Skip to content

Mantuwa

Mantuwa wani yanayi ne da ke wanzuwa a cikin ƙwaƙwalwa, ma’ana gaza tuna bayanin da ke cikin ƙwaƙwalwar. Misalin bayanin shi ne hirar da aka yi da mutum yanzu, yarintar mutum da komai ma. Domin duk wani abu da aka ji, ko aka gani, aka ɗanɗana da sauran su ya zama a cikin ƙwaƙwalwa. Saboda ƙwaƙwalwar mutum ce take dauke su kuma take adanawa.

Mantuwa cuta ce ta ƙwaƙwalwa

Matakan adana bayanai

1. Encoding (Naɗar bayanai)

Wannan na nufin shigar bayanai ko samar da bayanai a cikin ƙwaƙwalwa. Ta wace hanya bayanai ke shiga ƙwaƙwalwar? Ta ido idan a rubuce ne ko kuma, a takaice, ta hanyar gani. Haka idan aka yi magana bayanin zai shiga ta kunne ke nan. Idan taɓa mutum aka yi ta hanyar fata. Idan ƙamshi ne ko wari, ya shiga ta hanyar hanci. Idan ɗanɗano ne kuma ta hanyar harshe. Saboda waɗannan su ne hanyoyin da ƙwaƙwalwa take samun bayanai – ido, harshe, fata, kunne da hanci.

Ta hanyar da abu yake zaunawa a ƙwaƙwalwa na farawa ne da encoding. Kamar dai kwakwalwa ta fassara wannan information ɗin yadda za ta iya adana shi. (Abin da ya sa aka ce fassara shi ne duk abin da aka ji aka gani da sauran su ƙwaƙwalwa ce ta fassara shi haka. Idan aka ga mota, saboda ƙwaƙwalwar ta fassara wannan abin da aka gani a matsayin mota ne). Wannan hanyar ta encoding ta ƙunshi sensory inputs (sensory inputs shi ne duk bayanin da ƙwaƙwalwar za ta ɗauka daga hanyoyi biyar ɗin da aka faɗa), yadda kwakwalwa take fassara su sannan ta rarraba su zuwa ɓangarori na ƙwaƙwalwar, kamar irin su hippocampus da cortex.

2. Storage (Adana bayanai)

Yayin da ƙwaƙwalwa ta gama encoding (fassara) na information ɗin, za ta adana shi cikin bangarori na kwakwalwa domin tunawa. Bayanan da ƙwaƙwalwa ke adanawa irin biyu ne – bayani mai gajeren zango (short term memory) da kuma bayani mai dogon zango long term memory).

Bayani mai gajeren zango shi ne bayanin da ba zai daɗe ba mutum ya manta, misali, mutanen da mutum ya gani a kasuwa, hirar da mutum ya yi mara muhimmanci sosai, da makamantan wannan. Bayan mai dogon zango kuma shi ne bayanin da yana nan dindindin kuma zai yi wuyar mantawa.

Bambancin ƙwaƙwalwa mai lafiya da marar lafiya

3. Retrieval (Tuno bayanai)

Wannan shi ne yadda ƙwaƙwalwa take ɗauko wannan abin da ta adana (tunawa ke nan) kuma ya ƙunshi aikin neural networks waɗanda suke haɗe da bayanin sannan su dawo da bayanin zuwa hankalin mutum. Abubuwa da yawa suna haddasa faruwar wannan aikin. Misali, idan aka ga wani waje zai iya tunawa mutum wani mutumin da aka sani ko lokacin yarintar mutum. Ko idan an ji ƙanshin wani abu, shi ma za a iya tunawa mutum wani abu, ka saba da jin kanshin detol duk lokacin da ka shiga ajinka na furamare, kanshin detol zai iya tuna maka da lokacin da ka ke a furamare. Abin da aka tuna zai iya tunawa mutum wani abu shi ma, misali, kanshin detol ya tuna mini da rayuwar firamare, daga nan zan tuna da mutane da abubuwan da suka faru a makarantar. A haka dai dori-dori.

Rabe-raben tunani

– Conscious mind

Yana nufin abin da hankalin mutum yake a kansa a kuma daidai lokacin. Kamar abin da yake ran mutum a lokacin da ake ciki yanzu.
Misali tunanin da ake ji a zuciya (fushi, kunya, murna, da sauran su), da kuma abin da ke kewaye da mutum. Ma’ana kamar karanta rubutu a lokacin da ake karantawa, shi ne tunanin mutum yana kan rubutun. Domin hankalinsa ba ya kan abin da ya faru da safe, saboda an manta da shi na ɗan wani lokaci.

Sannan da abin da ake ji a rai daidai lokacin, waton farinciki, takaici ko kunya, to ko ma me ake ji a rai shi ne a tunanin. Kamar abin da ke kusa da mutum idan hankalinsa yana kansa hakan na nufin tunaninsa yana kan abin.

Subconscious mind

Bai kai concious mind ba – kamar tsaka-tsakiya ne. Amma duk da haka yana shafar tunanin mutum, halayyarsa. Misali a yi wa wani magana saboda akwai dalilin yi masa maganar. Hakan yana nufin daga Concious mind (tunani) abin yake zuwa. Idan abu daga subconscious mind ya zo, za a ji mutum ya ce ni ban san me ya sa ma na yi wannan abin ba. Abin da ake nufi a nan shi ne, idan abu yana subconscious mind, an manta da shi amma za a iya tunawa da shi kuma yana sa mutum ya yi abubuwa ba tare da ya san me ya sa ya yi ba, ko kuma ya ji tsoron abu babu dalili, ko ya ji kunya babu dalili, ko ya tsani wani abu babu dalili. Misali, za a ga mutum yana tsoron magana a gaban mutane amma ya rasa dalili. Watakila saboda tun yana yaro ya gwada yin magana a gaban mutane an yi masa dariya, ko an ba shi kunya, da sauran su.

Ko a ga mutum yana tsoron kare. Watakila saboda tun yana yaro ya ga kare ya ciji wani ne, ko ya cije sa, ko kuma ya taso ya ga mahaifiyarsa tana tsoron karen, to sai ya ɗauki wannan tsoron nata shi ma ya zama nasa tun da dabi’a daga wajen uwa ake ɗauka. Tun da tana tsoron kare, zai ɗauka karen abu ne da ya kamata a ji tsoron shi.
Mutum zai iya gano dalilin da ya sa yake yin wasu abubuwan (wanda subconscious mind take sakawa a yi kenan) ta hanyar kamar rubuce-rubuce, (wataƙila kun taɓa gano me ya sa ku ka yi wani abin da ku ka yi a lokacin da ake rubuta wani abin), ko ta hanyar zane, ko dream analysis, ko dogon tunani.

Unconcious mind

A taƙaice abin da mutum ya riga ya manta da shi wanda ba zai iya tunawa ba. Misali, abin da ya faru da safe, an manta da shi, amma idan za a faɗa za a iya tunawa, wannan ba ya unconcious mind; ya koma subconscious mind. Sannan idan akwai abin da ya faru shekara ɗaya da ya wuce wanda ba za a taɓa tunawa da shi ba in dai ba tunawa mutum aka yi ba. Wannan abin zai iya komawa unconcious mind, yadda ko an tunawa mutum ba zai iya tunawa da shi ba.

Ma’ana, abin da ake so a fahimta a nan shi ne, duk abin da yake a subconscious mind shi ma an manta da shi. Tuna shi ma abu ne mai wahala. Idan ba ta hanyar dogon tunani, ko rubutu, ko zane, ko mafarki ba. Amma abin da yake a unconcious mind ba za a tuna da shi ba an riga an manta shi amma duk da haka yana shafar dabi’ar mutum da kuzarinsa.

Sigmund Freud da Carl Jung (yan psychology) ne su ka fara gano ko da abu yana unconcious mind da subconcious mind, hakan ba ya nufin sun bar cikin ƙwaƙwalwa kuma ba za a iya tunawa da su ba.

Manazarta

Parsons, T. (1974). The interpretation of dreams by Sigmund Freud. PubMed.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×