Kaɓaki na nufin wani abinci, musamman tuwo don wata hidima, wanda aka mulmula madurguji-madurguji aka kai gudummuwa gidan da ake aiwatar da hidimar walau biki ko suna. Haka kuma, kaɓaki yana iya ɗaukar ma’anar masakin da ake zuba tuwon biki a ciki. Kaɓaki shi ne abincin gudummuwa wanda abokai ko ‘yan’uwa da abokan arziki suka kai wa wanda yake da wata hidima ta bukin suna ko ɗaurin aure ko walima, ko taron ta’aziyya na mutuwa. Babu tsayayyen nau’in abincin da ake kawowa na Kaɓaki saboda ana iya samun bambancin al’adu ta fuskar abinci daga wannan wuri zuwa wancan.
Al’adu da ɗabi’un Hausawa suna bambanta da junansu daga wannan wuri zuwa wancan a faɗin ƙasarar Hausa. Hakan ya faru ne sakamakon
bambancin wurin zama da yanayin rayuwa.
Ana sanya abincin kaɓaki a babban kwano ko masaki wanda zai ci dafaffen abinci na tsaba kimanin tiya guda da rabi ko tiya biyu. Wannan dalili ya sa ake kiran duk wani masaki ko kwano da ke iya ɗaukar abinci kimanin haka da suna Kaɓaki.
Ire-iren abincin kaɓaki
Kamar yadda bayani ya gabata a sama, abincin kaɓaki zai kasance duk wani nau’in abinci wanda al’umma ta saba da shi a matsayin abincin alfarma a yayin biki. Misali, ana yin abincin kaɓaki da shinkafa ko waina ko tuwo ko Fura. Kaɓakin shinkafa ana yin shi ne da shinkafa dafa-duka cikin masaki guda tare da dafaffar kaza ko soyayya a saman abincin.
Haka kuma, ana iya yin shinkafa da miya tare da dafaffa ko soyayyar kaza. Kazar da ake yin Kaɓaki da ita ba a yayyanka ta. Bayan an fige ta an feɗe an cire kayan cikin, haka nan ake dafa ta a banƙare ko a soya. Idan kuwa waina ce, za a kawo toyayyar waina cikin masaki guda tare da miya da kaza. Wasu kuma wainar da kaza za su kawo ba tare da miya ba. Fura kuwa, ana kawo manyan mulmule (Curi) guda uku ne tare da nono kima ga mai hali. Masu kawo tuwo su ma, suna kawo shi ne tare da miyar taushe da kaza dafaffa ko soyayya. Galibi tuwon mulmulallun curi ne manya ake yi wanda za a riƙa gutsura idan ana bukata. Magaji (2002) ya yi bayanin cewa yayin bukin Dubu da Tambarci, akan gudanar da al’adar yin Kaɓakin tuwo domin rabawa ga waɗanda suka zo taron.
Masu mawo kaɓaki da lokacin kawowa
Idan saurayi ya yi wa aboknsa gudummuwar Kaɓakin abinci, yakan ba yaran gidansu ne su kai. Idan sun kai za a ba su tukuici na alewa da cingam. Idan kuwa mutuum ya kai da kansa, ba a bin da za a ba shi na tukuici. In kuwa mutumin da ya yi kaɓaki yana da mata kuma ya ba ta kaɓaki ta kai wa wanda yake buki, to za a ba ta tukuicin goro da cingam da alewa (a zamanance), sannan za a ba ta gutsuren hura da waina da tuwa cikin wanda waɗansu suka kawo.
Ana kai Kaɓakin bukin aure washegarin ɗaurin aure da yamma. Idan kuwa na suna ne, ana kai shi ne ranar suna da yamma. Haka kuma idan walima ce ake yi, ana kaiwa ne lokacin da ake taron walimar idan ranarta zo. Don haka, abokai da ‘yan’uwa da abokan arziki ke taruwa su yi abincin Kaɓaki zuwa ga wanda ke yin buki ko wata hidima da ta danganci tara jama’a.
Rabon abincin kaɓaki
Yayin da aka tara abincin kaɓaki ga mai yin hidima, ana tara aƙalla kaɓaki hamsin zuwa saba’in ko fiye da haka. Yawan kaɓaki yana danganta ne da irin mu’amalar mai buki da jama’a da kuma irin tasa gudummuwa da yake yi yayin bukin ‘yan’uwa da abokan arziki. Idan abinci ya taru, akan ware na uban ango da na mahaifiyarsa da na amarya da na ƙawayenta da na abokai da na sauran jama’a. Wanda ya ragu mai yawan, akan tsame kajin da ke samansu a soye su domin ango ya samu abin da zai ci shi da amarya bayan an tashi taron biki. Abincin da aka samu dangin fura da tuwo da waina, su ma ana rarraba su ne bakin gwargwado ga kowane rukuni na waɗanda ake yi wa kason su samu ganin cewa ba da yawa ake kawowa ba.
Muhimmancin kaɓaki
Kaɓaki yana da muhimmanci ƙwarai a tsarin rayuwa mutanen karkara. Yana kawo haɗin kai da zumunci ga abokai da ‘yan’uwa. Hanya ce ta taimakon wanda yake buki ba tare da ya gajiya ba ta fuskar abincin da zai ba mutanen da suka zo taya shi murna.
Ire-iren abincin kabaki
Tuwo
Shi ne babban jigon abincin kabaki, shi ma yana da yawa, kashi-kashi ne. Daga ciki akwai:
- Tuwon biski, ana yin shi da gero ko masara
- Tuwon dawa; wannan turo kamar yadda sunan ya nuna ana yin shi da dawa ne.
- Tuwon tsari; ana yi da gero ko dawa da sauransu, ana shika nau’in hatsin da ake son yin tuwon da shi. Amma an fi yi da gero.
- Tuwon shinkafa, kamar yadda sunan ya nuna ana yin shi ne da shinkafar tuwo. Wato farar shinkafa.
- Tuwon masara, shi ma tuwo ne wanda ake yin shi da masara jo ko fara.
- Tuwon fulawa ana yin shi da fulawa.
- Tuwon alkama, shi ma nau’in tuwo ne da ake yi da alkama. Galibi masu ciwon sukari sun fi cin shi.
Gurasa
Abincin Larabawa ce daga baya ta zama ta Bahaushe musamman Bakane. Ita ma ana amfani da ita a matsayin abincin kabaki musamman a zmanance.
Waina
Abinci kabaki ce ko kuma wani bangare na abincin. Tana da nau’uka biyu:
- ‘Yar tsala ko ‘yar tsame: Ana jefa ta cikin ruwan mai a soya.
- ‘Yar tanda, ita ce wainar da ake soya ta da tanda. Ita ba ta shan mai sosai, ana yin ta gero ko ta shinkafa.
Manazarta
Magaji, A. (2002). Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-Yanayensu a ƙasar Katsina.
Kundin Digiri na Uku: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano
Sani, S. (1979). Sunayen Hausawa na Gargajiya da Ire-Iren Abincin Gargajiya. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero