• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Shafin Farko
  • Makalu
    • Browse Entries
  • Bidiyoyi
    • Browse Videos
  • Sautuka
    • Nemo Sautuka
  • Hotuna
    • Browse Albums
    • Browse Photos
  • Zauruka
    • Browse Groups
  • Tambayoyi
  • Sanarwa
    • Bukukuwa Masu Zuwa
    • Past Events
  • Ra'ayoyi
    • Browse Polls
  • Sana'o'i
    • Browse Listings
  • Updates
  • About
  • Abokai(54)
  • Hotuna(1)

Updates

The post was not added to the feed. Please check your privacy settings.
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY
    Muna mika ta'aziyarmu ga Ummyter Abdallah bisa ga rashin mahaifinta da ta yi.

    Allah Ya jikansa da rahma, Ya sa mutuwa hutu ce a gare shi.
    • Mar 31
    • 5 person likes this
    • ASEE BEAUTY
      Hafsat Tukur Amin
      • Mar 31
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Lawan Dalha Amin Ya Rabb
      • Mar 31
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Rahmatu Lawan Amin Ya Allah
      • Apr 1
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Rahmatu Lawan's post.
    Rahmatu Lawan
    Muna mika ta'aziyarmu ga Ummyter Abdallah bisa ga rashin mahaifinta da ta yi.

    Allah Ya jikansa da rahma, Ya sa mutuwa hutu ce a gare shi.
    • Mar 31
    • 9 person likes this
    • ASEE BEAUTY
      Mohammed Sani Hassan Rahimahullah
      • Mar 29
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Jiddah Washah Amin
      • Mar 29
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Lawan Dalha Amin Ya Rabb. Allah Ya gafarta masa
      • Mar 29
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Amin,Allah yayi masa rahama
      • Mar 30
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY commented on Jiddah Washah's post.
    Jiddah Washah
    Ina mika sakon ta'aziya ga ƴar uwarmu bisa rashin babban bango na rayuwarta.
    Alla ya jikansa ya yi masa Rahama.

    Ummita Abdullahi (Fulani Ɓingel)
    • Mar 31
    • 9 person likes this
    • View all 7 comments
    • ASEE BEAUTY
      Umar Allah yasa aljanna makomarsa .
      • Mar 29
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      MumAmnash2486 Ameen ya Allah ,Allah ya kyauta tamu bayan tasu
      • Mar 30
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Amin.\n\n\nMun gode ƙwarai
      • Mar 30
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Deleted Member Allah yajikansa
      • Mar 30
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      ASEE BEAUTY Allah yajikansa da rahama
      • Mar 31
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Jiddah Washah's post.
    Jiddah Washah
    Ina mika sakon ta'aziya ga ƴar uwarmu bisa rashin babban bango na rayuwarta.
    Alla ya jikansa ya yi masa Rahama.

    Ummita Abdullahi (Fulani Ɓingel)
    • Mar 31
    • 9 person likes this
    • View all 7 comments
    • ASEE BEAUTY
      Umar Allah yasa aljanna makomarsa .
      • Mar 29
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      MumAmnash2486 Ameen ya Allah ,Allah ya kyauta tamu bayan tasu
      • Mar 30
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Amin.\n\n\nMun gode ƙwarai
      • Mar 30
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Deleted Member Allah yajikansa
      • Mar 30
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      ASEE BEAUTY Allah yajikansa da rahama
      • Mar 31
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Hauwa Dalha's post.
    Hauwa Dalha
    𝘙𝘢𝘮𝘢𝘥𝘢𝘯 𝘤𝘰𝘶𝘯𝘵𝘥𝘰𝘸𝘯 2021:
    13 days!!

    𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙔𝙖 𝙆𝙖𝙞 𝙢𝙪 𝙍𝙖𝙢𝙖𝙙𝙖𝙣
    🤲🏽🤍
    • Mar 31
    • 6 person likes this
    • ASEE BEAUTY
      Rahmatu Lawan Amin Ya Rab
      • Mar 31
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Umar's post.
    Umar
    Aslm. Yau da Gobe da juyawar Dare da Rana sun isa mai hankali yasan inda ya dosa.
    • Mar 26
    • Rahmatu Lawan and ASEE BEAUTY like this.
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Muttaka usman's post.
    Muttaka usman
    Salam na dawo inayiwa kowa fatan alkhairi
    • Mar 26
    • 9 person likes this
    • ASEE BEAUTY
      Bakandamiya Muna maka barka da dawowa da kuma fatan alkhairi.
      • Mar 26
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Muna yi maka barka da dawowa
      • Mar 27
      • -
      • Report
  • Salisu  Abdullahi
    Salisu Abdullahi is now following ASEE BEAUTY.
    • Mar 26
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Nafisat Isma'il's post.
    Nafisat...  moreNafisat Isma'il
    🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    🐾🐾🐾🐾🐾
    🍇🍇🍇🍇🍇
    ...  more🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    🐾🐾🐾🐾🐾
    🍇🍇🍇🍇🍇
    *RAUDHA*
    🍇🍇🍇🍇🍇
    🐾🐾🐾🐾🐾
    🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

    *MALLAKAR😗 ✍️
    _Nafisat Isma'il Lawal Goma._

    *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻‍


    *بسم الله الرحمن الرحيم*


    *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

    ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)```

    /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

    *P.W.A*✍️


    *JIKAR LAWALI CE*✍️

    *Wattapad: UmmuDahirah*👈




    .


    *NOT EDITED* ___________________________📗


    *SEASON THIRTY SIX*


    _______📖 Ba don Allah yasa Daddy me saurin yarda da ƙaddara bane, da babu abinda zai sa be zube musu anan ba, sai dai kuma sosai ya dage wajen danne kaso sittin cikin ɗari na daga damuwar sa, amma hakan be sa fuskar sa ta hana bayyanuwar tsantsan damuwa da tashin hankalin da yake ciki ba, idanuwan sa gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur, muryan sa na rawa ya ce da su, "yanzu tana asibitin ne?"


    Rayyan ya ba shi amsa da "Eh".


    "Ok ku mu je ku kai Ni". Yafaɗa yana miƙe wa tsaye da hanzari


    Tare suka fice suka shiga motar Suhaib, Rayyan ne ya ja su zuwa asibitin.


    Suna isa ɗakin da aka kwantar da RAUDHA, Daddy yayi saurin ƙarisawa wajen ta, zama yayi ya ɗaura tafukan hannayen sa biyu saman fuskar ta yana shafa wa, ji yake yi tamkar yayi ta kurma kuka sabida tsananin tausayin ɗiyar sa. Wai yau RAUDHA ce kwance cikin wani hali na taɓin hankali, duk a sabida sakacin su


    Lumshe idanu yayi yana sake sauke wa akan kyakkyawar fuskar ta, wanda ya rame sosai, sai haske da ta sake yi, barci take yi har yanzu sabida alluran barcin da aka yi mata. Ahankali Daddy ya saka hannun sa ya ɗauke hawayen da ya silalo masa a kuncin sa, sannan ya juyo yana kallon su yace, "ina ne Office ɗin doctorn dake duba ta?"


    "Daddy bari in Kai ka". Rayyan yayi saurin faɗar haka


    Gyaɗa kai kawai yayi yabi bayan sa


    Shi kuma Suhaib ya koma kusa da ita ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun ta ɗaya wanda akayi mata ƙarin ruwa aka cire.



    Wajen mintuna ashirin da fitan su Daddy kafin suka dawo, dayake magriba tayi, sai suka wuce gaba ɗaya masallaci, har bayan sallan isha'i suna nan a asibitin, har sannan kuma RAUDHA bata farka ba, dole suka taho gida suka bar ta cikin kulawar likitoci, tunda dama asibitin ba kasafai suke barin mutane suna kwana da mara lafiya ba. Daddy ya so ya kwana amma sai su Rayyan suka taushe shi akan ya koma gida, tunda shima yana buƙatar hutu a wannan lokacin


    Sai da suka mayar dashi gidan sa, kafin suka wuce su ma, da zummar gobe Suhaib zai kawo mishi Haneep da Farida, sai su gaisa tunda yau basu samu sun haɗu ba.


    A taƙaice ranan Daddy be iya runtsa wa ba, kwana yayi a zaune yana nema wa ƴar sa samun lafiya daga wurin mahaliccin mu.


    Washe gari tare suka taho da Farida gidan Daddy ɗin, anan suka gaisa, Daddy ya amshi Haneep yana ta faman mishi wasa, sosai soyayyar yaron ya shiga ransa, kuma ya tausaya mishi da rashin lafiyan da yake yi, yayi masa addu'a sosai kafin ya miƙa ma Farida shi, sannan suka fito suka nufi asibitin, daga can Rayyan ya wuce wurin aikin sa.


    Wajen awanni biyu da zuwan su, sannan ne RAUDHA ta farka, amma kuma gaba ɗaya ta rikita su da koke-koken ta, kuka take yi sosai tana surutu kamar zautacciya, ba ma ta gane wanda ke kanta


    Sosai tashin hankali ya sake bayyana a wajen Daddy da Suhaib, sun rasa ya zasu yi, har kuka sai da Suhaib yayi, shi kuma Daddy sai faman sharan ƙwalla yake yi, musamman da ya riƙo ta yana faɗin, "shi ne Daddyn ta, tayi shiru". Yana rarrashin ta


    Sai tahau zagin sa, daga ƙarshe ta soma ɓaɓɓaka masa dariya tana tokarin sa da ƙafa, wai sai ya sake ta ta hau saman silling


    Da gudu Suhaib ya fice yana sharan hawaye


    Itama Farida dake riƙe da Haneep ta zauna a gefe tana kallon RAUDHA dake jikin Daddy, bata san sanda hawaye yayi ta kwarara a saman fuskar ta ba, sabida tsantsan tausayi


    Hauka tuburan RAUDHA take yi, an rasa yanda za'a yi da ita, tunda tuni Suhaib ya kira likitoci sun duƙufa akanta


    Ƙiri-ƙiri Daddy ya ƙi fita a ɗakin koda suka buƙaci su ba su wuri


    Yanda suka ga hankalin Daddy yayi ƙololuwar tashi, dole suka tausaya mishi suka bar shi a cikin ɗakin, haka suke iya yin su wajen taimaka wa RAUDHA, sai da suka yi mata alluran barci sannan suka samu lafiya, amma ta karaɗe ɗakin da waje da ihun ta


    Daddy kasa jure wa yayi ya faɗi ƙasa a sume, ai nan hankalin su Suhaib ya sake tashi da jin abinda ke faruwa


    A wani ɗakin aka kai Daddy aka soma ba shi taimakon gaggawa, sosai jinin sa ya hau, ga shi yana buƙatar hutu, dole suka yi masa alluran barci don ya samu ya huta ko jinin sa zai sauka


    Abun tausayi idan ku ka ga Suhaib, ya hana kansa sukuni duk ya tsangwami kan sa, shima ba don jarumta da ƙarfin hali ba; da tuni ya zube, sai Farida da ke ƙarfafa masa gwiwa tana masa nasiha akan ɗaukan ƙaddara. tabbas haka Allah ya so ƙaddaran RAUDHA ce, dole wannan ciwon sai ya same ta, sai dai su yi wa Allah godiya tare da roƙon Allah ya taƙaita abun haka.



    Wajen awanni uku Daddy yayi a kwance, sannan ya farka. duk yanda likitoci suka so ya zauna ya sake huta wa a ɗaura masa drip amma yaƙi, nan ya soma buga waya ya hau yi mata cuku-cukun yanda za'a yi a fita da ita Abroad, sai dai basu samu ba, tunda ko wani ƙasa ance a dakata da zuwa, shi kansa Nigeria an rufe, dole Daddy ya bar ta anan asibitin, sai dai ya samu an yi masa hanyar likitoci ƙwararru waɗanda za su iya kula da RAUDHA


    Abun ka da ma su kuɗi, a washe gari sai ga likitocin sun iso, nan aka duƙufa wajen duba RAUDHA, sosai take samun kulawa wajen likitoci, sai dai kamar ma ƙara haukan take yi, domin ciwon ci gaba yake ba baya ba, ta kai yanzu ɗaure ta ake yi a jikin ƙarfen gadon, sabida idan ta tashi daga alluran barcin da ake mata, ta rinƙa hauka kenan tana fashe-fashen kayan ɗaki, ko kuma tayi yinƙurin guduwa dole sai an kamo ta, har kayan jikin ta take yagawa, sai dai a sauya mata wani.



    Bazan iya misalta muku halin da bayin Allan nan suke ciki ba, har wani rama suka yi sabida tashin hankali, babu abinda su Daddy da Suhaib suke yi sai dana-sani, dana-sanin barin RAUDHA cikin shaye-shaye, ga shi yanzu ta haukace suna ji suna gani, kuma kuɗin su be iya ba ta lafiya ba, babu yanda za su yi yanzu sai bin ta da addu'ar samun lafiya, wuni kuwa cikin yin ta suke yi, duk idan suka zo asibitin nan sai sun zubar da hawaye


    Gefe ɗaya ma Rayyan duk ya shiga matsanancin damuwa sosai, duk a sabida ciwon RAUDHA, sosai yake matuƙar ƙaunar ta, ko barci ba ya iya yi sabida tunanin ta, da shi ake yin duk wani zirga-zirga na neman maganin ta, ya kasa hankalin sa gida biyu, a hankali shima a tsaye yake rame wa duk a sabida damuwar da ya ɗaura wa kansa.



    Yanzu haka dole aka mayar da RAUDHA asibitin mahaukata tunda abun yafi ƙarfin asibitin, an ware mata ɗaki daban a matsayin ta na ƴar gata, sai dai su Daddy su je can su riƙa duba ta, su kansu likitocin ma su kula da ita daban ne aka ajiye mata.



    Wasa-wasa sai ga RAUDHA ta shafe watanni huɗu a asibitin mahaukata, tana fama da mugun ciwon da ba ya baya sai dai gaba, kullum-kullum gaba ciwon nata yake yi ba baya ba, duk wani magani an yi mata amma har yanzu ba'a dace ba, ba'a taɓa samun ranan da aka wayi gari an samu nasarar ci gaba wajen samun lafiyan ta ba, sai dai gaba abun yake yi, da sarƙa ake ɗaure ta, abun mamaki kuma sai da safe a zo aganta a kwance. likitan da ke duba ta sosai yake mamaki idan ya zo ya ganta a kwance tana zaune tayi ta ɓaɓɓaka masa dariya.




    Yau ma kamar kullum a kwance ya ganta, sai dai kuma abun mamaki a saman cilling ya hange ta tana ta kwasan dariyan dake fita tamkar na mutane goma, ga shi ɗakin yayi duhu sosai sai uban sanyi tamkar ƙanƙara


    Da sauri likitan ya kunna wutan ɗakin yana me mamakin "ta ya ɗakin zai yi duhu bayan yanzu yamma ne ba dare ba?"


    Can ya hange ta a sama tana yawo tana wannan dariyan me ban tsoro. Da sauri ya bar ɗakin don kiran sauran ƴan uwan sa


    A time ɗin ne Daddy da Suhaib suka zo duba ta


    Nan likitan yayi kiciɓis da su, sai ya miƙa musu hannu suka gaisa sannan ya kai su office ɗin sa ya ajiye su, sai ya fita ya bar su suka koma tare da wasu Doctors ɗakin da RAUDHA take ciki


    Har a time ɗin tana saman tana shawagi tana wannan mahaukacin dariyan da yake karkasuwa da yawa, suna shigowa ta kallo su da idanuwan ta masu tsananin haske tamkar an ƙara musu haske, har wani walwali suke yi kamar an kunna tocila


    Sosai likitocin suka tsorata da wannan al'ajabin, har za su koma sai ɗayan ya dakatar da su


    Kamar ƙiftawar ido sai ganin ta suka yi ta koma ƙasa a yashe, gashin kanta ya rufe mata fuska duk ya barbaje


    Shi babban likitan shi ya ƙarisa gaban ta ya yaye mata gashin kanta, sai dai da alamun ba ta numfashi, duk inda yakamata ya taɓa don jin tana numfashi amma alamu sun nuna ta sume ne, dama ta saba haka, sai tayi wajen kwana biyar tana barci, ko kuma ta dena numfashi gaba ɗaya, hakan na basu mamaki, amma basu alaƙanta hakan da komi ba, tunda gashi result ɗin su na nuna musu ƙwaƙwalwan ta ta samu matsala sakamakon ƙwayoyin da take sha, kuma koda yaushe suna mata gwaje-gwaje amma abu ɗaya suke gani, duk maganin da zasu ba ta still dai babu ci gaba.


    Sake ɗaure ta suka yi da sarƙan, kafin suka soma aiki akanta, bayan sun gama suka fito daga ɗakin, likitan ya nufi Office ɗin sa da su Daddy ke ciki, yana shiga ya sake ba su haƙuri da zaman jiran sa da suka yi, sai da suka sake gaisawa sannan ya soma musu bayani, kamar dai ko yaushe babu wani ci gaba da ake samu


    Gaba ɗaya ransu duk a matuƙar damuwa suke sauraron likitan, kullum abu ɗaya yake faɗa musu, duk kuma hanyan da zai kawo yace a gwada, idan an gwada ɗin abu ɗaya ne babu sauƙi, gashi kuma babu yanda za'a yi a fitar da ita wani ƙasan, nan kuma asibitin yana ɗaya daga cikin asibitin da yafi ko wanne ƙwararrun likitoci na masu hauka, da ba don haka ba da tuni sun sauya mata wani wajen, su yanzu har sun fawwala wa Allah komi, sabida kullum babu ci gaba


    Ajiyan zuciya likitan ya sauke yana kallon su, sai da ya ɗan ja fasali kafin yace, "sai dai Ni akwai shawaran da nake so in baku idan babu damuwa".


    "Menene likita? Ka faɗa ko wani shawara ne idan har hakan zai kawo samun lafiyan ɗiya ta, muna maraba dashi". Cewar Daddy da tsantsan damuwa a maganar sa


    "Eh to Ni dai a haƙiƙanin hange na da nayi, ciwon ɗiyar ka ba na asibiti bane gaskiya, duba da yanda kuke ta wahala da ita, mu ma kuma muna yi wajen treating ɗin ta, amma kuma har yanzu babu ci gaba, sai kuma abinda ke ɗaure min kai a tattare da ita, musamman idan na je inda take, hakan yasa nayi tunanin tabbas ciwon ta akwai yiwuwar shafan aljanu a tattare da ita, ba wai zan ƙaryata cewa ƙwaƙwalwan ta be taɓu bane a sabili da shaye-shayen da take yi, tabbas hakane, sai dai kuma idan har akwai aljanu a jikinta, to, tabbas babu ta yanda za'a yi maganin da muke mata ya warkar da ita, duba da yanda aljanu suna irin hakan a jikin Mutum, zasu lafe su hana tasirin duk wani magani a jikin ta, haka za'a yi ta wahala da ita a kasa gane meke damun ta, ya kamata a gwada na Islamic tunda an kasa dacewa anan ɗin".


    Daga Suhaib har Daddy zuba ma doctor idanu suka yi suna sauraren sa, har sanda ya dire bayanin sa babu wanda yayi yunƙurin magana, gaba ɗayan su sun tafi ga tunanin abinda ya sa tun farko ba su yi wannan tunanin ba.  less  less
    • Mar 26
    • 7 person likes this
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked jamil Bashir's photo.
    • Mar 26
    • 7 person likes this
    • ASEE BEAUTY
      Jiddah Washah ka ce peak milk yana da protein a jiki? ka ga kuwa idan akwai protein a jiki ina da yakinin peak milk na bada gudunmuwa wajen karin jini
      • Mar 26
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Nafisat Isma'il's post.
    Nafisat...  moreNafisat Isma'il
    🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    🐾🐾🐾🐾🐾
    🍇🍇🍇🍇🍇
    ...  more🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    🐾🐾🐾🐾🐾
    🍇🍇🍇🍇🍇
    *RAUDHA*
    🍇🍇🍇🍇🍇
    🐾🐾🐾🐾🐾
    🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

    *MALLAKAR😗 ✍️
    _Nafisat Isma'il Lawal Goma._

    *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻


    *بسم الله الرحمن الرحيم*


    *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

    ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)```

    /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

    *P.W.A*✍️


    *JIKAR LAWALI CE*✍️

    *Wattapad: UmmuDahirah*👈




    .


    *NOT EDITED* ___________________________📗


    *SEASON THIRTY SEVEN*


    _______📖 Sun daɗe a wajen likitan yana musu bayani, har yayi musu hanyar wani babban Malami dake garin Zaria, kuma sun amince zasu gwada ɗin ko Allah zai sa a dace.


    Sai da suka duba RAUDHA kafin suka bar asibitin.


    A cikin kwana biyu har an gama shirye-shiryen yanda zasu tafi da RAUDHA zuwa Zaria, tunda an rigada an sanar wa malamin kuma ya ce a kawo ta, gaba ɗayan su zasu yi tafiyan har Farida, tunda dama gida ne zasu koma shiyasa zasu tafi gaba ɗaya


    Rayyan ya so ya bi su, sai dai yanayin aikin sa bazai bar sa ba, dole ya haƙura ba don ya so ba.


    A jirgi suka isa Zaria, gidan Daddy suka sauka inda anan ne Malamin zai zo ya riƙa duba ta, bisa alfarman da Daddy ya nema a wajen sa, (Chemist) cibiya ce babba suke da shi a Zarian, wanda aikin su ne cire ma mutane aljanu


    A ranan da suka zo, a ranan ne Malamin da zai duba ta shima ya iso gidan, a time ɗin RAUDHA na barci ne sabida alluran barcin da aka yi mata daga can asibiti, saboda samun sauƙin tahowa da ita


    A tare da Daddy da Suhaib suka raka sa ɗakin da aka ajiye RAUDHA, sai da ya nemi abubuwan da yake buƙata wajen su, sannan ya zauna ya saka mata magani a cikin kasko, ta yanda idan har tana da aljanu dole zasu bayyana kansu idan turaren ya shiga hancin ta


    Ilai kuwa, ana saka wa sai ta farka a firgice, gaba ɗaya zubo musu idanu tayi tana kallon su tamkar zata cinye su, sabida yanda ta waro idon nata waje, sai yamutsa fuska take yi tana cije baki


    Malamin ta kafa ma idanu, wanda shima ita yake kallo, nan da nan idanun ta suka soma sauya kala zuwa ja, sai ta kawar da kai ta koma ta kwanta batare da ta sake ko motsi ba




    Su dai su Daddy suna zaune akan sofa suna kallon ta, ko wannen su ya buga tagumi


    Ajiyan zuciya Malamin yayi kafin ya kalli su Daddy yace, "tabbas yarinyan ka tana da aljanu a jikin ta, da alamu dai manya ne, saboda duk wanda na saka mishi maganin nan, dole ne su tashi a lokaci ɗaya su bayyana kansu, amma kuma ita ba haka ba, sai dai ta yanda ta farka ɗin nan, da kuma yanda idanuwan ta suka sauya kala, to, tabbas tana tare da su. Insha Allahu zamu fara aikin mu nan ba da jima wa ba idan abokan aikina sun zo, zamu fara mata ruƙiya ne su fara bayyana kansu, sannan mu san abun yi".


    Suhaib da Daddy jinjina kai suka yi alamun gamsuwa.


    Suna nan zaune Sai ga wasu Maza su kusan biyar sun shigo ɗakin


    Malamin kallon su yayi yace, "su zauna su soma karatun".


    Gaba ɗaya zama suka yi suka zagaye RAUDHA da har yanzu tana kwance idanu a rufe taƙi motsawa


    Karatu suka soma yi da ƙarfin muryan su. sun daɗe suna karatun amma RAUDHA bata yi wani motsi ba, su kuma basu fasa karatun ba, sai da suka ɗau kusan mintuna talatin suna karatu kafin ta soma wani irin gurnani har yanzu idanun ta a rufe, hakan yasa suka sake dage wa suna sake ɗaga murya, nan da nan ta soma ihu tamkar wani ƙaton gardi, kukan yana fita ne kashi-kashi wanda baza ka gane na mutane nawa bane, kukan kawai take yi bata motsa ba, kuma idanuwan ta a rufe


    Sai malamin ya tashi ya matso kusa da kanta, ya soma yin wasu addu'o'i yana tofa mata akai, yayinda sauran mutanen suka ci gaba da karatun Alqur'ani da iyakan ƙarfin su, idan suka zo wasu ayoyi na jinnu sai suna maimaita wa kafin su wuce


    Addu'o'in da Malamin ke tofa mata, shi yasa ta buɗe idanunta da suka sake matuƙar girma tamkar ba nata ba, sun sauya kala zuwa kore, jajja-jajja, sai kawai ta soma ɓaɓɓaka dariya nan da nan ta tashi tayi sama tana shawagi, take ta tsaga wani uban ihu da ya razana su gaba ɗaya, ba su kaɗai ba gaba ɗaya gidan sai da ya amsa sabida ƙarar ihun nata. Babu shiri Daddy da Suhaib suka miƙe tsaye suna zazzare idanu sabida tsoron da ya shige su, ai nan suka soma addu'a jikin su na rawa, ga shi babu daman fita sabida Malamin sai da ya saka aka kulle ɗakin


    Malamin kallon abokan aikin sa yayi, yayi musu nuni su ci gaba da karatun, yayinda shima ya ci gaba da karanto addu'o'i waɗanda zasu saka su bayyana kan su


    Kuka ta soma yi sosai a wannan lokacin, sai dai babu hawaye amma gaba ɗaya idanun nata sun sauya kala, ko ɗigon fari ba'a gani, sai shawagi take yi a saman tana wani irin tururi tamkar ana dafa ta, hayaƙi sai fito wa yake yi a jikin ta


    Karatun su ke yi, ita kuma tana ƙara yawan ihun nata, gaba ɗaya ta cika ɗakin da kuka ko karatun nasu ba'a ji.


    Malamin sosai ya gane aljanun masu taurin kai ne akanta, sabida duk yanda suka yi karatun, sun ƙi yin magana sai kukan da suke yi, daga ƙarshe ma sai taci gaba da ɓaɓɓaka dariya, idan ta gaji kuma sai ta koma kuka, sun shafe wajen awa biyu ana abu ɗaya, sai daga baya da suka ji ayoyi na ƙona su, sun ji azaba na ratsa su sosai wanda baza su iya jure wa ba, sai ta faɗo ƙasa da ƙarfi ta kurma uban ihu, cikin ƙaton murya na gardi take cewa, "ku dena ƙona mu, ku dena ƙona mu, ku dena ƙona mu". Abinda take ta ambata kenan, har muryan ma ta koma tana faɗa ahankali sabida tsaban wahala


    Gashi sun ƙi dena karatun


    Sai ta koma kuka da hawayen ta tana roƙon su sosai


    Nan malamin ya ba su daman dakata wa, sannan ya soma tambayan su "su wanene akan ta?"


    Amma sai taƙi yin magana ta kafa wa Malamin idanu, idanun ta na zubar da hawaye


    "Baza ku yi magana bane?" Cewar Malamin yana kallon ta shi ma


    Sai ta ɓarke da dariya me fita muryoyi da yawa, nan ta miƙe da gudu tayi bakin ƙofa ta soma jijjiga ƙofan, kankace me ta kusa cire ƙofan, domin har ya ɓanɓaro tana shirin cire shi, nan suka yi kanta suna riƙe ta, tana bizgewa tana ihu, duk ta gama bibbige su


    Su Daddy babu inda jikin su ba ya rawa, yau sun ga tashin hankali.


    Daƙyar suka riƙe ta suka dawo da ita cikin ɗakin, haka suka soma kici-kicin kwantar da ita don su danne ta, amma sun kasa, sai ta fara zagin su tana musu gargaɗin "idan basu sake ta ba, sai ta halaka su"


    Malamin ganin dai tana son fin ƙarfin su, sai ya ɗauki waya yayi kiran wasu daga cikin malaman su, sannan ya kalli Daddy yace, "idan da hali ku ƙaro mana mutane, sabida tana ƙoƙarin guduwa ne, kuma tabbas idan har ta fice a ɗakin nan da akwai matsala".


    Jikin Daddy na rawa, ya umarci Suhaib ya kira masu aikin gidan maza su shigo


    Dasauri ya fita ya kira su, sai ga su kusan su shida sun shigo


    Nan Malam ya saka su duk suka taru wajen kwantar da RAUDHA, amma sun gagara, gaba ɗayan su sun kai su goma sha biyu kenan, amma sun gagara kwantar da RAUDHA ƙasa, ihu kawai take yi tana fizge-fizge, duk wanda ta samu ta mazge shi


    Karatu suka ci gaba da yi suna danne ta tana kuka da ihu. Ba su yi nasaran kwantar da ita ba sai da wasu daga cikin malaman suka shigo, kusan su huɗu ne, Malamai ne su ma masu cire aljanu, tare suka dage daƙyar suka danne ta a ƙasa, suka hau karatu babu ji babu gani, sosai suka wahalar da ita, kukan ma wani irin kuka take yi tamkar na mage, gaba ɗaya tayi yaushi sai fitar da huci take yi, amma tsabar taurin kai taƙi magana.


    Wani magani malamin ya samu ya fesa mata, take ta sandare tamkar ranta ya fita, sai kuma ta fashe da sabon kuka tana buɗe idanuwan ta daƙyar, ta hau roƙon sa wai "za su fita".


    "Ƙarya kuke yi mugaye azzalumai, uban me tayi muku da kuka shiga jikin ta, ku ka wahalar da ita har haka, tsawon lokaci kun haukatar da ita, shin ku wasu irin mugaye ne, na ce uban me tayi muku ne?" Yaƙarike maganar cikin tsawa


    Cikin kuka tana nishi tace, "wlh babu abinda tayi mana, kawai muna son ta ne, tayi mana ne shine yasa muka shige ta".


    "Tayi muku? Dama akwai wani abun da ya haɗa jinsin mutum dana aljanu ne?"


    Tari ta soma yi babu ƙaƙƙauta wa, gaba ɗaya idanuwan ta sun gama juye wa, sun ƙara tsananin ja har babu kyan gani


    "Shin zaku sanar damu ne meyasaka kuka shige ta? Ko kuwa sai mun ci gaba da gana muku azaba?".


    Shiru tayi taci gaba da tarin ta, yi take yi babu ƙaƙƙauta wa


    Malamin kaɗa kansa yayi, kafin ya kalli sauran ya ce, "ku ci gaba".


    Nan da nan suka ci gaba da karatun Alqur'ani, shima yana ci gaba da addu'o'i


    Atake anan taci gaba da kuka tana shirin bige su ta gudu, haka suka danne ta sosai suka hana ta tashi, kuka take yi sosai tana ihu, har da su majinu, ta jigata iya jigata sai ta hau zagin su tana faɗin, "wlh idan basu sake ta ba, sai ta kashe su". Amma ko sauraron ta basu yi ba. Sun shafe tsawon lokuta suna karatun, kafin ta soma ba su haƙuri akan zata yi magana, amma malamin ya hana su dakata wa, sai da ta sha baƙar wahala ta sake yin yaushi sosai, ta yanda duk wani taurin kanta sai da suka yi maganin shi, kafin malamin ya saurare ta ya ce, "to ina ji zaku faɗa dalilin da yasa kuka shiga jikin ta ne ko kuwa sai na ƙona ku gaba ɗaya na kashe ku? Shin ku nawa ne ma ajikin nata?"


    Cike da tarin wahala cikin wani irin babban murya tace, "muna da yawa a jikin ta, kuma Ni ne mijin ta, Ni na fara shiga jikin ta, sannan sai na jawo ƴan uwana su ma suka shiga jikin ta".


    Jinjina kansa Malamin yayi kafin ya ce, "har ma ka zama mijin ta kenan, sannan saboda tsaban mugunta sai ka jawo ƴan uwanka suka shiga jikinta don ku cutar da ita ko?"


    Girgiza kai ta soma yi tana hawaye, sai tayi shiru taƙi magana


    "Ina jin ka zaku yi magana ne ko sai na ƙona ku?"


    "Zamu yi Malam, zamu yi". Tafaɗa cikin mawuyacin hali tana juya idanuwa


    "Kar ku sume mana anan, ina sauraron ka yi magana".


    Shiru tayi tana rufe idanuwan ta tamkar ba ta numfashi


    Malam ya sake watsa mata wani farin magani


    Sai ta buɗe idanunta, sun koma fari a yanzu ɗin tamkar nata, cikin siririyan muryan ta da ya gama dishewa tace, "Daddy". Idanun ta akansa


    Ai da sauri Daddy ya nufo wajen shima yana kiran sunan ta


    Malamin ya dakatar da shi yana faɗin, "ba ita ba ce, suna son Raina mana hankali ne, ku muci gaba da karatun".


    Karatun suka ci gaba da yi, sai ta soma kuka, sai da taji azaba kafin ta ce, "kuyi haƙuri don Allah, wlh baza mu ƙara muku taurin kai ba, duk zan faɗa maka abinda ya sa muka shiga jikin ta".


    "To ina sauraron ku".


    "Tun farko abinda ya fara jan hankali na akanta sabida ba ta ibada, sannan tana shigan banza, tana barin kanta a buɗe, shine yasa na kamu da sonta, kuma na shiga jikin ta, sai na jawo ƴan uwana muka shiga, sannan sai suka ɗaura mana aure dani da ita".


    "Shin kai Musulmi ne ko kafiri?" Malamin ya sake tambayar sa


    "Ni ba kafiri bane, amma ba mu Sallah, kuma tunda muka shiga jikin ta mu ke hana ta yin Sallah, tunda dama ba ta yi sai ta ga dama, wannan dalilin ne muka sake mayar da ita me wasa da Sallah, daga ƙarshe muka rinjaye ta muka hana ta Sallah".


    "To tun yaushe kuke jikin ta?"


    "Mun daɗe sosai, tun tana ƙarama".


    Malam ya ce, "kenan duk ku kuke saka ta shaye-shaye har kuka samu damar haukata ta ko?"


    "Wlh ba mu bane, amma dai mun san mun ba ta gudunmuwa, ko tana son bari sai mu hana ta, mu riƙa saka ta tana son sha koda yaushe".


    "To yanzu meyasaka ka aure ta bayan kasan babu aure a tsakanin mu da ku?"


    "Ai na ce maka ina son ta ne, tayi min ne".


    Malam ya ce, "to yanzu zaku fita ne ko kuwa kun samu wurin zama ne baku da ninya?"


    Shiru tayi tana ci gaba da hawaye


    "Ina magana kuna ji na, muna son ku fita a jikin ta, ku bar ta ta huta tunda kun rigada kun azabtar da ita".


    "Malam wlh ina ƙaunar ta, ita matata ce".


    "To shine yanzu na ce ka sake ta ku fita a jikin ta, tun kafin in azabtar da ku".


    Shiru tayi taƙi yin magana.









    .







    _To ya za'a kaya, shin za su bar ta ko kuwa?_  less  less
    • Mar 26
    • 5 person likes this
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY
    *BAZAI AUREKI BA!!!*
    NA
    *ASEE...  more
    *BAZAI AUREKI BA!!!*
    NA
    *ASEE BEAUTY*

    ©🎆
    *Al'umma Writers Asso...✍🏻*

    _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
    https://www.facebook.com/102282991949826

    بسم الله الرحمن الرحيم...

    *WAN NAN PAGE SADAUKARWA NE GA ƘUNGIYATA ABIN ALFAHARINA AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION A QARQASHIN JAGORANCIN SHUGABA MAI GASKIYA DA AMANA ADALCI DA SANIN YAKAMATA (MOM SEEYAMA) SHUGABA MAI SON GANIN CIGABAN NATARE DA ITA, DA BAZARKI NAKE RAWA BAMANI KADAI BA HAR DA SAURAN MEMBERS, ALLAH YAQARAYI MIKI JAGORA YASA KIFI HAKA YAQARA MIKI BASIRA DA DAUKAKA HAFSAT A GARKUWA SON SO FISABILILLAH 💖💕💘💞*

    ```MASHA ALLAH MARYAM ISAH BK ANYI TARO LAFIYA AN WATSE LAPIYA, SUNAN YA" HAUWA,U {afnan} ALLAH YARAYA MAI SUNAN MAMANA YASA MATA ALBARKA ALLAH YA ALBARKACI RAYUWARTA DAMA SAURAN YAYAN MUSULMI BAKI DAYA, (MOMMY ISAH) ALLAH YA BAR KAUNA💞🥰```

    4️⃣➡️5️⃣

    ....... Bai sauketa ko ina ba sai can kusa da gidansu, San nan ya kashe mashin yace" to alhamdulillah na kawoki gida lapiya ban sayar dake ba' murmushi tayi mai batare da tace komi ba` tafara tafiya. Au bazaki tsaya mugaisa ba? Sai taji maganar wata iri Dan tasan sun gaisa tun a makaranta, bata tsaya ba taci gaba da tafiyarta har ta isa gida. Haka rayuwa tafara tafiyar musu wasa wasa soyayya mai qarfi tafara shiga tsakanin Sadeeq da Zainab batare da kowa yasani ba, har Maryam bata fadama ba` ta bangaren Habib kuma babu Wani labari kuma yana matsama Baban shi da maganar amma shiru, Ranar wata alhamis Baban Zainab ya kirata yana fada mata cewar" Habib ya turo zancen Neman aurenta!! Kamar mafarki haka taji zancen Dan ita ko a lissafi bata ta6a lissafo Habib cikin jerin mazan da zasu zo suce suna sonta ba, duk da bashi da wata makusa inma aka duba da kyau yafi Sadeeq komi fari da kyau. Amma ita Sadeeq takeso! Shiru tayi har yagama zancen shi yaqara da tambayarta ko akwai Wanda kikeso? Kamar zata ansa sai kuma tayi shiru`( ga alama shiru yazame mata jiki kamar ASEE BEAUTY🤣🤣🤣🤣🤭 ) haka ta koma daki cike da tunani kala kala, washe gari sun tashi islamiya ta boyema Maryam dama yanzu haka take mata intanason ganin Sadeeq ` sai ta boye in Maryam tanemeta bata gani ba ta tafiyarta ita kuma ta nufi inda zata ga Sadeeq can bakin masallacin Dr bello. Sai su nufi inda suke tsyi suna hira, yauma hakan tafaru bayan sun zauna kan Wani dutsi` tafara fada mai abinda Babanta yace" kan maganar Habib. Sosai ya nuna damuwarshi akan magana tare da bata tabbacin cewa insha Allah shine mijinta ta kwantar da hankalinta, sama sama sukayi hirar ya rakata har kusan gidansu inda ya tabbatar ba Wanda zai gansu tare. Baban Zainab baisake maganar Habib ba haka ma Mamanta , amma sunata bincike kan halayyar Habib. Ta bangaren Zainab kuma yanzu hankalinta yafara tashi tunda taji Habib yashigo Neman aurenta! Tashiga matsama Sadeeq ya turo manyan shi inyaso sai tace shi takeso adaina zancen Habib. Amma intayi mai maganar sai ya kauce yana Yan kame kame daga baya sai ya canza zancen' amma duk da haka bata gani Dan tayi zurfi cikin son shi. Ranar da Mahaifin Habib yasake zuwa da maganar sai Babanta yace " babu komi su zo ayi tambaya, sosai Abba yayi murnar jin anba danshi wadda yakeso!! Haka sukayi sallama yaje yasanar da Habib yanda sukayi, Habib yayi murna sosai shima harda rungume Baban nashi" batare da sanin Zainab ba aka zo Neman aurenta aka kuma bayar. Bayan angama komi ne ake sanar da ita, aiko tashin hankalinta bai misaltuwa danko mutuwa akayi mata iyakar tashin hankalin da zata shiga kenan' ranar juma' a da misalin qarfe takwas 8:00pm yayi wankan shi cikin wata farar shadda hula da takalmi agogon hannun shi duka ja ne, yayi kyau sosai sai Wanda yagani daga nesa zakajiyo qamshin turarensa. Qofar gidansu yaje yatsaya tunani yake yanda zaiyi ya ganta ! Can Wani yaro yabiyo zai wuce, da sauri yakirashi " Dan Allah shiga gidan nan kace ana sallama da Zainab, ba adade ba yaron yadawo yace' ance wake nemanta? Kace Habib ne, yaron yadawo yace' ance tabata nan. Cikin mamaki yake kallon yaro har yaron yawuce shi sai kuma yadawo da kallon gidansu Zainab, inazata yanzu? Naga bata fita da dare? Ahaka ya juya ya nufi gida rai ba dadi. Sai da akayi kwanaki San nan ta fadama Sadeeq Cewar anbada aurenta ga Habib, cikin mamaki Sadeeq ke kallonta` yanzu abinda kikayi min ki kyauta? Kina ganin ni BAZAN AUREKI BA ne? Nan yashiga mafisar taci amanar shi taje anba Wani aurenta duk irinson da yake mata, hakuri tashiga bashi harda kukanta tanace mai" wallhi ba laifina bane kayimin uzuri ba ayi shawara dani ba, ajiyar zuciya yayi yana tunanin yanda zai bulloma lamarin... NIMA ANAN ZAN DAKATA SABODA QARQNCIN CAJI IN ANKAWO WUTA KO NASAMU CAJI ZAMU CIGABA👌🏿


    TAKU MAI SON GANIN FARIN CIKIN KU

    ASEE BEAUTY✍🏿

    KE MUKU FATAN ALHERI🙏🏿🤝🏼🥰  less
    • Mar 26
    • 6 person likes this
    • ASEE BEAUTY
      Ibrahim Adam Dan Sarauta Sannu da kokari
      • Mar 26
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY
    *BAZAI AUREKI BA!!!*
    NA
    *ASEE...  more
    *BAZAI AUREKI BA!!!*
    NA
    *ASEE BEAUTY🖊️*

    ©🎆
    *Al'umma Writers Asso...✍🏻*

    _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
    https://www.facebook.com/102282991949826

    بسم الله الرحمن الرحيم..


    ```SADAUKARWA

    WAN NAN PAGE NAKINE QAWATA INA ALFAHARI DAKE IRIN SOSAN NAN SO FISABILILLAH NA KUMA GODE DA COMMENT DINKI, KINSANI NISHADI SOSAI QAWATA QUEEN NASMER ALLAH YAQARA MIKI BASIRA DA DAUKAKA DA DUBUN MASOYA👏🏾🥰 ASEE BEAUTY NA KAUNARKI SABODA ALLAH DA MANZONSA S A W 🤍```

    PAGE2️⃣➡️3️⃣

    ..... Kwana biyu da haduwarsu, bata sake ganin shiba kuma ko a hanya hakan bai dameta ba taci gaba da lamurranta. Saidai tanason sanin sakon da zaifada mata, kuma bata fadama kowa ba har Maryam ma. Inkagansu zakace sun kai shekara sha bakwai amma basu wuce sha dubu zuwa sha biyar ba, haka suke ta abubuwansu na rayuwa koyaushe tare suke duk inda zasu tare suke zuwa, yauma can nahango su suna tafiya akasa da alama inda zasu ba nisa amma ba cikin unguwarsu ne ba. Titin da zaikaisu bayan kara suka hau basu bata lokaci ba suka iso gidan, gidan wata yar ajinsu ce ta islamiya suna shiri da ita sosai' bayan sun gaida Mamarta akai kaisu har inda Ummin take ` qawartasu`Ummi lafiya kwana biyu bakizo makarantaba? Nagaji shine nace banida lapiya Dan kar inje" tana fada tana dariya!! Suka saki baki alamar mamaki suna kallonta, basu Dade ba sukayi mata sallama suka nufi gida. A hanya suka sake haduba dashi yauma kamar kullum yana zaune bakin masallacin Dr Bello` kamar bai gansu ba sai kuma yataso ya nufo inda suke tsaye, Habib ne Wanda ke tsalakar dasu titi ` kafin ya iso ma har sun tsallake abinsu, shima kuma yakoma inda yake ya zauna. Yau takama attanin akwai boko tunda wuri suka shirya suka fita, Habib da abin duniya ya ishe shi yau dai ya yanke shawarar zuwa yasami Baban Zainab yasanar dashi yanasonta! Sai kuma Wani tunani yafado mai' kodai in fadama Abba yaje da kanshi? Za afi daukar maganar da gaske , dafe ka shi yayi da hannu biyu kamar mai Wani dogon tunani! Can yace " yes haka za ayi bazan je da kaina ba wata kila bazai saurareni ba ma. Ahaka yasami Mahaifin shi da maganar , shiru Baban nashi yayi kafin yace" to naji maganarka kuma nayi murna da ita amma abinda nake gudu karsuce bazasu baka yarau ba, da sauri yad'ago yadubi Baban yace' Baba zasu bani insha Allah Baba inasonta kuma wallahi zan riqeta da gaskiya Baba yana maganar kamar mai jin tsoron kar ace ba abashi . Haka Baban shi ya shirya yanufi gidansu Zainab, Mahaifin Zainab Wanda suke kira da Baba qarami kasancewar shine qarami a gidansu asalin sunan shi Musa, bayan sun gaisa yake fada mai abinda ketafe dashi" Baba qarami yaji dadi sosai saidai ya6oye jin dadin nashi` yayi gyaran murya yace" to banqi maganarka ba amma kabani lokaci zanyi tunani akai Allah ya tabbatar muna da alherinsa, suka ansa da amin ` suka danyi hira kafin suyi sallama kowa yakama gabansa. Malam Haruna nadawowa gida yasami Habib zaune yayi shiru da alama yau ko girka baifita bama, jin muryar Baban yashi dawowa daga duniyar tunanin da yashiga! Baba sannu da zuwa ya kukayi dashi? bai gaisuwa ba komi sai tambayar yanda mukayi? To bansani ba' da sauri ya rungumi Baba yana dariya Baba yakira sunan shi, nasan dai inkina rai insha Allah babu abinda zai gagareni. Insha Allah Baba yafada tare da riqe hannun Dan nashi` amma sai ka natsu kazama mutum kadaina halayenka ba Dan niba Dan Allah kuma, insha Allah Baba karka damu wallahi zan dena nayi ma alqawari , bayan yashiga gida yasamu mai dakin shi da maganar' shiru tayi kafin tace" Allah ya tabbatar da alheri. Haka suka cigaba da binciken waye HABIB ya halinshi yake suwaye abokansa???? Duk wan nan basu fadama Zainab batasan anayi bama, shima kuma tunda Manya suka shiga maganar sai ya daina qoqarin tsallakesu titi in ma yagansu zaiyi kamar bai gansu ba` AYA DUK NAMIJIN DA KESONKI DA GASKIYA BAZAI TAREKI A TITI KO HANYA BA ZAIJE GIDANKU KO YA TURA MANYANSHI MUYI HATTARA👌
    Inna Saudi tashiga maqota suna hira ita da qawarta , sai taji yaran gidan yan samari suna ta surutu` shiru tayi danson jin abinda suke fada taji an kira sunan Habib da alama Wanda keson zama surukinta ne' sai tajiyo muryar Wani nacewa" wallahi ko jiya naganai. Sai kuma sukayi shiru kamar ance suyi, Bataji abinda takeson jiba haka tanufi gida.Yau Maryam bata ji dadin jikinta ba hakan yasa bataje makaranta ba` Zainab kadai ce ta tafi, antashi makaranta tana Neman mashin sai kawai ta hango Sadeeq tafe` batayi tunanin komi ba dan bata masan wurinta yazo ba komi oho, can taji yakira sunan ta` gaishe tafarayi' kafin yace ina qawarki yau?? Tana gida batada lapiya, ayya Allah yabata lapiya zo inkaiki gida' ah ah tafada" ah ah Zainab? Wai meyasa kike min haka? Nagane baki sona shiyasa kuma na gode, kamar yayi fushi zai wuce sai kuma yace" ki hau koda shi zai zama nafarko na qarshe. Bata da niyar hawa amma ba yanda ta iya dole ta hau suka tafi. Suna tafiya yake fada mata iron son da yake mata " Sadeeq mutum ne da ya iya bakin shi indai wurin magana ne da tsara zance yana sahun gaba` da haka yake saye zuciyar yan mata musamman irin Zainab da zuciyarta batada qarfi.
    ANAN ZAN DAKATA SAI KUMA GOBE IN ALLAH YAKAIMU ZAMUCI GABA😇

    ALLAH KASHIRYA MUNA ZURIAR MUSULMI ALLAH KA KAWO MUNA ZAMAN LAPIYA A JAHAR MU TA KEBBI DA SAURAN KASASHEN MUSULMI ALLAH KA DAUKAKA MUSULUNCI DA MUSULMI🤲🏾🤲🏾

    TAKU MAI SON GANIN FARIN CIKIN KU

    ASEE BEAUTY✍🏿

    KE MUKU FATAN ALHERI🙏🥰🤝🏼  less
    • Mar 26
    • 4 person likes this
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Umar's post.
    Umar shared Jiddah Washah's image. Muna gayyatarku daga ZAMAN AMANA WRITERS ASS. mungode.
    • Mar 26
    • 9 person likes this
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY
    *BAZAI AUREKI BA!!!*
    NA
    *ASEE...  more
    *BAZAI AUREKI BA!!!*
    NA
    *ASEE BEAUTY🖊️*

    ©🎆
    *Al'umma Writers Asso...✍🏻*

    _{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._
    https://www.facebook.com/102282991949826

    بسم الله الرحمن الرحيم...


    ```Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukacin sarki mai kowa mai komai, ina ƙara gdy a gareka da ka bani ikon dawowa a karo na barkatai yadda na fara lfy Allah kasa na gama lfy.```

    *DEDICATED TO NAFEESA ALEEYU ARGUNGU ( MAMAN UMMUL SALMA) KIJI DADINKI MAMAN SALMA WAN NAN PAGIN FARKON DAKE YAFARA🥰💃🏿💃🏿*

    PAGE1️⃣

    *...* Wasu yara na hango bakin titi, bakin garkar SARKIN ZABARMAWA suka tsaya suna jiran motoci su raqe sukuma su tsallaka. Saye suke da kayan islamiya kalar ruwan kasa mudu duhu sosai hijab ne har kasa da kuma riga da wando ciki sai jakarsu ta kowace ta rataya tata" sunfi minti goma wurin basu samu tsallakewa ba sakamakon titin babban titi ne, Wani Dan saurayi da bazai wuce shekara sha bakwai ko sha takwas ba shi na hango yana nufo inda yaran suke tsaye inkangashi tare dasu kamar qannenshi. Gaishe shi sukayi , San nan yariqa hannunsu ya tsallakesu. Da alama dai yasansu` basu tashi makarantar ba sai qarfe shidda 6:00pm, lokacin kuwa titin yacika tab da motoci da mashin dama duk Wani qarfe da ake tukawa. Ba yaro ba ko manya sai sunyi da gaske zasu iya tsallake titin, ahaka suka qaraso har bakin titin sukayi tsaye suna kallon motocin dake wucewa,har aka fara kiran sallar magrib suna wurin tsaye. kamar ance dashi ya juyo sai yahango su tsaye kamar yanda sukayi dazun, baije inda suke ba sai ya shiga tsakiyar titin ganin yara yan makarantar dazasu tsallaka sunada yawa` nan yashiga tsayar da motoci har saida yaran suka gama wucewa kafin shima ya tafiyar shi inda zashi.ahaka suka saba kullum shike tsallakar dasu titi in motoci sunyi yawa Wani lokacin kuma suke tsallakewa da kansu. Sundawo daga islamiya suna tafiya naji dayar takira sunan dayar, tanacewa" wallahi zainab bazan sake jiranki ba tunda ke Baki da sauri kullum sai naje gidanku in sameki ko wanka bakiyi ba, tana maganar cikin fushi . wadda aka kira Zainab tace" kiyi hakuri Maryam insha Allah zan dena dade banshirya ba, tafadi hakan tana jawota jikin ta` sai da suka kusa shiga gidajen su San nan sukayi ma juna sallama. Haka Zainab da Maryam sukeyi kullum tare suke fita islamiyarsu daya makarantar bokon su ma haka inkagansu kamar yan Biyu, sunatafi suna sauri zasuje kasuwa yau ba ranar karatu ceba Dan haka sukaji dadi sosai da ba a zuwa makaranta, nan ma suka kasa tsallakar titi Wani matashi da bazai wuce sa an Wanda ke tsallakesu ba yazo yafaka da mashin dinshi gabansu`yan mata ina zaku? Suka dubeshi atare' Maryam tayi tsaki ta koma gefe, ita kuma Zainab tace"kasuwa zamu. Kuzo in akaiku ko? Ya tambaya` Zainab tayi saurin juyawa ta dubi Maryam sai taga har tayi nisa da tafiyarta. Karki damu zo inkaiki kinji? Ah ah Mama na tace kar in haumashin d'in kowa in nahau ma Maryam fadi zatayi, shiru yana tunani ganin babu yanda zaiyi sai ya wuce yabarta. Da sauri da gudu ta iske Maryam da har ta kusa shiga kasuwar` Wallahi sai nafadama Mama ( mamar Zainab) kinsan tace ko Wani ya tsayar damu kar mu tsaya ko? To yau sai nafada mata. Ranar ya tsayar damu natafi nabarki nace zan fada kikace inyi hakuri yau ba hankurin da zaki bani karma ki bata lokacinki" haka sukayi sayayyarau suka nufi gida. Bayan kwan biyu Maryam kamar yanda tace zata fadama maman Zainab haka kuwa akayi fa kwashe duk ta fada mata, saida tafara da ja mata kenne kafin tasa bulala tazane mata jiki Tass Dan gobe karta sake. Ahaka rayuwarsu tafara Zainab da Maryam ko sunyi fada zakaga sun shirya, basu kuma sake tsayawa ahanya ba idan Wani yakirasu koda kuwa da sunan zai aiki sune, Dan ko Zainab zata tsaya Maryam bataza tsaya ba haka yasa basa tsayi su dukansu. Sadeeq wani yaron unguwarsu ne shine kuma Wanda ya tsayar da Zainab har Mamanta ta daketa. Yafito daga gidansu yana tafiya can ya hango Zainab' da murmushi afuskar shi , yakira sunanta bata ansaba bata kuma tsaya ba data niyar tsayawar kuma. Da sauri da sauri yasameta har inda take yana maida ajiyar zuciya, Zainab mai tawayen suna!! Yakike? Inazaki haka cikin rana? Shiru batace komi ba` muje in rakaki to tunda bazaki ansa min ba" ah ah kabarshi nagode' ah ah Zainab indai bakiyi dani insani inkama gabana, nagode zanje gida kar ajirani. OK bani number ki anjima zankiraki ` bani da waya, bakida waya? Eh in nasaya miki kinaso? Zaro ido tayi cikin tsoro tace " ah ha wallahi kasheni Mama zatayi. Yanda tayi maganar yagano irin tsoron da take ma Mamarta ta. OK ba damuwa amma zuciyata na dauke da Wani sako zuwa gareki da fatan zaki bani damar Isar da wan nan sakon? Murmushi tayi ta cigaba da tafiyarta. Bai kuma sake binta ba shima ya juya gudun kar Wani yagansu tare` NIMA ANAN ZANDAKATA KAR RUWAN BIRONA SU QARE.🥺

    SAI NAGA YANDA KUKA KARBI LABARIN KAFIN INCIGABA👌🏿


    MASU BINA BASHIN LITTAFI DAN ALLAH KUYI HAKURI WALLAHI BAN MANTA KUBA DAN NASAN HAKKIN WANI BAI CIYUWA GA WANI PLZ KU QARA HAKURI INSHA ALLAH BA DA DADEWA BA ZAMU FARA👏🏾👏🏾


    TAKU MAI SON GANIN FARIN CIKIN KU

    ASEE BEAUTY✍🏿

    KE MUKU FATAN ALHERI👏🏾🙏🏿🥰  less
    • Mar 26
    • 5 person likes this
  • Ibrahim Adam Dan Sarauta
    Ibrahim Adam Dan Sarauta is now following ASEE BEAUTY.
    • Mar 25
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked ALIYU MUHAMMAD's post.
    ALIYU MUHAMMAD
    IAM A NEW HERE, I WISH U ALL DE BEST AND SUCCESS.
    • Mar 13
    • 9 person likes this
    • ASEE BEAUTY
      Lawan Dalha Welcome to Bakandamiya
      • Mar 13
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • ASEE BEAUTY
      ALIYU MUHAMMAD TANK U.
      • Mar 13
      • -
      • Report
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY
    MUFEEDAH
    2020
    ...  more
    MUFEEDAH
    2020

    Na
    ASEE BEAUTY🖊️

    ©🎆
    *Al'umma Writers Asso...✍🏻*

    _{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


    بسم الله الرحمن الرحيم...

    WAN NAN PAGE SADAUKARWA NE GAREKU MASOYA NAKUSA DA NA NESA ALLAHU YABAR QAUNA KUMA KUSANI INA MUKUSO IRIN WANDA BAICANZAWA BAI KUMA QAREWA SO DOMIN ALLAH DA MANZONSA 🤝🏼INA GODIYA DA COMMENTS DA KUMA ADDU,O'INKU ALLAH YABIYA MUNA BUKATUN MU NA ALHERI YASADAMU CIKIN CITEON ANNABI S A W🤍🤍

    PAGE2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣

    ON 14 DECEMBER 2020

    ..... Baishigo gidan ba sai kusan qarfe goma, kafin yashigo tayiwa Yaranta wanka ta shiryasu cikin kayan bacci. Dakinta yafara shiga ya tarar ta shimfide Yaran itama ta kwanta` da alama ba bacci takeyi ba. MUFEEDAH yakira sunanta" bata ansa ba bata kuma nuna tajishi ba, bai qara kiranta ba yanufi nashi dakin.sai da yayi wanka yashirya cikin kayan baccin shi San nan yanufo dakinta. Gefen gado yasamu wuri ya zauna` MUFEEDAH!!! Yakira sunanta" Dan ki ansa min wallahi zuciyata na dauke da abubuwa da yawa ciki harda nadama da kuma tarin DANASANI." Saida naji kamar banji shi ba sai kuma nayi Wani tunani natashi nayi zaune, ganin nazauna ne yasashi tashi yazo inda nike shima ya zauna. "Sannunku da dawowa ya gajiya?? Ya tambeni" lapiya qalau alhamdulillah na fada'" "MUFEEDAH Dan girman Allah ki yafemin laifina " wallahi nayi NADAMA fiye da tunaninki nagane ba laifin da kikayi min sharrin shedan ne da kuma SON ZUCIYA ! Amma wallahi nayi NADAMA, ina kuma Neman yafiyarki Allah yasa zaki yafemin??" Tunda yafara maganar shi nake binshi da Wani kallo Wanda na keson gano gaskiyar abinda yake fada. Cikin maganar shi banga alamar akwai abinda yayi kama da qarya aciki ba" amma banjin zan iya yafe mishi cikin sauqi ba duk dacewa ni ba mutum ce mai riqe Abu arai ba. Jin nayi shiru yasashi sake kiran sunana Wanda yanzu na lura yafi komi sauqi awurinsa, jin kukan Hassana yasa shi saurin tasowa ya daukota yana lallashinta` saida yaga tayi shiru kafin yabani ita in sake shimfide ta, haka muka kwana batare da nace na yafe masa ba. Kwanaki sunja kullum kuma sake sabon salo Aliyu keyi Wanda har nafara jin inasonshi! Musamman yanda yake kulla da Yaransa. Sai naji kaina da sakin jiki dashi da kuma zama tare muyi hira` zaune muke muna hira yanata famar dariya" inata kallon shi Dan ni yanzu yadaina bani mamaki nagane yasauko daga kan dokin da ya haune, yauwa dama jira nake inji kince kinyafe min sai inbaki labarin rayuwata. Cikin son jin labarin nace ai nayafe maka tun ranar da na haifi su Hussaina. Baki bude yake kallona yace' "kika haifesu yaushe? Naga kamar likitoci suka cirosu ko? Kodai namanta ne?" Dariya nayi Dan yanayin da yayi tambayar cikin sigar jam magana ne. Yauwa inajinka nidai" nima haka yafada, kinga bari anjima yau ba maganar bacci hirar da zumuyi kenan. Allah yakaimu` gida yayi sallar magrib har aka kira isha' naga baida niyar zuwa masallaci" Abba anakiran sallah fa, "gida zanyi sallah yafada." Nadawo kusa dashi na zauna saboda mi bazakaje masallaci ba? Kawai dai ` ah ah saikatafi gaskiya' banqara magana ba yatashi yafita. Yau kamar kullum saida muka gama cin abinci Balkisu ta dauki na Ahmad taje kaimai bayan ta dauki Hassana taje da ita. Indai tana gida to Hassana na wajenta na lura sunfi ji da ita akan Hussaina, "Zo ki tausa min qafata ciyo take min"' saida yace "ya isa haka" San nan nabari, "yanzu kai nake saurare!! Tashi yayi zaune yana qaremin kallo uwayen son gulma to bazan fadaba" yanda yafadi maganar tasigar tsokana yasani shigewa jikin shi ina rama dukana da yayi, muna dariya, to yanzu dai kibari gobe ba inda zanje sai muyi labarin. Yafada yana rufe ido alamar rashin gaskiya, shiru nayi na hade rai kamar zanyi kuka` sai kuma yajawoni jikin shi zo zanbaki labarin yana murmushin dake qara mai kyau da qwarjini.
    ***************************WAYE ALIYU AHMAD DA KUMA BALKISU???? DUK ZAKUJI ANSAR WAN NAN DAMA SAURAN LABARIN KUBIYONI DAN JIN YANDA ABIN YAFARO ASALI👌🏿

    ANAN ZAN DAKATA SAI KUMA GOBE IN ALLAH YAKAIMU DA RAI DA LAPIYA ZAMUCI GABA🥱

    KUYI QOQARIN YIN COMMENTS COMMENTS DINKU SHINE QAFRIN QWIWARMU👏🏾🙏🏿🤝🏼

    BAMUYI SAIDA KU MASOYA🤝🏼


    TAKU MAI SON GANIN FARIN CIKIN KU🥰

    ASEE BEAUTY✍🏿
    KE MUKU FATAN ALHERI🙏🏿  less
    • Mar 12
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Mubarak Aminu's photo.
    Allah kasa murayi Cikin Aminci
    • Feb 10
    • 7 person likes this
  • ASEE BEAUTY
    ASEE BEAUTY liked Nafisat Isma'il's post.
    • Feb 10
    • 5 person likes this
View More
Loading ...

About

Abokai

  • Bakandamiya GORON JUMMA'A BA A YIN WUTRI BIYU A DARE DAYA Tambaya: Assalamu alaykum, Malam don Allah Malam amma naji wasu sunce wai idan mutum yayi wuturi a lokacin da ya yi sallan tarawi, toh wai idan zai yi nafila a cikin dare zai kara raka'a daya ya cika wuturin da ya yi da sallah tarawi. shine nake neman karin bayani plxx malam. Amsa: Wa alaikum assalam, Annabi S. A. W. yana cewa ba a wutiri biyu a dare daya, Na'am akwai malaman da suka faɗi siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon shafa'i, tun da wutiri daya ake yi a dare. Amma abin da yafi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama ,, wannan zai sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin Annabi S. A. W. yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare wutiri". Allah ne mafi sani. Amsawa: Dr Jamilu Zarewa 07/06/2017
  • Rahmatu Lawan Barka da jumma’a ‘yan uwa. Allah Ya sada mu alkhairan da ke cikinta!
  • Lawan Dalha Hello
  • Danladi Haruna *SAKAMAKON MUHAWARA* *RANAR MAGAJI DANBATTA (19/01/2021)* *KARAWA TA 55 FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 77 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI =76 *KARAWA TA 56 KARAMCI WRITERS ASSC.:- MAKI= 81 MARUBUTA KARE HAKKIN AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 80 #MuhawararBakandamiya2020
  • Ameenah usman Had to share: reminder for all of us ???????????? When the Dajjal appears whenever that may be - it shall be a time of hunger and drought. He will have endless sustenance and the treasures of the earth shall follow along with him. Those inclined towards greed and selfishness shall join his ranks. ???? If we are going as far as kicking off with eachother at Aldi for frozen chips, having cussing matches in Asda for Santizer, tackling eachother at Costco for toilet roll, stocking 50 bags of 10kg Basmati rice for a family of 4 at Tesco, buying 20 cases of long-lasting milk at Morrisons, competing with lonely old age pensioners for tins of baked beans, and acting like possessed animals for the final 2 boxes of fish fingers - then don't expect that you won't be inclined towards him regardless of whether you deem yourself to be pious and holy. And his fitna is greater than any virus and illness that we see or hear about in our time or any other time. ???? The people of Ras?lall?h ? have self dignity. The One who took care of you whilst you were in your mother's womb yesterday will take care of you tomorrow. The Lord who gives sustenance to the ants and to the hungry birds in the sky will provide for you. Islam is not against taking means and having sufficiency but it is against greed, selfishness, bad character, and excess. Stock what you need and do not deprive others, especially those with young children and those who are vulnerable in society. ???? Allah has made us a nation of moderation. This is our hallmark. We aren't cowards and those who deprive others due to gluttony. 'The Satan frightens you with the prospect of poverty and instructs you towards immortality. ???? Allah PROMISES you forgiveness from Him and bounty. And Allah is All-Encompassing, All-Knowing.' (Surah Baqarah)
  • Ummyter Abdallah Madam din Dana kewa aiki jiya ta aikeni na sayo mata semo 2kg,danaje shagon sai na tarar sai 1 kg,so na dawo ban sayo ba shine tace min ni Wawa ne bana amfani da hankalina na sayo 1kg guda biyu ya zama 2kg Kennan idan an hada,na bata hakuri dai ta hakura,yau kuma tace na sayo mata slippers number 8,danaje babu sai lamba 4 shine na sayo lamba 4 guda biyu,na kawo batace komai ba Naga tana hada mini kayana cikin jaka,shine nake tambaya ko wanki zatayimin koko daki zata canjamin🤪🤪🤪
  • Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Cinikin mutum ake kamar yanda ake cinikayya a kasuwa,farashi suke yanke wa kamar yanda ake yi a super market,basa yin ragi balle su nuna alamar sauki,idan ka biya kudi su baka,idan ka ki biya su kasheshi. Basa tsoron kowa,balle su yi tunanin akwai wanda zai iya tunkararsu,dole akwai abin tsoro fa,kasar nan ta mu akwai firgici sosai,Ya Allah ka karemu daga wannan masifar ta satar mutane. Allah ka bamu lafiya da zama lafiya amin
  • Haleema Hassan Leemat day 4 Allah ka yafemana Allah ka jikanmu Allah kazama gatanmu Allah ga bayinka Allah kadafa musu
  • Umar Aslm. Yau da Gobe da juyawar Dare da Rana sun isa mai hankali yasan inda ya dosa.
  • Haupha123 Sallama nake ina ƙarawa, Ban san me ke faruwa ba da Ni, Amma dai na gane ina da damuwa. Rabbi ka ban mafita kan lamarina.
  • Umar Nuhu Babangida Masoya
  • adamu uba Assalamu alaikum barkanmu da safiya dafatan muntashi lafiya. Allah yayi maganin abinda yadamemu.
Previous
Next

Hotuna

  • Wall Photo­s 12 photos

Previous
Next
© 2021 Bakandamiya  -  About  -  Terms  -  Privacy  -  Talla  -  Support  -  Contact  -  Mobile Site
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram