Skip to content

Kada

Kada na ɗaya daga cikin sanannun dabbobi masu ban tsoro a duniya kuma ana kallon su a matsayin mafarautan mutane da wasu halittun. Jikinsu na da ƙarfi sosai, tare da ƙaƙƙarfan muƙamuƙi, da ƙarfin gudu da ƙarfin hali da juriya tare da ƙwarewarsu wajen iya sanɗa mara misaltuwa. Waɗannan siffofi sun kai kada ga zama ɗaya daga cikin manyan mafarauta a duniya a yankin muhallinsu.

Asalin halittar kada

Kada suna da alaƙa ta kut-da-kut da sauran halittun da ake kira ‘crocodilians’ ciki har da dabbobi nau’in alligators, caimans, da gharials, kada sun ɗan canja kaɗan a yanayin juyin halittarsu a cikin shekaru miliyan 200.

Ba kamar sauran nau’ikan dabbobi masu rarrafe ba, kada su ne tsofaffi jinsin rukunin dabbobi masu rarrafe waɗanda kuma suka haɗa da dinosaur. Duk da cewa Dinosaurs sun ɓace shekaru miliyan 65 da suka gabata, ana kyautata zaton cewa kada sun rayu sosai a tsawon lokaci saboda sun dace da muhallinsu.

A halin yanzu akwai nau’ikan kada iri-iri har guda 13 waɗanda ake samun su a cikin yanayi mai daɗi da ruwa mai ɗanɗanon gishir, a Arewacin Amurka da Kudancin Amurka, Afirka, Asiya da Ostiraliya.

Kalmar kada a haƙiƙa ta samo asali ne daga tsohuwar kalmar Girkanci, wato krokódilos ko wani ɗan bambanci. Sai aka sauya “k” zuwa “c”. Wasu masana sun yi imanin cewa kada haɗi ne na kalmomi guda biyu wato, (krokè) da kuma (drilos).

Siffofin kada

Kada manyan dabbobi ne masu rarrafe kuma masu kauri tare da fata mai kauri wacce ke ɗauke da sulke waɗanda dukkansu ke ba su kariya daga masu cin zarafi da kuma hana cikin jikinsu bushewa.

Kada na suna zuwa da launuka iri-iri kama daga kore zuwa launin ruwan kasa, launin toka da baƙa, wannan launuka sun sa kada na da sauƙin kamawa a cikin ruwa da ciyayi da ke kewaye.

Kamar sauran nau’in kada, idanunsu da hancinsu suna saman faffadan kai da hancinsu. Wannan yana da amfani yayin da suke cikin ruwa ba tare da kusan kowane ɓangare na jikinsu ba ya bayyana ba domin samun nasarar yin kwanton bauna.

Domin samun kariya a cikin ruwa, kada na da fatar ido ribi uku ta musamman wadda ke ba su damar barin idanunsu a buɗe amma tana hana lalacewa daga ruwa.

Haka kuma suna da bangarori na waje da ke rufe kunnuwansu da hancinsu, da tsarin numfashi na musamman wanda ke ba su damar kasancewa a cikin ruwa har na tsawon sa’o’i biyar a lokaci guda.

Wutsiyoyinsu suna kwance a tsaye suna da ƙarfi sosai kuma suna amfani da su don yin tafiya ko motsi a cikin ruwa, ko da yake suna da ƙafafu masu kauri, amma ba sa amfani da su lokacin yin iyo.

Kada suna da girman girman daɗi kimanin mita 2, zuwa tsayin mita 7 (wannan a nau’ikan kadojin ruwa mai ɗanɗanon gishiri ne). Kada shi ne nau’in halitta mafi nauyi mai rarrafe a duniya wanda yakan kai har kilogiram 1,000.

Rarrabuwar kada da muhallinsu

Ana samun kada a wurare daban-daban na dausayi a ko’ina cikin ruwan mai zafi a kudancin Hemisphere.

Amurka

Kadojin Amurka su ne nau’in kada mafi girma a Arewacin Amurka da Kudancin Amurka kuma ana samunsa yana zaune a cikin koguna da tafkuna, da ruwan tekun da ke kusa da bakin teku da kuma cikin lagoons daga kudancin Florida, cikin tsakiyar Amurka.

Nahiyar Afirka

A cikin Afirka, Kadojin tafkin Nile sun taɓa yaɗuwa a gabashi da kudancin Afirka, amma yanzu sun yi ƙaranci. Suna zaune a cikin ruwa mai daɗi, koguna, tafkuna da fadama. Mafi girma kuma mafi yawan nau’in kada ita ce crocodile estuarine.

Yankin Asiya da Ostiraliya

Ana samun kadoji a bakunan kogi da fadama tun daga ɓangaren Bay of Bengal a cikin tekun Indiya, zuwa ko’ina cikin kudu maso gabashin Asiya har zuwa Ostiraliya.

Halaye da salon rayuwar kada

Masu bincike da masana kimiyya da yawa sun yi nazari da yawa don fahimtar halayen kada da kyau. Kodayake yawancin nau’o’in kada ba a yi nazarin su sosai ba, a nan akwai wasu nau’o’in dabi’a na yau da kullum da ake samu a tattare da kada.

Rashin iya daidaita zafin jiki

Kamar yadda sauran dabbobi masu rarrafe ke yi, kada su da kansu ba sa iya daidaita yanayin jikinsu, maimakon haka su dogara da zafin rana don dumama jikinsu. A lokacin zafi da rana, sai su taso zuwa bakin kogi suna dumama jikinsu. Ƙananan nau’o’in kada kamar gajerun kadoji (wadanda su ne mafi ƙanƙanta a cikin nau’in kadoji, suna hawan bishiyoyi don samun ɗumi.

Wata hanyar da kada ke iya daidaita zafin jikinsu ita ce ta yin nitso sama da kasa a cikin ruwa, suna dumamuwa da rana a sama sannan su kwantar da kansu a karkashin ruwa. Kadoji dabbobi ne masu mu’amala da juna da yawa waɗanda ke kasancewa tare cikin gungu manya da ƙanana.

Kada dabbobin zamantakewa ne

An lura da halaye irin su matsayi da cin abinci a tsarin rukuni a yawancin nau’ikan kada. Babban namijin kada yana can saman a tsarin matsayi, kuma suna jin daɗin mafi kyawun wuraren zama. Matan kada koyaushe suna samun fifiko yayin ciyarwa a tsarin rukuni lokacin da gungu ko rukuni ya samu babbar dabba. An lura da wannan hali musamman a cikin kadojin Nilu da kuma kada nau’in Mugger.

Wannan tsari yana canjawa idan lokacin barbara ya fara, mazan suna zama a yanki ƙasa sosai kuma suna kare bakin kogi daga kutsawa daga masu abokan hamayya ta hanyar tayar da manyan kawunansu sama tare da yin ruri ga masu kutse. Lokacin da irin waɗannan ƙararraki suka ja hankalin ‘yanmatan kadojin Nilu, sai mazan sukan fara murza jikinsu har ma da harbin iska a cikin ruwa daga hancinsu.

Yadda kadoji ke sadarwa

Saɓanin sauran dabbobi masu rarrafe kadojin suna da ikon sadarwa da juna. Ya danganta da nau’in da ake magana, yanayin girma, jinsi, da hali ko yanayin da suke ciki, kada suna yin sauti iri-iri don sadarwa. Ga wasu sautukan gama gari da ma’anarsu:

Chirping

Lokacin da ƙwayayen kada ke shirin ƙyanƙyasuwa, ‘ya’yan kadar da ke cikin ƙwan suna yin wata irin hayaniya wanda hakan ke sa uwar ta ɗauki ƙwai a cikin ruwa da bakinta. Daga nan sai ƙwayayen suna ƙyanƙyasuwa a cikin ruwa, mahaifiyar kuma ta ajiye ‘ya’yan a cikin ruwa, tana ba su kariya da ciyar da su na wani lokaci.

Distress

Lokacin da matasan kada ke cikin haɗari ko kuma suka ji barazana, suna fitar da sauti mai ƙarfi wanda zai iya faɗakar da sauran kadojin yankin.

Hiss

Lokacin da kadoji suke so su tsoratar da wasu, ko dai kada ko wasu dabbobi da ganima, suna yin sauti mai kama da tsaki.

Mating call

Kadoji mata suna yin wani takamaiman sauti mai suna hatching call.

Bellowing

Kadoji maza suna yin wani sauti mai ban tsoro wanda ke haɗe da girgiza wanda ke haifar da hargitsi a cikin ruwa da girgiza a cikin ƙasa kanta. Wannan yawanci yana faruwa a lokacin yin barbara a cikin yanayin bazara. Hakazalika kuma suna amfani da wannan amo don tsoratar da sauran mafarauta da barazana a yankinsu.

Hankali da tunanin kada

Kadoji suna da lura sosai kuma suna nazarin halayen abubuwan da suke ganima da su sosai. Suna nazarin tsarin da aka saba da shi game da halayen dabbobin da ke zuwa shan ruwa kusa da mazauninsu. Wasu kadojin suna amfani da wasu dabaru don jawo tsuntsaye kusa da su su kama.

Kadaoji suna da haɗin kai wajen farauta. Suna yin cincirindo a kan manyan dabbobi, yayin da babban kada ya riƙe dabbar da aka kama wasu kuma sukan kashe ta ta hanyar tsaga ta. Haka kuma suna kama kifaye ta hanyar zagaye su rukuni-rukuni suna cafke su ɗaya bayan ɗaya.

Haihuwa da tsarin rayuwar kada

Bayan sun yi barbara, kada mace takan yi ƙwai tsakani 17 (gejerar kada), zuwa 100 (kadar yankin Nailu) a cikin wani irin muhalli da ya ƙunshi ƙasa da ciyayi kamar ganyaye, wanda ke hana kwan ya yi sanyi sosai idan gidan ya cika da ruwa a lokacin ƙyanƙyasa.A yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa, kada suna gina gidaje a kan tudu domin kiwo da kula da ƙwayaye daga hatsarin da ruwa kan iya haifarwa.

Lokacin ƙyanƙyasar yawanci yana ɗaukar kusan watanni 3 kafin ‘ya’yan su fito, wannan yakan dace da farkon lokacin damina don hana jikinsu bushewa. Duk da kasancewar su masu ban tsoro, kada mata suna da matuƙar kula, suna kare gidajensu sosai don kare ƙwayayen daga maharbi har sai sun isa ƙyanƙyasa. Da zarar ‘ya’yan sun fara fitowa, sai uwar ta taimaka musu zuwa ruwa ta hanyar ɗaukar su a cikin bakinta.
Yawanci, kadoji suna yin tsawon rayuwar da ya kai kusan shekaru 25 zuwa 75.

Abinci da ababen farauta

Kadoji dabbobi ne masu cin nama, ƙarfafa ne wajen kai hari kan abin farauta. Rashin iyawa ko damar tauna abinci ya haifar musu da wasu dabarun farauta da yin kwanton bauna tare da samun ƙaƙƙarfan muƙamuƙi da haƙora waɗanda suke amfani da su don yaga abinci.

Matasan kadoji sun dogara kacokan akan kifi a matsayin abinci, da ƙananan dabbobi masu shayarwa, tsuntsaye da dabbobi masu rarrafe, amma yayin da suke girma suna iya ɗaukar manyan nau’ikan ababen farauta da suka haɗa da, barewa, jakin dawa da dorinar ruwa.

Kadoji sun fi samun sukuni da kai kawo da daddare, wasu nau’ikan kadojin suna yawo sosai da kutsawa wurare don kama dabbobi da kuma a wasu lokuta, mutane.

Saboda yanayin zamantakewar su, kadojin yankin tafkin Nile (waɗanda galibi suna cin kifi), suna haɗuwa don datse kifin a sassan kogii lokacin da suke yin ƙaura. Catfish shi ne kaso mafi yawa a abincinsu.

Abubuwa masu ban sha’awa da fasali

Kodayake yawancin nau’ikan kada suna zaune a yankuna masu ruwa irin su fadama, koguna, da tafkuna, akwai nau’ikan da ke shiga cikin ruwa mai gishiri a kusa da bakin teku. Ana yawan samun kada a Amurka, a cikin tudu da magudanan ruwa da ke kusa da gabar teku.

A lokacin fari, sukan zurfafa cikin laka don hana jikinsu bushewa kuma ba za su ci komai ba har sai ruwa ya dawo. A wani bangare na duniya, an ga wasu kadojin esturine suna cin duwatsun da aka samu a bakin kogi. Ana tunanin wannan tsarin yana taimakawa wajen niƙa abincinsu, don haka yana taimakawa wajen narkewar abincin.

Amfanin sassan jikin kada

Fatar kada

Kamar yadda suke da girma, ana kiwon kada a sassa da dama na duniya, wanda ake sarrafa fatarsu zuwa tufafi, takalma, jakunkuna, belts, da dai sauransu. Fatar kada ta kasance abin nema sosai kuma tana da daraja a cikin manyan masana’antun ƙera kayayyaki a faɗin duniya.

Naman kada

Ana sarrafa naman kamar yadda ake ɗaukarsa a matsayin abinci mai daɗi kuma ana ci a ƙasashe daban-daban kamar China, Thailand, Cambodia, Korea, Philippines, New Zealand, Bahamas, har ma da Amurka.

Man kada

Ana fitar da kitse daga tantanin jikin kada kuma ana sayar da shi a matsayin mai. Ana yi amfani da shi sosai a maganin gargajiya a yawancin yankunan Asiya da Afrika. Ana amfani da shi wajen magance cutukan fata, gyaran raunuka da kuma kansar fata.

Manazarta

Ross, P, J., Wermuth, & Fritz, H. (2025, March 20). Crocodile | Habitat, Species, Diet, & Facts. Encyclopedia Britannica.

Ryan, M. (2024, October 22). Alligator vs. Crocodile: What’s the Difference? HowStuffWorks.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×