Skip to content

Kansar mahaifa

Ciwon daji na mahaifa wani nau’in ciwon daji ne wanda ke farawa a cikin ƙwayoyin halitta (cells) na cikin mahaifa. Mahaifa ita ce gaɓar da ke jikin ƙashin ƙugu, mai siffar pear, wurin da ɗan-tayi ke girma. Cutar dajin kan kama bakin mahaifar mace, wato hanyar da ɗa ke fitowa daga mahaifarta.

Ciwon dajin yana farawa a cikin tantani da ƙwayoyin halitta (wato cells & tissues) waɗanda ke samar da tantanin rufin mahaifa, wanda kuma ake kira endometrium. Ciwon dajin wanda ake kira da endometrial a turance, wani lokaci ana kiran shi da kansar bakin mahaifa. Sauran nau’ikan ciwon daji na iya samuwa a cikin mahaifa, ciki har da sarcoma na uterine, amma ba su cika samuwa ba idan aka kwatanta da ciwon dajin mahaifa.

A yayin da aƙalla mata 8,000 ne suke mutuwa a Najeriya sakamakon kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa a duk shekara.

Ana kamuwa da ciwon dajin mahaifa sau da yawa a karon farko saboda yana haifar da alamomi da dama. Sau da yawa alamar farko ita ce zubar da jini na al’ada ba yadda aka saba ba. Idan an sami ciwon dajin da wuri, cire mahaifa ta hanyar tiyata sau da yawa yana warkar da shi. Duk da cewa sau da yawa ƙwayar cutar kan mutu da kanta kuma ba lallai ta jawo wasu alamomi ba a jiki, idan ta daɗe a jikin mace takan haifar da kansar bakin mahaifa.

Kansar bakin mahaifa ita ce cutar daji ta huɗu mafi shahara da ke kama mata. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce a shekarar 2018, an yi ƙiyasin mata 570,000 ne aka gano suna ɗauke da kansar bakin mahaifa a faɗin duniya kuma mata 311,000 ne cutar ta kashe. A yayin da aƙalla mata 8,000 ne suke mutuwa a Najeriya sakamakon kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa a duk shekara.

Hukumar Lafiya ta duniya WHO, ta ce kashi 99 cikin ɗari na matan da ke kamuwa da kansar bakin mahaifa na da ƙwayar cutar ‘human papillomavirus ko HPV’, wadda ƙwayar cuta ce ake saurin ɗauka ta hanyar jima’i.

Manyan alamomin kansar bakin mahaifa

Zubar jini ba na al’ada ba

Wannan na ɗaya daga cikin alamomin farko-farko da mace za ta gani. Akan ga jini kafin ko bayan al’ada ga matan da ke tsakanin shekaru haihuwa, wato dai a lokacin da ba su saba ganin jininsu na al’ada ba. Wannan jinin na iya zama da yawa ko kaɗan. Wani lokaci, jinin kan fara zuba ne da zarar an gama saduwa.

Ga matan da suka kai shekarun ɗaukewar al’ada ma, zubar jinin ne alama ta farko. Masana kiwo lafiya sun bayyana cewa idan mace ta kai shekarun ɗaukewar al’ada, ko yaya ta ga jini daga al’aurarta ta gaggauta zuwa asibiti saboda alama ce da ke nuna cewa akwai wata matsala. Sai dai ba ko yaushe ne wannan alama ke zama ta kansar bakin mahaifa ba.VAkwai cutukan da kan zo da irin waɗannan alamomin. Wata alama da dajin bakin mahaifa kan zo da shi iat ce ruwan da ke zuba daga al’aurar mace kan ƙara yawa fiye da yadda ta saba gani. Kuma wani lokaci ya kan zo da wari.

Ciwon mara baya da ƙafa

Idan kansar bakin mahaifa ta fara yaɗuwa sosai, mace kan ji ciwon ƙafa da ciwon baya da ciwon mara sosai. Wani lokaci ma ƙafa ɗaya ko duka ƙafafuwan biyu kan kumbura baya ga yawan ciwo da zugi. Wannan na faruwa ne idan cutar dajin ta danne wata jijiya da ke haɗe da ƙafa da mara da baya.

Haka kuma, akan ji zugi ko nauyi a mara daga ƙasan cibiya. Mata da yawa masu wannan cuta na bayyana yadda suke ji a mararsu kamar ana tsira masu wani abu mai tsini, sannan zugin kan daɗe wani lokaci kuma ya kan ɗauke sannan ya dawo.

Matsalar fitsari da bahaya

Wannan na iya haɗawa da jin zafi a lokacin yin fitsari ko bahaya. Wani lokaci kuma, fitsari ko bahayar kan fita daga jikin mace ba tare da saninta ba. Wato zai zamo ba ta iya riƙe fitsari da bahaya. Wannan na faruwa ne idan cutar dajin ta yi ƙamarin da har ta shafi ƙoda da mafitsara da hanji. Duk da dai ba a fiye ganin haka ba, kansar bakin mahaifa kan danne hanyoyin fitsari da bahaya har mace ta kasa yin kowanne daga cikinsu.

Jin zafi yayin jima’i

Kansar bakin mahaifa kan sa mace jin zafi ko raɗaɗi a lokacin saduwa. Wannan raɗadi na iya kasancewa a al’aura ko a mara. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, da zarar mace ta ji haka, ta garzaya asibiti ta bayyana wa likita damuwarta. Da yawa daga cikin waɗannan alamomi na bayyana ne idan cutar ta daɗe.

Dalilan da ke haifar da kansar bakin mahaifa

Babu wani tabbataccen dalilin da ke haifar da ciwon kansar bakin mahaifa. Abin da aka sani shi ne cewa wani abu yana faruwa ga ƙwayoyin halitta a cikin tantanin rufin bakin mahaifa, wanda ke canja su zuwa kwayoyin cutar kansa.

Ciwon dajin bakin mahaifa yana farawa ne lokacin da ƙwayoyin da ke cikin tantanin rufin mahaifa, wato endometrium, suka sami canje-canje a cikin DNA. DNA dai tantanin halitta ne, yana riƙe da sashen da ke sanar da tantanin halitta abin da ya kamata ya yi. Canje-canje suna shafar ƙwayoyin halitta (cells) su ninka sauri. Canje-canjen kuma har ila yau suna ba da dama ga ƙwayoyin halittar su ci gaba da rayuwa lokacin da ƙwayoyin cuta suka mutu. Wannan yana haifar da ƙarin ƙwayoyin halitta masu yawa. Kwayoyin na iya mamayewa tare da lalata lafiyayyen tantanin halittar jiki. A hankali kuma ƙwayoyin halitta na iya watsuwa su yaɗu zuwa wasu sassan jiki.

Abubuwan haɗari

Abubuwan da ke ƙara haɗarin ciwon dajin mahaifa sun haɗa da:

  • Canje-canjen yanayin hormones a cikin jiki. Manyan hormones guda biyu da ovaries ke samarwa su ne estrogen da progesterone. Canje-canje a cikin adadi na waɗannan hormones suna haifar da canje-canje a cikin a tsarin endometrium.
  • Cuta ko yanayin da ke ƙara yawan adadin esrogen a cikin jiki na iya ƙara haɗarin ciwon dajin mahaifa. Misalai sun haɗa da ƙiba da ciwon sukari da kuma tsarin ƙwayaye marasa daidaito, wanda zai iya faruwa dalilin ciwon ovary na polycystic. Shan maganin hormone wanda ya ƙunshi estrogen amma ba progesterone ba bayan al’ada yana ƙara haɗarin ciwon dajin mahaifa.
  • Wani nau’in ciwon daji na ovarian da ba kasafai ake samun shi ba, wanda ke samar da esrogen shi ma zai iya ƙara haɗarin ciwon dajin mahaifa.
  • Fara haila kafin shekaru 12 ko farkon ɗaukewar jinin al’ada yana ƙara haɗarin ciwon dajin mahaifa.
  • Idan ba a taɓa samun ciki ba, akwai haɗarin kamuwa da ciwon dajin mahaifa fiye da wacce ta sami ciki aƙalla sau ɗaya.
  • Tsufa, yayin da ake girma, haɗarin kamuwa da ciwon dajin mahaifa yana ƙaruwa. Ciwon dajin yana aukuwa sau da yawa bayan daina jinin al’ada kwata-kwata.
  • Ƙiba tana ƙara haɗarin ciwon dajin mahaifa. Wannan na iya faruwa saboda karin kitsen jiki na iya sauya adadin hormones ɗin jiki.
  • Shan maganin maganin hormone tamoxifen don ciwon nono na iya ƙara haɗarin kamuwa da ciwon dajin mahaifa.
  • Ciwon gado wanda ke ƙara haɗarin cutar kansa. Ciwon daji na Lynch yana ƙara haɗarin ciwon daji na hanji da sauran cututtuka, ciki har da ciwon dajin mahaifa. Ciwon daji na Lynch yana haifar da canjin DNA wanda ke yaɗuwa daga iyaye zuwa ‘ya’ya. Idan an gano wani a cikin iyali yana da ciwon Lynch, sai a tuntuɓi masana kiwon lafiya domin ɗaukar matakan kariya.

Riga-kafin ciwon dajin mahaifa

  • Wannan ciwo yana da wuyar sha’ani kuma yana addabar dubban mata, don haka akwai wasu hanyoyin riga-kafi da suka haɗa da:
  • Bin shawarar ƙwararrun likitoci dangane da amfani da maganin hormones musamman bayan daina jinin al’ada.
  • Idan ana buƙatar yin amfani da maganin hormone don taimakawa wajen sarrafa alamomin bayyanar haila, a nemi shawarar likita.
  • Maganin hormone wanda ya haɗu da estrogen da progesterone zai iya rage wannan hadarin.
  • Yin amfani da maganin hana haihuwa na baki na aƙalla tsawon shekara ɗaya na iya rage haɗarin ciwon dajin mahaifa. Maganin hana daukar ciki na baka magungunan ne da ake sha a sigar ƙwayar. Ana kuma kiran su magungunan hana haihuwa. Ana tsammanin raguwar haɗarin zai ɗauki shekaru da yawa bayan an daina shan maganin. Sai dai kuma wannan magani yana da illa, don haka a nemi shawarar ƙwararrun likitoci.
  • Matsananciyar ƙiba da nauyi suna ƙara haɗarin kamuwa da ciwon dajin mahaifa, don haka idan kana buƙatar rage nauyi da ƙiba, sai a ƙara yawaita motsa jiki kuma a rage adadin adadin sinadarin kuzarin da ake ci kowace rana. (carbohydrates)

Manazarta

BBC News Hausa. (2021, November 17). Alamomi 4 na kansar bakin mahaifa.  BBC Hausa

NHS inform. (2024b, October 9). Womb (uterus) cancer  NHS Inform.

Mayo Clinic (n.d). Endometrial cancer – Symptoms and causes.

Saleh, S. K. (2024, May 8). Cutar Kansar Bakin Mahaifa Na Kashe Mata 8000 a Najeriya. Aminiya.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×