Skip to content

Muhimmanci da falalar hakuri ga musulmi

Share |

Bismillahir Rahmanir Rahim

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, lalle rayuwar dan adam bata tafiya daidai ba tare da hakuri ba; yana bukatar hakuri don inganta addininsa da rayuwarsa, saboda duk wani aiki dole ya hadu da wahalhalu da kunci, mai yawa ne, ko kadan. Dole a samu hakuri wanda zai dace da kowani aiki, shi yasa Musulunci ya kwadaitar da yin hakuri. Abdullahi Bin Mas’ud yace: “Hakuri rabin imani ne”. Malamai suka ce: Imani: rabinsa hakuri, rabinsa godiya.

Matsayin hakuri a addinin Musulunci kamar matsayin kai ne ga gangan jiki. Kuma babu imani ga wanda bai da hakuri. Kuma saboda matsayin hakuri Allah Ya yawaita ambatonsa a cikin Al-Kur’ani mai girma. Imam Ahmad Bin Hambal yace: “Allah madaukakin sarki Ya ambaci hakuri sau casa’in a cikin Al-Kur’ani saboda muhimmancin sa”.

Rabe-raben hakuri

Hakuri ya kasu kashi uku:

1. Hakuri kan yiwa Allah biyayya

Ya wajaba ga bawa ya lizimci yiwa Allah biyayya cikin abinda Ya yi umurni a aikata shi. Saboda wanda zai yi salloli biyar na farilla a kowace rana, ya yi tsayuwar dare yana bukatar hakuri. Allah Ya ce a kissar Lukman, inda yake yiwa dan sa wasiyya: “Ya karamin dana! Ka tsai da sallah, kuma ka yi umurni da kekkyawa, kuma ka yi hani da mummuna, kuma ka yi hakuri a kan abinda ya same ka. Lalle wancan yana daga muhimman al’amura“. Suratu Luqman, aya ta 17.

2. Hakuri kan bari sabawa Allah

Wajibi ne musulmi ya yaki zuciyar da shedan, ya yi hakuri kan bari sabon Allah, ya kauracewa barna. Allah Ya ce: “Kuma wadanda suka yi hakuri domin neman yardan Allah Ubangijinsu, kuma suka tsayar da sallah, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da kuma a bayyane, kuma suna tunkude mummunan aiki da mai kyau. Wadancan suna da akibar gida mai kyau“. (Ma’ana: Aljanna) Suratur Ra’adi, aya ta 22.

3. Hakuri kan kaddarar Allah

Wajibi ne bawa ya yi hakuri ya maida al’amarin sa ga Allah kan duk abinda ya same shi. Allah Ya ce: “Kuma ka yi bishara ga masu hakuri. Wadanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce: lalle mu ga Allah muke, kuma lalle mu gare Shi masu komawa ne. Wadannan akwai albarka a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma wadannan su ne shiryayyu“. Suratul Baqara, aya 155-157.

Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Al’amarin mumini abin mamaki ne, lalle duk al’amarin sa alheri ne, kuma babu wani wanda ya dace da haka sai dai mumini. Idan abin farin ciki ya same shi sai ya gode, hakan sai ya zamar masa alheri. Idan kuma abin bakin ciki ya same shi, sai ya yi hakuri, sai ya kasance alheri a gare shi”. Muslim ne ya rawaito wannan hadisi.

Mumini idan musiba ta same shi, ya kan yi hakuri, ya sallama, ya nemi lada, kuma ya koma ga Allah, ya tuba, ya nemi gafarar Allah. Hakika Allah yana jarraban bawa ne gwargwadon imanin sa. An tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a kan wanda aka fi tsananta wa jarrabawa cikin mutane? Sai yace: “Annabawa, sai wadanda suka biyo bayansu, mataki bayan mataki. Ana jarrabar mutum ne gwargwadon addininsa, idan addininsa mai karfi ne sai bala’insa ya tsananta. Idan kuma addininsa mai rauni ne sai a jarrabe shi gwargwadon addininsa. Bala’i  ba zai gushe ga bawa ba, har sai ya kasance yana tafiya a kan kasa ba shi da wani zunubi a kansa”.

Falalar hakuri

Hakuri yana da falaloli masu yawa, daga ciki:

Na farko: Mai hakuri yana samun lada mai yawa a wajen Allah, ba tare da ya kididdiga ladar sa ba. Allah Yace: “Hakika masu hakuri kawai ake cika wa ladar su ba tare da lissafi ba“. (Suratuz Zumar: 10).

Wannan na nuna Allah yayi alkawarin lada ba tare da kididdigewa ba ga masu hakuri, wato; ba tare da iyakancewa ko adadi ko gwargwado ladan ba.

Na biyu: Albishir mai girma ga masu hakuri. Masu hakuri suna da albishir guda uku wadanda Allah ya musu. Allah Ya ce: “Kuma ka yi bishara ga masu hakuri, wadanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce: lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne zuwa gare shi muke zamu koma. Wadannan akwai albarka a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama, kuma su ne shiryayyu“. Suratul Bakara: 155-157).

Na uku: Hakuri shi ne mafi girman kyauta ga mumini. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu wata kyauta mafi yalwa da alheri da ake bai wa bawa irin hakuri”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Na hudu: Hakuri alheri ne ga mai yin sa. Allah Ya ce: “Kuma idan kuka so rama abinda aka muku, to ku rama daidai da abinda aka muku. Kuma idan kun yi hakuri, lalle shi ne mafi alheri ga masu hakuri“. (Suratun Nahli: 126). Haka kuma Allah Ya ce: “Duk wanda ya yafe kuma ya kyautata, to ladarsa tana ga Allah”. (Suratush Shura: 40).

Na biyar: Masu hakuri suna samun kusanci da Allah, kuma Allah Yana son su. Allah Ya ce: “Kuma ku yi hakuri, lalle Allah yana tare da masu hakuri“. (Suratul Anfal: 46). Kuma Ya ce: “Kuma Allah Yana son masu hakuri”. (Suratu Aal Imran: 146).

Na shida: Allah yana sakantawa masu hakuri da mafi kyawun sakamakon abinda suka aikata. Allah Ya ce: “Abinda yake a wurinku yana karewa, kuma abinda yake a wurin Allah mai wanzuwa ne. Kuma lalle ne, Muna sakawa wadanda suka yi hakuri da lada mafi kyawun abinda suka kasance suna aikatawa“. Sunataul Nahl: 96).

Na bakwai: Hakuri yana kankare zunubai; mutum ya kan hadu da jarabawa a rayuwar sa, to idan ya yi hakuri Allah zai kankare masa zunubansa. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan Allah ya nufi bawa da alheri sai ya jarrabe shi”. Bukhari ne ya rawaito shi. Ma’ana: zai jarrabe shi, don ya tsarkake masa zunubansa, ta yadda zai hadu da Allah yana tsarkake.

Na takwas: Mai hakuri yana tare da nasara. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ka sani, lalle nasara tana tare da hakuri, kuma lalle budi yana tare da kunci, kuma tare da wahala akwai sauki”. Imam Ahmad da Hakim ne suka rawaito shi.

Abubuwan da za su taimaki bawa don ya zama mai hakuri

Akwai abubuwa masu yawa da zasu taimaki bawa don ya zama mai hakuri, daga cikinsu akwai:

Na farko: Yin zurfin tunani kan girman ladan da ake baiwa masu hakuri ranar lahira. Allah Ya ce: “Lalle ne wanda ya ji tsoron Allah, kuma yayi hakuri, to lalle ne Allah baya ladar masu kyautatawa”. (Suratu Yusuf: 90).

Na biyu: Addu’a; bawa ya yawaita rokon Allah ya azurta shi da hakuri yayin saukar musiba.  Allah Ya ce: “Ya Ubangijinmu! Ka zuba hakuri a kanmu, kuma ka dauki ranmu muna musulmai”. Suratul A’araf: 126).

Na uku: Son Allah da kuma tsoron Sa: Lalle idan bawa yana son Allah, to hakan zai ja shi zuwa ga hakuri kan biyayya ga Allah. Haka nan idan bawa yana tsoron Allah, to hakan zai sa ya hakura da sabawa Allah, da kuma hakuri idan musiba ta same shi.

Na hudu: Karanta kissoshin magabata daga cikin Annabawa da salihai, da kuma daukan darasi cikin hakuri da suka yi na ibtila’in da ya same su a rayuwarsu. Misali: Annabi Ayyub (A.S) ya yi hakuri kan rashin lafiyan da ya same shi. Haka Annabi Yusuf (A.S) ya yi hakuri akan kamewa da barin aikata sabo. Haka Annabi Ibrahim (A.S) wanda har mutanensa sun jefa shi a wuta. Da kuma hakurin da cikamakin annabawa ya yi kan isar da sakon Allah, da wahalhalun da ya sha don daukaka addinin Musulunci.

Karshe

Muna rokon Allah Ya sa mu cikin bayinSa masu hakuri, wandanda ake basu lada ba tare da an lissafa ba.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading