• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Home
  • Rubutu
  • Bidiyoyi
  • Sautuka
  • Hotuna
  • Zauruka
  • Profile Type: Personal
  • Profile Views: 6,134 views
  • Followers: 50 followers
  • Last Update: April 8, 2021
  • Last Login: January 26, 2021
  • Joined: October 23, 2019
  • Member Level: Basic
  • Update
  • About

Update

The post was not added to the feed. Please check your privacy settings.
  • Madu AD
    Madu AD liked Maryam Haruna's post.
    April 8, 2021
    Maryam Haruna → MARUBUTA:
    Assalamu alaikum jama'ar wannan gida🙋🙋
    • 4 people like this
    • View all 17 comments
    • Madu AD
      Maryam Haruna Babu wanda ya hana fa
      • April 8, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Amrah Auwal 🤣🤣🤣
      • April 8, 2021
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Amrah Auwal Me ya sa za a hana
      • April 8, 2021
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Rahmatu Lawan Wa’alaikum salam. Gaisuwa, likta bokan turai!
      • April 8, 2021
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Wa'alaikissalam Jika barka da safiya
      • April 11, 2021
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD joined the group HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION
    April 8, 2021
  • Madu AD
    Madu AD liked Mustapha musa abu Aisha's post.
    March 18, 2021
    Mustapha musa abu Aisha
    #YIN SALLAR NAFILA RAKA'A HUƊU KAFIN LA'ASAR

    Yin sallar nafila raka'a hudu kafin sallar La'asar hanya ce ta samun addu'ar samun rahama ta Manzon Allah SAW ga mai yin wannan nafila.

    Manzon Allah SAW...  more
    Mustapha musa abu Aisha
    #YIN SALLAR NAFILA RAKA'A HUƊU KAFIN LA'ASAR

    Yin sallar nafila raka'a hudu kafin sallar La'asar hanya ce ta samun addu'ar samun rahama ta Manzon Allah SAW ga mai yin wannan nafila.

    Manzon Allah SAW yana...  more#YIN SALLAR NAFILA RAKA'A HUƊU KAFIN LA'ASAR

    Yin sallar nafila raka'a hudu kafin sallar La'asar hanya ce ta samun addu'ar samun rahama ta Manzon Allah SAW ga mai yin wannan nafila.

    Manzon Allah SAW yana cewa:-
    *(Allah kayi rahama da jin kai ga wanda yayi sallah raka'a huɗu kafin sallar la'asar)*.
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏( 1271 ‏)، ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 430 ‏)،ﻭﺃﺣﻤﺪ ‏( 2/117 ‏).

    #FALALA GA WANDA YA KIYAYE NAFILA KAFIN SALLAR LA'ASAR DA ITA KANTA SALLAR LA'ASAR DIN_

    Wanda ya kiyaye wannan sallar nafila kuma ya dauwama yin ta,yana samun falala kamar haka:-
    *_Samun addu'ar Manzo Allah SAW ta rahama a gareshi_*. Kamar yadda Manzon Allah SAW ya faɗa:-
    *(Allah kayi rahama da jin kai ga wanda yayi sallah raka'a huɗu kafin sallar la'asar)*.
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 430 ‏)

    *2-Samun sallar la'asar cikakkiya kuma a cikin lokacin ta*.

    *3-Shaidar mala'iku da halartar su sallar la'asar da canjin aiki tsakanin su*

    Manzon Allah SAW yana cewa:-
    *(Mala'iku suna canjin aiki da bibiyar junan su a cikin dare da yini,suna haɗuwa a sallar La'asar da assuba......)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 555 ‏) ، ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 632 ‏) .

    *4-Albishir da aljanna ga wanda yayi sallar assuba da La'asar acikin lokacin ta*

    Manzon Allah SAW yana cewa:-
    *(Wanda ya sallaci sanyi guda biyu zai shiga aljanna)
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 574 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 635 ‏)

    Sanyi guda biyu ana nufin:-
    _Sallar La'asar da Assuba acikin lokacin ta_

    *5-Ana lullumka ladar sallar La'asar*

    Manzon Allah SAW yace:-
    *(Hakika sallar la'asar an shar'antata ga mutanen da suke kafin ku sai suka tozarta ta, dukkan wanda ya kiyayye sallar La'asar yana da lada guda biyu......)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 830 ‏)

    *6-Dukkan wanda ya kiyayye sallar La'asar acikin lokacin ta ba'a kange shi daga ganin Allah a ranar alƙiyama*

    Manzon Allah SAW yana cewa:-
    *(Lallai hakika zaku ga Ubangijin ku kamar yadda kuke ganin wata yana daren haske,dukkan wanda yake da iko kada ya bari sallar assuba da La'asar su kuɓuce masa to ya aikata Hakan......).
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 554 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 633 ‏)

    *_ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍِﺟْﻌَﻠْﻨَﺎ ﻣِﻦْ ﺍﻟﻤُﺤَﺎﻓِﻈِﻴﻦَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﺼَّﻠَﻮَﺍﺕِ ﻭَﻣِﻦْ ﺍﻟﻤُﻜْﺜِﺮِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﺍﻟﻄَّﺎﻋَﺎﺕِ ﻳَﺎ ﺭَﺏَّ ﺍﻟﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ_*  less  less
    • 9 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked ALI EL-ADI's post.
    March 18, 2021
    ALI EL-ADI
    So shi yakan sa wa Soko riga yaje cikin mutane ya yi sokoko a soro.
    • 6 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked Bakandamiya's post.
    March 18, 2021
    Bakandamiya shared Dandalin Dr. Bukar Usman, OON's item.
    • 5 people like this
  • Madu AD
    Madu AD commented on Maryam Haruna's photo.
    March 3, 2021
    Jibrin Adamu Rano Ummyter Abdallah Rahmatu Lawan Lawan...  
    • 9 people like this
    • View all 47 comments
    • Madu AD
      Lubna Sufyan Amin thumma amin. Nima ina godiya da gayyata. Allah yayi jagora
      • March 2, 2021
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Madu AD Kamar dai bakuwar ba ta fahimci tambayar ba. Fadin yanda...  
      • March 3, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Madu AD Kamar bakuwarmu na nufin a da bai samu karbuwa ba kenan?
      • March 3, 2021
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Rahmatu Lawan Masha Allah, Malama Lubna! Allah Ya kara wa rayuwa albarka.
      • March 3, 2021
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Rahmatu Lawan Sannun da kokari ke ma mai gabatarwa. Allah Ya yi jagora.
      • March 3, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD commented on Bakandamiya's blog entry.
    February 24, 2021
    Takaitaccen tarihin Fela Kuti
    An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun.
    Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ra...
    • 12 people like this
    • Madu AD
      Sadik Na'am
      • February 24, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Madu AD Sannu da ƙoƙari. Mun ƙaru sosai.
      • February 24, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Jamilu Abdulrahman Dakyau
      • February 26, 2021
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD liked Bakandamiya's blog entry.
    February 24, 2021
    Takaitaccen tarihin Fela Kuti
    An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun.
    Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ra...
    • 12 people like this
    • Madu AD
      Sadik Na'am
      • February 24, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Madu AD Sannu da ƙoƙari. Mun ƙaru sosai.
      • February 24, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Jamilu Abdulrahman Dakyau
      • February 26, 2021
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD liked Mustapha musa abu Aisha's post.
    February 9, 2021
    Mustapha musa abu Aisha
    DAGA CIKIN TAMBAYOYIN DA MANZO ALLAH S. A. W YA AMSA

    #TAMBAYA TA...  more
    Mustapha musa abu Aisha
    DAGA CIKIN TAMBAYOYIN DA MANZO ALLAH S. A. W YA AMSA

    #TAMBAYA TA TAKWAS-🎵
    *Mafi girman kyautar da Allah zai yiwa...  moreDAGA CIKIN TAMBAYOYIN DA MANZO ALLAH S. A. W YA AMSA

    #TAMBAYA TA TAKWAS-🎵
    *Mafi girman kyautar da Allah zai yiwa musulmi*

    Daga Usamatu bn Sharik رضي الله عنه, yana cewa:-
    "Ya Manzon Allah صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ,Minene mafi girman kyautar da Allah zai yi wa musulmi??, sai Manzon Allah صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ yace:-
    *(Mafi girman kyautar da Allah zai yi wa musulmi itace KYAWAWAN ƊABI'U)*
    @صحيح إبن حبان ٤٧٨
    📚 الوادعي الصحيح المسند ١٦
    @أخرجه أحمد ١٨٤٥٤
    🍃🍂🍃🍂

    🌴ابن القيم رحمه الله:
    Yana cewa:-
    "Idan kaga mutum da kyawawan halaye na kwarai, mai kamala da ɗabi'u masu kyau, to wannan ya hada kyawun fili da na boye kuma ya sami babbar kyauta ta musamman daga Allah......"
    @كتاب الفوائد لابن القيم رحمه الله تعالى .
    🍃🍂🍃🍂🍃🍂🍃🍂

    kyawawan ɗabi'u ya kunshi abubuwa hudu biyar:-
    *1-Kamewa daga cutar da mutane da bakin ka ko da hannun ka ko da matsayinka*.

    2-Yin afuwa ga wanda ya zalumceka da mayar da alkhairi ga wanda ya cutar da kai.

    *3-Sakin fuska da saukin kai lokacin mu'amala da mutane wanda ya kunshi girmama babba da jin tausayin na kasa da kai*.

    4-Sadar da zumuncin wanda ya yanke maka da baima wanda ya hanaka.

    *5-Yaɗa alkhairi tsakanin mutane da yanyo masu alkhairi*

    Allah ne mafi sani  less  less
    • 7 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked Nafisat Isma'il's post.
    February 9, 2021
    • 6 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked Nafisat Isma'il's post.
    February 9, 2021
    • 5 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked Lawan Dalha's video.
    February 8, 2021
    Bayanin Malam Nasir El-Rufai game da matsala banditry a Arewa
    Ku saurari bayanin Malam Nasir El-Rufai game da matsala banditry a Arewacin Najeriya.
    • 9 people like this
    • Madu AD
      Muttaka A. Hassan Wannan karon dai ina tare da El-rufa'i, babu wani sulhu da zai yiwu da 'yan ta'adda sai fa idan film za a ci gaba da haska mana. Allah Shi kyauta.
      • February 8, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Rahmatu Lawan El-Rufa'i muke bukata domin magance wannan ta'addanci. 'Yan ta'adda ba su bukatan lallaba sam.
      • February 8, 2021
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Lawan Dalha Ka fadi daidai, Muttaka, sai fa idan film za a ci gaba da haska mana.\n\nAmin Ya Rabb.
      • February 8, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      MumAmnash2486 Wannan gaskiyane Allah ya yi mana maganinsu
      • February 9, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD liked Aysha ALIYU GARKUWA's post.
    February 8, 2021
    Aysha ALIYU GARKUWA
    📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

    ...  more📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

    ...  more
    Aysha ALIYU GARKUWA
    📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

    ...  more📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

    *GARKUWA*

    PAGE 2

    NA
    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

    📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘



    *LITTAFINA na kuɗine, akwai na 300 wanda a wata ɗaya za'a gama Part 1, akwai kuma na 1k wanda a mako biyu kacal za'a gama Part 1 da izinin Allah. Yimin TRANSFER ɗin darinki uku ko 1ooo ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar BIYANKI ta number 09097853276 Ayyah ƴan SP Group banda kati, in baki da ac bada a POS. Kuna ƴan 300 in dai da hali turamin ta ac yafi, in babu kuma to turo katin mtn na ɗari uku ta layin 09097853276. Na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar iyayenki in dai kin san niyarki ki saya ki fiddamin littafina, dan daraja da girman Allah da tsarkin al'ƙur'ani kada ki saya Please kuwa darajar iyayenki kada ki saya, ba don niba sai ɗan Allah da manzonsa da iyayen da suka haifeki/ka*


    ~AKWAI KAYAN GYARA HAƊIN AMARE DA MASU JEGO, DA MASU SABUNTA AMARCI, IN KINASO KI TUNTUƁI WANNAN NUMBER 09097853276~


    Ta juye ta dawo mutun *bani Adam* mace fara ƙal mai tsananin kyau da cikar sura da haiba.

    Wani irin zabura sukayi cikin tsananin tsoro da firgici da tashin hankali suka zaburi gaba ɗayansu, Giɗaɗo kuwa da azaban ƙarfi ya afka jikin Arɗo Babayo,
    Inna kuwa gaba ɗaya jikinta rawa da karkarwa yakeyi tamkar mazari wata iriyar fitinenneyar zufa mai azabar ƙarfice taketa tsastsafo mata tako wani sashi na jikinta.
    Seyoji, Gainako, da Ja'eh, gaba ɗaya jikinsu karkarwa yakeyi tamkar mazari.
    Giɗaɗo kuwa wani irin juyawa yayi a firgice ya yunƙura zai gudu, Arɗo Babayo ne yayi hamzarin kamo hannunshi ya rikeshi gam.

    Zabura sukayi.
    Gaba ɗayansu sabida wata iriyar fitinenneyar iska mai azabebben sanyi daya fara kaɗawa yana rausaya ganyayyaki da dukkan tsirran dake yakin surururururu haka iskar ke kaɗawa a hankali tana ratsa jikinsu.

    "Innalillahi wa innalillahi rajiun. Hasbunallahiwani'imanwakil".
    Shine abinda suketa maimaitawa gaba ɗayansu cikin tsananin kaɗuwa, ruɗani, firgici, tashin hankali da tarin tsoro, da nitsuwar ganin ikon Allah.
    Iskar dake karkaɗawa ce tasa gaba ɗaya suka hautsine.

    Parvina kuwa da sauri ta faɗa jikin baiwar Allah'n tare da ruggumeta.
    Baki na rawa ta fara addu'a.
    "Allahumma inni as'aluka khairaha wa'azubika min sharri ha".
    Da ƙarfi take fidda sautinta tana maimaita addu'ar.
    Wanda sanadin haka suma kab suka fara bin bakinta.

    Allah cikin ikonsa da ƙudurarsa sai ga iskar nan ta fara lafawa a hankali.

