Bismillahi rahmanir Rahim
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa.
Mece ce layya?
Layya ita ce: Abinda ake yankawa na dabbobin ni’ima (rakumi da shanu da rago da akuya) ranar idin babbar sallah, don neman kusanci ga Allah madaukakin sarki.
Yanka dabbar layya ibada ce mai girma wacce Allah Ya shar’anta ga musulmai. Dalilin shar’ancinta ya zo a Al-kur’ani da Hadisai da ijma’in malamai.
Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “To ka yi sallah don Ubangijinka, kuma ka soke (dabba)”. Suratul Kausar, aya ta 2. Wasu daga cikin malaman tafsiri sun ce ayar tana nufin: “wato ka yi sallar idi, kuma ka soke ko ka yanka dabbar layyar ka”.
Daga Anas Bin Malik (Allah Ya yarda da shi) yace: “Lallai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi layya da raguna guda biyu masu rodin fari da baki, madaidaita kaho guda biyu, ya yanka su da hannayensa, yana mai anbaton sunnan Allah, da yin kabbara, ya kuma dora kafarsa a gefen wuyansu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito wannan hadisi.
Haka nan hadisi ya tabbata daga Ummu Salma (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Idan kwanaki goma suka shiga, kuma dayanku ya so yin layyah, to kada ya taba wani abu daga gashinsa da fatarsa”. Muslim ne ya rawaito shi.
Ibn Qudama (Allah Ya masa rahama) yace: “Musulmai (Malamai) sun yi ijma’I akan shar’ancin layya”.
Hukuncin layya
Malamai sun yi sabani dangane da hukuncin layya zuwa maganganu biyu:
- Layya sunna ce mai karfi, wannan shine ra’ayi mafi yawa da cikin maluma.
Dalilinsu:
- Sun kafa huffa da dalilai kamar haka: Hadisin Ummu Salama (Allah Ya yarda da ita), Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “Idan kwanaki goma suka shiga, kuma dayanku ya so yin layyah, to kada ya taba wani abu daga gashinsa da fatarsa”.
Suka ce: Fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Wanda ya so” dalili ne da yake nuna layya ba wajibi bane, saboda Manzon Allah S.A.W ya rataya hukuncin ga wanda ya so.
- Haka nan ya tabbata Abubakar da Umar (Allah Ya yarda da su) sun taba barin yin layya, saboda tsoron kar mutane su kudurta wajabcin ta.
- Layya wajibi ne, wannan shine kaulin Abu Hanifa da wasu daga cikin malamai.
Dalilinsu
- fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Wanda ya samu ikon yin layya, sai bai yi layyar ba, to kar ya kusanci masallacinmu”. Imam Ahmad da Ibn Majah da Hakim ne suka rawaito wannan hadisi.
Magana mafi rinjaye
Daga abinda ya gabata na dalililan bangarori biyu na malamai, zai bayyana mana cewa layya sunna ce mai karfi ga duk wanda Allah ya bashi iko yin layyar.
Saboda Annabin (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi layya kuma ya umurci al’umarsa da su yi Layya. Don haka bai dace ba ga wanda Allah Ya bashi iko, ya ki yin layya ba.
Hikimar shar’anta layya
- Kusanci ga Allah madaukakin sarki, ta hanyar bin Saboda yanka dabbar layya ya fi yin sadaka da kudin ta a wurin mafi yawa daga cikin maluma. Saboda haka duk lokacin da aka samu dabbar layya mafi tsada, to hakan shi ya fi.
- Akwai ciyarwa ga talakawa da mabukata, da kuma yalwatawa iyalai, ta hanyar basu kyauta da sadakar naman layya da za a yanka.
- Nuna godiya ga Allah ta hanyar dukiyar da za a sayi dabbar layyar.
Yadda za a raba naman layya
Za a raba naman ne kasha uku. Sulusi (daya bisa uku) za a yi sadaka da shi, sulusi kuma za a kyautar, daya sulusin kuma za a ci.
Dabbobin da ake layya da su, da kuma shekarun su
Ana yin layya da lafiyyar dabba, wanda bata da aibi ko kadan. Ba a yin layya da dabba mai ido daya, ko gurguwa, ko mai karyayyen kaho, ko mai gutsurarren kunne, ko busasshiya, ko ramammiya, ko kyamusassa, ko mai yankakken kunne, ko tsohuwar dabba, ko mai guntulallen bindi da sauran nakasu. An fi so ayi layya da lafiyya kuma kosashiyar dabbar da bata da aibu.
Saboda hadisin Al-bara’u dan Aazibin (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Dabbobi guda hudu basa isarwa a layya: Dabba mai harari-garke wacce matsalan idonta ya bayyana, da maras lafiyan da cutarta ta bayyana, da gurguwar da gurguntakanta ya bayyana, da kuma ramammiyar da bata da kitse”. Imam Ahmad da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
Dabbobin da ake layya da sune:
- Rakumi: ya zama ya cika shekara biyar.
- Saniya: ta zama ta cika shekara biyu.
- Rago: ya zama ya cika wata shida.
- Akuya: ta zama ta cika shekara daya.
Lokacin yanka dabbar layya
Lokacin yanka dabbar layya yana farawa ne bayan sallar idi. Bai halatta a yanka ta kafin sallar idi ba, saboda hadisin da Al-Barra Bin Azib (R.A) ya rawaito, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata gare shi) ya ce: “Duk wanda ya yi sallah irin tamu, ya kuma yi yanka irin namu to lallai ya dace da yankan layyah akan tafarki. Amma mutumin da ya yi yanka gabannin ya yi sallar idi to sai ya sake yanka wata a madadinta”
Lokacin yankan zai ci gaba har zuwa kwana uku bayan ranar sallah. Wato yana karewa ne da faduwar rana a rana ta hudu daga cikin ranakun idi.
Wasu hukunce-hukunce da suka shafi layya
- Ana yin layya ne da dabbobin ni’ima kadan, wato rakuma ko shanu ko tumaki ko awaki. Bai halatta a yi layya da wasu dabbabi da ba dabbobin ni’ima ba.
- Idan watan Zul Hijja ya shigo, to bai halatta ga wanda ya yi niyyar layya, ya aske wani abu na gashin sa ba, haka nan bai halatta ya yanke farshen sa ba, saboda hadisin Ummu Salma (R.A) da ya gabata. Idan kuma ya manta ya aske gashin sa ko ya yanke farshen sa, to babu komai a kan sa. In kuma dagangan ya aikata, to yayi laifi, sai ya yi istigfari ya tuba ga Allah, ya yi layyarsa, babu kafara akan sa.
- Ya halatta mutum ya karbi bashi ya yi layya idan har zai iya biya.
- Mafificiyar dabbar layya it ace wacce ta fi lafiya, ta fi koshi, ta kuma fi tsada.
- Ya halatta mutane bakwai su yi tarayya don sayan rakumi ko saniya don yin layya. Amma bai halatta su yi tarayya don sayan rago ko akuya ba. Amma ya halatta magidanci ya saya shi kadai, sai ya yanka da sunan iyalan gidansa gaba daya. Saboda hadisin Abu Ayyub (R.A) yace: “Namiji ya kasance a zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana layya da akuya ga kansa da iyalan gidansa, sai su ci kuma su ciyar”. Tirmizi ne ya rawaito shi.
- Bai halatta ga wanda ya sayi dabbar layya ya sayar da ita ko ya kyautar da ita ba, sai dai idan ya zama zai musanya ta da wanda ta fi ta ne.
- Haka nan bai halatta mai layya ya sayar da wani abu na dabbar layyarsa ba.
- Ya halatta masu hali su sayi dabbobin layya su rabawa talakawa don su ma su yi layya. Saboda ya tabbata Manzon Allah (tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi) ya rabawa sahabban sa dabbobin layya. Muslim ne ya rawaito shi.
- Abida ya fi shine mai yin layya ya yanka dabbarsa da kansa. Kuma ya halatta ya wakilta wani ya yanka masa.
- Ya halatta a ajiye naman layya fiye da kwana uku; saboda hadisin Buraidah (R.A), Lallai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata gare shi) yace: (Na kasance na hana ku ijiye naman layya fiye da kwanaki uku, to ku ajiye na tsawon yadda ya yi muku). Muslim ne ya rawaito shi.
Muna rokon Allah mai girma da daukaka Ya bamu ikon yin layya, Ya kuma karba mana ayyukan mu.