Skip to content

Makanta

Makanta cuta ce da ta shafi idanu, wato mutum kan rasa damarsa ta gani da idanunsa a dalilin kamuwa da cutar makanta. Makanta kan samu sakamakon faruwar wani abu a ido, wasu kuma sukan samu cutar ne tun daga ciki. Haka nan makanta na nufin nasakar gani ga ɗan’adam ko dabba dalilin faruwar wani abu ko kuma haka kawai.

Nau’ikan makanta

Cutar makanta na iya zama ta gado..

1- Makanta kai tsaye: Akwai makantar da mai ɗauke da cutar ba ya gani kwata-kwata a rayuwarsa, wannan shi ake kira da makaho na kai tsaye.

2- Dundumi: Ita makantar da mai ita ba ya iya rasa ganinsa sai da daddare, wannan makanta ita ake kira dundumi.

3- Dishi-dishi: Wannan nau’in makanta ne da mai ɗauke da ita ba ya iya gano abu daga nesa, sai ya matso gab da shi sannan yake iya tantancewa. Wannan nau’in na uku ita ce akasari makantar da ake yankawa gilashi (tabarau).

Su wa makanta take kamawa?

Makanta cuta ce don haka tana iya kama kowa da kowa, babba ko ƙarami, tsoho ko kuma matashi haka kuma mutum ko dabba kowa na iya kamuwa da ita.

Dalilan makanta

Dalilan samuwar makanta suna da yawa, wasu ma kai tsaye da ita ake haihuwar shi, wato abin da ya shafi gado. Wasu kuma sukan kamu sakamakon aukuwar wani sababi ne na rayuwa. Wasu daga cikin dalilan kamuwa da makanta sun haɗa da:

Tsufa

Tsufa na ɗaya daga cikin abin da ke raunana duk wata gaɓa ta ɗan’adam a rayuwarsa. Cikin abin da tsufa ya fi nasarar raunatawa ta fuskar lafiya shi ne ido, sai dai kuma ba ga kowa ba domin wasu suna tsufa da idanunsu.

Fashewar hanyoyin jini

Hanyoyin jini da ke kaiwa da kuma dawo da jini ga ido duk wacce ta fashe cikinsu za ta iya janyo makanta.

Cuttutuka

Akwai jerin cutukan da ke janyo makanta, yawancin manyan cutukan da suka zama gagrarru kuma ruwan dare kan janyo makanta. Cutuka irin su hawan jini da ciwon suga masu tsanani, da cutar sikila, da ciwon daji, suna iya toshe hanyoyin da ke kai jini zuwa ga ido, wanda zai iya kawo makanta a hankali ga mutum idan suka taɓa wasu sassa na idanu masu muhimmanci da abin da ya shafi gani.

Glacoma

Wata cuta ce wadda take kama idanu, ta sa ganin mutum ya samu matsala, wanda hakan kan jawo makanta. Kazalika wannan cuta, mafi yawancin lokaci ta fi kama masu shekaru, wadanda shekarunsu suka haura 40.

Sannan, idan akwai masu wannan cuta a gidanku ko a danginku, akwai barazana ko yiwuwar kamuwa da ita. Haka zalika, masu fama da hawan jini da kuma wadanda suka jima suna shan sha-ka-fashe, su ma akwai barazana tare da yiwuwar kamuwa da wannan cuta a tare da su. Ba a warkewa daga wannan ciwo idan ya yi kamari ko ya ta’azzara.

Har wa yau, yadda mutum zai san ya na da wannan ciwo na ‘glacoma’ shi ne, idan ya ga yana yawan yin ciwon ido ko ya ga ba ya gani sosai ko ya rika ganin hawaye na fita a idanuwansa ko kuma ya ga idanun nasa yana yin ja.

Wasu ƙarin dalilan da ke kawo makanta

Ciwon idon gama-gari: Ana iya kamuwa da makanta a dalilin ciwon idon yau da kullum.

Anophthalmia: Yana faruwa ne yayin da aka haifi mutum da ido daya yana gani ɗaya kuma ba ya gani, hakan kan shafar raunin ganinsa har ta kai ga gabaɗaya idanun sun kamu.

Microphthalmos: Cuta ce da ake haifar yaro da ƙananun ido sosai, wanda hakan kan taka rawa wurin raunata ganinsa har ma a iya rasa ganin baki ɗaya.

Ciwon kai: Ciwon kai mai tsanani yana iya haddasa wa mutum makanta, musamman ciwon kai na gefe ɗaya (migrain).

Rufewa ko kuma gocewar zinariyar Idanu: Akwai zinariya ta idanu wadda take a bayan ido da ke sarrafa haske, kuma ta tura wa ƙwaƙwalwa har mutum ya iya tantance launi. Wannan zinariyar tana iya kaucewa daga mazauninta wanda shi ma ke janyo makanta. Akasari idan hakan ta kasance babu wani abu da ake iya yi wa wannan ido, domin ita babu maganinta, sai dai kuma idan da rabo tana juyowa ta dawo mazauninta wanda hakan kan sa a samu waraka.

Duka: Mummunana duka na iya haifar da makanta, musamman a gefen fuska ko kuma kusa da idanu.

Jarirai: Yara jarirai waɗanda iyayensu ba sa haƙurin kama musu kai da sunan kitso, hakan kan iya haifar musu da makanta ta kai tsaye, domin lokacin da ake kama kawunansu ba su isa kamawa ba. Masana kuma sun tabbatar da yadda jijjiyar gashi take da kusanci da ta idanu. Wanda hakan kan ba su matsaloli da dama, sai a samu makanta ta kai tsaye ba tare da an ankare ba.

Amfani da abubuwa barkatai a ido: Yawan amfani da magunguna barakatai, ko amfani da wasu abubuwa kamar kayan ado da mata suke amfani da su, yawaitar hakan kan iya taɓa ido ya soma da ciwo, idan ya ta azara ya kan iya zama makanta ta kai tsaye.

Haɗari: Haɗari na kai tsaye kan iya samun ɗan’adam ya rasa ganinsa sakammakon buguwa. Akwai kuma haɗari irin na sakacin barin yara suna wasa da kibiya ko allura da kuma sauransu. Akwai kuma haɗarin afkuwar jifa ko harbi da danƙo da gwafa da sauransu.

Matakan kariya daga makanta

  • Zuwa asibiti akai-akai don duba lafiyar idon na ɗaya daga cikin babban matakin kariya da zai iya ɗauka. Yana da muhimmanci haka kawai mutum ya je a duba lafiyar idonsa, musamman waɗanda suka yi shekara 40 da abin da ya yi sama, saboda galibi ciwon ido ya fi bayyana ga waɗannan mutane.
  • Waɗanda ke da ciwon ido a cikin zuriyarsu, su ma yana da kyau su je a dinga duba musu lafiyar idonsu ko da ba su da alama ta wata lalura. Saboda abu ne da ya shafi gado.
  • Mutum ya dage da amfani da duk abin da ya shafi kariya ta ido daga rauni musamman ga waɗanda aikinsu ya shafi tsautsayi ga ido, kamar masu walda da masu acaɓa, da iska ke dukan fuskarsu kodayaushe, da masu sana’ar kafinta, da kanikawa, da ma waɗanda ke amfani da kamfutoci.
  • Dangane da masu fama da ciwon hawan jini da na suga. Bayan kula da hawan jinin da ciwon suga da ake yi, ya kamata su dinga samun awon ido ko duba lafiyar idonsu lokaci-lokaci saboda a ɗauki matakin da ya kamata idan an gano wata matsala dangane da idon.

Manazarta

AOA. (n.d.). Low Vision and Vision Rehabilitation AOA.

EyeWiki. (n.d.). Eye  Eyewiki

  1.  The American Foundation for the Blind. (n.d.). Key Definitions of Statistical Terms. The American Foundation for the Blind.

Vision and eye health. (2023, November 29). Vision and Eye Health.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×