    Cikin al'ajibi da tsoron ƙudurar Allah suka ware idanunsu baki ɗaya a kan baiwar Allah'n nan, da
    shigar suturar dake jikinta ne yayi masifar sasu ruɗani.
    Cikin dakiya da ƙarfin zuciya Arɗo Babayo ya kalli Buba a hankali yace.
    "Buba ɗauki su Giɗaɗo ku tafi garke kuje kuyi tatsa".
    Kai ya gyaɗa mishi domin baki da jarumar Buba sun tafi,
    Dan a iya tsawon tarihin rayuwarsa ko a films ko a books story bai taba ji da katari da makamancin abinda ya yagini a zahiriyaba, tsuntsuwar Kurciyar ta zama mutun mace a gabanshi ba labari aka bashiba ra'anul ayni.
    Cikin yanayin tarin kaɗuwa da rawan jiki yasa hannu ya jawo hannun Giɗaɗo daya kifa kanshi jikin babanshi.
    Cikin fillanci yace.
    "Zo Giɗaɗo zomu tafi".
    Da sauri ya miƙa hannunshi ya kama na Buba kana suka juya suka fita.

    Appa kuwa kanshi ya kauda daga kallon wannan kekyawar halittar dake gabanshi a cikin ransa yace.
    "Anya kuwa, wannan mutunce ba iskaba".
    Inna kuwa gefe ta ɗan matsa cikin rawan murya na tsoro da hausar da sai ka dage zaka gane me take cewa tace.
    "Ra ga Allah bewar Allah mutun ko al'jan?".
    Ido suka tsurawa matar a zatonsu ko zata basu amsa.
    Sai dai ganin yanayin da take cikine ya sasu cire tsammanin samun amsarta.

    Domin gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, tamkar mazari.
    Kana sai zufa dake tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta,
    ta rumtse idanunta da azaban ƙarfi, tasa haƙoranta ta datse lip ɗinta na ƙasa,
    duk mace data taɓa haihuwa in ta ganta tasan naƙudace ke azazzabarta.

    Tausayin ta ne ya cika zuƙa tansu baki ɗaya.

    Arɗo Babayo ne yayi ɗan gyaran murya tare da kauda kanshi daga kallonta sabida kwarjininta yafi ƙarfin ƙwayar idanunsu cikin sanyi murya yace.
    "Allahu wahidun ƙahhar, Mutunce ba al'jana bace, Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin kasan ce warta a cikin tsuffofin tsuntsaye, amman kam tabbas al'amarine mai tarin girma da sarƙaƙiya, Tine taimaka mata, da zuciya ɗaya ina ji a jikina ba mai cutarwa bace. Kuma akwai tabbaci da kekyawan zaton musulmace".

    Ido ta zubawa mijin nata da yake bata ƙarfin guiwa.
    Appa ne ya kalleta tare da gyaɗa mata kai, alamun eh ta taimaketa,
    Ita kuwa Parvina cikin tausayawa da zubda hawaye tace.
    "Appa kalli hannunta ya kumbura gashi jikinta zafi Appa a taimaka mata".
    Hannu ya miƙo ya kama Parvina cikin tausayawa yace.
    "Zo nan Parvina za'a taimaka mata kinga bata da lfy tashi a jikinta,
    kinga ki dena danne mata hannun da cikinta".
    kai ta gyaɗa kana ta kalli matar cikin sanyi tace.
    "Sannu!". Bata basu amsa bata kulasu bata kuma hafimtar komai daga garesu,
    haka yasa su Arɗo Babayo juyawa suka fita, ita kuwa Inna matsowa gareta tayi cikin tarin ƙarfin guiwa irin na fulani. Fulaninma irinsu na daji ba irin wasunku na birniba.
    cikin sanyi tace.
    "Taso muje daga ciki".
    ido ta zubawa Inna cikin yanayin wahalar da takeji,
    hannu Inna tasa ta kamo hannunta mai lafiyar, ta miƙar da ita tsaye.
    Allah da ikonshi, sai gata a tsaye cas.
    Haka yasa Inna ta jata suka koma cikin gida, cikin ɗakinta ta kaita,
    a bakin katifar da suka kwana ta ajiyeta,
    da sauri ta koma woje wuta ta hura ta ɗaura ruwan zafi.

    Kana ta dawo ciki.
    Cikin mamaki take kallonta ganin taja ta jingina da jikin gini kana, ta rumtse idanunta ga hawaye nata kwaranya daga idanunta.
    Gefenta ta zauna ta zuba mata ido.
    Jin an zauna gefen tanne yasa ta buɗe kekyawan idanunta, cikin kula Inna tace.
    "Sannu baiwar Allah, kamar naƙuda kikeji ko?".
    Kai ta gyaɗa mata alamar eh naƙudar takeji,
    murmushi inna tayi tare da cewa.
    "Alhamdulillah naji sanyi na ƙara gamsuwa ke mutunce, kuma kina gane me nake faɗa a yanzu, to amman kiyi magana mana".
    Kanta ta jujjuya mata alamun.
    "Bazan iyaba".
    Jin muryarsu Arɗo Babayo ne yasa inna tayi maza ta fito,
    Ganin Arɗo Babayo da Appa da kuma Malam Liman da sarkin bakansu wanda yake rugar makotansu ne yasata saurin fitowa tare da cewa.
    "Sannun ku da zuwa Malam Liman, Baka barka da zuwa".
    Taburma ta shimfaɗa musu, jin muryar Malam Liman ne na cewa.
    "A a bar taburmarnan ina baƙuwar tamu?".
    "Tana cikin ɗaki, da alamun tana fama da yanayin naƙuda ne".
    Inna ta faɗa cikin alhini.

    Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
    "Ina son ganinta".
    Arɗo Babayo ne yace.
    "To bisimilla, shigo daga ciki".
    Ɗakin suka nufa Inna na gaba Arɗo Babayo na biye da ita a baya, kana Appa da Malam Liman da Sarkin Baka suka rufa musu baya.

    Suna shiga suka sameta zaune ta haɗe jikinta wuri ɗaya,
    jin motsin shigowar mutanene yasa ta ɗago kanta,
    da sauri ta kauda idanunta.
    Shi kuwa SARKIN Bakan, kanshi ya rinƙa jinjina wa cikin al'hini yake cewa.
    "Mutun ce ba al'janba, baiwar Allah an tozarta rayuwarki."
    Sai kuma ya kalli Arɗo Babayo cikin sauri yace.
    "Maza a bani madarar shanu mai ɗumi wanda aka tatsa yanzu".

    To Arɗo Babayo yace tare da juyawa ya fita, a harabar gida yayi arba da Gainako da yake shigowa da kwaryar nono,
    da sauri ya iso, kana yasa ƙaramar kwarya ya kamfati madarar shanun daketa tururi sannan ya juya ya koma cikin ɗakin.

    Yana zuwa ya miƙawa sarkin Bakan,
    yana amsar ƙoryar,
    ya ajiyeta a gabanshi jakar fatar ruƙimi da yakesa magungunanshi a cikine ya sauƙe daga kafaɗarshi, kana a hankali ya fara harhaɗa magunguna a cikin madarar,
    saida yasa komai sannan ya kalli Inna yace.
    "A bani zuma da zam-zam".
    Da sauri tace.
    "To". Kana ta miƙo ta ɗauko mishi, koda ta kawo da sauri yasa zumar da zam-zam ɗin ya gaureyasu,'.
    Kana ya bawa Malam Liman da Arɗo Babayo sukayi mata tofin ayatul shifa, a ciki, kana ya amshi kwaryar.
    Inna ya miƙawa kwaryar yace.
    "Gashi bata tasha".
    Amsa tayi kana ta matso kusa da matar a hankali tasa mata bakin kwaryar a bakinta.
    Tare da cewa. "Bismillah ki Sha".
    A hankali ta buɗe bakinta, ta fara shan madarar shanun nan da magungunan, masu haɗe da zam-zam da zuma da kuma rahamar ayatul shifa.
    Saida ta sha mai yawa sannan ta kauda kanta.

    Ae fa a take saiga naƙuda ta tashi gadan-gadan. Ganin haka yasa su Arɗo kab suka fito woje ya rage daga ita sai Inna.

    Ganin haka yasa Malam Liman tura Ori da yanzu ya shigo yaje ya kira matarsa ta taimakawa inna su amshi haihuwar.

    Ba jimawa kuwa Iya laure tazo, kai tsaye cikin ɗakin ta wuce.

    Cikin ikon Allah a take a sauƙaƙe Allah ya sauƙeta lfya, ta haifi yarta mace ƴar ƙanƙanuwa.

    Bayan sun yanke cibiya sun gyara,
    komai na wurin.
    Kana Inna ta taimaka mata tayi wonka,
    ita kuwa iya laure wonka tayiwa jaririyar ta haɗeta cikin zanin Inna ta bawa Parvina daketa tsalle.

    Koda suka fito daga wonka,
    konciya tayi a kan katifar, kana iya laure ta kontar mata da ƴar a gabanta.

    Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana a hankali ta lumshe idonta, tana son ta tuno wani abu na rayuwarta ta baya amman ina ta kasa tunowa,
    Abu ɗaya takeji bata manceba sunan Allah wanda tunda ta dawo mutun taketa maimaita kiranshi a zuciyarta dan taji bakinta bazata iya magana ba, amman a ranta tanaji tana bitar karatun al'ƙur'ani mai girma da tarin addu'o'in kamar yadda takeyi tun tana a tsunstsuwar ma.


    Ganin tayi shiru ne kamar maiyin bacci yasa inna da iya laure suka fito woje.
    Sashin Arɗo Babayo suka nufa,
    suna shiga sukayiwa juna barkar haihuwarta lfy.
    Shiru sukayi baki ɗayansu bayan duk sun zauna kamar yadda Sarkin Baka ya umarcesu, gyaran murya yayi kana a hankali ya fara magana.
    "To da forko dai sai dai muce. Alhamdulillah, mun godewa da yasa sanadinmu wata baiwar Allah zata samu waraka daga mugun cuta na magauta maƙiya azzalumai marasa tsoron Allah".
    Kai suka jinjina alamun gamsuwa, shi kuwa tonkoshe ƙafa yayi kana yaci gaba da cewa.
    "Kamar yadda kuka gani a yanzu mutunce bani adam ce ba tsunstsuwa bace kamar yadda kuka gani da zata a baya, aikin sihirine kawai ya maidata haka.
    Amman Alhamdulillah tunda gashi yanzu Allah yayi ikonshi ya karya abun da akayi mata ya kuma sauketa lfy dama shi asiri tasirinshi kaɗanne ga wanda yayi imani da Allah kuma dole gsky zatayi halinta watan-watarana".
    Arɗo Babayo ne yace.
    "Allah mai iko, mutun a maidashi tsuntsuwar Boleru kai abinnan da al'ajabi".
    Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa.
    "Ɗan Adam kenan mai wuyar gane hali babu mai sanin halin mutum sai Allah, domin shi ɗan adam dare".
    Sai ya kuma kalli Inna tare da cewa.
    "Yanzu tayi magana ne?".
    Da sauri Inna tace.
    "A a batayi mgna ba sai dai in anyi magana tanaji kuma tana ganewa".
    Kai ya rausayar tare da cewa.
    "Zatayi magana in sha Allah, yanzu aci gaba da kula da ita yadda ya dace zan bata magunguna kuma,
    sannan kada kuji tsoronta ko kaɗan in sha Allah ba mai cutarwa bace".
    Malam Liman ne ya gyara babbar rigarshi tare da cewa.
    "To wannan baiwar Allah'n ko daga ina ta fito? Ko ta yaya zamu gano yan uwanta danginta ahlinta ko wani nata a duniya?".
    Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
    "In sha Allah ita in ta dawo haiyacinta, zatayi mana bayanin komai zata faɗa mana sunanta sunan garinsu sunan iyayenta sunan mijinta da anguwarsu sai mu mikata garesu".
    Appa ne ya ɗanyi ajiyan zuciya tare da cewa.
    "Allah ya bata lfy ya kuma dawo da ita cikin haiyacinta, kuma in sha Allah duk wani abu daya kamata ayimata a duniya zan mata har sai munga ta samu' lafiya ta koma ga iyayenta".

    Da haka sukayi ta tattauna duk abinda ya dace ayi mata.
    Anan kuma sarkin baka yaje da kanshi ya ɗaure mata karayar hannunta yayinda Parvina kuwa ke like da ita...!

    Haka Inna da iya laure sukayi ta kula da ita a cikin wannan satin sunan...!

    ************

    ...Bayan shekaru Goma sha biyu...

    Cikin Ƙasar Kautal A Jihar Ɓadamaya state.

    A wani yanki na Ɓadamaya state, cikin Shikan local Government area a wata rugar FULANI mai suna.
    *RUGAR BANI*

    Garin Shikan wani yankine daga yankunan Ɓadamaya yankine mai tarin ƙabilu ma banbanta addinai da al'adu wanda duk yankun Ɓadamaya shida Bimu sune sukafi tarin ƙabilun sai dai babbancin mafiya yawan kabilun Bimu musulmaine saɓanin mafiya yawan ƙabilun Shikan kafurine maƙiya Allah da Manzonsa.

    Shikan shine sashin da yafi tara ƙabilu mafiya yawa, masu baƙaƙen zuciya ƙabulun da hasken addini bai cimmusuba.
    Ƙabila mafi rinjaye a yankin Shikan itace ƙabilar ɓachama. Mafi akasari Ɓachamawa mutanene kafurai ne marasa ɗigon imani a zuƙatansu marasa son zaman lfya, mugunta da kisa shine abinda ke sasu farin ciki, abinda kawo ya sanine duk sanda akaji jihar Ɓadamaya cikin wani tashin hankali to daga ƙabilar ɓachama ne.

    Duda yawan ƙabilu na garin Shikan hakan baisa fulani sun sakar musu garinba, domin tushen garin na fulanine, sabida kowa yasan makiyayi basa nesa da wurin damshi da ruwa, domin rayar da ababen kiwonsu.
    Haka yasa akwai musulmai Hausawanmu da tarin yawa cikin garin Shikan, wanda duk rintsi da wahala sunƙi barin garin, koda yake hakan baya rasa nasaba da irin al'barkatu da ni'imomin da Allah yayiwa garin.

    Daga gefen. Garin Shikan akwai babban kogin da yakeda ruwa biyu wanda ko wucewa zakayi ta kan babban gadan da titin da zai kaika cikin Ɓadamaya zaka hangi ruwane kala biyu a kogi ɗaya basu kuma taɓa haɗewa wuri ɗaya ba da izinin ubangiji.

    Gefen kogin ta dama wata babbar *Rugar fulani mai suna Rugar Bani* ce mai tarin tarihi, rugace mai girma wacce Ubangiji ya ƙawatata da ababen buƙatar yau da kullum, wannan Ruga itace yanki mafi sanyi a yanki Ɓadamaya state rugace damu fulani muke ce musu *JOTTAN MA'EN* Bi ma'ana fuli mazauna wuri ɗaya, ba ire-iren fulani makiyaya masu tafiye-tafiye bin rugageba, fulanin Rugar Bani fulanine makiyaya masu tarin dabobi masu tarin yawa, Rugar Bani Rugace da aƙalla fulaninmu sunyi sama da shekaru dari da ashirin awannan Rugar, shiyasa harda gini zamani da kyawawan gidaje fulanin sukayi, yayinda kuma akwai bokkokinma a cikin Rugar tasu wanda kuma suka sayi filin da kuɗinsu zufansu a hannun sarkin Shikan na wancan zamanin ya sayar musu yankin wurin gaba ɗaya sun biya kuɗinsu ya kuma basu takardu su, suna zaune a nan suna noma suna kiwo.
    Rugar Bani na zagaye da ƙauyukan ƙabilun Ɓachamawa da tarin yawa, wanda nan gefensu ƙauyen Bonon yake wanda nanne dodon tsafin ƙabilar ɓachamawan take wanda sunan dodon tsafin nasune suka sawa suna ƙauyen suna Bonon. Kauyen Bonon shine zuciya da karfin kafuran nan, sunyi imani dashi, fiye da zaton mai zato, koda laifi wani yayi bonon ake kaiwa ƙara kuma muddin bonon ya tsinewa mai laifinsun to zai lalace ya ɗai-ɗaice dashi da zuriyarsa baki ɗaya, da yake sunyi imani da hakan kuma yana faruwa suna gani shiyasa bonon yake tamkar zuƙatansu, kamar dai yadda in jikin ɗan adam idan zuciya ta ɓaci gagganji na ɓaci to haka bonon take a wurinsu... Wannan kenan

    Rugar fulanin Bani yafi ko wani yanki na Ɓadamaya sanyi mai ɗan karen daɗi.
    Koda yake hakan ya samune sanadin ƙawanya da wani babban dutse mai fesar da numfashin sanyi yayi musu, wanda ya kasance musu tamkar rufar garin.
    Gefen hagun Rugar Bani kuwa wani babban fadama ne mai cike da lamɓu mai ɗauke da ababen more rayuwa wanda ya kasance mallakinmu Fulanin Rugar Bani, lambun yana da duk wasu kayan marmari kamarsu.
    Lemu, mangoro, gwaiba, ayaba, dabino,kwakwa, kashu, kankana, abarba, da jefi-jefin tuppa da inabi.
    Wanda wannan fili yake mallakin Fulanin Rugar Bini'nne, kana bayan filin kuma akwai wani rafin da ya kasance masarrafin noman shinkafawa ne wanda suke yinshi noman rani da damina, kuma shina mallakin Fulanin Rugar Bani ne, wanda komawa yasan iya filinshi,

    Daga gaban Rugar Bani kuwa kogin Shikan ne malale a gabansu iya ganin mai hange da ido biyu gefen hagunsu kuwa nan garken shanunsu ke shimfiɗe bila adadin.

    Rayuwar Fulanin wannan Rugar rayuwace mai cike da aminci da amana da hakuri da kauda kai duk da tarin zalunci da kafurai ƙabulun Ɓachamawa keyi musu.

    "Kamar yadda duk kowa ya sani duk duniya anyi ittifaƙin ba fulatani ko ba fulatana basa neman tsokana ko tada husuma bare tada zaune tsaye. Akan cutar da bafulatani yayi kamar bai san an cutar dashi ba ko bai ganeba, wannan dalilin yasa duk ƙabilun ƙasar Afirka sukeyiwa ƙabilarmu kallon wawaye ne ko basu san abinda sukeyiba ko sokayene, masu ƙarancin wayewa Gidadawa.
    Mu kuwa a namu sashin fulani mun kasance masu kauda ido kan cutarwar forko data biyu, sai dai a haƙiƙinin gsky bama lamunta ko jurar cutarwa ta uku! Domin rama cuta ga macuci ibadace. Kuma Ba'a sarar mumini a rami ɗaya sau uku".
    Wannan shine jawabin da wani farin dottijon bafulatanin dake zaune tsakiyar al'ummar wannan rugar bayan sun dawo daga jana'izar mutun ɗaya da ƙabilun ɓachama suka kashe musu cikin sunkuru, a daren jiya wanda ya kasance ɗane ga Arɗon Yabani shugaban Rugar tasu kenan.
    Hannu yasa ya share zafafan hawayenshi dake kwaranya daga ida nunshi cikin ɗaga sauti yaci gaba da cewa.
    "Fulani basa ɗaukar mataki domin yaƙi ko zalumci sai dai dan kare kawunansu. Kuma kun sani duniya duk ta sani FULANI BA ƳAN TA'ADDA BANE! Ba ƴan bindiga daɗi bane, makiyayene masu ƙare rayuwarsu dan samawa mazauna cikin birane jin daɗin rayuwa, muyi kiwo mu kai musu suci naman susha madarar shanu kana muyi noma mu ciyar dasu.
    Meyasa su mutanen birane basa ɗaukar matsalarmu tasu matsalar ana kashemu tamkar kiyashi kuma babu masu kulawa".
    Tsagaitawa ya ɗanyi tare da shashsheƙa cikin bada umarni a matsayinsa na shugaban Rugar uban wanda aka kashe kuma yace.
    "Na roƙeku da Allah kada wanda ya ɗauki makami domin ramuwa duk da munga yankan rago akayiwa Hashimu amman bamu san wayeba kuma bamu da hujja, dan haka kada wanda yace zai ɗauki makami.
    Muyi rubutu mu aikawa maimartaba sarkin Ɓadamaya, domin Al'ƙalami yafi tokobi, mu kai kukanmu gareshi, tunda shi sarkin wannan yanki na Shikan mun kai mishi kukanmu a karo na barka tai bai kulaba, kuyi hakuri mu miƙa lamarinmu ga sarakuna mu, inada yaƙinin zasuyi mana adalci".
    Shiru mutanen da aƙala sun kai ɗari da ashirin sukayi.
    Yayinda kowa ya keta zubda hawaye.
    Sai ɗaya daga cikine da ya kasance baƙin jakada Ɓachama ruwa biyu uwarshi ƙabilar ɓachama, wacce ubanshi bakura babarbaren borno wanda shike saida kanwa a rugartasu ya auro Uwar Ba'ana. yana naɗa komai a wayarshi,
    domin miƙawa shugaban mayaƙan ƙabilar ɓachama, komai ya gani, domin shi ɗin ya kasance, makashinsu ne kuma taburmarsu ne, domin dama bahaushe yace sai da ɗan gari akanci gari da yaƙi!...


    A cikin babban birnin Ɓadamaya kuwa. *Land of beauty* Garin Modibbo Joɗa,
    Mai tutar fulɓe garinda duk arawacin ƙasar Kautal mune kaɗai muka rage da tutar Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo.
    Wanda ya dasashi ya kafashi da hannunshi masarautar fulbe mai ƙarfi Masarautar Joɗa...

    Cikin birnin matsarautar Joɗa.

    A cikin babban birnin Ɓadamaya.
    Wasu irin tsala-tsalan motocine wanda a ƙalla sun kai Goma suke jere suna fitowa daga harabar shaharerriyar makarantar Jami'a ta dake cikin babban birnin Ɓadamaya wato J.U.B Joɗa University Ɓadamaya

    Yayinda suke tafiya a jere a jere cikin tsananin gudu tamkar zasu tashi sama kana ga jiniya daya karaɗe illahirin sashin wurin wanda dole yaja hankali duk wanda ke wurin gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama da titin.
    Motoci huɗune a gaba, wanda suka kasance masu kyau.
    Sai wata Rolls Royce, mai kuɗi kimanin naira million 4, 959,630. Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai sheƙi da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine ƙal sai glass ɗinta daya kasance tin tek mai duhu.
    Wani kekyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine ƙal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa.
    Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin yadin Super Nour a jikinsa wanda a ƙalla zai kai tamanin ɗ kuɗinshi, ya ɗaura baƙar al'kebbarsa ta jinin larabawan saudia Al'kebbar baƙace mai faɗi, kana yasa farin hirami a kanshi da zagayen baƙin saman hiramin.
    Fuskarshi nan ta fito ras sajenshi mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya komta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido, wani irin tsabtaceccen gemune da bazai wuce kamu ɗaya ba ne yayi lib a haɓarsa.
    Zaune yake cikin motar ya jingina bayanshi da sit ɗin, ya lumshe fararen idanunshi,
    A hankali yake motsa tattausan jajayen laɓɓansa yana tasbihi.
    "Subahanallahi wal'hamdulillah wa la'ilahaillah Allah Akbar, Astagafillaha wa'atubu ilaik".
    Yanaji a jikinshi kudun da akeyi yayi yawa, to amman dolene ayi irin wannan gudun domin lokaci na gab da ƙurewa, dan sosai sallan jumma'ar ya gabato, yasan yanzu masallacin ya fara cika, wannan dalilin yasa bai hana drevernshi gudunba, kuma bai hana fadawanshi sakin jiniyarba, dan ta hanyar jiniyarce zaisa a basu hanya su samu su isa kan lokacin daya dace.
    Bawai ya bari ayi jiniyar da gudun dan nuna isa da ɗagawa bane, sai dan son isa masallacin Masarautar Joɗa da yake limanci kuma yake gabatar da Hudubar jummar matuƙar yana ƙasar tiyatar da yayiwa watace ya sa lokaci yaso ƙure mishi.
    Motoci, biyar kuma na bayanshi wanda uku daga ciki na ɗaliban J U B da ya fitone, wanda yana aiki cikin Hospital ɗin makarantar, bayan kuma asibitinshi da kuma Genaral Hospital Ɓadawaya da yake zuwa sau ɗaya cikin ko wanne sati.
    motoci biyun bayanshin kuma, Jalal ne da abokanshi.
    Shiyasa motocin suka taho a jere-a jere dan shi bai fiye yarda ya fita da mota sama da biyarba, suma ba kullum ba, wani lokacinma yakan fita shi ɗaya.

    A haka dai har suka fara ratsowa cikin Ɓadamaya, a dai-dai mashigar laleko ne,
    Cunkoson ababen hawan ya yawaita, yayinda suka danno kai wurin yasa da yawa suka fara komawa gefen titi suna kauce musu dan basu hanya dan jiniyar dake musu nunin akwai uzurin gaggawa ga kuma fadawa a motocin.

    Wani mai keke Napep ne ya gangara gefen titi har kusa da wani mai saida su Oranges Banana da dai sauransu.
    Dogon tsaki mai Napep ɗin yaja tare da cewa.
    "Wannan ai mulkin mallaka ne da izza duk an tsaidamu sabida wani can zai wuce ai duk nan muma saurin mukeyi munada babban uzuri, saurin da duk mutanen wurin nan keyi duk an katse mana hamzarinmu na son isa masallaci kan lokaci muji huɗubar jumman wannan rana".
    Mazan dake cike a bayan napep ɗin ne suka haɗa baki wurin cewa.
    "Wallahi kuwa, gashi motocin nasu nada yawa.
    zasu sa mu rasa jin hudubar wannan fasihin Malamin".
    Wani mai motane dayake gefensu ya amshi zancen da cewa.
    "Kuma gaba ɗaya mutanen nan wurin masalacin zasu tafi, sabida duk mai son jin huɗuba mai ratsa jiki da zuciya baya ƙaunar ko furuci ɗaya na wannan malamin ya wuce shi domin Allah ya rigada ya mishi baiwar lafazi mai shiga zuciya".

    Wanda ke gefensu ne ya amshi zancen da cewa.
    "Gaskiya ne wannan sabida shi Allah yayi mushi baiwar lafazi da iya tabsiri mai nusar da gafalelle".
    Mai saida kayan yayan itatuwan dake gefen sunne yayi ɗan murmushi kana ya miƙawa ƴan matan daketa kallon motocin da ido, lemun da suka saya ya miƙa musu.
    Kana ya kalli dan-dan zo matasa daketa wuce da kafa,
    mutanen daketa maganar Malamin ya kalla tare da cewa.
    "Eh kam gsky duk malaman ƙasar nan babu yashi a lafazi, cikin second ɗaya zai yi maka lafazin da zai gamsar da kai tsawon shekaru Talatin,
    koda yake hakan baya rasa nasaba da tsatson mahaifiyarshi, da ta kasance balarabiya kuma alarabawanma a cikin ƙabilar da tafi dukkan ƙabilun duniya a baiwar lafazi da iya sarrafa harshe".
    Cikin mamaki suka kalleshi,
    Alhajin dake cikin zazzafar motar shin nanne yace.
    "Haba sai haka mana ashe Balarabe ne wani yanki na tsatsonshi Allah yayi mishi rahamomi masu tarin yawa.
    Gashi wannan zai hanamu muje muji Kuɗubar".
    Murmushi mai Appul ɗin yayi tare da kallon gefen baya yadda ya hango dandazon motoci da keke Napep dama masu tafiya da sawu ma.
    Wasu na meda motocinsu gefe sukayi suna fitowa da sallayoyinsu a hannu suna takowa da ƙafa,
    kanshi ya ɗan rausayar ya kalli mutanen dake gaban nashi tare da cewa.
    "Kasan su wayene a cikin motocin nan da kuketa zagin kuwa?".
    Da sauri suka jujjuya kai tare da cewa.
    "A a waye ne?".
    Tsala-tsalan motocin ya zubawa idanu zazzafar farar mota kirar Rolls Royce ɗince ya zubawa ido a hankali ya maida kallonshi garesu tare da cewa.
    "Shine Sheykh J....!



    Uhummmm wasa farin girgi.



    By
    *GARKUWAR FULANI*  less  less
    • 8 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked Ummyter Abdallah's post.
    February 8, 2021
    Ummyter Abdallah → TSEGUMI ZALLA:
    Dan Allah posting nikeso kiyimin amma kiboye sunana plss
    yadda lamarin yake wato ubangiji ya jarabceni shekaruna 30 ynx kanne da kawaye duk sunyi aure amma ni shiru ina jinnu Sun sani gaba nayi magani hr na gode...  more
    Ummyter Abdallah → TSEGUMI ZALLA:
    Dan Allah posting nikeso kiyimin amma kiboye sunana plss
    yadda lamarin yake wato ubangiji ya jarabceni shekaruna 30 ynx kanne da kawaye duk sunyi aure amma ni shiru ina jinnu Sun sani gaba nayi magani hr na gode Allah kusan 10yr ina neman magani amma...  moreDan Allah posting nikeso kiyimin amma kiboye sunana plss
    yadda lamarin yake wato ubangiji ya jarabceni shekaruna 30 ynx kanne da kawaye duk sunyi aure amma ni shiru ina jinnu Sun sani gaba nayi magani hr na gode Allah kusan 10yr ina neman magani amma abin sai dai gdy nayi axumi nayi sallah nayi Addu'a hr xuciya tafara tsinkewa tayi rauni ibadata ta ragu nafara tunani ko wani laifi nayi Allah wlh ibada nake sosai
    Ina kuka ina rokon Allah akan yakawomin karshen wannan jarabawa amma shiru wlh banda muni inada ilmin addini sosai haka Na boko dan inada diploma nayi samari dayawa duk maganar aure amma dga baya sai abu ya lalace matsalar ma ynx sbd yawan
    Maganin danake amfani dasu na hayaki to hayakin...    less
    • 5 people like this
    • Madu AD
      Madu AD Allah Ya kawo miki mafita mafi alheri.
      • February 8, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Ummyter Abdallah Amin
      • February 28, 2021
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD liked Mohammed Sani Hassan 's post.
    January 31, 2021
    Mohammed Sani Hassan
    Wallahi Quran is the most calming thing 😭
    • 7 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked surajo abdullahi's photo.
    January 31, 2021
    • 12 people like this
    • Madu AD
      Aminu Danyaya Allah ya raya
      • January 31, 2021
      • -
      • Report
    • Madu AD
      surajo abdullahi Ameen nagode
      • February 3, 2021
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD liked Rahmatu Lawan's post.
    January 31, 2021
    Rahmatu Lawan shared Rahmatu Lawan's video.
    • 5 people like this
  • Madu AD
    Madu AD liked Bakandamiya's photo.
    January 31, 2021
    • 9 people like this
    • Madu AD
      M.I. Musaddam Masha Allah. Congratulations to them all
      • January 31, 2021
      • -
      • 3 like this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Maryam Umar Congratulations winners\uD83D\uDE02\uD83D\uDE02\uD83D\uDE02\uD83D\uDE02
      • January 31, 2021
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD liked Safiyya Mrs Haruna's post.
    January 31, 2021
    Safiyya Mrs Haruna
    RABI'ATUL ADDAWIYYA.

    By...  moreRABI'ATUL...  more
    Safiyya Mrs Haruna
    RABI'ATUL ADDAWIYYA.

    By...  moreRABI'ATUL ADDAWIYYA.

    By Mrsjmoon.

    *9 ~ 10*

    A sannu tasoma motsa idanunta har ta bud'esu duka tayi mik'a tare da salati ta d'ora da addu'ar tashi daga barci, ta dafe kanta tana son tuno abinda yafaru da ita mai kama da mafarki.

    A zabure ta duro daga bisa gadon tasoma bin d'akin da kallo, jikinta na rawa sai kuma tafashe da kuka ta durgushe a k'asan d'akin tana yarfe hannaye "Wayyo Allah na ni Addawiyya naga takaina, nan kuma ina nakawo kai? Ya Ubangijin sammai da k'assai ka kawomin d'auki bisa wand'an nan abubuwa dasuke faruwa dani, ka nemomin hanyar dazankoma zuwa ga mahaifana badan halina ba."

    "Amin." Taji an amsa mata daf da kunninta.

    Mik'ewa tayi tana kalle-kalle. Alamar tafiya taji yasa tayi tsam tana saurare can ta kuma jin kamar ana magana kusa da ita ta sai ta bud'e kunniwanta sosai tana saurare amma sai taji shiru, a tsorace ta k'arewa d'akin kallo k'aton d'akine wanda yake d'auke da kayan alatu masu mugun kyau da had'uwa, tunda Addawiyya take bata taba ganin wuri mai kyawunsa ba duk kyau da tsarin d'akin mama Ramlat batajin yakai ko kwatan wannan a had'uwa.

     "Oh ni ko inane nan?"

    "Baza'acutar dakeba mai babban suna, kidai hanzarta rama sallolin da'ake binki shi muka fi so da ke."

    A gigice ta ja da baya tana duba ta ina maganar yake fitowa, jitayi anja hannunsa har zuwa bakin toilet ance "Kiyi wanka ki d'auro arolla sai kizo ga abinci can yana jiranki."

    Wannan karan muryan mace taji a maimakon na miji da yayi mata magana afarko.

    Murya ta bud'e ta kwalla ihu "Wayyo Ummi na fad'a gidan aljannu, nashiga uku, rashinjin magana baiyi ba wallahi musanman na iyaye, gashinan nazo inayin nadama mara amfani.

    Wani uban tsaki taji anja mai k'arfi tare da turata bayin, jikinta ya d'auki bari. "Inbaki hanzarta sauke bashin sallar da ake binkiba Allah zan maidaki biri yanzunnan ki koma daji dazama."

     Tanajin haka jiki na bari tasoma cire kayanta ta hau wanka tana gamawa ta d'auro alwalla ta fito kaya tagani agefen gadon tabishi da kallo saiji tayi ance "Oya d'auki kisaka."

    Bamusu ta cire na jikinta ta sanya wannan, ta duba gefen damarta taga sallaya shinfid'e tare da hijab tamatsa ta hau tasoma gabatar da sallolin.

    Tana idarwa ta takure wuri d'aya ta zuba uban tagumi, cike da kewar su Abbi tasan yanzu duk inda suke sunanan cikin tashin hankalin rashinta musanma ma Ummin ta domin tasanta da rud'ewa.

    'Uhmm ko ya Adda Salma zakaji? Ga Aunty Hindu da sauran dangi,Allah gani gareka.'

    Duk cikin zuciyarta take wannan zancen sai tafashe da kuka sadda tayi tunanin k'ilama gidan yankan kai ne ta fad'o, Kukan nata sai ya k'aru tayi-tayi bamai rarrashinta.

    "Oh ya Salam! nidai kam Yaya ya had'ani kula da sangartattan bil'adama."

    Wani tsalle ta daka ta koma gefe tana raba idanu, tanason ganin wake mata magana amma bataga kowa ba sai sautin tsaki dataji ankuma ja tare da buga k'ofar fita daga room d'in da k'arfi ta ja baya tana gwama numfashi.

    K'amshin abinci taji yasa ta kai dubanta inda k'amshin ke fitowa arba tayi da girke-girke masu rai da lafiya ai cikin sarsarfa ta k'arasa wurin tasoma bama cikinta hakkinsa bata kojin tsoro domin jitayi kamar tana d'akin Ummin ta ce.

    Tana gama ci taji wani barci yazo mata tazame awurin ta kwanta, rufe idanunta ke da wuya barci yayi gaba da ita.

    * Washe gari Abbi da mutanen gari suka koma dajin neman Addawiyya, sunsha yawo har sun gaji basu gantaba don haka sai suka hak'ura suka dawo gida, Ard'o yayi ta jajantawa Abbi tare da iyayen yaran dasuka rasa 'ya'yansu kuma yace ya soke dukkan wani yawon gudu Amarya ayankinshi sannan hatta wasan iyon ruwa na kogin Cigogo ya soke kuma dole kowa yasa yaronshi makarantar addini, zaije cikin gari yasamo malamai su had'u da na garinsa arik'a koyar da mutane karatun sanin Allah da hukunce-hukuncensa dan kaucewa sab'a masa.

    A haka aka watse taron kowa yana fad'an albarkacin bakinshi tare da yin na'am da maganar Ard'o domin sun gaji da wannan muguwar al'ada.

    Salma kam sumarta biyu kafin su iso Jangaba. Sosai ta d'imauce dajin labarin b'atar 'yar'uwanga. Koda suka iso kuka tafashe dashi mai cinrai barinma da taga kayan shopping d'inta tare da a kwatin kayan makarantarta ajiye a gefen d'akinsu. Sai ta sake sumewa da k'yar aka samu ta dawo hayyacinta Abbi yasata agaba yayi tayi mata nasiha nata dauki k'addara tazamo mai juriya tareda tawakkali.

    Mushaffa'u shi ne yak'ara yi mata nasiha harta soma ta rage  yawan kuka.

    Kwanar su uku Mama Ramlat tare da Aunty Hindu da Mushaffa'u suka yi sallama dasu suka  koma garin Kwantagora yayin da Salma tak'i binsu fafur tace ita sai taga dawowar 'yar uwanta sannan zata dawo, ba'ason ran Mushaffa'u ba yabi su Mama amma ya k'udurta kwana biyu zaiyi yadawo su wuce.

    Wasa-wasa Addawiyya takai kwanaki goma da b'ace kuma har yanzu ana zuwa nemanta cikin dajin amma ba'ayi sa'ar ganinta ba.

    Salma kuwa ta rame sosai, ta maida bakin itaciyar tumfafiyan nan inda Addawiyya take yawan zuwa wurin zamanta, intaje ta had'akai da guiwa tayi ta kuka tun Ummi nayi mata fad'a har ta zuba mata idanu. Abbi kam baima iya ce mata komi sabida duk in yaganta awurin Addawiyya ce ta fad'o mishi arai.

    Adda'a kam tanasha na Allah yabayyanata intana raye in kuma ta rasu ne Allah yaji kanta da rahama.

    *Zaune take gefen gadon dayazama nata ayanzu.

    Inuwar Muta ne take gani suna ta gilmawa ta gabanta kamar kullum, ta runtse idanunta ta bud'e sai kawai taga wata k'atuwar mage kwance ta turo k'afafunta gaba ta zuba mata idanu, itama idanum ta zuba mata tana k'are mata kallo, tabbas itace take yawan gani duk inta kwanta barci tun sadda tasamu kanta awannan d'akin domin dik tsawon kwanakin bata fita waje ba komi a d'akin gakeyinsa kuma dik abinda take so ganinsa kawai takeyi a d'akin.

    Yauma magen rik'id'a tasoma yi mata kamar yarda take gani cikim amafarki  ta koma  bak'a, kore, yelo, ja sai kuma ta dawo golden zuwa can ta dawo faranta tas kamar yarda take, ita dai Addawiyya k'uri tayi tana kallon ikon Allah sabida yanzu tabarjin tsoron duk abinda ta ji koa ta gani a d'akin.

    Koda ta kuma kallon inda magen take sai tanemeta tarasa, ta mik'e tsaye cike da sanyin jiki ta shige bayi tayo alwalla tayi sallar la'asar sabida taji ana kira.

    A cikin charming garden take ta shawagi cike da nushad'i can nesa ta hango shi yana zaune bisa buzu yana jan tasbaha kansa sunkuye.

    ahankali ta k'arasa wurin ta zauna gefenshi tace "Abbi." D'agowa yayi taja baya bakinta bud'e yasakar mata murmushi yace "Ni uncle Habibullah ne ba Abbi ba. Abbinki gashi can cikin kasuwa yana saida dabbobinshi zaiyi hijira da mahaifarshi zuwa nesa da it."

    Sai ta durk'ushe tana wani irin kuka mai taba zuciya, ya kai hannunshi ya dafa mata kai yana girgizawa alamar rarrashi, sai kuma yakamo hannunta atake wani sanyi ya jiyarci jijiyoyin jikinta tare da bargon ta, tayi wani irun zabura ta farka sai ganinta tayi agadon umminta kuma cikin d'akin ummin.

     K'ara ta saki mai k'arfi tana fad'in "Ummie!."

    Salma wacce take waje tana share tsakar gida ta saki tsintsiyar ta nufi d'akin da gudu sakamakon jin muryan 'yar uwarta da tayi, tanaganin Addawiyya zaune, ta kuma yo waje da gudu tana fad'in "Ta dawo wallahi, Ummi! Abbi!! gata can a saman gadon Ummi."

    A tare su ka tambayeta...    less
    • 14 people like this
    • Madu AD
      Zainab Alhamdulillah Masha Allah
      • January 31, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • Madu AD
    Madu AD liked Rahmatu Lawan's post.
    January 28, 2021
    Rahmatu Lawan shared Rahmatu Lawan's video.
    • 7 people like this
    • Madu AD
      Auwalu Adamu Sabongida Madallah da ƙoƙari.
      • January 28, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Madu AD
      Rahmatu Lawan Yauwa, ni ce da godiya. Da fatan an wuni lafiya Mal. Auwal?
      • January 28, 2021
      • -
      • Report
View More
Loading ...

About

Personal Information

  • Sunan Farko Madu
  • Jinsi Namiji
  • Ranar Haihuwa October 23, 2019
  • Relationship Status Married
  • Takaitaccen Bayani Makaranci, Manazarci kuma mai ƙoƙarin kawo gyara cikin adabin hausa.

Contact Address

  • Sunar Unguwa Dakata [map]
  • Sunan Gari Kano
  • Karamar Hukuma Nassarawa
  • Sunar Jaha Kano
  • Sunar Kasa Nigeria

Contact Information

  • Phone No. 8068987331
  • WhatsApp No. 8068987331
  • Email Address myalmustapha50@gmail.com
  • Facebook Em Al-Mustapha
  • Twitter @emalmustapha
  • Instagram @emalmustapha
  • LinkedIn Muhammad Al-Mustapha
© 2022 Bakandamiya About Terms Privacy Subscription Earn Money Advertise Contact
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram