Skip to content

Kanwa

Kanwa wani farin sinadari mai ɗan kauri da ake samu daga tafkunan ruwa masu ɗanɗanon gishiri ko kuma daga wasu nau’ikan duwatsu. Ana amfani da ita a fannoni da dama na rayuwa, musamman a girki, magani, da gyaran fata. Kanwa suna ne da ake kiran rukunin ma’adanan ƙasa ko sinadarai da ke ƙunshe da sinadarin gishiri ko kuma wani ɗanɗano wanda ke gina jikin tsirrai.

3 450
Kanwa.

A Hausance kanwa tana nufin tushen toka ko gishiri mai kama da toka da ake amfani da shi a girki ko magungunan gargajiya. Wanda ake samunta daga ƙonawar wasu tsirrai ko kuma daga wasu ma’adinai. Kanwa tana da matuƙar amfani a rayuwar yau da kullum, musamman a al’adar Afirka.

Ire-iren kanwa

Kanwa ta kasu zuwa kaso uku. Wanda duk wannan rukunan guda uku ana amfani da su ta hanyoyi mabambanta wanda suka haɗar da:

Farar kanwa

Ita ce kanwar da take da yanayi kamar ƙasa ko kuma taɓo. Wata tana da haske wata kuma tana da duhu. Sannan tana da yanayin a dunƙule kamar yanayin dutse, amma kuma ba ta cika girma ba. Sannan tana da sauƙin tauri da ake iya wargazata ko da da hannu. Wasu lokutan tana kasancewa kamar gari. Ita ce aka fi amfani da ita wurin yin tuwon dawa ko kuma ɗan wake. Wanke wani abu domin fitar da datti.

Akwai farar kanwa wadda ake kawo ta daga garin Naija, a tarayyar Najeriya. Kanwar fara ce tas kamar yanayin kalar yadda gishiri yake sai dai kuma yanayinta guda-guda ne kamar yadda sukari yake amma ta fi sukarin girma. Kanwa ce mai ƙarfin gaske duk ta fi sauran nau’in kanwa ƙarfi da kuma aiki cikin sauri.

Kanwa ungurnu

Ita ma ungurnu yanayinta kamar dutse yake, sai dai kuma tana da tauri da sai an yi amfani da wani abu sannan take wargazuwa. Tana da yanayin ƙyali a wasu lokuta. Wata kuma ba ta da shi. Sannan tana da karci-karci a jikinta. Wata kuma jikinta yana kasancewa suluf, ma’ana da santsi. Amma a dunƙule take kamar dutse. Ita ce aka fi amfani da ita wurin dafa wake, ko kuma jiƙawa yayin murɗawar ciki.

Jar kanwa

Yanayinta ɗaya da kanwa ungurunu, sai dai kuma ita a mafi yawancin lokuta akan sameta da faɗi. Kuma ba ta zuwa da girma kamar na ungurunu. Akasari ita ƙanana take zuwa. Ma’ana ana samun mai kamar dutse amma kuma akwai mai faɗi, sannan yanayinta yana da kalar ja a wasu lokutan ko kuma hoda-hoda haɗe da launin fari.

Asalin kanwa

Idan aka ce asalin kanwa ana nufin asali ko tushen da wannan sinadari ya samo asali. Asalin kanwa na samuwa ne daga:

Haƙowa daga ƙasa

Ana samun kanwa daga ƙasa, musamman a wuraren da ke da sinadarin sodium carbonate ko potassium carbonate. A Najeriya, ana samun ta a yankunan kamar Borno, Yobe da Adamawa.

Daga tafkuna masu ɗanɗanon gishiri

Ana samun wasu nau’ikan kanwa suna fitowa daga tafkunan da suka ƙafe, yayin da ruwa ya bar sinadarai masu ɗanɗanon gishiri.

Daga dabbobi ko tsirrai

A wasu yankuna na duniya, ana samun wasu nau’ikan kanwa daga tarkacen tsirrai ko kashi da ba ya ƙonewa gaba ɗaya. Ana samun kanwa daga tarkacen shuke-shuke da kashin dabbobi a Yammacin Afirka, musamman a Najeriya, Nijar, Ghana, da Mali. A waɗannan yankuna, ana samar da kanwa ta hanyar:

  • Ana tara tarkacen shuke-shuke kamar ganyen dawa, gero, ko zogale, da kuma kashin dabbobi kamar na shanu ko tumaki.
  • Ana ƙone tarkacen shuke-shuke da kashin dabbobi domin a samu toka.
  • Ana wanke tokarnan da ruwa domin fitar da sinadaran alkaline kamar potassium carbonate da sauran nau’in gishirin kanwa.
  • Ana tace ruwan sannan a tafasa shi har sai ya ƙone, a haka ake samun kanwa mai tsafta da inganci.

Wannan hanya ta samar da kanwa ta dabbobi da shuke-shuke ta fi shahara a yankunan da babu ma’adanan kanwa kamar na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya (Misali: Borno da Yobe) inda ake samun kanwa kai tsaye daga ƙasa.

Ƙasashen da aka fi samun kanwa

Akwai ƙasashe da dama da ake samun kanwa kuma mabambanta. Wanda suka haɗa da ƙasasshen ƙetare musamman waɗanda ke da manyan wuraren da ke da albarkatun ma’adinai. A yawancin lokuta, ana samun kanwa a yankunan da ke da tsoffin tafkuna ko gishirin ƙasa. Ƙasashen da ake fi samun kanwa sun haɗa da: Najeriya, Chadi, Nijar, Mali, Sudan, Masar, Indiya, China, Mexico da, Amurka.

Adadin kanwar da wasu ƙasashe suke fitarwa

  • China – tan 7,195,10
  • Canada – tan miliyan 21,97,531
  • Rasha – tan miliyan 13,81,620
  • Isra’ila – tan l3,830,5
  • Canada tana fitar da kashi 31 na kanwar da ake cinikayayya a duniya duk shekara zuwa 2020.
  • Belarus – tan miliyan 12,205,17

Sinadaran da ke cikin kanwa

Kanwa tana ɗauke da sinadarai da yawa, ciki sun haɗar da:

  • Potassium carbonate
  • Sodium bicarbonate
  • Calcium carbonate

Abubuwan da ake sarrafawa da kanwa

  • Kashi 95 cikin 100 abubuwan da ake samarwa da kanwa a fannin masa’antu shi ne haɗa takin zamani.
  • Sinadarin potassium da ke cikin kanwa kan gina jikin tsirrai, da ba su garkuwa daga cutuka, da alkinta ruwa a jikinsu.
  • Akan yi amfani da kanwa ƙalilan wajen samar da kayayyaki masu ƙunshe da sinadarin na potassium kamar:
  • Tangaran da tukwane
  • Ƙwayoyin magani
  • Garin sabulu
  • Sinadaran tsaftace ruwa

Amfani kanwa ga lafiya

Kanwa na da amfani ga lafiyar jiki idan aka yi amfani da ita yadda ya dace. Ga wasu daga cikin fa’idodinta ga lafiya:

  • Kanwa na taimakawa wajen narkar da abinci cikin sauƙi, tana hana kumburin ciki da yawan gas.
  • Ana amfani da kanwa a maganin gargajiya don rage ciwon ciki, musamman wanda ke da alaƙa da ciwon gyambon ciki ko zafin da gas ke haifarwa. Kamar hana ƙwarnafi ko kuma magwas.
  • Wasu mutane na amfani da kanwa domin rage ƙiba saboda tana taimakawa wajen narkar da kitse a jiki.
  • Kanwa na ɗauke da ma’adanai kamar calcium da potassium, waɗanda suke taimakawa wajen gina ƙashi da haƙora masu ƙarfi.
  • Ana amfani da kanwa wajen wanke fata domin rage ƙaikayi, kuraje, da sauran matsalolin fata.
  • A wasu lokuta, shan ruwa da kanwa yana taimakawa wajen rage ciwon kai da gajiya, musamman ga masu fama da rashin isasshen sinadarin potassium a jiki.
  • Wasu mata na amfani da kanwa don rage ciwon mara da rashin jin daɗi lokacin al’ada.
  • Kanwa na da matuƙar amfani ga fata, musamman a magance matsalolin fata. Ga wasu daga cikin amfaninta ga fata:
  • Kanwa na taimakawa wajen busar da ƙuraje da rage ƙaikayi saboda tana da sinadarai masu kashe ƙwayoyin cuta a fata.
  • Idan aka yi amfani da kanwa da ruwa ko sabulu, tana taimakawa wajen cire dattin fata, tana sa fata ta yi haske da laushi.
  • Idan aka haɗa kanwa da ruwan wanka, tana rage warin jiki saboda tana kashe ƙwayoyin cuta da ke haddasa wari.
  • Idan aka haɗa kanwa da man zaitun ko man kwakwa, tana taimakawa wajen moisturize ɗin fata, tana hana ta bushewa.
  • A maganin gargajiya, ana amfani da kanwa don wanke fata daga cututtuka kamar eczema da fungal infections.
  • Ana amfani da kanwa a wasu magunguna na gargajiya, musamman don narkar da abinci da rage zafin ciki.

