Skip to content

Marubuci

Share |

Marubuci

Idan aka ce marubuci ana magana ne akan wani mutum na musamman, kuma mai gudanar da rayuwa ta musamman cike da gwagwarmaya tare da ci da zucin cimmawa ko kuma kasawa. Sai dai hakan ba ya taɓa sarar da shi daga manufar da take tattare da zuciyarsa.

Masana da dama sun yi bayani kan wanene marubuci? Bari mu ɗauki mahangar uban marubuta kuma jagoran cimma muradansu a kowa ce tafiya cike da mutuntawa wato Ado Ahmad Gidan Dabino. Fittacen marubucin nan Ado Ahmad Gidan Dabino ya ce, Marubuci ɗan baiwa ne, haihuwarsa ake yi ba yin sa ake ba. Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan ƙirƙiri wani yanayi na gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da abubuwa waɗanda yake amfani da su don isar da saƙo ga al’ummar da ke karatun rubutunsa.”

Shi wannan saƙo ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da hikima da hazaƙa don isarwa a sauƙaƙe, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa da shafuka har zuwa cikakken littafi.

Wani ana haihuwarsa da rubutu wani kuma koyo yake yi, amma duk marubuta za mu kira su. Shi marubuci mutum ne na daban, ba wai ya fi sauran rukunonin bil’adama ba ne, a’a, shi dai daban yake da sauran mutane, wato dan baiwa ne. Marubuci na yin tunani ne iri na daban, yana kuma kallon rayuwa da al’amuran rayuwa da wata irin fahimta tasa ta daban, sannan ya bayyana ta a rubuce. Kamar yadda aka ambata a sama shi marubuci dan baiwa ne, sannan shi kansa rubutun baiwa ne.

Abu ne sananne ga al’umar da take da ilmi cewa marubuci yana da matuƙar muhimmanci da tasiri. Saboda haka ya wajaba a kan al’ummar da ta sami marubuci a cikinta ta yi kokaririn jawo ra’ayinsa ko yin tasiri a kan tunaninsa don ya yi rubutu na kwarai, in ba haka ba duk abin da ya rubuta zai yi tasiri a kan ita al’ummar.

Marubuci kan haska wa al’umma hanya

Marubuci kan yi rubutu saboda dalilai da dama ko wani hali ko yanayi da ya sami kansa ko wani tarihi na kasa ko dadadde ko kuma wata manufa ko ra’ayi. Don haka marubuci na iya yin rubutu don ilmantarwa ko wayar da kai ko kyautatawa ko fadakarwa ko farfaganda ko ta da zaune tsaye ko cin zarafi ko kuwa tsokana.

Yana iya yin rubutu don gina wata aƙida ko rusawa ko kuwa don lurar da jama’a ko kawo sauyi ko kuma don tabbatar da wani ra’ayi ko manufa. Saboda haka marubuci na iya zama dan ƙwarai ko kuma baragurbi, sai dai a koyaushe yana kokari ne ya ga cewa ya shawo kan makaranta su amince da shi. Domin kuwa zai yi iya ƙokarinsa ya nuna musu cewa sakon nan nasa gasgatacce ne, amintacce ne kuma dauwamamme ne mai farin jini.

Yana da kyau mu fahimci cewa marubuci na da matukar muhimmaci ga duk al’ummar da yake zaune a ciki domin kuwa kadara ne ga wannan al’umma kuma yana iya jawo wani ci gaba ko dakushewa da alkalaminsa. In har ba ka fahimci manufar marubuci a rubutunsa ba, to ka ɗauka cewa ka jahlci fahimtarsa. Don haka duk irin abin da marubuci ya rubuta akwai manufa a cikinsa sai dai ko ba a fahimta ba. Amma fa ba dole ne a ce koyaushe marubuci na yin rubutu mai ma’ana ba.

Zama marubuci

Wani abin lura shi ne, zama marubuci wani al’amari ne babba. Duk lokacin da mutum ya zamo marubuci ko yake son zama marubuci, to yana shiga wani hali ne mai wuyar gaske. Na farko marubuci a kullum cikin tunani da ƙoƙaririn fahimtar al’ummarsa yake. Na biyu duk lokacin da yake rubutu dole ne ya rinƙa sanya tunaninsa da kuma mutuntakarsa. Shi ne zai zama na ƙwarai yanzu, wani lokacin kuma ya zama mugu. Ya zama yaro ya zama babba ya zama namiji ya zama mace, kuma duk lokacin da yake rubutu yana tunani ne na irin mutumin ko halin da yake rubutu a kansa.
Wani lokaci kuma marubuci tamkar ɗan-leƙen asiri ne domin kuwa muddin zai yi rubutu in har marubucin ƙwararre ne sai ya yi bincike don gano wasu bayanai ko fahimtar su. In da za ku gamu da shi a irin wuraren da yake neman bayanansa sai ka rantse ba wani abu yake yi ba. Alal misali idan marubucin yana yin rubutun da a ciki sai an yi maganar karuwai ko mashaya, kada ka yi mamaki don ka gan shi a mashaya ko yana tattaunawa da karuwa neman bayani ne ya kai shi. Ta haka yakan bi sauran hanyoyi don gudanar da binciken sa.

Muhimmancin marubuci a al’umma

Duk al’ummar da ubangiji ya albarkace ta da tarin marubuta to tana cikin ni’ima da kuma hasken rayuwa. Domin babbar ni’ima ce wadda za ta zagaye wannan al’umma ta fuskoki da dama. Kaɗan daga muhimmancin marubuci shi ne samar da mafita ga rayuwar al’umma. Domin wani zaren labarin sai bayan marubuci ya rubuta shi ya samar masa mafita sai ya yi dai-dai da rayuwar wani.

Babban muhimmancin da marubuci ke da shi ga al’umma shi ne, na yin amfani da alƙalaminsa wurin sauya al’umma. Ya zama lallai a fahimci cewa ayyukan marubuta kan yi tasiri ga al’umma kai tsaye ko kuma ta rashin sani. Don haka ya zama wajibi ga al’umamr da take da marubuta a cikinta ta ga ta taimaka musu ta kuma yi tasiri na kwarai ga tunaninsu don rubutunsu ya yi tasiri nagari ga al’umma.

A dalilin marubuci an samu gyaruwar zamantakewar rayuwa da dama, musamman rayuwar aure. Domin makaranta da dama su kan zamo masu kwaikwaiyo daga ɗabi’un jaruman da suka karanta labarai a kansu.Manyan Philosphers da dama da ake da su a faɗin duniya duk wanzu ne dalilin rubutu, domin kullum ƙoƙarin su shi ne binciko ko kuma rubuta wani abu wanda suke da ja akan sa ko kuma yaƙini akan tabbatuwarsa.

Rayuwar marubuci

Rayuwar marubuci kacokan ɗin ta sadaukarwa ce, domin yana rayuwa ne da tunanin rayuwarsa da mutanen dake kewaye da shi yayin da kuma yake rayuwa da wata duniyar daban cikin tunanin mafitar rayuwarsu. Zuciyarsa kodayaushe cikin tunani take me zai faru idan kaza ya faru?

Kimar marubuci

Marubuci nada ƙima tare martaba a idon al’umma. Ko wuri ka ratsa aka nuna wannam aka ce marubuci ne za ka ga ana ta ƙoƙarin ƙula alaƙa da shi. Kimar marubuci ta sa ko bayan ya rasu matuƙar ya yi rubutun abin a yaba duniya ba ta mantawa da rayuwarsa. Domin za a ɗaga rubutunsa ace wannan rubutun wane kaza ne. Babban mizali garemu shi ne. Abubakar Imam.har gobe rubutukansa na yawo akowa ce kafa, haka kuma ƙasashe da birane tare d garuruwan da shi kansa bai je ba amma kuma rubutunsa ya samu zuwa. Ya kuma ja masa ƙimar da har gobe ana kallonta matsayin madubi ta fuskara rayuwa da kuma ilmin amfana.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading