Skip to content

Kansar hunhu

Kansar hunhu ciwo ne da ke faruwa a lokacin da cututtuka suka cika ma’adanar iska a cikin hunhu wato (alveoli) haɗe da ruwa ko majina, tana haddasa wuyar numfashi a matsayin alamar farko. Yaran da ke ƙasa da shekaru biyu (2) da manyan da suka haura shekaru sittin da biyar (65) suna cikin haɗari mafi girma saboda raunin tsarin garkuwar jikinsu. Cutar kansar huhu nau’in kansa ce da aka fi yawan samu a fadin duniya. An kuma fi danganta shan taba sigari wajen haifar da cutar, amma kuma za ta iya kama waɗanda ba sa shan taba sigarin.

An fi danganta shan taba sigari wajen haifar da cutar kansar hunhu.

Kansar hunhu ta kashe mutane miliyan 2.5, ciki har da yara 672,000, a cikin shekarar 2019 kaɗai. Haɗarin tasirin cutar COVID-19 da sauyin yanayi da rikice-rikice suna haifar da matsalolin hunhu. Cutar tana jefa miliyoyin mutane cikin haɗarin kamuwa, a wasu lokutan har ma da mutuwa. A cikin shekarar 2021, kiyasin mace-mace daga cututtukan numfashi, gami da COVID-19, ya kai miliyan shida (6).

Alamomin gama-gari

Akwai alamomin kansar hunhu da yawa da ke bayyana bayan kamuwa da cutar, wasu alamomin na gama-gari na iya haɗawa da:

  • Kaki mai launin kore, rawaya, ko jan baki
  • Zazzaɓi, gumi, da jin sanyi
  • Numfashi da sauri ko numfashi marar tsayi
  • Ciwon kirji mai tsanani yakan kara muni ta hanyar zurfin numfashi ko tari
  • Rashin cin abinci, ƙarancin kuzari, da gajiya
  • Tashin zuciya da amai, musamman ga yara ƙanana
  • Rudani, musamman a cikin manya

Manyan alamomin kansar hunhu

Ba kasafai kansar hunhu ke saurin nuna alamu ba har sai ta girma a kusa da hunhun sannan ta ƙara bazuwa a sauran sassan jiki. Alamomin farko-farko na cutar kansar hunhu kan iya kasancewa yawan tari, da sarƙewar numfashi da kuma kakin jini. Haka nan ana iya samun wasu alamomi kaɗan kamar su ciwon baya, da ciwon kafaɗa har ma da ciwon gwiwa.

Har ila yau, alamomin cutar kan iya bambanta, wanda ya danganta da ko mace ce ko namiji ne ya kamu da ita, ko mai shan taba sigari ko kuma wanda bai taɓa sha ba, har ma da batun yawan shekaru. Kowa za iya kamuwa da cutar kansar, kuma ko ba tare da yin gwaji ba akwai buƙatar wayar da kai game da alamominta don gano cutar da wuri. Akwai alamomi da dama na cutar kansar da aka fi samu, duk da cewa za a iya danganta ta da wasu abubuwa.

Sarkewar numfashi

Wannan alama ce da mafi akasari ake dangantawa da cutar kansar hunhu, (musamman ma ga waɗanda ba su taba shan taba ba) A lokuta da dama ba a cika kulawa sosai ba, akan danganta hakan da tarin tsufa ko kuma kiba. Da zarar an fahimci cewa ana gaza yin wani aiki ko kuma da zarar an fara yi ana saurin gajiya, sai a yi saurin ganin likita. Wannan na faruwa ne a lokacin da cutar kansar ta fara tsanani, da dama waɗanda suka kamu da cutar kan fara ganin jini kaɗan na fita a cikin majina a lokacin da suka yi tari ko kaki.

Tari ba jinkirtawa

Tari a kodayaushe ba ƙaƙkautawa shi ne alamar da aka fi samu na cutar kansar huhu kuma zai iya kasancewa busasshen tari ko kuma mai majina, yakan faru a ko wane lokaci a rana. Mutane da dama kan yi watsi da yawan tari, su kan danganta shi da irin murar da aka saba yi lokacin sanyi, ko kuma kura da makamantansu. Ko kuma a rika tunanin tari ne na mai shan taba sigari. Sai dai duk tarin da ya wuce ‘yan makonni kan iya kasancewa alamar cutar kansar huhun.

Kumburi

Idan har cutar kansa ta ƙara tsananta ta kan haifar da kumburin fuska da na  kafaɗu har ma da wuya.

Ciwon kirji

Ciwon kirji kamar yadda ake bayyana shi da ciwon hunhu kan faru ne bayan mutum ya kamu da cutar kansar huhun, yawanci an fi samu a farko-farkon kamuwa da da cutar. Kuma wanda ya kamun kan riƙa jin zafi da kuma ciwo a zagayen mazaunin huhunsa, haka nan ciwon yakan kasance kamar yana fitowa daga cikin huhun ne.

Ciwon baya

Ko shakka babu ciwon baya kan faru a lokacin da mutum ya kamu da cutar kansar huhu, kuma yana dana cikin alamomin farko. Hakan na faruwa ne saboda tsiron da cutar ke yi a mazauni da kuma gefen huhun wanda kan bazu zuwa sauran sassan da ke kusa da koda. Matsalar

Mutanen da suka fi shiga haɗari

Kowane mutum na iya samun ciwon huhu, amma wasu mutane suna cikin haɗari mafi girma:

  • Yara da jarirai masu raunin garkuwar jiki
  • Manya tsofaffi tare da raunin tsarin garkuwar jiki
  • Masu juna-biyu
  • Mutanen da ke kan magungunan riga-kafi
  • Mutanen da ke da cututtukan da ke raunana tsarin garkuwar jiki (misali, ciwon daji, HIV, AIDS)
  • Mutanen da ke da cututtukan sanyi (misali, rheumatoid)
  • Masu ɗauke da wasu cututtukan hunhu kamar; (COPD), cystic fibrosis (CF), ko tarin fuka

Gwaje-gwajen matsalolin hunhu

Gwajin hoton x-ray zai ba likita damar ganin hunhu da zuciya da tasoshin jini na taimakavwa wajen gano matsalolin hunhu ciki har da kansar hunhun. Wasu ƙarin gwaje-gwajen na iya haɗawa da:

  • Gwajin Pulse oximetry da ake yi don auna matakan iskar oxygen a cikin jini.
  • Gwajin sputum, ana yin shi don bincika ruwan da ke cikin hunhu wanda kan haddasa kamuwa da cuta
  • Bronchoscopy don bincika hanyoyin da suka toshe ko wasu matsaloli.

Manazarta

BBC News Hausa. (2022, February 4). Ranar Kansa Ta Duniya: Cutukan kansa mafiya haɗari shida da suka kamata ku sani.

Edha Care. (n.d.). Alamun Ciwon Huhu | Nau’in Ciwon huhu

Gd-Admin. (n.d.). World Pneumonia Day. .

Katsina City News. (n.d.). KIWON LAFIYA; Lamoniya (Kangarewar Hakarkari) – Ciwon Huhu Mai Tsanani. Katsina Times.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×