Skip to content

Maciji

Ɗaya daga cikin halittun da ake firgita da shi a duniya shi ne maciji. Macizai halittu ce masu rarrafe marasa fuka-fuki da gabobin jiki. Jikinsu siriri ne yana farawa da kai kuma yana ƙarewa da wutsiya mai murɗawa. Suna iya zama a ƙasa ko a cikin ruwa dangane da nau’in da suka kasance. Wasu macizan na iya haɗa duka biyun. Wasu suna yin sara su zuba dafinsu kafin su ci abin da suka farauta. Wasu sukan kai hari da mugun nufi su kacaccala abin farautar, su kashe sannan su.

Macizai kan yi amfani wannan abin na bakinsu wajen fahimtar kusancinsu da abin farauta ko abin cutarwa.

Akwai nau’ikan macizai sama da 3,000 a duniya kuma ana samun su a ko’ina amma ban da Antarctica, Iceland, Ireland, Greenland, da New Zealand. Kimanin nau’ika 600 suna da dafi, kuma kusan guda 200, kaso bakwai cikin ɗari ke nan suna iya kashewa ko raunata ɗan’adam sosai. Macizai na daga cikin halittu masu ban mamaki da tsoro a duniya. Suna zuwa da sifofi, girma da launuka iri-iri kuma ana iya samun su a kusan kowane lungu da saƙo na duniya.

Kusan dukkan macizai suna rufe da fatar saɓa, suna rarrafe ne ko jan ciki kasancewar su marasa ƙafa ko fiffike, suna da jini mai sanyi amma su daidaita zafin jikinsu har ya dace da waje. Suna amfani da saɓarsu don dalilai da yawa: kamar ɗaukar danshi a cikin yanayi mara kyau don su rage zubar da saɓa a yayin da suke tafiya. Akwai nau’ikan macizai da yawa waɗanda galibi marasa saɓa ne, amma duk da haka waɗansu suna saɓa a iya a cikinsu.

Yadda macizai ke farautar abinci

Macizai suna da harshe mai yatsu, wanda sukan yi amfani da shi ta hanyar fito da shi suna kada shi a wurare daban-daban don jin warin kewayensu. Wannan yana ba su damar sanin ko suna kusa da haɗari ko kuma abinci.

Macizai nau’in-nau’i ne kuma suna da launuka mabanbanta.

Maciji suna da wasu hanyoyi da yawa don gano abin ciye-ciye. Wata kofa da ke a gaban idanunsu suna amfani da ita don jin zafi da gano abin kalaci mai jini a jikinsa. Kuma ƙasusuwa a cikin muƙa-muƙansu na ƙasa suna jin girgizar gudun beraye da sauran dabbobi masu yawo. Lokacin da macizai suka kama abin kalaci, suna na iya cin abin har ninki uku fiye da faɗin kawunansu saboda muƙa-muƙansu na ƙasa suna kwance daga muƙa-muƙan sama.

Yadda macizai ke tafiya

Nau’in macizai daban-daban suna tafiya ta hanyoyi daban-daban. Kamar yadda masanan dabbobi suka ce, akwai rukuni iri-iri da ake samu a cikin dangin maciji.

• Ta hanyar serpentine

Wannan ita ce hanyar da maciji ke tafiya gabaɗaya a ƙasa. Ba su da ƙafa don haka suna amfani da tsoka don lanƙwasawa da haifar da motsin da suka saba da shi. Za a yi mamakin cewa suna amfani da saɓar da ke cikin ƙananan sashin jiki na tsaye wanda ya taɓa ƙasa. A cikin irin wannan motsi, macizai ba za sa shawo kan kowace matsala ba sai dai su yi ƙoƙari su samar da hanya su ci gaba da tafiya. Wannan shi ne yadda nau’ikan macizai ke motsawa a ƙasa.

• Ta hanyar concertina

Wannan salon tafiya ne wanda bai dace ba idan ya zo ga macizai. Maiyuwa ba shi ne hanya mafi kyau don tafiya cikin sarari ba wajen kama abin farauta ko guje wa mafarauta, amma tana da fa’ida sosai don yin tafiya a cikin sarari mai kunci. A cikin wannan hanyar, maciji yana riƙe sashin bayansa yayin da yake faɗaɗa ɓangaren gaba ta amfani da baya a matsayin garkuwa. Sannan kuma ya daidaita sashin gaba don matsar da sashin baya.

Macizai na da hanyoyin da suke tafiya daban-daban.

• Ta hanyar slide winding

Wannan hanya ce mai wahala ta yin tafiya a sararin ƙasa, amma tana da tasiri sosai lokacin da saman ƙasa ya daidaita ko ƙasa ta zama mai laushi. Kamar tafiyar macizai a yankunan hamada. Ba sa tafiya gaba kai tsaye, sai dai su yi motsi ta hanyar lankwasawa su naɗe jikinsu sannan su miƙa da jikin. Hanyar tafiyar ta dogara da inda macizan ke zaune. Wannan tsarin tafiyar ta dace da macizan da ke zaune a wurare masu laka, fadama, da hamada.

• Ta hanyar rectilinear

Wannan hanyar tafiya ce a hankali marar sauri, amma tana da fa’ida sosai a yayin da maciji ke tunkarar wani abu mai cutarwa ko abin kalaci. Macizai na iya yin tafiya mara sauti ta hanyar amfani da wannan hanya mai jinkirin motsawa, wacce ba sa lankwasa jikinsu. A wannan hanyar suna yin amfani da natsuwa, saɓar cikinsu tana kama saman ƙasa kuma tana aiki sosai.

Tsarin haihuwa da rayuwar maciji

Kamar yadda aka bayyana a sama, maciji dabba ce mai rarrafe kuma mai yin ƙwai. Don haka, rayuwar maciji tana farawa daga ƙwai.

• Ƙwai

Bayan gama barbara tsakanin macizai mace da na namiji, mace takan adana maniyyi da aka tattara daga namiji. Maniyyi na iya kasancewa a cikin oviduct (wani bututun da ƙwai da maniyyi, na dabbobi kan bi) na akalla wata ɗaya ko biyu. Da zarar maniyyin halittun biyu ya gama haduwa, kwai zai fara tasowa da girma a cikin mahaifar mace. Tana yin ƙwai 10 zuwa 15 a lokaci guda. Ɓawon ƙwan ba shi da ƙwari sosai kamar na tsuntsaye. Don haka za ta kula tare da ba wa ƙwayayen kariya da dukkan ƙarfinta har sai sun fara ƙyanƙyashewa. Tsawon lokacin ƙyanƙyasar ya bambanta daga wannan nau’in zuwa wancan. A zahiri ma dai, ya dogara da yanayin muhallin da macizan suka kasance.

Macizai sukan haihu ne ta hanyar yin ƙwai.

• Matasan Macizai

Bayan ƙwayaye sun kyankyashe, macizai za su fito. Hakan dai tana faruwa lokacin da yanayin muhalli ya ba da isasshen adadin zafin da ake buƙata. Ƙananan macizai suna fasa ɓawo da haƙoransu masu laushi. Gwagwarmayar neman abinci da tsira ta fara. Macijiya ba ta shayar da ‘ya’yanta. Dole ne su nemi abinci kusan da kansu. Suna rayuwa ta hanyar cin ƙananan ɓeraye, dabbobi masu rarrafe, da sauransu. Suna zubar da saɓa aƙalla sau 4 a lokacin girma. Wannan yana taimaka musu wajen samun sabuwar fata da kuma kawar da kwayoyin cuta da ke zaune a jikin fata.

• Babban maciji

Wannan matakin na rayuwar macizai ya bambanta dangane da nau’ikan macizan. Idan maciji ya kai shekarun girma, yana zubar da fata sau biyu a shekara. Suna farautar abinci da tsira da kuma rayuwa, kuma suna neman macijiya don yin mata barbara. Da haka ne tsarin rayuwarsu ke tafiya.

Dafin maciji

An bayyana nau’in macizai nawa ne a cikin daular dabbobi ta hanyar ƙiyastawa. Macizan ruwa sun bambanta kuma sun fi macijin kan ƙasa dafi. Idan ana maganar dafin macizai, ana kama macizan don fitar da dafin da yin magunguna. Ana samar da dafin a cikin jaka. Ana makala wannan jakar ga haƙoran (canine) na gaba ta hanyar wani bututu. Babban maciji na iya sarrafa adadin dafin da yake son yi wa abin farauta ko mafarauci. Jaririn maciji yana ɗaukar makamancin wannan adadi kuma yana ƙoƙarin yin harbin fiye da dafin da ake buƙata wanda kan haifar da asarar rayuka.

Sama da kashi 40% na harbin da maciji ke yi na bawa kansa kariya ne a yanayi. Ba sa so su zubar da dafin ga wani abu babba ko kuma abin da ba za su iya ci ba. A wasu lokuta, suna yin sara amma ba sa zuba dafin. Suna yin hakan a matsayin barazana ga dabbar da ke tunkaro su. Ɗaya daga cikin shahararrun nau’in macizai masu zafi shi ne rattlesnake. Yana da mummunan suna idan ana maganar dafin maciji. Yana kai hari ne kawai lokacin da aka yi masa lalata ko aka tsokane shi. Haka lamarin yake ga Indian cobra.

Alaƙar mutane da macizai

Macizai sun kasance wani bangare na tatsuniyar ɗan’adam tsawon shekaru dubu. Ana fassara macizai a matsayin mugaye da maciya amana a cikin kowace tatsuniyoyi ko tatsuniyoyi. Wannan a zahiri yana cutar da macizai fiye da yanayin canjin yanayi. Mutane ba sa ko ƙoƙarin koyon yanayin macizai kuma suna son kawar da su ko da nau’in jinsin ba shi da lahani. Akwai nau’ikan macizai daban-daban inda mafi yawansu ba su da dafi.

Mucizai na ɗaya daga cikin halittun da ake jin tsoro a duniya.

Mutane sun mutu sakamakon saran maciji. Yana faruwa ne kawai lokacin da maciji ya yi barazanar kasancewar wani dabba da ba ya so. Asarar rayuka da dabbobi ta dalilin saran macizai, ya sa ake yin tunanin cewa maciji ba komai bavne illa makiya ga mutane.

Wuraren da macizai suke rayuwa

Za a iya samu macizai kusan a ko’ina cikin duniya. Dabba ce mai sanyi don haka yana da wuya ta rayu a cikin tsananin sanyi. Shi ne kawai yanayin da macizai suka kasa jurewa su tsira a cikinsa. Don haka za a same su a cikin maɓuɓɓugar ruwa, ƙasa, tekuna, marshes, da kuma tafkuna. Ana samun su a cikin dazuzzukan wurare masu zafi, hamada, ciyayi, har ma a ƙarƙashin tsoffin gine-gine. Suna samun rami kuma suka shiga don tsira daga duniyar barazana a waje. Abu ɗaya da ya kamata a sani game da maciji shi ne koyaushe yana zaɓar wurin kebantacce mai ƙarancin tashin hankali.

Saran maciji na iya hallaka mutum har lahira.

Siffofi da ɗabi’un macizai

  • Macizai suna jin wari da harshensu
  • Wasu macizai suna da dafi
  • Wasu macizan ba su da dafi
  • Mafi tsayin maciji ya wuce mita 6, ana kiran shi da python
  • Maciji mafi sauri zai iya tafiyar mil 12 a awa ɗaya
  • Macizai suna jin motsin jijjiga a ƙashin muƙamuƙi
  • Macizai suna zubar da saɓa
  • Macizai suna da ɗaruruwan ƙasusuwan hakarkari
  • Macizai suna da fata da launi iri-iri
  • Macizai na iya faɗaɗa don haɗiye manyan abin farauta
  • Macizai na tsawon jiki, ba su da gaɓa

Manazarta

Divers, S. J. (2020, September 8). Description and physical characteristics of reptiles. MSD Veterinary Manual.

Georgia. (2024, March 12). Top 10 Facts About Snakes! – Fun Kids – the UK’s children’s radio station. Fun Kids – the UK’s Children’s Radio Station.

Pythons 101. (n.d.). [Video]. Animals.

Vedantu. (n.d.). Snake. VEDANTU.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×