Skip to content

Kura-kuran masu azumi

Bismillahi rahmanir Rahim

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai Girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da sahabansa.

Akwai daga cikin kura-kurai da dama wadanda mai yin azumi kan yi. Ga su nan na kasa su kamar haka:

Na farko: Kura-kurai lokacin fuskantar watan Ramadan

 1. Yin azumi kwana daya ko biyu kafin shigowar Ramadan. Yin hakan ya saba wa sunnah. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Kada ku rigayi Ramadan da azumtar yini daya, ko biyu, sai dai ga mutumin da ya kasance yake yin wani azumi (na nafila), to ya azumce shi”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
 2. Rashin kulawar wasu Musulmai ga lissafin kirgen watan Sha’aban.
 3. Dogaro da abinda masu ilimi falaki suka fada wajen ganin watan Ramadan. Allah Ya ce: “To duk wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi“. Suratul Bakara, aya ta 185. Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan kuka gan shi –wato jinjirin wata- sai ku yi azumi, idan kuma kuka gan shi, sai ku ajiye azumi, idan kuma aka yi muku hazo, sai ku kaddara masa”. A wata riwayar: “Idan aka yi muku hazo, to sai ku cika kirgen sha’aban talatin”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
 4. Dogaro da ganin wata na wata kasa.
 5. Akwai masu bakin ciki da zuwan Ramadan, ma’ana basu farin ciki da zuwan sa, wannan ma kuskure ne. Saboda ya tabbata Manzo Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yiwa sahabbansa albishir da zuwan Ramadan. Daga Abu Huraira (R.A), yace: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ramadan ya zo muku, wata mai albarka, Allah ya wajabta azumtar sa akan ku….”. Nisa’I ne ya rawaito shi.
 6. Rashin kwana da niyyar daukan azumi. Wannan kuskure ne. Duk wanda ya ji labarin ganin watan Ramadan, to dole ne ya daura niyya kafin ketowar alfijir. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda bai kwana da niyyar azumi gabannin ketowar alfijir ba, to bashi da azumi”. Tirmizi da Nasa’I da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
 7. Rashin kame baki ga wanda ya samu labarin ganin wata da rana.
 8. Jahiltar abubuwan da suke karya azumi ko suke bata shi.
 9. Tarbar watan Ramadan ta hanyar kade-kade da raye-raye.

Na biyu: Kura-kurai a sahur

 1. Wasu masu azumi sukan ki yin sahur, ko kuma su yi sahur tun cikin dare su kwanta bacci. Wannan ya sabawa sunnah. Mustahabbi ne mutum yayi sahur kafin ketowar alfijin, saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ku yi sahur, saboda cikin yin sahur akwai albarka”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Haka nan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya na jinkirta sahur.
 2. Wasu masu azumi na dogara wajen kame baki da kiran sallah a masallaci, basu san cewa mafi yawan masallatai basu san lokacin kiran sallah ba. Wajibi ne ga musulmi ya san lokacin sallah, ko ya dogara ga masallacin da suke kiran sallah akan lokaci.
 3. Cika ciki nak lokacin sahur, wanda hakan zai saka shi kasala.
 4. Yin bacci bayan sahur, wanda yin hakan zai iya jawo a rasa sallar Asuba.

Na uku: Kura-kurai a wunin Ramadan

 1. Gafala kan zikiran safe da yamma.
 2. Wasu masu azumi na tunani wunin azumi dama ce ta yin bacci da hutu. Sun manta watan Ramadan wata ne na nishadi da ibada, har ma akwai yakokin da Musulmai suka yi su a cikin watan Ramadan, kuma suka samu nasara, kamar yakin Badar.
 3. Wasu masu azumi sukan jinkirta yin sallan Azahar da La’asar, saboda yawan bacci da suke yi.
 4. Wasu masu azumi sukan yi sakaci a wunin azumi da kuma bata lokutan su ta hanyar taro a tituna ko dandali ko ta hanyar kallon fina-finai, da sunan rage lokaci.
 5. Wasu masu azumi kan yi zagi da karya da shedar zur a yayin da suke azumi.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda bai bar zancen karya ba, da aiki da shi ba, to Allah baya da bukatar barin cinsa da shansa”. Bukhari ne ya rawaito shi. Haka nan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Azumi garkuwa ne, idan ranar azumin dayanku ya zo, to kada ya yi batsa, kada kuma ya yi shewa, idan wani ya zage shi ko ya nemi fada da shi, to ya ce: ‘Ni mai azumi ne’”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Kuma Manzon Allah ya fada cewa: “Da yawa ana samun mai azumi baya samun komai a matsayin lada sai dai kawai yunwa da yake sha”. Ibnu Maja ne ya rawaito hadisin.

Na hudu: Kura-kurai a buda baki

 1. Wuce gona da iri wurin tanadar abincin buda baki, ta yadda mai azumi zai tanadi nau’uka daban-daban na abinci har ma su kai goma ko fiye da haka. Wannan zai shiga layin barna, wanda shari’a ta hana. Allah Ya ce: “Kuma ku ci, kuma ku sha, kuma kada ku yi barna. Lalle ne Shi (Allah) ba Ya son masu barna“. Suratul Araf, aya ta 31.
 2. Barin yin addu’a lokacin buda baki. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance idan ya yi buba baki yana cewa: “ZAHABAZ ZAMA’U, WABTALLATIL URUKU, WA SABATAL AJRU IN SHA ALLAH“. Abu Dauda ne ya rawaito shi. Ma’ana: “Kishin ruwa ya tafi, jijiyoyin wuya sun jike, lada ya tabbata in Allah Ya so”. Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Mutum uku ba a mayar da addu’o’insu; Shugaba mai adalci, mai azumi har sai ya yi buda-baki, da kuma addu’ar wanda aka zalunta”. Tirmizi da Ibnu Majah ne suka rawaito shi.
 3. Jinkirta buda-baki. Wannan ya sabawa sunnah. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Mutane ba zasu gushe suna kan alheri ba, matukar suna gaggauta buda-baki“. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
 4. Wasu masu azumi sukan jinkirta buda baki har sai bayan sun yi sallar magariba. Wannan kuskure ne, ya sabawa sunnar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yin buda-baki kafin yayi sallar magariba koda da ruwa ne. An karbo daga Anas Bin Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana buda-baki da dayyen dabino gabanin ya yi sallah, in kuma bai samu danyen dabinon ba, sai ya yi buda-baki da busasshen dabino, in kuma bai samu ba, sai ya sha ruwa”. Abu Dauda da Tirmizi ne suka rawaito shi.
 5. Jinkintar sallar magariba da wasu masu azumi ke yi sakamakon shagaltuwa da ciye-ciye bayan buda-baki.
 6. Wasu masu shan taba da zaran sun ji kiran sallar Magariba, zasu dan ci wani abu kadan, sannan su gaggauta kunna sigari su sha, har ma ana iya samun wanda zai fara buda-baki da sigari, kafin ya ci wani abu. Ya kai dan uwa mai albaka! Watan Ramadan dama ce ka samu don ka nisanci shan shigari.
 7. Wasu masu azumi sukan shagalta da buda-baki, basu iya bibiyar mai kiran sallah.
 8. Wasu masu azumi basu yin buda-baki har sai ladan ya gama kiran sallah.

Na biyar: Kura-kurai a sallar tarawihi

 1. Wasu mutane sun jahilci falalar sallah tarawihi, hakan yake sa basa yin sallar. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda yayi tsayuwar Ramadan (Sallah Tsarawihi) yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
 2. Akwai mai yin sallar tarawihi shi kadai, da hujjar wai liman baya yin raka’a goma sha daya, ko kuma wai liman yana tsawaita karatu, ko kuma wai liman baya tsawaita ruku’u da sujada, da makamancin haka.
 3. Wasu masu sallar tarawihi tare da liman sukan bibiyi karatun limami su rika yi tare da shi, ko kuma su rike al-kur’ani suna kallo, da hujjar wai suna koyon karatu da kuma sanin inda liman yake karantawa. Wannan yana kore kushu’i na nitsuwa a cikin sallah, yadda mai yin hakan zai rika shagaltuwa da bude shafukan al-kur’ani, haka nan zai zama ya rike shi lokacin ruku’i da sujada ba zai sanya hannun sa inda ya dace ba, ko kuma ya ajiye Al-kur’anin a kasa, duk wannan ya sabawa siffar sallar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam.
 4. Wasu masu sallar tarawihi tare da liman su kan ki su jira su karasa sallar tare da liman, musamman in sun ga liman yana sallah fiye da taka’a goma sha daya ko raka’a goma sha uku. Abinda ya fi dacewa shi ne su yi hakuri su jira liman ya kammala sallar tare da su, saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda ya tsaya tare da liman har ya kammala, to za’a rubuta masa ladan tsayuwar dare”. Abu Dauda da Tirmizi da Nasa’I da Ibn Majah ne suka ruwaito hadisin.
 5. Yin witiri sau biyu a dare daya, wannan ya sabawa sunnah. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu witiri biyu a dare daya”. Tirmizi ne ya rawaito shi.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading