Skip to content

Karin magana

Share |

Ma’anar karin Magana

Farfesa dangambo a shekara ta alif (1984), da ya ce, “Karin magana dabara ce ta dunkule magana mai yawa a cikin zance ko kuma dan kalmomi kaɗan, cikin hikima”.

Karin magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da ma’ana gamshasshiya, mai faɗi, mai yawa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki, ashe ke nan karin magana taƙaitacciyar magana ce ‘yar ƙil wadda ta ƙunshi hikima da zantuttukan ma’ana.

Asalin karin magana

Karin maganganu sun fito ne daga cikin rayuwar al’umma, shi ya sa suka ƙunshi yawancin abubuwan da suka shafi ɓangarorin rayuwar al’umma. Haka kuma ba harshen Hausa ba ne kawai yake amfani ko ya mallaki karin magana ba. A’a sauran harsuna ma suna da tasu dabarar ta sarrafa magana cikin hikima.

karin magana

Kodayake harsunan mutanen duniya sun bambanta, amma a wajen yin azancin karin magana suna da baiwa iri ɗaya, sai dai yadda ake tsara karin maganganun ne yake canzawa daga wannan harshen zuwa wancen.

Hanyoyin ƙirkira

Yana da wuya matuka a ce ga mutumin da ya ƙago karin magana, a lokaci kaza ko a wuri kaza, ko kuma saboda dalili kaza, amma a iya cewa naso ne na al’adu da dabi’un Hausawa ya samar da karin maganganu.

Sauye-sauyen zamani da shuɗewar al’umma ke saka juyawar karin magana ta hanyar mantawa da wasu, ƙirƙiro sababbi. Aukuwar abubuwa a rayuwa suke taimaka kirkirar karin magana.

Ana jin mutanen da suke yin karin magana da ƙirƙirar sababbi su ne:

  • Mata
  • Maroka da makada
  • Makada
  • Yan Daudu

Bayan haka, karin magana ya kan zo cikin labaru da zantuka da waƙe-waƙe da sauransu.

Amfanin gajerce magana na da yawa, daga ciki ta yiwu akan yi haka ne saboda rashin isasshen lokacin magana ko dan yin hannunka mai sanda da fadakarwa, ko don fito da so ko don ƙin abu, karin magana a mafi yawanta kukan kurciyane inda yakan sanya magana ta yi armashi da dadi kamar an zuba kafi-zabo a miya, sannan akan nuna gwaninta da naƙaltar harshen mai magana ga kuma rashin kawo kosawar mai sauraro.

Matsayin karin magana

Matsayin karin magana a harshen Hausa yakan ƙara wa zance daɗi da armashi sannan ya nuna zalaƙa da iya zurfin tunani da balaga da ƙwarewar mai zance. Haka kuma karin magana na bayyana wasu sassan rayuwar Bahaushe zunzurutunta.

Mahimmancin karin magana

Karin magana ya danganci abubuwa da yawa tamkar al’adun da tarihi da fasaha da hikimomin hausawa.

Ku san karin magana komai da rayuwanka ne ya kan yi katsalandan a duk cikin ɓangarorin rayuwa.

Yakan ayyana falsafar Hausawa dangane da wasu abubuwa da suka shafi rayuwa kamar arziki da alheri da ilimi yana taimakawa ƙwarai wajen kyautata tarbiya yadda za a gina halaye nagari.

Karin magana yakan daidaita ɗabi’un mutane ya kyautata zumunta ga shi kuma kotun tafi-da-gidanka ne wajen bayyana matsayin abu sannan taƙaita zance da ƙara masa armashi.

Sauye-sauyen karin magana

Karin magana ya sami ci gaba da bunƙasa dangane da sauye-sauyen zamani da rayuwa a kowanne yanayin zamani akan sami karin maganganun da suka dace da shi.

Dubi karin maganar nan da aka ce: “Duniya juyin-juyi, kwaɗo ya faɗa ruwan zafi” k“Zamani riga, kowane da tasa”

Sun yi nuni ne da abin da ake magana na cewa a kowane zamani za a sami karin maganganun da suka da dace da shi.

Ga wasu misalan karin maganganu dangane da lokuta.

Lokacin maguzanci:

  • Kiɗa a ruwa mai ta da haukan dodo
  • Duk Dodo ɗaya ake yi tsafi.

Lokacin Addinin Musulunci:

  • Gobara daga kogi magani nata Allah
  • Kaza tara ta isa layya, sai fa in fata ake so

Lokacin zuwan Turawa:

  • Da sauran lokaci, ɗan sakandare ya ga mai vespa
  • Allah ya kiyaye, siniya sabis ya yi mafarki ya zama gyartai

Nau’o’in karin magana:

Inda aka dubi siga ko ma’anar karin maganganu za a iya rarraba su kamar haka:

Mai tambaya da amsa

  • Mu na wasa ne? Gwari ya ba da magani an sha an mutu.
  • Ya na iya da raina? Mummuna ya ga mata.

Mai labari

  • Rufin kan uwar Daɗi(gabanta babu kariya)
  • Jifan gafiyar Ɓaidu

Mai in ji

  • Ala sutura buƙul,in ji kishiyar mai doro.

Mai an ce

  • Idon da wari, an ce wa makaho ga ido.
  • Har ka tuna mini an ce wa mahaukaci ba ka duka.

Mai “Da” da “An”

  • Da sanin ango, an yi wa yan biki duka.
  • Da alamar zaƙi, an ba bera ajiyar angurya.

Mai tsarin Ba… Ba Ko Mai ”Ba… Sai”

  • Ba wahalalle, sai mai kwadayi.
  • Yaro ba mutum ba, sai ya girma.
  • Ba don tsaho akan ga wata ba.

Mai akan

  • Da ruwan ciki akan ja na rijiya.
  • Ana bukin duniya akan na ƙiyama.

Mai ya fi ko ta fi

  • Zuwa da Kai, ya fi sako.
  • Karamin goro, ya fi babban dutse.

Mai ba ya ko ba ta

  • Zomo baya kamuwa daga zaune.
  • Banza Ba ta kai zomo kasuwa.
  • Kifin fadama ba ya gasa da gulbi.

Mai kowa

  • Kowa ya bar gida,gida ya bar shi.
  • Kowa ya ci tuwo dani,miya ya sha.

Mai nasiha:

  • Sannu bata hana zuwa.
  • Hana wani hana kai.

Mai habaici

  • Ko ba a gwada ba,linzami ya fi karfin bakin kaza.
  • Mai tsoron ta mutu,shi yake maho.

Mai Hausawa sun ce

  • Tsoro na daji, kunya na gida.
  • Ana ta kai, wa ke ta kaya.

Wasu daga cikin karin Maganar kai tsaye

  • Sara da sassaƙa, ba ya hana gamji toho.
  • Shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne.
  • Talaka baya tashin talaka, sai tashin talaka ya zo.
  • Tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe.
  • Tsuntsu duka tsuntsu ne.
  • Tura ta kai bango.
  • Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho.
  • Wane kare ne ba bare ba?
  • Wayo ya san na ƙi.
  • Wayon a ci, an kori kare daga gindin ɗinya.
  • Yaro bari murna, karenka ya kama zaki.
  • Yaya gara takan yi da dutse? Sai kallo.
  • Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana muzuru ana shaho sai ya yi.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading