Skip to content

Ido

Share |

Ido ɗaya ne daga cikin sassan cikin ɗan’adam masu matuƙar amfani da kuma muhimmanci. Ta fuskar gudanar da rayuwarsa, mu’amalarsa da duk wani cigaban rayuwarsa.

Ido wani sashi ne na jikin ɗan’adam mai matuƙar amfani, wanda da shi ne mutum ke amfani wajen gani da kuma tura wa ƙwaƙwalwa saƙon abin da ya gani. Ita kuma ta yi aikinta wurin ba shi tabbacin lallai kaza ɗin ya gani.

maganin ɗigawa na idanu

Ɓangarorin ido

Ido yana da ɓangarori da dama a tare da shi waɗanda suke taimakawa ɗan’adam wurin sadar da tunani da kuma tabbatuwar zahirantar da abin da ƙwalƙwalwa ke shaida masa ya gani.

Ƙwayar ido

Ido yana da ƙwaya wadda ta kasance baƙa, sai dai kuma Allah mai hallita wasu da yawa tasu ta bambanta akwai masu (brown) kalar ƙasa-ƙasa akwai kuma masu (blue) wato kalar ruwan bula. Akwai kuma masu (golden) wato kalar zaiba-zaiba. Sai dai anƙasar Hausa da dama mun fi sanin ƙwayar ido da baƙa. Sai dai ƙwayar idanu ba ita ce take da alhakin ba mu damar gani ba face zinariya idanu ita kuma ƙwaƙwalwa ta ba mu tabbaci na abin da muka gani.

Gashin ido

Gashin ido, shin ko mutum ya taɓa tunanin ni’imar dake tattare da gashin ido? Ƙaddara a ce an bar gashin ido yana toho kamar gashin kai, a ce babu wani tsari da mahaliccin ido ya halitta wanda zai hana gashin ido ci gaba da toho, to ya ya mutum yake zaton zai tsinci kansa? Kafin ma a yi batun kariya da gashin idon yake bai wa idanu daga faɗawar abubuwa cikin ido irin su gashi ko ƙura ko kuma ɓurɓushin wani abu.

Fatar ido

Haka idan muka je ga fatar ido, mutane sukan ƙifta idonsu sau dubban lokaci a rana ba tare da sani ba. To wannan fata ta saman ido ita ce mataki na biyu na kariya ga ido wajen hana shigar wani datti ko burbuɗin wani abu. Sannan kuma akwai wasu sinadarai na musamman da akodayaushe suke tabbatar da cewa cikin fatar bai rabu da danshi ba, don haka a duk lokacin da mutum ya kifta idonsa to kamar yana goge idon ne.

Kamar dai yadda magogin gilashin dake gaban direban mota yake aikin wanke gilashi idan ana ruwa ko kuma domin goge datti. Da ace fatar ido ba tai dai-dai da ƙwayar ido ba, to da wataƙila ba za ta iya goge idon gabaɗaya ba, kuma da ba zai taɓa yiwuwa mutum ya goge dattin da ya tattaru a cikin idonuwansa gaba ɗaya ba. To kuma a ƙaddara ma fatar ba da kanta take wannan aiki ba, sai datti ya taru sannan mutum zai farga ya goge ko kuma ace babu fatar idon duk abin da ya taho haka zai faɗa kaitsaye, babu shakka da rayuwa ta yi wahala ƙwarai, amma mutane da dama ba su damu da tunanin wannan ni’ima ba.

Hawaye

Haka zalika hawaye na da matuƙar muhimmanci ba wai lallai sai na kuka ba, shi ya sa idan wani abu ya yi wuf ya faɗa ido kai tsaye, nan da nan sai hawaye su zubo dai-dai gwargwado yadda za su taimaka wajen kore wannan datti da ya faɗa cikin ido. Kuma hawaye suna kare ido daga kamuwa da cututtuka, hasalima wannan ɗanɗanon gishiri-gishirin da ake ji a cikin hawaye to wani sinadari ne mai kashe ƙwayoyin cuta na cikin ido wanda ƙarfinsa ya fi na sinadarin kashe kwayoyin cuta irin wanda ake amfani da shi a banɗaki, amma sai mahaliccin ido ya daidaita shi yadda zai yi daidai da ido ba tare da ya cutar da shi ba.

