tsakanin mawadatan jihohi ne da sauran ‘yan Rabbana ka wadata mu ne. Domin kuwa, an yi ƙididdigar cewar jihohi huɗu zuwa biyar ne ke samar da VAT na kimanin 87%. Wannan ta sa ake ta faɗi tashi tsakanin masu bayarwar da masu karɓa.
Bisa nazari, akwai wasu dalilai da suka jawo ƙara haɓakar wannan kallon hadarin kaji.
Abu na farko shi ne yadda ƙwararru da masana lugogin haraji ke ta hanƙoro ganin sun samu tagomashi a wajen gwamnoni. Su ƙwararrun nan ta fuskar doka da lissafin haraji, yawanci sukan yi lissafi irin na dokin rano, su nuna muhimmancin abu idan an aiwatar da shi da irin romon da za a samu. Wannan ke sa wa hukumomi ke ta ɓullo da shirye-shirye. Walau shirin ya yi nasara ko bai yi ba, su dai ƙwararrun nan ruwa ta sha. Domin kuwa sun fisgi rabonsu da sunan bincike da ƙididdiga (Research, Analysis and Forecast).
Misali, daga lokacin da jihar Ribas ta shelanta soma karɓar harajin VAT zuwa aljihunta, an samu tawagar ƙwararru sama da hamsin da suka nuna buƙatar aiki da gwamnatin domin samun dacewa. Haka nan, kowacce jiha ƙwararru na ta bibiyar gwamnatoci domin su tsara musu hanyoyin da za su ƙara haɓaka kuɗin shigar su.
Abu na biyu kuma, FIRS na son wuce makaɗi da rawa wajen tattara haraji. Shugaban hukumar na yanzu, Muhammad Mamman Nami, ƙwararre ne akan harkar haraji. Ya san lungu da saƙo na hanyoyin samun kuɗin shiga. Don haka yake ta ƙoƙarin ɓullo da wasu hanyoyin tara kuɗaɗe ciki kuwa har da shiga muhallin wasu jihohi tare da ɓullo da wasu harajin da babu su. Wannan ta sa hukumar tasa ke ta haƙilon ganin an shigar da wasu harajojin kamar harajin hanya (Road Tax) da kuma ɓullo da sabuwar hanyar karɓar haraji ta intanet (Tax Pro Max). Sannan kuma wai yana so a samar da wata doka da za ta riƙa duba harkar haraji (Revenue Tribunal) da sauransu. Ganin haka ya sa wasu jihohin suka yi yunkurin taka masa burki duk da ƙoƙarin da yake yi na majalisa su shigar da batun harajin VAT a kundin tsarin mulki.
Na uku kuma, gwamnatin tarayya ta yi awon gaba na yin ƙarin harajin VAT duk da ta sauƙaƙa a wasu wuraren amma kuma ba a yi duba da irin ɗawainiyar da ke cikin wannan aiki na wuyan mafi yawan jihohin da ke bayar da manyan kwangiloli ba. Don haka tana iya yiwuwa jihohin nan su ga irin ɗumbin kuɗaɗen da ake zabtare musu da sunan haraji sannan a sa musu cikin cokali. Wasu na ganin duk da cewar an daɗe ana taƙaddama akan mallakar harajin VAT ko samar da wani makamancinsa, da ba a yi ƙarin nan ba, da ba a samu wasu jihohin na ta da jijiyar wuya akan haka ba.
Na huɗu kuma ‘yan jarida da ke zuzuta zancen tare da bayar da ƙididdigar iska (mafi yawanci ba daidai suke bayar da alƙaluman ba). ‘Yan siyasa na amfani da irin abin da ‘yan jarida suka ruwaito su sake hura wutar ba tare da gane ainihin yadda lissafin yake ba. Kodayake yawanci rahotonni ne kurum jaridun ke bayarwa tare da bin ba’asi, sai dai sau da yawa ana samun tasgaro wajen isar da saƙonnin nasu akan VAT yadda ya kamata.
Me zai iya faruwa idan jihohi suka yi nasara?
Idan jihohin Ribas da Legas da sauran gwamnonin kudu suka samu nasarar ƙaddamar da nasu dokokin akan harajin VAT, hakan zai ba wa kowacce jiha damar samar da irin nasu dokokin. Za a samu gasa tsakanin kowacce jiha ta yi hoɓɓasa wajen tara kuɗin haraji. Hakan zai yi kyau ga gwamnatocin su samu ƙarin kuɗaɗen shiga. Sai dai kuma za a iya samun wasu mishkiloli kamat haka:
– Ana iya samun ƙaruwar haraji hawa-hawa (Multiple Taxation) da yadda kafin kayan su isa ga mai saye, an biya masa haraji sau barkatai. Tana iya yiwuwa ma kuɗin harajin ya ninninka ainihin farashin kayan. Lissafin harajin VAT ta fuskar input da output ne magance wannan matsala. Ta wata fuskar kuma, akwai ruɗani wajen sanin ainihin jihar da ya kamata kamfani ya biya harajin nasa. Misali, idan kamfani na da babban ofishi a Legas, kuma yana da rassa a jihohi, shin ta yaya zai tantance harajin kowacce jiha ya biya ta gwargwadon cinikin da ya samu a cikinta? (Nan ma ƙwararru za su samu abin yi!)
– Wata tambayar kuma, yaya mutum zai ci ribar tsarin VAT na input da output? Wacce jiha ce za ta ci girma wacce ce za ta ɗau zafi? Wannan zai jawo rigingimun lissafin haraji da yawa a manyan kotuna (Alƙalai da lauyoyi ma sun samu abin yi!)
– Wata mishkilar kuma, ana iya samun gasa da rige-rige tsakanin jihohi. Idan wannan jihar ta saka kuɗin haraji da yawa, sai waccan ta rage domin ta samu mutane su shiga cikinta. Wannan zai sa gwamnatocin su yi ƙoƙarin daƙile wannan ta hanyar fito da dokoki barkatai. Sai abubuwa su cakuɗe a rasa tudun dafawa.
– Wani abu kuma da ya shafi siyasa da zamantakewa shi ne, idan an tabbatar da ikon karɓar VAT a hannun jihohi, to zai zama tamkar ɗigon ‘baa’. Jihohin za su cigaba da zaƙulo wasu abubuwan suna yin gaban kansi. Hakan zai sa ikon da gwamnatin tarayya ke da shi na jujjuya jihohin ya bar hannunta. Gwamnatin tsakiya za ta zama tamkar je-ka-na-yi-ka. Sai kowacce jiha ta zama mai zaman kanta. Idan tana son haska kanta, sai kurum a samo ƙwararrun ‘yan jarida su yi ta buga famfo har ya zamana an rasa waye mai gaskiya tsakanin dutse da ƙwai.
Kammalawa
Idan ya zamana jihohi ma’azurta sun kasance suna son daina shiga wannan tsarin, yana da kyau a duba maslahar zamantakewa da kuma yau da gobe.
Abu na farko shi ne, kasancewar akwai hukumar lura da tsarin karɓar kuɗaɗen haraji tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi wadda ake kira ‘Joint Tax Board’. Ɗaya daga aikinta ya haɗa da daidaitawa da kuma inganta hanyoyin harajin jihohi yadda wata jihar ba za ta shiga haƙƙin wata ba. Idan ya zama wajibi kowacce jiha ta karɓi harajin VAT da kanta, JTB na iya ruɗanin da hakan zai haifar.
Na biyu kuma a sake duba kayayyakin da aka ɗorawa VAT waɗanda sannu a hankali su ne ke haifar da hauhawar farashi ga kayan yau da kullum wanda bai kamata su yi ta tashin gwauron zabi ba.
Tana iya yiwuwa nan gaba wani daga gwamnonin nan da ke tada jijiyar wuya su haye bisa kujerar shugabancin ƙasa,a lokacin kuma gwamnoni sun riga sun ƙwace kuɗaɗen shigar. Ta yiwu kuma a lokacin zai soma haƙilon dawo da bara bana.