Skip to content

Kudaden cryptocurrency

Share |

Cryptocurrency wasu kudade ne da ake cinikayya da su a yanar gizo. Kamfanoni daban-daban ne suka kirkiri na su, wadanda yawanci ana amfani ne da su domin sayyaya a wajen wadannan kamfanoni da suka kirkire su kawai. Su irin wadannan kudade mutum ba ya mallakarsu sai an biya kudi, wato sai an canza su da asalin kudi da muka sani. Misali ka ciri kudinka na naira ka sayi wannan kudin domin samun daman mallaka da kuma amfani da shi. Shi wannan tsarin yana amfani ne da wani fasahar taknoloji mai suna blockchain.

Baicin kalmar cryptocurrency, kalma mafi yawa a wannan harkar it ace kalmar bitcoin. To wai shin mene ne bitcoin nan ne?

Mene ne kuma Bitcoin?

Bitcoin kudi ne na yanar gizo wato internet wanda ake amfani da shi domin saya da sayar da abu. Kamar yadda mutum ke turawa mutane kudi daga account din sa na banki shima haka ake tura shi idan an sayi wani abu. Haka zalika idan abinka aka saya kamar yadda za ka kawo lambar account a tura maka haka zaka kawo “Wallet Address” na Bitcoin din ka a tura ma. Don haka siffar su daya da kudin da ya ke na zahiri wato Fiat currencies.

Sannan kuma ana iya sayen Bitcoin domin a sayar a ci riba kasancewar farashinsa yana hawa yayin da bukatarsa ta karu a kasuwar Blockchain Network. Sanann kuma yana iya faduwa yayin da bukatar sa ta ragu. Ko kuma aka sami wani issue na “Government Regulation” akansa ko kuma misali wata kasa a cikin kasashen duniya ta sanar officially cewar ta yadda da Bitcoin ko kuma wani babban kamfani a duniya ya ce daga yau shima zai dinga karbarsa.

Sannan kuma farashinsa na iya tashi idan mutane da yawa suka saye shi a wani yanki na duniya. Sannan farashin yana raguwa kasa kadan idan al’ummomin wani yanki na duniya suka sayar da na su.

Sannan yana da kyau ku sani bitcoin daya ne daga cikin cryptocurrencies. Sai dai bitcoin ya fi ko wannensu yawa ne kawai.

Ga jerin wasu daga cikin cryptocurrencies da muke da su a kasuwa a yau

Duk da cewa ana da cryptocurrencies fiye da 4,000 a yanzu hakannan to amma yawancinsu basu yi wani tasiri ba. Ga misalin wasu daga cikin jerin wadanda suke gaba gaba a duniyar cryptocurrencies a taburin da ke kasa.

CryptocurrencyMarket Capitalization
Bitcoin$563.8 billion
Ethereum$142.9 billion
Tether$25.2 billion
Polkadot$13.9 billion
XRP$11.4 billion
Cardano$9.7 billion
Chainlink$8.3 billion
Litecoin$8.1 billion
Bitcoin Cash$7 billion
Binance Coin$6.2 billion

Ta yaya mutum zai fara kasuwancin Bitcoin? Wasu sharudda mutum zai cika kafin ya fara?

Sannan a game da sharadi ko kuma ka’idojin da ake nema kafin mutum ya fara saye da sayar da Bitcoin kuma babu wata takamaimai din ka’ida da ta zama dole. Akwai exchange platform wadanda za ka yi sign up a platform din su. Idan ka yi sign up automatically za su bude maka “Wallet” wanda zaka dinga ganin Bitcoin din ka a cikin da kuma address din Bitcoin din naka wanda a duk lokacin da za ka karbi Bitcoin daga wani waje zaka yi clicking and copy it to clipboard sai ka turama wanda zai turo maka ya turomaka. Haka zalika akwai space na inda zaka sanya Bitcoin address na wanda za ka turawa idan tura masa za ka yi.

Sannan kuma acikin exchange platform din akwai inda zaka shiga ka sayi Bitcoin din. Idan ka rubuta misali kana son sayen na dubu 10 automatically za su nuna maka adadin Bitcoin din da zasu baka a wannan dubu goman. Zaka iya biya kudin with card ko kuma with bank transfer. Ya danganta da platform din da ka zaba ka ke amfani da shi.

Dazaran ka saya za ka ganshi a cikin wallet din ka. Za ka ga adadin sa, sannan za kuma kaga yawan kudinka a naira. Idan farashinsa ya tashi za ka ga kudin ka na Naira ya karu. Haka kuma idan farashinsa ya sauka za ka ga kudinka ya yi kasa. Misali idan na dubu goma ka ke da shi a wallet dinka, in ya tashi za ka iya ganin kudinka ya zama dubu 11 ko kuma 10500 idan kuma ya yi kasa za ka iya ganin kudinka ya koma dubu 9 ko kuma 9500.

Za ka iya siyarwa duk sanda ka ke so a yayin da ya tashi ko kuma ya karye.

