Skip to content

Kwarangwal

Tsarin kasusuwa ko kuma tsarin ƙwarangwal wani tsari ne da aka shirya domin ya zama gimshiƙi ko dirka ga hallitar gangar jikin ɗan’adam. Kamar dai a zubi na fasalin ƙirar lema, inda za a ga cewa, wannan ‘yan ƙarafunan da ke cikin lemar ne ke sarrafawa haɗi da ba wa gangar jikin lemar kariya. Ƙwarangwal shi ne jerin ƙasusuwan jiki kuma ginshiƙin da ke rataye da dukan sassan jiki.

Ƙwarangwal

Ƙashi

Ƙashi wani nau’in ne na ƙwayoyin tantashi, masu tauri, da suke aikin taimakon kai-da-kai domin zame wa gangar jikin ɗan’adam dirka, ko majingina da kuma ba da kariya ga waɗansu muhimman massarafai da ba sa iya jure aiki mai ƙarfi.

Adadin ƙasusuwan jikin ɗan’adam

Bayani daga kimiya ya bayyana cewa, akwai ƙasusuwa daban-daban har guda 206 a jikin mutum. Har ila yau wani binciken ya nuna jarirai sun fi manya yawan ƙasusuwa, a yayin da manya ke da ƙasusuwa 206, jarirai na da ƙasusuwa 270, inda yawansu zai riƙa raguwa yayin girmansu saboda haɗewar wasu daga cikin ƙasusuwan har su zama daidai da na manya.

Guraran da ƙasusuwan suke

1-Fiye da rabin ƙasusuwan ƙwarangwal ƙasusuwa 106, suna nan a tattare a hannaye, tsintsiyoyin hannu, da kuma tafukan sawu.

2-A tafin sawu ɗaya kawai, akwai ƙasusuwa har guda 26.

3-Ƙashin cinya shi ne ƙashi mafi tsayi kuma mafi ƙwari a jikin ɗan’adam.

4-Ƙashi mafi ƙanƙanta kuma mafi ƙarancin nauyi shi ne ƙashin ‘stapes’ da ke tsakiyar cikin kunne, wanda ɗaya ne daga cikin ƙasusuwa uku da ke tsakiyar cikin kunne da suke taimakawa wajen sarrafa sauti.

Ƙashin baya

5-Hannu haɗi da tsintsiyar hannu na ɗauke da ƙasusuwa har guda 27.

6-Ƙashin ‘hyoid’ shi ne ƙashi ɗaya tak da bai jingina da wani ƙashi ba. Wannan ƙashi mai sifar “V” na nan tsakanin maƙogaro da tushen harshe.

7-Ƙasusuwa na gama tsayi ne bayan balaga zuwa wajejen shekara 25, amma kauri, nauyi da ƙwarin ƙashi za su ci gaba da sauyawa tsawon rayuwa.

Muhimman sinadaran ginin ƙashi

Muhimman sinadaran ginin ƙashi sun haɗa da kalsiyam (calcium), fasfaras (phosphorus), sodiyam (sodium) da sauransu. Domin haka, cin abincin da ke ɗauke da waɗannan sinadarai na taimakawa wajen gina ƙashi.

Kamar yadda ƙwarangwal ya zama ginshikin jiki, haka nan tsokokin jiki su ne ke samar da ƙarfi / yunƙurin da ke motsa sassa ko gaɓɓan jiki.

Ƙwarangwal na samar da kariya ga muhimman sassan jiki kamar ƙwaƙwalwa da ke ƙunshe cikin ƙoƙon kai, laka da ke ƙunshe cikin kwaroron ƙashin gadon baya, ƙwayar ido da ke cikin gurbin ido da kuma zuciya da huhu da ke cikin kejin haƙarƙari.

Dogayen ƙasusuwan ƙwarangwal da ke ƙunshe da ɓargo a cikinsu na daga cikin sassan jiki da ke samar da ƙwayoyin jini. Kusan rabin karayar da take afkuwa ga manya na faruwa ne a ƙasusuwan damatsa, wato dantsen sama ko na ƙasa.

Nauyi, ƙwari da aikin ɓargon ƙashi na samar da ƙwayoyin jini duk suna ƙaruwa da motsa jiki / atisaye akai-akai, kamar yadda suke raguwa da rashin motsa jiki / atisaye.

Amfanin ƙashi

Kamar yadda bayani ya gabata, amfanin ƙashi shi ne; tallafawa da sarrafa motsi na zahiri haɗi da ba da kariya ga jikin ɗan’adam. Yakan kuma taimaka wajen ajiye waɗansu sinadaran albarkatu, da suke ƙara ƙwarin da kuma girman ƙashin, wato (calcium).

Awasu ƙasusuwan kuma wato masu ɗauke da ɓargo sukan taimaka wajen ƙyanƙyasar ƙwayoyin halittar jajayen jini, har ma da fararen. Wani nau’in na ƙashi kuma kan ajiye maiƙo domin amfanin gaba.

Bayanan wasu ƙasusuwan jiki

1-Ƙashin ƙoƙon kai: Ƙasusuwa ne guda ashirin da biyu, 22, da suke manne da juna domin samarwa ƙwaƙwalwa muhalli tare da ba ta kariya.

2-Ƙashin baya: Ƙashin baya haɗaka ce ta guntayen ƙasusuwa haɗi da dandatsi a tsakaninsu , su na aiki a goye da juna ne domin samarwa jelar ƙwaƙwalwa muhalli, da kuma samar da dirka daga ƙashin ƙwanƙwaso zuwa ga ƙashin ƙoƙon kai.

3-Ƙasusuwan haƙarƙari: Ƙasusuwan haƙarƙari wasu ƙasusuwa ne, da aka yiwa huhu da zuciya rumfa da ma sauran hallitun da ke cikin ƙirji. An yi wannan rumfar ne, domin samar musu da muhalli hadi da ba su kariya. An kafa ƙasusuwan ne, daga ƙashin baya zuwa ga ƙashin dandatsin ƙirji. Ta yadda za su iya ba huhu damar kumbura da kuma sacewa.

4-Ƙashin zira’in hannu: Ƙasusuwan zira’in hannu, waɗansu ƙasusuwa ne guda talatin, masu tsawo guda uku, da kuma gajeru guda ashirin da bakwai. Amfanin su shi ne samar da motsin hannu da kuma tallafawa wajen baiwa hannu damar gudanar da ko wannne irin aiki, musamman aiyukan da a ke yi da ƙarfin cin tuwo.Dogayen ƙasusuwan na hannu masu ɗauke da ɓargo kuma kan taimaka wajen ƙyanƙyasar jajayen ƙwayoyin hallitar jini.

5-Ƙashin zira’in ƙafa: Ƙashin zira’in Kafa,wasu ƙasusuwa ne guda talatin su ma dai guda uku, dogaye ne guda ashirin da bakwai kuma gajeru. Amfaninsu shi ne; tallafe jiki, da kuma ma ba da damar tafiya haɗi da dai-daito. Su ma kuma suna ɗauke da jajayen bargo a cikin su, wanda hakan na nufin a cikin su ma a na ƙyanƙyasar ƙwayoyin jini.

6-Ƙashin kwankwaso: Ƙashin kwankwaso wani ƙashi ne da ya haɗa ƙasusuwan cinyoyi da ƙashin baya, kuma shi ya ke taimakawa wajen dai-daituwar mutum a tsaye ko a zaune.

6-Girtsi da Dandatsi: Girtsi wata hallita ce da a ke ƙullawa kasusuwa ƙawance da shi. Kamar dai yadda aka ƙulla ƙawance ƙasusuwan nan na ƙashin baya.

An sanya faifan zagayen dandatsi a tsakanin ko waɗanne ƙasusuwa guda biyu, ta yadda za ka iya lanƙwasa jikinka, ka kuma jiuya shi na kusan 180% a ma’aunin zagayen saiti, wato (Cardinal direction).

Da shi ne kuma a ka ƙera faifan kunne, da karan hanci, da kuma maƙogwaro. A jikin jinjiri ma za ka samu cewa rabin ƙasusuwansa duk girtsi ne, domin a kan haife shi ne da kusan ƙasusuwa ɗari uku. Amma a hankali, ya na girma, sai su riƙa canjawa su na harhaɗewa, yana wayau su na za ma ƙasusuwa, har dai su dawo ɗari biyu da shida 206.

Dandatsi

Shi kuma dandatsi wata hallitta ce mai gautsi haɗi da sulɓi da za ka samu a duk wata guiwa ko mahaɗa da ke jikin ɗan Adam. Tana aiki ne da waɗansu ruwan romo, domin samar da kyakykyawan yanayin da zai baiwa kowacce mulmullalliya da rammammiyar gaɓa damar jujjuyawa iya son ranta.

Banbancin ƙashin mace da namiji

A duk cikin ƙasusuwan da qka yi bayaninsu, duk iri ɗaya ne tsakanin na namiji da na mace, sai dai ka samu dan banbancin girma. Amma a fasalin ƙashin kwankwaso, za ka iya samu cewa, na mace, yana da faɗi sosai, fiye da na namiji.

An yi hakan ne domin a faɗaɗa kwankwason mace, ta yadda idan ta zo wajen haihuwa ya kasance cewa kan jaririn zai iya fitowa a cikin salama.

Manazarta

Admin, L. (2022, September 8). Tsarin kwarangwal na mutum – nau’in kasusuwa, tsari, ayyuka, cututtuka.Food near me.com

Kashe mutum. Anatomy: (n.d.) ƙasusuwan mutane. Kwancen ɗan adam da sunan kasusuwa. Atomielyme.com

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading