Skip to content

Kudan Zuma

Ƙudan zuma wani nau’i ne na kwari waɗanda suke da tsarin zamantakewa irin na ɗan’adam, akwai sarki akwai sarauniya, akwai ma’aikata, akwai sojoji, da dai sauransu. Waɗannan kwari suna samun abincinsu daga jikin furanni, a cikin furannin nan da akwai abinda suke zuƙa, wani ruwa-ruwa ne mai kamar majina, wanda a Turance ake ce masa ‘Nectar’, a Hausa kuma ana kiransa ‘Darba’. To idan suka zuke shi, shibne kamar abincinsu a matakin farko.

Ƙudan zuma suna rayuwa ne a kungiya-kungiya, wato gungu-gungu.

Ƙudan zuma ɗaya ne daga cikin ajin kwari Insecta. Waɗannan kwari mambobi ne na dangin Apinae, waɗanda ke samarwa da adana sinadarin sukari mai laushi, wanda aka fi sani da zuma.

Siffar ƙudan zuma

Tsayin ƙudan zuma ya kai kimanin milli-mita 15. Ƙudan zuma yawanci halittu ne masu siffar ƙwai da launin zinari-rawaya da ƙafafuwa masu launin ruwan kasa. Kodayake launin jikin ƙudan zuma ya bambanta tsakanin nau’ikan ƙwarin kuma wasu ƙudan zumar jikinsu baƙi ne, kusan dukkanin ƙudan zuma suna da bambancin duhu zuwa haske. Waɗannan bambance-bambance na haske da duhu suna yin su ne don ci gaba da wanzuwar ƙudan zumar, saɓanin sauran nau’ikan da suke ɓoyewa idan suka ga mafarauta a kusa da su, jikin ƙudan zuma masu launi mai haske yana yin gargadi ga mafarauta ko masu ɗibar zuma a kan cewa ƙudan fa na iya yin harbi.

Fasalin jikin ƙudan zuma

Jikin ƙudan zuma ya kasu kamar haka: stinger, legs, antenna, thorax (da ya kasu gida uku) da kuma sassan ciki guda shida.

Kan ƙudan zuma ya ƙunshi idanu, antenna da ɓangaren cin abinci. Idanun ƙudan zuma nau’i biyu ne, wanda ake kira da compound eye da simple eye: compound eye yana taimaka wa ƙudan zuma su fahimci launi da haske da sashen da hasken rana yake, yayin da aikin simple eye ya kasance taimakawa ne wajen ƙayyade adadin hasken da ke a wajen da ƙudan zumar ya kasance a lokacin. Ayyukan antenna shi ne jiyo wari da kuma sauri tashi yayin da suke tashi. Mandible shi ne muƙamuƙin kudan zuma, wanda suke amfani da shi wajen cin tsirrai da yanka saƙar zuma,’ da ciyar da matasan ƙudan zuma da sarauniya da tsaftace sheƙa da gyaran jikinsu da kuma yin faɗa.

Gangar jikin ƙudan zuma ta ƙunshi fuka-fuki da ƙafafu da tsokoki waɗanda ke sarrafa motsinsu. Suna amfani da fuka-fuki na gaba, wanda ya fi girma fiye da na baya don tashi da kuma a matsayin ɓangaren sanyaya jikinsu, yayin da suke amfani da na ƙarshe don kawar da zafi da sanyaya sheƙa.

Sai kuma ɓangarori shida na cikin ƙudan zuma sun haɗa da gaɓoɓin haihuwa na mata a jikin sarauniya da gaɓoɓin haihuwa na maza a jikin sarki da dafin harbi a jikin ma’aikata da sarauniya.

Yadda ƙudan ke samar da zuma

Kudan zuma yana da ciki kashi biyu. Kashi na farko shi ne abincin da ya ci a matakin farko yake tafiya, ciki na biyu kuma shi ne yake karɓar abincin da zai sarrafa shi zuwa zuma. Idan suka zuki darɓar za ta shiga cikin cikinsu, akwai wasu sinadarai da ake kira enzayims, su ne za su sarrafa wannan darɓar ta koma ta zama zuma, ɗaya daga cikin sinadaran ana kiransa da Lebules, shi ne idan ya yi aiki a kan darɓar nan sai ya canja ta ta zama nau’i na suga da ake kira Lebulos, maimakon suga irin wanda ake kira Sukuros.

Ƙudan zuma na iya kora dubban mutane da dabbobi daga waje.

Wannan nau’i na zuma da aka sarrafa a cikinsu, shi ne suke kashinsa a cikin wannan saƙar tasu da suke yi, sannan kuma daga baya shi ne zai kasance abincinsu a mataki na biyu, shi ya sa idan mutum ya je ɗiba, waɗannan sojojin na cikinsu, za su yiwo kansa suna harbi, domin suna ƙoƙarin su kare abincinsu ne.

Ɗabi’u da halayen ƙudan zuma

A cikin daji, sau da yawa ana samun sheƙar kudan zuma a cikin kogunan bishiyoyi da duwatsu. Suna samar da shekar ne daga sakar zumar da ke fita daga cikin ƙudan zumar da suke ma’aikata. Waɗannan ma’aikata suna fito da wani ɓangare kaɗan na sakar zumar daga cikinsu, su tauna su har sai zumar ta yi laushi. Daga nan sai ma’aikata su ƙera sakar zumar kuma su yi amfani da ita wajen ƙirƙirar cell don su samar da sheka. Ba kamar sauran nau’in kudan zuma ba, kudan zuma ba sa yin barci a lokacin sanyi. Madadin haka, suna kasancewa a cikin gidajen da ke maƙulle tare, suna raba zafin jiki da cin kayan abinci da aka adana.

Kudan zuma halittu ne masu tsarin zamantakewa kuma suna rayuwa a cikin gungu ba a ɗaiɗaiku ba. Duk da haka, suna nuna wasu halaye na tayar da hankali a cikinsu, misali akan fitar da wasu mazajen ƙudan zuma daga cikin gidajensu a lokacin sanyi, kuma sarauniya a wasu lokutan takan kai wa wata sarauniyar hari a lokacin saduwa da namijin ƙudan zuma.

Haihuwa da rayuwar ƙudan zuma

Ƙudan zuma suna da tsarin zamantakewa irin na mutane, suna rayuwa a cikin gungu da yawansu ya kai dubbai. Nau’o’in ƙudan zuma manya guda uku suna zama a yanki ɗaya, wato sarauniya da sarki da ma’aikata mata marasa haihuwa.

A kowane rukunin ƙudan zuma, akwai sarauniya mai yin ƙwai guda ɗaya, sannan akwai dubban ma’aikata. Sarauniyar ƙudan zuma tana haɗuwa da sarki, suna kafa sabbin rukunai. Sarauniya tana sanya ƙwayaye a cikin cell da ke cikin shekarsu, kuma idan ƙwayayen suka ƙyanƙyashe, sai su zama tsutsa (larva). Kowane rukuni ya ƙunshi sarauniya guda ɗaya kawai, wacce ke iya samar da ƙwayaye 2,000 a rana.

Manya ma’aikata suna kula da larva a cikin cell kuma suna ciyar da su da tsirrai da zuma har tsawon makonni uku, a lokacin sun zama manya. Manyan ƙudan zuma (waɗanda suka girma suka wuce matakin tsutsa) suna tauna kansu daga cikin cell ɗin da aka rufe don fitowa.

Sarakuna ko ƙudan zuma maza, su ne tsiraru a cikin rukunin ƙudan zuma kuma suna aiwatar da aiki ɗaya kawai, shi ne yin jima’i da budurwar ƙudan zuma. Bayan yin jima’in, ba sa dadewa sai su mutu.

Sauran matan ƙudan zuma da ba sa haihuwa yawanci ba sa samar da ƙwayaye, don haka ba sa kafa sabbin rukunai na ƙudan zuma, sai dai suna yin ayyuka masu mahimmanci da yawa. Matasan ma’aikatan ƙudan zuma suna yawan samar da larva ta hanyar wani sinadarin ruwa daga cikinsu. Yayin da ma’aikatan ke girma, su kan kama aikin ɗauka da adana abincin da masu nemo abinci suka tara. A matsayinsu na manya masu ƙarfi da jini a jika, suna neman abinci tuƙuru har sai sun mutu.

Wuraren da ake samun ƙudan zuma

Ana samun nau’in kudan zuma a duk duniya kuma ana iya ganin su a wurare daban-daban, ciki har da Turai da Amurka. An fi ganin su a lokacin rani da kuma ƙarshen bazara, lokacin da sababbin sarauniya suka bar tsoffin dangoginsu tare da dubban ma’aikata don gina sababbin gidaje. A wannan lokacin, ana iya ganin manyan gungun ƙudan zuma suna ta tururuwa tare domin samun sabon wurin tsuguno. Yana ɗaukar gungun ƙudan zuma kamar sa’o’i 24 don gano sabon wurin zama. Yayin da yawancinsu ba su da lahani, amma wasu nau’in ƙudan zuma suna da muni sosai kuma suna iya kai hari ba tare da an tsokane su ba.

Domin ana samun kudan zuma a duk duniya, yanayinsu da halayensu na iya bambanta. Alal misali, yayin da ƙudan zuma na Italiya suke da sauƙin kai da haƙuri, ƙudan zumar Afirka da Jamus na iya nuna ɗabi’ar kariya ga kansu. Amma dukkan ƙudan zuma na iya zama masu ba wa kansu kariya idan an tsokane su kuma suna iya korar mutane ko dabbobi.

Haɗa barbarar tsakanin tsirrai

Sama da miliyoyin shekaru, ƙudan zuma sun kasance manyan masu jigilar furanni, saboda haka, shukoki masu furanni sun dogara ga wannan aiki na ƙudan zuma. Manufar shuka ta ce girma haihuwa, wato samar da abin moriya da shukar ke fitarwa. Ƙudan zuma suna taimakawa wajen cimma wannan manufa ta hanyar (pollen), ƙwayoyin maniyyi na shuka namiji, daga wannan furen zuwa wani. Idan babu wannan jigilar, yawancin shukoki ba za su iya haihuwa ba kuma a ƙarshe za su mutu.

Mutane suna amfana da wannan dangantakar ta hanyar samun amfanin gona da kuma zuma. Yawancin amfanin gonakin da mutane ke ci, ƙudan zuma ne ke haɗa barbararsu. Manoma da dama suna kula da gungun ƙudan zuma saboda wannan dalili. Idan babu shi, shukoki ba za su samar da ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari ba. Bayan wannan, ƙudan zuma na fitar da darɓa daga cikin furanni. Wannan darɓar ita ce ke sauyawa zuwa zuma bayan ƙudan zumar sun kawo ta cikin sheƙarsu.

Manazarta

BBC News Hausa. (2017, May 2). Ka san baiwar tamatar kudan zuma? 

Orkin. (n.d.). Honey Bees: Overview of honeybee types, habitats & Characteristics | Orkin

Welle, D. (2007, January 22). Yaya Kudan-zuma yake yin zuma. dw.com.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×