Skip to content

Kudin cizo

Kuɗin cizo dai wasu ƙananan ƙwari ne waɗanda ke cizo da zuƙar jinin ɗan’adam. Yawanci suna da launin ja da launin ruwan kasa, suna da siffar ƙwai, sannan kuma yanayin tsayinsu kusan millimeters 4 zuwa 5 ne. Kuɗin cizo ba alamar rashin tsafta ko rashin kula da gida ba ne ke kawo shi, saboda haka za a iya samunsa ko’ina.

Kuɗin cizo ƙwaro ne da ke addabar mutane da cizo.

Akwai wasu mahimman abubuwan da ya kamata a sani game da kuɗin cizo, ga wasu daga cikinsu:

1. Kuɗin cizo yana ɓuya ne a cikin ƙananan ramuka da ke jikin bango a cikin gadaje da kuma kayayyaki kamar shimfiɗa da zanen gado.

2. Yawanci da dare suke fitowa domin su ciji mutane su kuma tsotsi jini.

3. Cizon kuɗin cizo na iya haifar da raɗaɗi da jajayen ƙuraje da ƙaiƙayi ko kumburi a fata.

4. Cizon kuɗin cizo yakan iya haifar da rashin lafiya da kuma damuwa.

5. Ana iya samun kuɗin cizo a otal-otal da ɗakunan kwanan ɗalibai da gidaje.

6. Kuɗin cizo na yaɗuwa zuwa wasu wuraren ta hanyar kai kayan da aka yi amfani da su a wurin da suke da shi.

7. Kuɗin cizo na da wahalar magancewa, sai an yi da gaske ta hanyar amfani da ingantaccen magani.

Alamomin gane kuɗin cizo a wuri

• Ganin ƙanana kuma jajayen ƙwari ko launin ruwan ƙasa ko ganin ɗigon jini a kan zanen gado ko tufafi.

• Ganin ƙananan ƙwayaye masu haske a jikin bango ko kaya.

• Jin wani irin ƙarni.

Matsalolin da cizon kuɗin cizo ke haifarwa

1. Jan ƙurji da kumburi: Wurin da aka ciza zai iya zama ƙurji kuma ya yi kumburi.

2. Ciwo da kaikayi: Cizon kuɗin cizo na iya haifar da ƙaiƙayi mai tsanani da raɗaɗi.

Wuraren da kuɗin cizo ya fi ciza

Yawanci cizon kuɗin cizo yana bayyana a jere kamar a layi-layi, a kan fata bayyananniya kamar fuska da wuya da hannaye da kuma ƙafafu.

Illoli da kuɗin cizo kan haifar ga lafiya

1. Rashin lafiya: Cizon kudin cizo na iya haifar da mummunan rashin lafiyar jiki, kamar anaphylaxis.

2. Cututtukan fata: Cizon kuɗin cizo na iya haifar da cututtukan fata, kamar cellulitis ko impetigo.

3. Ciwon barci: Kuɗin cizo na iya kawo cikas ga yawan barci har ma da rage daɗin barcin.

4. Tasiri ga tattalin arziki: Matsalar kuɗin cizo na iya haifar da asarar kuɗi mai yawa, musamman wajen sayan magani.

5. Ciwon asma: Abubuwan da cizon kuɗin cizo ke haifarwa na iya tsananta matsalar cutar asma da ta numfashi.

Kuɗin cizo na iya bayyana a ko’ina.

Lokacin da suka fi cizon mutane

Kudin cizo sun fi aiki a cikin sa’o’i biyar na dare – tsakanin 12 na dare zuwa 5 na safe. A lokacin ana iya kasancewa a yanayin barci mai zurfi, kuma da wuya a farka don dakatar da su.

Kwarin na afka wa mutane masu barci da taimakon alamu guda biyu – wato iskar carbon dioxide (CO2) da kuma ɗumin jiki. Kwarin na iya gano iskar CO2 daga nisan kafa uku, kuma sukan ji ɗumin jiki daga ɗan kusa da haka.

Duk da haka, ba sai an yi barci kusa da muhallansu ba kafin su cije mutum – kwarin na iya yawo mai nisa a cikin dare don neman wanda za su afkawa.

Yadda kudin cizo ke cizon mutane

A ƙoƙarinsu na neman abincinsu, kudin cizo kan lalubo tare da nutsa bakinsu can cikin fata domin neman jijiyoyin jini su tsotsa- wanda shi ne abincinsu, kamar yadda masu bincike suka bayyana.

Kudin cizon ba sa iya samun jijiyar jinin a cizon farko, hakan na nufin wanda ake cizon zai sha wahala sosai, domin kuwa sai ƙwarin sun cije shi da yawa kafin su iya samo jini a jikinsa. Ƙwarin kan iya ɗaukar tsawon mintuna biyar zuwa goma kafin su iya huda jijiyar jinin, domin samun abincinsu.

Bayan samun jinin da ƙwarin suka tsosa, sukan yi kimanin mako guda kafin su ƙara buƙatar abinci

Hana yaduwarsa

Maganin kwari na guba ba zai iya magani ba shi kadai, kuma ba wata hanya da ita kadai za ta kasance ta ganin bayan wannan kwaro a yanzu kamar yadda Micheal Potter masani kan kwari daga Jami’ar Kentucky ya ce.

Abin yi shi ne za a iya haɗa maganin guba da sauran dabaru, misali yadda ake sanya wasu abubuwan da ke yada zafi a wuri domin shi kudin cizo yana mutuwa ne a yanayin zafi da ya kai maki 45 a ma’aunin Selshiyas (celcius).

Akwai kuma hanyar amafani da fasahar halitta wajen hana yaduwar, inda za a yi amfani da maganin da ke takaita girman kwari ta yadda maganin zai hana kudin kaiwa cikakkiyar halittarsa wato ya tsumbure ta yadda ba zai iya yin kwai ba har ya yadu. To sai dai matsalar wannan dabara ita ce, duk da ta hana kudin girma ko haihuwa amma zai iya cizon mutum.

Wata hanyar kuma ita ce, za a iya amfani da kwayar halittar bakteriya wadda ke cikin kudin cizon shi kansa (Wolbachia), ko kuma amfani da kwayar halittar kudin cizon wadda ke gaya masa inda zai je da kuma wadda zai sadu (barbara) da ita, za a iya sake yanayin halittar ƙwayar a sa ta rika illata shi.

Manazarta

BBC News Hausa. (2015b, October 26). Anya za mu iya kawar da kudin cizo? BBC News Hausa

Mayo Clinic. (2024, January 5). Bedbugs – Symptoms and causes – Mayo Clinic.

US EPA. (2024, January 26). Bed bugs appearance and life cycle US EPA.

Undefined, U. (2023c, October 7). Kudin-cizo: Abu shida game da kwaron da ya addabi Faransa. Kudin-cizo: Abu Shida Game Da Kwaron Da Ya Addabi Faransa TRT Afrika.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×