Masu hada-hadar Bitcoin

Masu hada-hadar Bitcoin da sauran cryptocurrencies sun ka su gida uku. Ga su kamar haka:

Traders

Su ne masu saya don ya dan tashi sai su sayar. Misali idan na dubu goma suka saya da zarar ya kai dubu goma sha daya ko kuma dubu goma da dari biyar sai su sayar. Sannan sai su dan jira kadan ya dan kara yin kasa sai su kuma saya (recommended and less risky – wato wannan shi ya fi rashin hatsri sosai).

Holders

Su ne masu sayen na kudi mai yawa daga 100k har zuwa 1million sannan ba za su sayar ba sai ya kai kololuwa sun ga kudin su ya zama 1.2 ko 1.3 million (ma’ana sai sun ga sun sami ribar irin dubu dari biyun nan ko uku) sai su siyar. Sannan su jira idan ya sake yin kasa sai su sake saya.

ICO investors

Ma’anar ICO investors shi ne Initial Coin Offering Investors (the riskiest one. Highly not recommended for beginners, wato wadda ya fi hatsari sannan ba a shawartar sabon shiga ya fara da wannan tsarin). Su wadannan kamar ace a lokacin maulidi akwai masu taron wata, ma’ana suna fara maulidi tun kadin watan ya zo. Su wadannan suna sayen cryptocurrency ne tun kafin a kaddamar da shi. Suna sayen mai yawa akan farashi mai sauki, sai su jira yayin da ya karbu sosai kudinsa zai iya nunkawa sau da yawa. Misali a ce sun saye shi naira 3 idan aka kaddamar da shi successfully ya soma karbuwa zai iya kai naira 100 ko 200, ko 500. Kenan idan a ce mutum ya sayi guda dubu 1 to duk guda ya ci ribar naira 497 kenan (497000) ko fiye ma da haka. Wannan ya fi riba amma ya fi hadari.

Mu kamfaninmu na Gonar Bitcoin bama dora beginners a wannan hanyar sabanin wadansu masu koyar da sana’ar ta Bitcoin da Cryptocurrency.

Abinda yasa wannan ya kasance mai hadari shine na farko kamfanin cryptocurrency din zai iya kasa cimma target din sa. Hakan na nufin kuda ku ka saya za ku iyayin asara idan suka kasa kaddamar da shi a kasuwar ta Blockchain Network. Sannan kuma babu money refund domin  yawancin kamfanunuwa daga Amurka suke da kuma Turai. Sannan kuma hukumomin da ke sanya ido akan IPO na kamfani wato Initial Public Offering na Tarayyar Turai da Amurka sunce babu ruwansu da ICO na cryptocurrency. Don haka duk abin da ya je ya dawo mutum ya yi kuka da kansa.

Sannan kuma ko da an kaddamar din farashinsa zai iya kin tashi yadda ake so. Ko kuma ya dade bai tashi ba.

Muna da courses da guides da yawa akan ko wani level.

Shin mutum daya zai iya yin hada-hadar cryptocurrencies daban-daban?

Eh kwarai da gaske zaka iya yin hada-hadar cryptocurrencies da yawa kuma ko wanne da wallet dinsa a cikin platform guda. Ai hasali ma yawanci duk exchange platforms din suna da different cryptos a cikin su. Kuma lokaci zuwa lokaci har suna karo wasu options na wasu cryptos din su kara a platform na su..

Mene ne ma’anar Blockchain?

Blockchain tsari ne da kudin internet na crypto suke a kai wanda ke hade da miliyoyin kwamfutoci yake kuma baiwa irin wannan kudi kariya daga kutse ko kuma duk wani abu da zai samar da kudin ya kara yawansu a duniya sabanin ta hanyar da ake kira mining.

Domin idan aka ce ana samar da duk wani crypto anyhow to da drajar sa za ta karye miliyoyin mutane da kamfanunuwa su yi asara.

Shin su waye ke da hakkin ba da daman kirkiran cryptocurrency?

Ai shi crypto decentralized ne, wato babu mai iko akansa. Ko wanda ya kirkiroshi wato Satoshi Nakamoto ba shi da iko akansa. Babu wani wanda ya ke juya kudin ko kuma ya fitar da doka akansa. Ko shi tsarin na Blockchain kariya kawai ya ke ba shi. Amma ba control din sa ya ke ba. Mutane su ne su ke kawo shi cikin kasuwar (exchange platform) kuma su su ke sayen sa su kuma sayarwa da junansu. Babu mutum daya da ya ke da ikon.

A duk sanda ka mika bukatar sayen Bitcoin a cikin exchange platform to adaidai wannan lokacin wani ma ya mika bukatar sayarwa. A yayin da ka ke ganin farashinsa sa ya tashi bari ka sayar ka sami riba. To shi Kuma wani a dai-dai wannan lokacin zai bukaci ya saya domin ya yi wata bukatar da shi. Sannan Kuma zata iya yiwuwa shi ma kuma yana ganin a dai-dai wannan lokacin da za ka sayar to in ya saya gaba zai ci riba. Sai dai bawai tsakanin kai da shi ne zaku yi magana ba, a’a automatically kawai za ka ga an saya an sanya maka kudin ka. Ku yi register da Gonar Bitcoin akan kudi Naira dari 2 kacal domin samun Basic Knowledge da skills akan yadda ake farawa da kuma exchange platforms din da ya kamata ka yi joining.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading