Kalmar Petroleum ta wanzu ne ta hanyar haɗuwar kalmomi guda biyu na Girka “Petra” da kuma kalmar Latin “Oleum”. Ma’ana man dutse. A yayin da aka haƙo shi daga cikin ƙasa ana kiran shi crude oil (wato ɗanyen mai).
Man fetur, ana kuma yi masa laƙabi da baƙin zinare. Wannan suna kawai ya isa ya bayyana cewa man fetur abu ne mai matuƙar mahimmanci ga jama’a. Makamashi ne mai ɗauke makamasai da saurann sinadarai dangoginsa, waɗanda ake amfani da su wajen sarrafa wasu abubuwa daban-daban kamar samar da sauran makamasai tun daga shekarar 1950.
Man fetur abu ne mai sigar ruwa-ruwa wanda akan samu ta hanyar wasu halittu da kuma cikin manyan duwatsu. Wannan ya ƙunshi wasu hadaddun sinadaran ƙwayar halitta daban-daban na hydrocarbons, da sauran sinadarai.
Samuwar man fetur
An gano man fetur tun tsawon shekaru 4000 da suka wuce. Sai dai an yi amfani da man fetur na farko da aka haƙo daga ƙasa shekaru 2500 da suka gabata a China, kuma rijiyar mai ta farko a duniya da aka fara haƙar man fetur ita ce wacce take a Pennsylvania, Amurka a shekara ta 1859.
Yadda man fetur ke samuwa
- Ana samun man fetur daga matattun tsirrai da dabbobi.
- Lokacin da tsirrai da dabbobi suka mutu, suna nitsewa su zauna a karkashin teku.
- Miliyoyin shekaru da suka wuce, waɗannan matattun dabbobi da tsirrai suna bazuwa kuma suna haɗuwa da ƙasa su daskare.
- Wasu ƙwayoyin halitta suna taimakawa wajen ruɓar da waɗannan matattun halittun kuma su haifar da wasu canje-canje na sinadarai.
- Ƙwayoyin halitta sun ƙunshi yawancin carbon amma babu hydrogen. Kamar yadda babu isasshiyar iskar oxygen a kasan teku, matattun halittun ba za su iya ruɓewa gabaɗaya ba.
- Waɗanda suka ɗan ruɓe ɗin za su kasance a ƙasan teku kuma daga baya sai ƙasa ta rufe su.
- Wannan rufewar da ƙasa ta yi yana ɗaukar miliyoyin shekaru, kuma a ƙarshe, saboda tsananin zafi da matsi, matattun halittun nan za su ruɓe gabaɗaya sai su samar da man fetur.
Matatun man fetur
Matatun man fetur wasu manyan masana’antu ne da suke da ɓangarori da sashe-sashe a cikinsu, waɗanda suka haɗa da sashen tace man fetur ɗin da kuma ma’adanarsa. Waɗannan matatun suna da kyakkyawan tsarinsu da ya haɗa hanyoyin aiwatar da ayyuka a bisa tsari da buƙatar fitar da albarkatun da ke cikin man fetur ɗin da kuma manufar tattalin arziki.
Matatar man fetur masana’anta ce ko wurin da aka tanada don sarrafa ɗanyen mai, ta yadda zai zama mai amfani, ana fitar da abubuwa da dama kamar man fetur, kalanzir, da gas da man jirgi. Masana’antun tace ɗanyen mai yawanci suna da girma, kayan aikin ma masu girma ne tare da bututun da ke jigilar tura man zuwa ko’ina.
Man fetur (Petroleum) gamayyar abubuwa ne da yawa kamar gas, fetur, diesel, kalanzir, man injina, makamashin paraffin wax, da sauransu.
Kamar yadda waɗannan makamasai suke daban-daban kuma suke da amfani mabanbanta, don haka wajibi ne a raba su, kowanne a ware shi. Wannan hanya ta ware ko rarrabe waɗannan abubuwan da ake kira Petroleum ko crude oil, ita ake kira da tace mai. Kuma ana yi ne a matatar mai, sannan ta ƙunshi matakai guda uku.
- Mataki na farko shi ne ware abubuwan da ke cikin ɗanyen man ta hanyar tacewa. Sinadarai masu na nauyi za su zauna a ƙasa, yayin da marasa nauyi za su taso sama kamar tiriri, ko kuma nau’in ruwa-ruwa.
- Bayan haka, sauran abubuwa waɗanda suke da nauyi sosai, ana canja su, su koma makamashin gas da dizal. Don haka, mataki na gaba shi ne canjawa.
- Ragowar sinadaran da ke da nauyi kuma suke ƙasa har yanzu ba su tatu ba, don haka mataki na ƙarshe shi ne sarrafa su ta wata hanyar, ana sarrafa su har a samar da wasu nau’ikan sinadarai da makamasai.
Amfanin man fetur
Albarkatun da aka fitar ko aka tato daga ɗanyen mai suna da alfanu da yawa, daga ciki akwai:
- Ana amfani da iskar gas, ko gas mai nauyi ko LPG gidaje da kuma a masana’antu.
- Diesel da fetur ana amfani da su a ababen hawa. Mafi akasari diesel ana amfani da shi don manyan motoci da injina.
- Haka nan ana amfani da fetur a matsayin sinadari mai ƙarfi don busar da abu, yayin da ake amfani da diesel a injinan samar da wutar lantarki.
- Ana amfani da kalanzir a rusho don yin girki da kuma ƙananan jirage.
- Ana amfani da baƙin mai a injina.
- Ana amfani da makamashin paraffin don yin kyandir, man shafawa, tawada, crayons, da sauransu.
Haɗarin man fetur
Tun daga wutar lantarkin da ke haskaka gidajenmu zuwa motocin da muke tukawa zuwa aiki, rayuwarmu a wannan zamanin ta ginu ne kacokan bisa albarkatun ɗanyen mai kamar kwal, fetur, baƙin mai da iskar gas.
Sai dai kuma ƙona su na haifar da sauyin yanayi kuma yana fitar da gurɓatattun abubuwa waɗanda ke janyo mutuwa da wuri, bugun zuciya, cututtukan numfashi, bugun jini da cutar asma.
Yawaitar amfani da man fetur da dangoginsa ta hanyar ƙonawa yana haifar da gurɓatacciyar iska wacce ke cutar da lafiyar al’umma, kuma tana haifar da hayaƙi mai guba wanda ke janyo gurɓata da ɗumamar yanayi.
Bincike daga Jami’ar Harvard, tare da haɗin gwiwar Jami’ar Birmingham da Jami’ar Leicester da Kwalejin Jami’ar London, sun gano cewa fiye da mutane miliyan 8 ne suka mutu a shekarar 2018 sakamakon gurɓatacciyar iska daga ƙonannun albarkatun ɗanyen mai. Abubuwa kamar kwal da dizal ne ke da alhakin mutuwar kusan kashi 1 cikin 5 a duniya.
Manazarta
Chen, J. (2024, April 17). What Is Petroleum? Why It’s Important and How To Invest in It. Investopedia.
Petro Industry News. (n.d.). What is in Petrol? Petro Online.
Chan School of Public Health. (2022, June 28).Fossil fuels & health. C-CHANGE | Harvard T.H.