Hoton abin da aka kalla kan bayyana a tsakiyar ƙwayar idanu

Zinariyar ido

Da ita ne muke gani, ita ce ke da alhakin haska mana abin da yake gabanmu wadda ko yaya aka samu matsala sa ita ganin mutun kan iya ɗaukewa. Tana iya samun matsala sanadin haɗari, ko faɗuwa ko makamantansu. Tana kuma iya samun matsala haka kawai mutum yana zaune ta goce, aiki ko kuma wani abu baya sa ta dawo daidai ko wani magani har sai lokacin da ubangiji ya ba da ikom dawowa daidai.

To idan muka yi nazarin yadda aka tsara gani ya tabbata, za mu ga cewa, tun ɗan Adam yana cikin mahaifa, mahaliccinsa ya tsara masa yadda tsarin ganinsa zai kasance. Kuma an tsara gani akan yadda ƙwaƙwalwa zata iya ajiye abin da mutum ya gan shi ya kuma san shi. Misali abubuwan da mukan iya tunawa a rayuwarmu kamar su yarintarmu, makarantun da muka taɓa yi, gidajen da muka sani, muna gane su ne ta hanyar ganinsu da muka taɓa yi da kuma zama da suka yi a wani ɗan ƙanƙanin bigire a ƙwaƙwalwarmu.
Gane rahamar wannan ni’ima zai yiwu ne kawai idan mutum yai tunanin cewa, yanzu ace duk abin da mutum ya taɓa gani komai sanin da kai masa, sai ace kuma idan ka ɗauki wani lokaci shike nan ka manta shi, kuma ko da ka sake ganinsa ba za ka iya tuna cewa ka sanshi ba, to ai da rayuwa ta shiga ruɗu ƙwarai. Kuma sau tari irin wannan na faruwa a cikin al’umma, amma a wasu lokuta musamman ma a rayuwa irin ta Afirka, sai ace mutum ya samu taɓin hankali.

Ido biyu

Mutum ya tsinci kansa ne an haife shi da idanu biyu, amma mutane da yawa ba su taɓa tunanin dalilin haka ba. Domin a haƙiƙa kowane ido cin gashin kansa ya ke yi, kuma zai iya gani ba tare da taimakon ɗaya idon ba. Don haka wani ma zai iya cewa , to idan haka ne mene ne amfanin idanuwa biyu.

To amfanin kasancewar idanuwa biyu shi ne. Idanun mutum an haliccesu ne kuma aka sanya aƙalla tazarar santimita 5 tsakanin ido da ido. Amma kowanne ido yana da wata baiwa da ɗayan bai da ita wajen ganin abubuwan duniya. Akwai abubuwa uku da suke haɗuwa su bayar da cikakken gani; na farko shi ne iya nisan da ake iya gani ta gefen dama, na biyu shi ne iya nisan da ake iya gani ta gefen hagu, na uku kuma shi ne nisa ko zurfi da mutum ke iya gani kai tsaye ta gabansa. To ƙwayar ido guda ɗaya tana iya kallon surar abu ne kawai ta ɓangarori biyu wato dama da hagu. To akwai wani abin mamaki dake faruwa anan. Ita ƙwaƙwalwa ita ce take haifar da ɓangare na uku na gani wato zurfi.

Kuma tana yin haka ne ta hanyar haɗa surar abin da idanuwan biyu suka ɗauko tare domin a samu cikakken gani. To ta hanyar tantance banbancin abin da kowanne ido ya ɗauko ne ƙwaƙwalwa take tantance zurfi ko nisan abu, yadda surar abin za ta fita dai-dai mutum ya gani radau. In ba don wannan aiki da ƙwaƙwalwa take yi ba, to da sai mutum ya riƙa ganin surorin abubuwa bi-biyu bi-biyu. Ba tare da tantance zurfi ba.

Za mu iya tabbatar da wannan batu ta hanayar buga misali. Yanzu ace mutum yana kallon rassan wata bishiya da ke gabansa, farko sai ka kalle ta da duk idanunka biyu a buɗe. Bayan ɗan lokaci kaɗan sai ka rufe ido ɗaya sai ka riƙa bin rassan bishiyar da kallo da ido ɗaya, to bayan kamar minti ɗaya kuma sai ka buɗe ɗaya idon, za ka fahimci cewa rassan bishiyar sun ɗan yi zurfi ba kamar yadda kake kallonsu da farko ba.
Muhimmancin ido: Hausawa kan ce wai na rufe idanuna ban ga kyan makanta ba, wannan karin magana ne dake sake tabbatar mana da mihimmancin ido da kuma amfaninsa ga rayuwar ɗan Adam ta kowace fuskar rayuwa. Muhimmancinsa ne ya sa masana kiwon lafiya suka bayyana wasu hanyoyi biyar da za a bi wajen inganta shi kamar haka:

1. Motsa jiki

Motsa jiki na da matuƙar muhimmanci da tasiri ga lafiyar jiki, ciki har da ido. Ido na da nashi irin atisaye da ake yi masa, mutum zai juya ganinsa zuwa ɓangaren dama sai ya kwanta da ɓarin jikinsa na hagu na tsawon minti uku. Sannan sai ya sake juya ganinsa zuwa ɓangaren hagu ya kwanta da ɓangaren jikinsa na dama, shi ma na tsawon minti uku.

2. Abinci mai gina jiki

Cin lafiyayyen abinci mai gina jiki yana taimaka wa lafiyar ido sosai; musamman cin abinci mai ɗauke da ganyayyaki na da matuƙar tasiri ga lafiyar ido.

Misali:
Likitoci sun yi bayanin cewa gwanda na ƙunshe da sinadaran da ke ƙara wa ɗan’adam lafiyar jiki, musamman ma ido. Bugu da ƙari, likitar ido Aisha Shariff Kalambe ta ce gwanda na da sinadarin vitamin C mai yawa.

“Idan mutum ya ci yankan gwanda sau ɗaya a rana ya ishe shi ya samu vitamin C da yake buƙata,” in ji ta. Haka nan gwanda tana taimakawa wajen rage hawan jini, da ciwon zuciya, da kare kumburin cikin jiki, da kuma rage kaifin cutukan da tsufa ke jawowa.

3. Dokar 20-20-20

Ga wanda yake yawan amfani da kwamfuta, yana da kyau ya bi dokar 20-20-20. Doka ce ta buƙaci idan ana amfani da kwamfuta, to ya kamata duk bayan minti 20 a kalli wani abu wanda ya kai tazarar ƙafa 20 har na tsawon dakika 20.

4. Taba-Sigari

Ga wanda yake shan sigari yana da kyau ya daina domin sigari na haddasa cututtuka kamar cutar daji, ciwon huhu, rage ƙarfin gani da sauransu.

5. Tarihin lafiyar idanu

Yana da kyau mutum ya ziyarci likita don sanin tarihin lafiyar idanun danginsa, ma’ana idan akwai tarihin matsalar gani hakan zai taimaka wajen shawo kanta kafin ta zama babba.

Inganta lafiyar ido

Akwai abubuwan da suka kamata mu kula da su wurin inganta lafiyar ido. Ta fuskar cima ko kuma kulawar da ta kamata.

Yin amfani da kayan gayayyaki kamar karas da kifi za su taimaka mana wajan kula da lafiyar idan mu. Inganta yanayin cimar mu ta hanayar cin abinci me ɗauke da sinadaran da za su haɓakka lafiyar mu zai ƙara mana lafiyar idanu, dama rage saurin tsufan idanu.

A riƙa duba lafiyar idanu aƙalla sau biyu a shekara

Akwai abin da ake kira da (get enough sleep) wato samun wadataccen bacci zai taimakawa idanun mu daga bushewa domin huta gajiyyar aikin da suke yi mana akodayaushe kuma yana ƙara mana lafiyar gani.

Sai mataki na gaba shi ne (Protect your eyes from the sun) wato mutum ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajan ganin bai bar hasken rana kai tsaye yana shiga idanunsa ba, domin hasken rana ko kuma haske irin na waya kan iya ba ido matsala. Hakan zai taimaka wurin samun ingantacen gani, za kuma a iya amfani da gilashi.

Ƙungiyar likitocin idanu ta amurka sun tabbatar da yawan cin matsalolin idanu da ake samu na da alaƙa da samun rauni ko faɗawar wani abu a idanun sakammakon ƙarancin amfani da abin kariyar a lokutan aiyuka.

Shaye-shaye yana ƙara wa abubuwa da suke ƙalau matsala ko da wanda a lafiyance su aikinsu ne kuma a bayyane zai haifar da matsalar ga jijiyar kula da idanu (Optic nerve) hakan zai iya haifar da (macular degeneration) ko matsalar (cataract), duka waɗannan kuma suna cutar da idanu.

A inganta wanke hannu da fuska yadda ya kamata kuma akai akai. A ƙaurace wa saka kayan kwaliyya masu ɗauke da sinadari chemical kamar su abin saman gira, idan kuma ana yawan amfani da glass ya kasance ka na gogeshi da abin gogewa mai tsafta dama ajiyeshi cikin kulawa da kuma tsafta yadda ya kamata.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading