Skip to content

Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, fitaccen malamin addinin Musulunci ne daga jihar Bauchin Nijeriya. Sanannen malamin ya yi fice wajen tsayuwa kan koyarwar addini, tare da tsauri a cikin wa’azozinsa. Dr. Idris na ɗaya daga cikin malaman da suka yi muƙabala tare da shugaban kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf.

Haihuwa da kafa iyali

An haife Sheikh Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi a garin Gwaram da ke karamar hukumar Alkaleri, a cikin shekarar 1957, kuma ya yi rayuwarsa ne tsakanin jihohin Bauchi, Gombe da Nasarawa.

Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya auri mata huɗu, yayin da ya haifi ‘ya’ya sama da talatin da jikoki da dama.

Karatunsa na neman ilimi

Iliminsa na farko ya kasance mai tsananin sha’awar Al-Qur’ani da Hadisai, wanda ya kai shi ga ci gaba da karatun Al-kitab Sunnah, ya yi fice a ilimomin Alqur’ani da Hadisai, tare da daidaita kansa da koyarwar Salafus Salih, (magabata na kwarai). Ƙwarewarsa a harshen Larabci da Hausa sun ba shi damar isar da da’awa ga jama’a masu dimbin yawa.

Ya yi karatu a College of Education, Legal and General Studies Misau, jihar Bauchi da kuma Bayero University Kano. Dr Idris ya fara karatun degree a Jamhuriyar Nijar kafin daga bisani ya wuce kasar Saudiyya inda ya karanci fannin shari’ar Musulunci a jami’ar Madina.

Bayan ya dawo ne ya fara karantarwa a jihar Bauchi, yana tsaka da karantarwar kuma ya wuce Jami’ar Plateau inda ya yi digiri na biyu. Hakazalika Malamin ya yi karatun digirin digirgir na PhD a kasar Sudan a fannin Usulul Fiqh sai kuma ya tsunduma karantarwa tuƙuru.

Da’awa

A matsayinsa na fitaccen malami  daga ɓangaren Izala, lakcocinsa, wanda ya saba gabatar da su cikin harshen Hausa, suna jaddada ka’idojin Ahlussunnah Wal Jama’ah da Manhajus Sunnah. Falsafar koyarwar Malam Abdul’aziz ta samu gindin zama a cikin Alkur’ani da Hadisai, inda ya mayar da hankali kan rayuwar da ta yi daidai da koyarwar Annabi Muhammad (SAW).

A kokarinsa na da’awa, ya kafa shirye-shiryen ilimantarwa da ke inganta ayyukan Musulunci tsantsa, ba tare da sabbin abubuwa ba. Amsa tambayoyi da Tafsirinsa masu tasiri sun karfafa imanin musulmi marasa adadi, tare da barin gado mai ɗorewa.

IMG 20230531 WA0010 750x636 1
Marigayi Sheikh Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, yake jawabi ga manema labarai a wani lokaci.

Tun daga lokacin fitowar Alfijir har zuwa faɗuwar rana babu abin da Malam yake yi idan ba harkokin ilimi ba walau dai bayar da ilimin ko kuma yin bincike

Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya bar tarihi mai cike da koyi da jajircewa wajen yada ilimin addinin Musulunci da kuma tsayuwa kan gaskiya, duk da kalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa.

An dade ana kwatanta Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya – fitaccen malami da ya rayu da koyarwar da ta sha bambam da ra’ayin yawancin manyan malaman Izala na lokacinsa. Sheikh Albani da Dr. Idris sun yi fice wajen caccakar abubuwan da suka sabawa Sunnah, ko da kuwa daga cikin malaman Izala ne ko wasu kungiyoyi.

Halayensa

Faɗin gaskiya

Shi mutum ne mai tsananin son faɗin gaskiya kuma ba ya ɓoye-ɓoye. A duk lokacin da ya karanta wani abu na ilimi kuma ya fahimci al’amarin to zai fito ya faɗe shi ba tare da nuƙu-nuƙu ba.

Ra’ayi

Sannan kuma akwai wani abu, idan malam ya yi maka magana ko kuma samu saɓani ta fahimta to ka tabbatar da zarar ya faɗi ra’ayinsa to wallahi wannan ya wuce. Ba ya riƙe mutane a ransa.

Sauƙin kai

Mutum ne mai sauƙin kai amma sai an matso kusa da shi za ka gane. Mutum ne mai son jama’a da son taimaka musu da kuma yi musu gargaɗi.

A baya-bayan nan, an samu takun saka tsakaninsa da hukumomin jihar Bauchi, wanda ya kai ga cafke shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin haddasa fitina da tayar da tarzoma, kafin bayar da belinsa cikin watan Mayun 2023 bayan shafe wani lokaci a gidan yari.

Sana’a da kasuwanci

Dangane da batun sana’a baya ga karantarwa da da’awa, marigayi Sheikh Dutsen Tanshi ɗan kasuwa ne kuma manomi. Yana noma sosai domin daga safe har lokacin da zai bayar da karatu yakan je gona. Sannan yana da makarantu nasa tun daga kan matakin reno da firamare da sakandire har ma da kwalejin ilimi duka a jihar Bauchi. Yana kuma da shagunan sayar da kayayyakin masarufi da na kayan sha da kuma irin waɗanda ake kira ‘business centres da na sayar da magunguna.

Zumunci da ayyukan jinƙai

Marigayin yana tattaki da iyalansa su tafi ƙauyensu domin sada zumunci da ‘yan uwansa. Idan ya tashi zuwa zai tafi da tsarabar kuɗi da kaya, ya yi musu kyauta. Malam mutum ne mai zumunci. Yana ƙaunar ‘yan uwansa sannan yana taimaka musu.

Dangane kuma da ayyukan jinƙai da marigayin ke yi, idan ka shiga azuzuwan makarantar malam za ka adadi mai yawa na marayu da suke yin karatu kyauta sannan kuma yana saya musu littafai da sauran kayan karatu.

Akwai ma wani lokacin da a ka shiga yanayin tsanani a ƙasar nan kamar shekaru biyu baya, da malam ya lura da yanayin tsananin da ake ciki jama’a na fama da kuɗin abinci ba ta karatu suke yi ba, sai ya ce ya yafe wa kowa kuɗin makaranta. Kowa zai yi karatu kyauta a lokacin.

Rasuwarsa

Sheikh Dutsen Tashi dai ya rasu da misalin karfe 11 na dare ranar Alhamis, a gidansa da ke Bauchi, bayan fama da jinya. An yi jana’izars da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Juma’a a birnin Bauchi. Dandazon al’umma ne suka halarci taron jana’izar tasa da aka gudanar a masallacin Idin malamin na Games Village, da ke birnin Bauchi.

Marigayin ya yi doguwar jinya kafin rasuwar tasa, inda ya yi yawon neman magani a ƙasashen da suka haɗa da Saudiyya da Indiya.

Sheikh Tanshi ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mata guda uku da kuma ‘ya’ya 32.

Manazarta

BBC News Hausa. (2025, April 4). Abu biyar da ba ku sani ba kan Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi. BBC Hausa.

Bello, H. (2025, April 4). Renowned Bauchi cleric, Abdulaziz Dutsen Tanshi is dead. Daily Post Nigeria.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page