Skip to content

Kunne

Share |
Kunne yana ɗaya daga cikin sassa masu muhimmanci sosai a jikin ɗan Adam. Wanda ba kasafai ake gane muhimmancinsa ba, sai ya kamu da wata matsala.
Ɓangarorin kunnen ɗan’adam

Amfanin kunne

Ƙwarai kunne yana da matuƙar amfani ga rayuwar ɗan Adam. Kuma amfaninsa ba wai kawai a jin magana ya tsaya ba, a’a yakan taimaka wajen sa daidaito idan mutum ya miƙe tsaye ta yadda ba zai faɗi ƙasa ba. Haka kuma ya kan taimaka wurin ƙawata fuskar ɗan Adam ta fita cikin cikakkiyar kamalar da ta kamata.

Ɓangarorin kunne

Kunne na da ɓangarori uku, na waje da tsakiya da kuma can ciki. Fatar kunne da ƙofar kunne ta waje su ne ɓangare na waje ɗin. Amfanin wannan sashe shi ne tare iska da amo ya saita su zuwa cikin kunnen. Wannan ɓangare bai cika samun ciwo sosai ba, sai dai akan iya yanke shi a haɗari, ko kuma da abubuwa masu kaifi idan wata tarzoma ta tashi misali. Ita kuwa ƙofar kunne ana iya ganin dattin kunne a ciki a fitar ta wannan ɓangare. Ɓangare na tsakiyar haɗe yake da maƙogoro ta yadda ƙwayoyin cuta daga maƙogwaron kan yi saurin shiga kunne, musamman ga yara tunda hanyar da ta haɗasu gajeriya ce. Ruwa ma kan iya shiga wannan ɓangare na kunne a yayin wanka ya hana mutum sakat. Daga can ciki kuma akwai wani ɓangaren, inda dodon kunne yake wato (cochlear) da wasu ƙasusuwa ƙanana guda uku. Jijiyar da ke da alhakin sa mutum jin magana a jikin dodon kunnen take. Wato ke nan dodon kunne shi ne ke da alhakin jin magana. Su kuma ƙasusuwan sukan taimaka wa jiki wajen daidaito.

Ciwon kunne

Ciwon kunne babban ciwo ne da yake adabar yara da kuma manya a yanayi kala-kala. Wani haihuwarsa ake yi da shi, wani kuma daga baya yake kamuwa da shi sakammakon waki ibtila’i ko kuma kaucewa wasu ƙa’idoji ko kuma ciwo haka kawai daga Ubangiji.
Kunne mai ciwo

Ire-iren ciwon kunne

Ƙananan yara tsakanin wata shida zuwa shekaru uku sukan yi fama da wani irin ciwon kunne da ake kira (Otitis media) shi (otitis media) ciwo ne wanda yake ciwo a tsakiyar kunne. Ciwon kunnen yafi faruwa da damina kuma yana zuwa da zazzaɓi wani lokaci mai tsanani sai dai sau da dama bai cika zama abun damuwa ba. Akwai kuma wani ciwon kunnen da ake kiransa (otitis external), wanda shi kuma yake shafar wajen kunne. Koda yake yara ba su cika kamuwa da shi ba kamar na farkon ba. Yawanci ƙananan yara suna fama da ciwon tsakiyar kunne musamman ƙananan yaran da suka kasance daga cikin wannan jerin: Yaran da aka haifa basu kai lokacin haihuwa ba. Akwai yaran da suke yawan jin sanyi sosai. Sannan akwai yara waɗanda basa son wari, kamar hayaƙin taba da sauran su. Ko kuma yaran da ba’a basu nono ba wato waɗanda basu sami shayarwa daga mahaifiya ba. Da kuma yaran da aka baiwa abincin gwan gwani. Mafi saurin kamuwa daga cikinsu su ne irin yaran da ake shayar da su abincinsu daga kwance. Wasu ƙwayoyin cuta suke kawo ciwon tsakiyar kunne. Ƙwayoyin cutar na tafiya daga bayan maƙogoro yayin da (Eustachian tube) ta lalace. Wannan ne yake kawo ciwon tsakiyar kunne. Shi yasa yara masu yawan jin sanyi ko masu fama da ciwon maƙogoro ke kamuwa da ciwon kunne. (Otitis external) shi kuma yawanci yana faruwa saboda rashin tsabtar fatar jiki da ƙwayar bacteria…” A wata tattaunawa da aka yi da Dr Sumayya, ma’aikaciya a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ta bayyana wa masu sauraro cewa alamomin ciwon cikin kunne (Otitis media), yawancin manyan yara suna fama da ƙaiƙayin kunne da kuma zafi. Ƙananan yara basa iya magana, amma zasu kasance da zazzaɓi marar misali. Haka nan zasu kasa yin bacci su riƙa sosa kunnen su. A wasu lokutan har ya yi jinni, kuma sukan kasa iya sauraron ƙara ko amo me ƙarfi. Za’a iya samun fitar ruwa mai ƙwayoyin cuta daga kunnuwan. Ciwon bayan kunne shi ma yana da zafi sosai, yana sa ƙuraje sosai a bayan kunnuwa. Wanda a hausance muke kira da ‘ƙimi’. Ana iya ba yara ‘yan ƙasa da wata shida maganin kashe ƙwayoyin cuta (Antibiotics). Shan maganin rage zafin ciwon.Yara suna jin sauƙi yayin da suka fara amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta. A nan yana da muhimmanci ga iyaye su kiyayye umurnin likita har ƙarshe. Shan (Topical antibiotics) da man shafawa suna maganin (otitis external). Sake ganin likita na da amfani idan yaron yana da ciwon kunne ko yana amai sossai. Idan kuma yana zazzaɓi fiye da sa’a araba’in da takwas da kumburi bayan kunne, idan yana bacci sosai, ƙuraje a kunne, baya ji sossai ko gaba ɗaya. Abubuwa da dama kan taɓa lafiyar dodon kunne har a rasashi ta hanyar hujewa;abubuwan su ne ƙwayoyin cuta (kamar sanƙarau) ko wasu magunguna, na nasara ne (kamar gentamicin) ko na gargajiya, ko kuma a huɗa shi ta hanyar susa da abu mai tsini. Ko kuma ta hanyar faɗawa ruwa da ƙarfi, ko buguwa ta sanadiyar haɗari. Ko ta yawan jin ƙara fiye da ƙima, ko ma abin ya faru tun a ciki, a haifi mutum haka ba ya ji. Akan iya yin dashen wani dodon kunnen idan buƙatar hakan ta taso. Idan ruwa ya shiga kunne, misali kamar a lokutan wanka, za a iya sa tsinke mai auduga a goge. Idan bai fita ba a bari bayan kamar kwana biyu zai tsane da kansa. Sai dai idan ba a ji ya tsane da kansa ba ya kamata a je asibiti. Masu aiki a kamfanin da suke da injina masu ƙara ko filin tashin jirgin sama, dole su riƙa toshe kunnensu a kullum. Domin kiyaye lafiyar dodon kunne. Irin wannan ƙara ma takan iya fasa dodon kunne. Masu aiki a irin waɗannan wurare yana da kyau su riƙa zuwa wurin likitocin kunne a kalla sau ɗaya a shekara don kula da lafiyar kunnensu. Haƙƙinsu ne su nemi kamfanin ya samar musu abin rufe kunne da kuma likitoci domin kula da lafiyar kunnensu. A ƙasashen da suka ci gaba, idan babu irin wannan a kamfanin ma’aikata za su iya kai kamfani ƙara kotu don a tabbatar an samu yanayin aiki wanda ba zai taɓa lafiya ba. Waɗannan su ne hanyoyin da za su iya sa a kamu da ciwon kunne, dama wasu hanyoyin daban-daban.

Kariya

A mafi yawan lokuta ba sai an fitar da dattin kunne ba, dattin da kansa yake fita. Wato kunne shi ke wanke dattinsa da kansa. Yakan wanko shi ya turo shi ƙofa kunne. Za a ga dattin launin ruwan ƙasa a naɗe a jikin wani abu mai danƙo. Idan har ta kama sai an cire wannan abu mai danƙo, to kada a yi amfani da abu mai tsini. 1- A sa irin abin goge kunnen nan mai auduga a bakin kunnen a fito da shi a hankali. 2- Wanke hannuwanka da na yaro kodayaushe. 3- Shayar da yara da nonon uwa. 4-Dena ba yara abincin kwalba lokacin suna kwance. Ko shayar da su a kwance. 5- Daina amfani da kayan susa masu tsini. 6- Daina shan taba a ɗakin da ƙananan yara suke. 6- Yiwa yaro rigakafi yana rage wannan ciwon. Yin allurar rigakafin mura mai zafi (Fluvaccine) kowacce shekara. 7- A ƙarshe, idan yaro ya kamu da ciwon kunne: Kada ayi amfani da auduga a kunnen, domin zata iya ƙara girman ƙwayar cutar. Kada a ɗiga maganin kashe ƙwayoyin cuta a kunnuwan yara, zai iya kawo fashewar kunne. Kada a share kunne da auduga domin kauda danƙon kunne.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading