Kasuwancin yanar gizo ko intanet, wanda aka fi sani da (e-business ko online business ko e-commerce) a Turance, kasuwanci ne kuma hanyar saye da sayarwa ce ta kafar sadarwar intanet. Wato kasuwanci ta kafar intanet wata fasaha ce da ke ba da damar gudanar da ma’amaloli, s da kayayyaki ko ayyuka, da yin hulɗa tare da abokan ciniki.
Kasuwancin intanet ya ƙunshi
1. Shagunan yanar gizo (online store)
2. Kasuwannin yanar gizo (marketplace)
3. Ayyukan yanar gizo (consulting, online tuition)
4. Ƙirƙirar kayayyaki (misali software, littafan e-books)
5. Koyarwa ta intanet
6. Tallace-tallace ta intanet
7. Tsare-tsare da gudanarwa ta intanet
8. Kafa kungiyoyi ta yanar gizo
9. Kafofin watsa labarai na da nishaɗi
Kasuwanci ta kafar intanet na da sauƙi kuma ya game duk duniya. Ya mayar da harkokin saye da sayarwa masu ban sha’awa ga ‘yan kasuwa da ƙananan kasuwanni. Haka nan fasahar kasuwancin na da matakai na atomatik, wato tsarin da na’ura mai ƙwaƙwalwa za ta yi aiki maimakon mutum, misali rage farashi, da bunƙasa aiki. Fasahar dai na samun farin jini da karɓuwa ga masana’antu da yawa.
Muhimman ɓangarorin kasuwancin intanet
1. Shagon nanar gizo: Shagon intanet ko yanar gizo waje ne ko dandamali wanda ke nuna kayayyaki ko ayyuka da farashinsu.
2. Abubuwan cikin shagon: Rubutu ne da hotuna da bidiyo da sauran bayanai waɗanda ke bayyana nagarta da ingancin kayayyakin tare da farashinsu ga abokan ciniki.
3. Kasuwanci: Wannan sashen ya haɗa da dabarun jawo hankalin abokan ciniki dangane da kayayyaki da ayyukan da ake aiwatarwa.
4. Tsarin biyan kuɗi: Akwai kyakkyawan tsarin aiwatar da biyan kuɗi da ma’amaloli cinikayya cikin aminci da nagartattun manhajoji, (misali, PayPal, Stripe).
5. Tsarin isar da kaya ga mai saye: Wannan tsari ne don isar da kayayyaki ko ayyuka ga abokan ciniki cikin sauƙi da kuma gamsarwa.
6. Sauraron abokin ciniki: Wannan bangare ne na taimaka wa abokan ciniki ta imel ko hira ko waya, a yayin da suke da ƙorafi ko tambaya kan wasu abubuwan da suka shige musu duhu.
7. Bin diddigi: Na’urorin aiki ne don bin diddigin zirga-zirga a shafukan yanar gizo da tallace-tallace da kuma halayen abokin ciniki (misalin irin wannan na’ura ita ce, Google Analytics).
8. Tsaro: Wannan bangare ya ƙunshi matakan kare bayanan abokin ciniki da kuma hana zamba da damfara.
9. Tsarin shari’a: Wajibi ne a yi rijistar kasuwanci don samun lasisi, da yarjejeniyoyin dokoki (misali, sharuɗɗa da manufofi keɓantattu).
10. Ayyuka: Wannan ɓangare ne da ya ƙunshi ayyukan yi waɗanda ci gaba ya mayar da su ta intanet kamar neman shawara, koyarwa, ko wani aikin mai zaman kansa.
Waɗannan ɓangarorin suna aiki tare don tabbatar da ingancin kasuwancin yanar gizo.
Nau’ikan kasuwancin yanar gizo
1. E-commerce: Nau’in kasuwancin yanar gizo ne da ya ƙunshi shagunan onlayin da ke sayar da kayayyaki, (misali Bakandamiya Shopping).
2. Consulting Services: Wannan nau’in kasuwanci ne da ke aiwatar da aikace-aikace, wato ba kaya ba ne ake sayarwa. Aiki suke yi wa mutane, (misali, ba da shawara consulting, koyarwa tuition).
3. Digital product creation: Kasuwancin yanar gizo ne na kirƙira da sayar da kayayyaki (mislai littafan e-books, darusa, manhajoji, ko wasu nau’ikan kayan daban).
4. Online education: Wannan ma kasuwanci ne na yanar gizo da ke kirkira da koyar da kwasa-kwasai ta kafar intanet. Ana koyar da ɗimbin ilimai ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo a bisa matakai daban-daban na ilimi.
5. Online forum: Samar da wata kungiya ko dandalin don aiwatarwa wani aikin haɗaka na jama’a.
6. Podcasting: Wannan ma nau’in kasuwancin yanar gizo ne da ke ƙirƙira da sarrafa bayanan sauti domin taimaikawa ko tallafawa wajen yin tallace-tallace ko bayar da damar sauraro.
Fa’idojin kasuwancin intanet
1. Ci gaban duniya: Babu shakka an samu cigaba ta fuskar kasuwanci ga duniya, fasahar na isa ga abokan ciniki a duk inda suke a duniya kodayaushe, ba dare ba rana.
2. Sauƙi: Ana iya yin kasuwanci ta yanar gizo daga ko’ina tare da haɗuwa ba, wannan ya sauƙaƙawa al’umma sosai.
3. Ƙarancin farashin farawa: Akwai rangwamen kashe kuɗaɗe da yaw yayin farawa idan aka kwatanta da kasuwancin gargajiya. Misali, Malami mai koyarwa, baya buƙatar sai ya samu aji na zahiri da sauran kayan aikin koyo da koyarwa.
4. Automatik: Akwai na’urorin da ke gudanar da ayyuka da kansu kuma kodayaushe tamkar ɗana’dam, hakan na rage yawan kuɗin da ake kashewa don tafiyar da kasuwanci.
5. Ƙarinsamun kuɗin shiga: Akwai kuma damar samar da kudaden shiga ta hanyoyi daban-daban (misali, ɗora tallace-tallace).
6. Rage kashe kudaden: Misali, a kasuwancin yanar gizo babu buƙatar mallakar shaguna ko ma’ajiyar kaya, ko kayan aiki na zahiri.
7. Tattaunawa da abokin ciniki: Kasuwancin yanar gizo na ba samar yin hulɗa tare da tattaunawa da abokan ciniki ta hanyoyi daban-daban na kafafen sadarwa na zamani.
8. Saurin tallatawa: Babu shakka akwai saurin bayyanarwa da ƙaddamar da sabbin kayayyaki ko ayyuka ba tare da iyakancewar ƙasa ba ko yanki ba.
9. Tabbatuwa: Kasuwancin yanar gizo yana bayar da damar yin aiki kuma a ci gaba da yi kodayaushe ba tare da ƙayyade wasu sa’o’i ba kamar yadda yake a kasuwancin gargajiya.
Ƙalubalen kasuwancin intanet
1. Gasa: Akwai gasa kuma mai tsanani tsakanin masu hulɗar cinikayyar yanar gizo, mutane da dama kan shiga cikin kasuwanci iri ɗaya.
2. Matsalar Tsaro: Ana samun matsalolin tsaro misali, hare-haren yanar gizo, keta bayanai, da zamba ko damfara ta yanar gizo.
3. Matsalolin na’ura: Lalacewar ko dakatawar wasu manhajoji da sauran matsalolin fasaha na iya tasiri ga harkokin kasuwancin yanar gizo.
4. Ƙarancin masu saye: Rashin huduwa gaba da gaba ko ganin fuska da fuska, na haifar da rashin fahimta, kuma a dalilin haka wasu mutanen kan ƙaurace wa tsarin kasuwancin yanar gizon gabaɗaya.
5. Ƙalubalen Amana: Tabbatar da gaskiya da amana tare da abokan cinikin a yanar gizo abu ne mai wahalar gaske.
6. Satar fasaha: Akwai ƙalubalen wahalar kare haƙƙin mallaka.
7. Dogara ga Fasaha: Harkokin kasuwancin intanet na iya fuskantar matsaloli sosai ta hanyar gazawar fasaha.
8. Matsalar harshe: Sadarwa da bambancin harshe na iya haifar da rashin fahimta.
Hanyoyin magance matsalolin kasuwancin yanar gizo
1. Bunƙasawa: Bambance kasuwancinku ta hanyar haɓaka ayyuka da nuuna gogewa ta musamman. Mayar da hankali kan kasuwanci da manufa, tare da sauraron ƙorafin abokan ciniki.
2. Hatsarin Tsaro: Samar da ingantattun matakan tsaro kamar takardun shaida da lasisi. Sabunta manhajoji akai-akai, da yin amfani da sanannun ƙofofin biyan kuɗi da kayan aikin gano zamba ko damfara.
3. Batun Fasaha: Zuba jari a cikin amintattun kafafen yanar gizo da abubuwan more rayuwa. Ajiye bayanai akai-akai tare da amfani da kayan aikin sa ido na yanar gizo don gano al’amura da sauri.
4. Inganta hulɗa da abokan ciniki: Yin amfani da allon bidiyon ga-ni-ga-ka,(video conferencing) da yin hira kai tsaye, ko kiran waya don tattaunawa da abokan ciniki. Haɓaka abubuwan da ake wallafawa a shafukan yanar gizon su zama masu jan hankali.
5. Tabbatar da amana: Nuna shaidar abokin ciniki, tare da bayar da tsare-tsare da bayanai na jigilar kayayyaki. Bayyanar da takardun shaida na tsaro.
6. Kare dukiya: Yin rijistar kasuwanci da haƙƙin mallaka, tare da saka idanu don hana cin zarafi da kuma ɗaukar matakin doka idan ya cancanta.
7. Dogara ga Fasaha: Rarraba kasuwancinku ta kafofi da tashoshi da yawa. Ɗaukar nauyin horar da ma’aikata. Yin bincike tare da tabbatar yin amfani da sabbin fasahohin zamani.
8. Harshe da al’adu: Yin amfani da manhajojon fassara da ke fassara harsuna da yawa kuma ingantacciyar fassara. Haɓaka abubuwan da ke da alaƙa da al’adu da dabarun talla.
Ta hanyar magance waɗannan ƙalubalen, kasuwancin yanar gizo na iya rage haɗari, kuma a samu amana da yarda tsakanin mai saye da mai sayarwa.
Manazarta
Shopify (2024, June 20). 25 best online business ideas for 2024. Shopify.
SCAYLE GmbH. (2024, June 5). Enterprise Evolutions: The best eCommerce Features | SCAYLE. SCAYLE.
Hashemi-Pour, C., & Lutkevich, B. (2023, December 13). e-commerce. CIO.
Mailchimp. (n.d.). E-Commerce: Advantages and Disadvantages Mailchimp.