Skip to content

Hauka

Hauka ko taɓin hankali ciwo ne da ya danganci rasa tunani. Haka kuma ciwo ne da yake da wuyar sha’ani ta fuskar mu’amala musamman cikin mutane. Taɓin hankali na ɗaya daga cikin cuttutuka da aka fi ƙyamatar mai ɗauke da ita a ko’ina a faɗin duniya. Musamman a ƙasashen Afrika, inda ba a cika taimaka wa masu ɗauke da waɗannan cuttutukan ba a cikin gaggawa. Musamman idan ba su da ‘yan uwa da suke da ƙarfi, domin kuwa gwamnatoci ba su cika ba da ƙarfi a wajen taimaka wa masu irin wannan lalura ba.

Lalurar taɓin hankali cuta ce da mutane da dama suka santa, walau dai kana da wani ɗan uwa, ko wani da ka sani da ke fama da ita. Ciwon hauka lamari ne da ya yaɗu, kuma mutane da yawa na kamuwa da cutar taɓin hankali a rayuwar su.

Hauka na sa ashin samun bacci ko baccin zai ragu

Su wa ciwon hauka yake kamawa?

Ciwon hauka yana iya kama kowa da kowa, yaro ko babba kuma babu, sai dai bi sa binciken lafiya ya bayyana cewar ciwon hauka ya fi saurin kama masu shaye-shaye. Sai kuma wasu daga cikin matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa da aka fi sani sun haɗa da baƙin ciki, rashin damuwa, matsalar damuwa bayan tashin hankali (PTSD), da rashin abinci.

Kula da masu ciwon hauka

A wasu lokutan ana iya killace waɗanda ke fama da larurar a gida ko cibiyoyin kula da masu taɓin hankali na gwamnati, yayin da wasu lokutan kuma masu irin wannan cuta ke bazama su yi gararamba a gari ba tare da an san yan uwansu, ko daga ina suke ba.

2-Jan su a jiki tare da ba su kulawa ta musamman.

3-Yawan kai su ɓangarorin lafiya da suka shafi ciwon su ana duba su akai akai.

4-Kula da shan magununansu kan lokaci.

5-Lura da abin da ya fi ba su farinciki ko kuma tunzura laurar su.

Lokutan da ciwon ya fi ta’azara

Wani abu da mutane da dama suka sani shi ne cutar na ƙara ƙamari a lokacin sanyi, sannan yawan masu taɓin hankali da ake gani a kasuwanni da tashoshi musamman a Najeriya na ƙaruwa a wannan lokaci.

Matsalolin Hauka ta fuskar al’umma

1- Sau da dama idan mutum ya taɓa kamuwa da irin wannan cutar, ko da ya warke za’a ga cewar ba’a ba su aure ko ɗaukar su aiki, ana ƙyamatar su.

2- Shi da kansa mai lalurar ko da ya warke ba ya sakewa cikin mutane yadda ya kamata.

Alamomin gane ciwon na neman tashi

Alamomin taɓin hankali ko hauka ba su bayyana farat ɗaya, lamari ne da ke bayyana cikin tsawon lokaci bisa yadda cutar ta shafi mai fama da ita. Amma ga wasu fitattun alamu da ke iya nuni da cewa mai yiwuwa wanda ke jin irin wadannan alamomi ba mamaki yana fama da yiwuwar tabin hankali. Da zarar ka ji alamar ɗaya daga cikin waɗannan alamu sai ka yi sauri ka garzaya zuwa wajen likita domin a duba ka:

1- Idan ka ji aa yawan samun damuwa wajen yin tunani ko mayar da hankali a kan wani lamari.

2- Idan ka ji cewa ka fara zargin makwabta da jama’a da ke tare ko kewaye.

3- Idan ka ji kana jin sauti ko wata amsa kuwa da ba wanda ke ji sai kai kaɗai.

4- Idan ka ƙaurace wa masoyanka amma ka fi son ka zauna kai kadai alhali ba haka kake ba a da can.

5- Idan wata sabuwar aƙida ta shigo tunaninka kuma ba wanda zai gamsar da kai cewa ba gaskiya bane.

6- Idan ka fara daina yin wanka kuma ka daina kula da lafiya ko tsabtar jikin ka

7- Idan ka fara jin wani nau’in matsanancin ɓacin rai ko bakin ciki a ka da yaushe

8- Idan ka kula cewa ka fara jin haushin masoyanka haka kawai ba tare da sun yi maka laifi ba ko jin haushin mutane ko wani mutum ko mata.

9- Rashin samun bacci ko baccin zai ragu.

10- Ƙaruwar kasala da rashin jin ƙwarin jikin mutum zai ƙaru.

11- Damuwa da ɓacin rai za su ƙaru.

12- Yawan fushi na ƙaruwa.

13- Tunani iri-iri, ciki har da na son kashe kai ko illata wani

14- Yawan zama shiru ko kuma wuri mai duhuwa.

15- Magana haka kawai ba tare da wani na magana ko kusa da su ba. Jiye-jiye da gane-ganen abubuwan da ba kowa ne ke ganinsu ba.

Ciwon tabin hankali na da wuyar sha’ani

Shawarwari kan ciwon hauka

1- A duk lokacin da ka ga mutun yana yawan keɓe kan shi daga cikin jama’a, kuma ba ya son magana, da dai ƙoƙarin yi ma kan shi abu batare da neman taimakon wasu ba, a lokacin da ya kamata ya nema don gazawar ɗan Adam.

2- Idan aka ga mutun bai damu da tsaftar jikin shi, ko wajen da yake zama ba, to lallai akwai buƙatar duba irin waɗannan mutane.

3- Haka kuma a duk lokacin da aka ga mutum yana shan magunguna da ba likita ne ya rubuta mi shi ba, to a ƙoƙarta nesanta shi da irin waɗannan shaye-shayen, don guje wa kamuwa da taɓin hankali.

Kauce wa ciwon hauka

1- Guje wa shaye-sheyen miyagun ƙwayoyi ko kuma suk wani nau’i na abu mai kawar da tunani ko nutsuwar ɗan Adam.

2- Guje wa shan wata ƙwaya da sunan hana jiki gajiya ko kuma zaburarwa bisa wani aiki.

Manazarta

Md., MD PhD. (2021, March 2). Yadda ake magance cutar hauka. memtrax.com

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×