Aisha abdulhamid
For fruit custard we need:
Pomegranate (Ruman)
Custard
Banana (Ayaba)
Apple
Grapes
Dafarko mu fara hada custard,ki zuba chokali uku na sugar a cikin madaran da yake kan wuta,ki zuba garin custard da kika hada da ruwa a kan madaran da yake kan wuta,kiyi ta juyawa har sai yayi kauri.ki barshi ya sha iska, sai ki saka a fridge, in kina son kiyi decorating dinsa sai ki ciro custard din daga fridge ki dauko glass cup guda biyu sai ki debi chokali guda biyu ki zuba a cikin glass cup din,ki zuba custard Din a karshen cikin kofin,ki dauko pomegranate(ruman) ki zuba a kai,ki dauko grapes naki (inib )ki zuba a ciki.ki dauko ayabanki da kika yanka ki zuba a ciki, in kina da whipped cream sai ki zuba a kai in babu kuma ba sai kin sha wahala ba, ki dauko yankaken apple din ki saka a ciki.sai ki dauko ragowar custard dinki ki zuba a ciki,ki sake dauko ruman ki zuba a kai, dasu Ayaba, apple (tufa)da inib (grapes)ki zuba kamar yanda kikayi a farko