Amfanin kanwa a girke-girke

Kanwa tana da amfani sosai a girki, musamman a cikin girkin gargajiya na Afirka. Ga wasu daga cikin amfaninta:

  • Idan aka saka kanwa a cikin nama yayin dafa shi, yana taimakawa wajen taushar sa da sauri. Ma’ana ya dahu ya kuma yi laushin da ake buƙata.
  • Kanwa na taimakawa wajen narkar da abinci, musamman abincin da ke da nauyi kamar wake.
  • Wasu nau’ikan abinci kamar kunu ko tuwo suna iya samun ɗan ɗaci ko tsami, amma idan an saka kanwa kaɗan, tana rage wannan ɗacin ko tsamin.
  • Tana sa abinci kamar fura ko waina ya zama mai laushi da kuma haske.
  • A girkin abinci irin su alkaki da ƙosai, kanwa na ƙara wa abinci ƙwari da ɗanɗano mai daɗi.
  • Ana amfani da kanwa wajen daka ko niƙan gero da dawa don samun garin kunu mai kyau.

Amfanin kanwa ga masana’antu

Kanwa na da matukar amfani a masana’antu daban-daban saboda sinadaranta masu ƙarfi. Ga wasu daga cikinh muhimman amfaninta:

  • Ana amfani da kanwa wajen sarrafa sabulu, saboda yana taimakawa wajen haɗa sinadarai da ƙarfafa sabulu.
  • Kanwa na ɗauke da sinadaran da ke taimakawa wajen ƙarfafa girbin amfanin gona, don haka ana amfani da ita wajen ƙara sinadarai a takin zamani.
  • Ana amfani da kanwa wajen shirya fata don yin takalma, jaka, da sauran kayan fata. Tana taimakawa wajen cire gashi da laushin fatar.
  • Kanwa na taimakawa wajen tacewa da tsaftace ƙarfe, musamman a masana’antun da ake sarrafa zinariya da azurfa.

Matsalolin da kanwa ke haifarwa

Duk da cewa kanwa tana da amfani sosai, amfani da ita da yawa ko ba daidai ba na iya haifar da matsaloli ga lafiya. Ga wasu daga cikin matsalolin da kanwa zata iya haddasawa:

  • Idan aka sha kanwa da yawa, tana iya haifar da ciwon ciki ko kumburin ciki
  • Idan aka yi amfani da ita da yawa, maimakon taimakawa, tana iya haddasa matsala a tsarin narkewar abinci.
  • A wasu mutane, kanwa na iya haddasa gudawa ko amai idan aka sha fiye da kima.
  • Kanwa tana ɗauke da wasu sinadarai da ke iya kara yawan gishiri a jiki, wanda ke iya haddasa matsalar hawan jini.
  • Yawan amfani da kanwa na iya haddasa cututtukan ko dan saboda yawan sinadaran da ke cikinta.
  • Mutanen da ke fama da ciwon gyambon ciki (ulcer) bai kamata su sha kanwa ba, domin tana iya kara musu matsala.
  • Idan aka yi amfani da kanwa da yawa a wanka, tana iya busar da fata ta haddasa ƙaiƙayi.
  • Idan aka sha kanwa da yawa, tana iya rage ƙarfin haƙora saboda sinadarin da ke cikinta.
  • Idan aka sa kanwa fiye da kima a abinci, zai iya sa abincin ya yi wari ko ya rasa kyau.
  • A wasu nau’in abinci, yawan kanwa na iya rage wasu sinadaran gina jiki da ke cikin abincin.

Hanyoyin kariya

  • Kada a yi amfani da ita fiye da ƙima, musamman a girki ko magani.
  • Masu hawan jini ko ciwon ciki su guji yawan amfani da ita.
  • A dinga shan ruwa sosai idan an sha kanwa don kauce wa bushewar jiki.
  • Idan an lura da wata matsala bayan amfani da ita, a dakata ko a tuntuɓi likita.

Manazarta

Okpala, B. (n.d.). BENEFITS OF KAUN POTASH (AKANWU). Global Food Book.

BBC News Hausa. (2022b, July 2). Shin kanwa na da amfani a jikin ɗan Adam?  BBC Hausa.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa
<p>You cannot copy content of this page</p>