Skip to content

Lantarki

Kalmar “Lantarki” na ɗaya daga cikin ararrun kalmomin da Hausawa suka aro daga harshen Turanci. Wato “electricity” wadda ita kuma asalin gundarin kalmar ta samu ne daga “elactron” wato asalin sinadarin madda, da Allah ya samar a bigiren duniya.

Babbar tashar wutar-lantarki

Makamashin lantarki na daga cikin nau’ikan makamashin da Allah ya samar don moriyar ɗan Adam a wannan duniya. Akwai sinadaran lantarki da ke samuwa daga walƙiya (hasken dake bayyana kafin samuwar cida) da ke ɗarsuwa a sararin samaniya. Akwai kuma sinadarai na musamman da Allah ya samar a mahallin duniyar nan da muke rayuwa. Waɗannan sinadarai na madda (Atoms) su ne suke haɗuwa da juna don samar da caji ko wutar lantarki a mahallinmu. Sinadaran kuwa su ne: “Protons,” da “Neutrons,” da kuma “Electrons.”

Haɗakar waɗannan sinadarai ne ke samar da makamashi ko wutar lantarki. A zamanin da al’ummomi kan haɗa abubuwa daban-daban don samar wannan nau’in makamashi. Bayan waɗannan har wa yau, tarihi ya nuna cewa al’ummomin da suka gabata musamman na ƙasar Masar da daular Girka na cikin waɗanda suka fara gano samuwar makamashin lantarki daga jikin wasu daga cikin dabbobin dake cikin ruwa, musamman kifaye.

Akwai nau’in kifi da ake kira – “Electric Fish,” wanda ke ɗauke da sinadaran lantarki a jikinsa. Irin wannan kifi idan ka taɓa shi nan take zai ja ka, kamar yadda wutar lantarki ke jan wanda ya taɓa ta ba tare da wani shamaki ba. Irin wannan nau’i na kifi shi ake kira: “Electrogenic Fish.”

A ɗaya ɓangaren kuma akwai waɗanda su ba sa ɗauke da wannan caji na lantarki a jikinsu, sai dai kuma duk inda akwai cajin lantarki ko sinadaran lantarki, suna iya fahimtarsa. Waɗannan su ake kira – “Electro-receptive Fish.” Masana kimiyyar lantarki suka ce ire-iren kifayen da ke ɗauke da sinadaran lantarki suna da yawa, sannan an kiyasta cajin lantarkin da ke jikinsu na tsakanin 60 zuwa 600 ne a ma’aunin lantarki na “Volts” (60 – 600volts).

Bayan dabbobin ruwa da sinadaran mahalli dake haddasa samuwar makamashin lantarki, jikin ɗan Adam ma yana ɗauke da sinadaran lantarki. Wannan ɓangare kuwa shi ne ƙwaƙwalwarsa. Idan muka bincika a kimiyance tsakanin ƙwaƙwalwa da zuciya kwai jijiyoyin dake ɗauke da sinadaran lantarki mai suna: “Neurons.” waɗanda kai tsaye sune suke isar da saƙo tsakanin waɗanan abubuwa biyu cikin sauƙi da kuma gaggawa tamkar wutar lantarki. Waɗannan jijiyoyi masu ɗauke da tubalin halitta (Neural Cells), su ne ke aikin sadar bayanai ɗan Adam da sauran sassa.

Malaman kimiyyar ƙwaƙwalwa na wannan zamani sun tabbatar da cewa akwai ire- iren waɗannan jijiyoyi masu dauke da sinadaran lantarki sama da biliyan ɗari (100,000,000,000) a jikin kowane ɗan Adam mai rai. na ƙwaƙwalwar da jikinsa.

A wannan zamani kuma da muke rayuwa, fannin lantarkin da muke amfana da shi ya samo asali ne daga gaggan masana guda uku. Waɗannan masana kuwa su ne:

Benjamin Franklin, ɗaya daga cikin masana fannin kimiyya a ƙasar Amurka, wanda ya fara kwatanta cewa – walƙiya da ke samuwa daga sararin samaniya yayin da ake cida, tana ɗauke ne da sinadaran lantarki. Ya gudanar da bincike na musamman a kan haka.

Edison, wanda aka fi danganta wannan fanni gare shi, shi ne babban sanadi wajen samar da ƙwan lantarki, don janyo makamashin lantarki da kuma tabbatar da iƙirarinsa.

Nikola Tesla, ya rayu ne tsakanin samar da lantarki da yaɗa shi ko rarraba shi. Ɗaruruwan jama’a da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen ganin fannin ya haɓɓaka kamar yadda yake a halin yanzu suna da dama amma waɗanan su ne suka fi fitowa a zahirance.

Ana cajin wayoyi da wutar-lantarki

Amfanin wutar lantarki

Wutar lantarki na da amfani matuƙa ta fuskar gudanar da rayuwar ɗan Adam ta yau da kullum. Kama daga kan kasuwanci da karatu da hidindimun rayuwa ta kowace, fuska wutar lantarkin tana ba da gudunmawa.

Caji

Ta hanyar caji kaɗai idan muka duba za mu ga amfanin da ake yi da wutar lantarki, wayoyinmu na buƙatar caji domin gudanar da rayuwa wanda akasarin saye da sayarwarmu ya koma ta fuskar sadarwa.

Siye da sayarwa

Sosai muna amfana da makamashin lantarki ta hanyar cinikayya, wanda hakan kan taimaka wurin bunƙasa fannin. Ana samun naƙasu a wasu kasuwancin namu idan aka samu rashin wutar lantarki wanda hakan har ya janyo wasu kan juyqvsu yi amfani da fasahar solar system domin samun wannan haske don gudanar da lamuransu.

Cigaban Kimiya da Fasaha

Wutar lantarki ta taimaka kwarai wajen hauhawar Kimiya da Fasaha ta fuskar kawo sauyi da kuma cigaba, domin da wutar lantarki ne wasu ayyukan suke samuwa cikin gamsarwa da kuma sauƙaƙawa. Wutar lantarki ita ce injin cigaban fasaha da kimiyya da yawa waɗanda suka faru a cikin ƙarnukan da suka gabata.

Tafkin Kainji, wanda ke samar da wutar-lantarki

Sadarwa

Mafiya akasari manyan hanyoyin sadarwa na zamani an haife su ne daga wutar lantarki, waɗanda a yau duk abubuwan da ke tattare da su kayan aikin da ake buƙata don watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo da muka fi so duk da makamashin lantarki suke amfani.

Illolin wutar lantarki

Wutar lantarki, da sauran nau’ikan makamashin lantarki suna da matsaloli ko haɗura, har ma suna iya cutar da rayuwar ɗan Adam. Kaɗan daga ciki sun haɗa da;

Samuwar cuttutuka

Tabbas a lokacin ɗaukewar wutar lantarki akan iya samun wasu cuttuka musamman a lokacin irin na zafi. Idan akwai samuwar wutar lantarki to akwai samuwar iska da za ta taimaka wa numfashin ɗan Adam sarrafuwa yadda ya kamata. Faruwar ɗaukewar ta a lokacin buƙata irin na zafi kuma kan iya haifar da sarƙewar numfashi ga ɗan Adam har ma a kamu da lallura irin ta sanƙarau.

Durƙushewar ayyuka

A lokacin gazawar samar da wutar lantarki kamar katsewar wutar lantarki na iya faruwa, wanda zai iya shafar ɗimbin jama’a a wani yanki. Wutar lantarki na haifar da girgizar wutar lantarki kuma tana iya haifar da ƙuna ma fi muni.

Kammalawa

Idan muka yi duba ga bayanan sama zuwa ƙasa, za mu fahimci lallai makamashin lantarki na taka muhimmiyar rawa cikin duniyar ɗan Adam da kuma rayuwarsa ta kowace fuska.

Manazarta

https://www.renovablesverdes.com/ha/wutar-lantarki-b/

https://babansadik.com/kimiyyar-lantarki -a- sawwake-2/

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×