• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Shafin Farko
  • Makalu
    • Browse Entries
  • Bidiyoyi
    • Browse Videos
  • Sautuka
    • Nemo Sautuka
  • Hotuna
    • Browse Albums
    • Browse Photos
  • Zauruka
    • Browse Groups
  • Tambayoyi
  • Sanarwa
    • Bukukuwa Masu Zuwa
    • Past Events
  • Ra'ayoyi
    • Browse Polls
  • Sana'o'i
    • Browse Listings
  • Updates
  • About
  • Abokai(32)
  • Zauruka(1)

Updates

The post was not added to the feed. Please check your privacy settings.
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello is now following Ibrahim Adam Dan Sarauta.
    • Feb 15
  • Ibrahim Adam Dan Sarauta
    Ibrahim Adam Dan Sarauta is now following Jamila Abubakar Bello.
    • Feb 15
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello is now following Zaharadden Nasir.
    • Feb 15
  • Zaharadden Nasir
    Zaharadden Nasir is now following Jamila Abubakar Bello.
    • Feb 15
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello is now following Nayyara  Modibo .
    • Feb 15
  • Nayyara  Modibo 
    Nayyara  Modibo  is now following Jamila Abubakar Bello.
    • Feb 15
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello commented on Almustapha Adam Muhammad's post.
    Almustapha Adam Muhammad → MARUBUTA:
    *SAKAMAKON MUHAWARA*

    *RANAR DR. AMINU LADAN ABUBAKAR...  more*SAKAMAKON...  more
    Almustapha Adam Muhammad → MARUBUTA:
    *SAKAMAKON MUHAWARA*

    *RANAR DR. AMINU LADAN ABUBAKAR...  more*SAKAMAKON MUHAWARA*

    *RANAR DR. AMINU LADAN ABUBAKAR (28/12/2020)*

    *RUKUNIN BALARABA RAMAT YAKUBU*

    *KARAWA TA 35*


    ZAMAN AMANA WRITERS ASSOCIATION = MAKI 72


    STRONG PEN WRITERS...    
    • #MuhawararBakandamiya2020
    • December 29, 2020
    • 10 person likes this
    • Jamila Abubakar Bello
      Nana Aicha Hamissou Muna taya murna.
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Amrah Auwal Ma shaa Allah! Muna murna
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Rahmatu Lawan Masha Allah tabarakallah
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      maman labyb Wow masha Allah
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Jamila Abubakar Bello Masha Allah
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello liked Almustapha Adam Muhammad's post.
    Almustapha Adam Muhammad → MARUBUTA:
    *SAKAMAKON MUHAWARA*

    *RANAR DR. AMINU LADAN ABUBAKAR...  more*SAKAMAKON...  more
    Almustapha Adam Muhammad → MARUBUTA:
    *SAKAMAKON MUHAWARA*

    *RANAR DR. AMINU LADAN ABUBAKAR...  more*SAKAMAKON MUHAWARA*

    *RANAR DR. AMINU LADAN ABUBAKAR (28/12/2020)*

    *RUKUNIN BALARABA RAMAT YAKUBU*

    *KARAWA TA 35*


    ZAMAN AMANA WRITERS ASSOCIATION = MAKI 72


    STRONG PEN WRITERS...    
    • #MuhawararBakandamiya2020
    • December 29, 2020
    • 10 person likes this
    • Jamila Abubakar Bello
      Nana Aicha Hamissou Muna taya murna.
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Amrah Auwal Ma shaa Allah! Muna murna
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Rahmatu Lawan Masha Allah tabarakallah
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      maman labyb Wow masha Allah
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Jamila Abubakar Bello Masha Allah
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello liked Mukhtar Musa Karami Abu Hisham's post.
    Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
    KAMMALAWA.
    Assalamu...  more
    Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
    KAMMALAWA.
    Assalamu alaikum

    Alhamdulillahi mun godewa Allah da yasa wannan Muhawara ta kammala cikin aminci,za mu yi amfani da wannan dama mu mika sakon bangajiya ga Alkalai da wakilan kungiyoyi da suka fafata a wannan muhawara,tare da sauran dukkanin...  moreKAMMALAWA.
    Assalamu alaikum

    Alhamdulillahi mun godewa Allah da yasa wannan Muhawara ta kammala cikin aminci,za mu yi amfani da wannan dama mu mika sakon bangajiya ga Alkalai da wakilan kungiyoyi da suka fafata a wannan muhawara,tare da sauran dukkanin mahalarta da akayi komai akan idonsu, da ma duk wadanda suka samu halartar wannan Muhawara muna yi musu bangajiya.

    Insha Allahu gobe Alkalai za su zo mana da sakamakon muhawarar da akayi yau 28/12/2020 kafin muhawara ta gaba.

    Sai kuma idan...    less
    • December 29, 2020
    • 11 person likes this
    • Jamila Abubakar Bello
      Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) Amin
      • December 29, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello is now following Nafisa Aliyu.
    • December 29, 2020
  • Nafisa Aliyu
    Nafisa Aliyu is now following Jamila Abubakar Bello.
    • December 29, 2020
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello is now following Yunusa Abdullahi.
    • December 29, 2020
  • Yunusa Abdullahi
    Yunusa Abdullahi is now following Jamila Abubakar Bello.
    • December 29, 2020
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello liked Rahmatu Lawan's post.
    Rahmatu Lawan shared Rahmatu Lawan's blog.
    • December 29, 2020
    • Danladi Haruna, Jamila Abubakar Bello, and maryam A___Ja'aphar like this.
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello liked Sumayyat Ibrahim Gambo 's post.
    Sumayyat Ibrahim Gambo → MARUBUTA:
    Madalla da Strong Pen Writers.
    • December 28, 2020
    • 6 person likes this
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello liked Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma)'s post.
    Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) → MARUBUTA:
    Z.A.W

    Da farkon fari Ubangiji subhanahu wa ta'ala Yana cewa "Ni nafi kowa kishi" kalmar kishi tanada girma a tarihi, babu abinda ke girgiza al'arshi sama da kishin ubangiji ga halittar sa, wannan...  more
    Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) → MARUBUTA:
    Z.A.W

    Da farkon fari Ubangiji subhanahu wa ta'ala Yana cewa "Ni nafi kowa kishi" kalmar kishi tanada girma a tarihi, babu abinda ke girgiza al'arshi sama da kishin ubangiji ga halittar sa, wannan dandanon kishin na halitta shine a jikin kowanne dan...  moreZ.A.W

    Da farkon fari Ubangiji subhanahu wa ta'ala Yana cewa "Ni nafi kowa kishi" kalmar kishi tanada girma a tarihi, babu abinda ke girgiza al'arshi sama da kishin ubangiji ga halittar sa, wannan dandanon kishin na halitta shine a jikin kowanne dan Adam na...    less
    • December 28, 2020
    • 16 person likes this
    • View all 15 comments
    • Jamila Abubakar Bello
      BADARUDEEN YUSHAU
      • December 29, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      BADARUDEEN YUSHAU
      • December 29, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Ameeratouh umar faruq Gsky ne Allah Kara basira
      • December 29, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Ameeratouh umar faruq
      • December 29, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) Amin ngd sosai
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello → MARUBUTA:
    Ayi man afuwa nasamu matsalar network, dan ko yanzun bani ganin komai typing kawai nike ina turowa Allah yasa yana isowa gareku Shugaban mahawara da kuma abokan mahawara, gami da masu saurare ngd
    • December 28, 2020
    • 8 person likes this
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello → MARUBUTA:
    STRONG PEN WRITER'S (MANAZARTA)

    Karshe....  more
    STRONG PEN WRITER'S (MANAZARTA)

    Karshe.



    Ya Shugaban mahawara da Alkalan wasa,mai girma mai duba lokaci, anan zan tsaya ba dan banda abun fada sai dan duba da lokaci yana hararomu da wannan hujojin nawa nike son ya Shugaban mahawara ya duba hujojin da na bada akan tsananin so yana illa zuciya, dan so yana iya ilata zuciya bama iyakar zuciya ba har ma da gangar jiki baki daya.




    Nagode na barku lafiya, bissalam.  
    • December 28, 2020
    • 8 person likes this
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello → MARUBUTA:
    STRONG PEN WRITER'S (MANAZARTA)


    Hujja ta goma....  more
    STRONG PEN WRITER'S (MANAZARTA)


    Hujja ta goma.


    Sannan kuma mutun zai iya ji zai iya bada rayuwarshi ko wani abu mai mahimmanci a gareshi, dan kawai jindadin wannan masoyi nashi, koda kuwa shi hakan zai kawo mashi illa da nakasu a rayuwa bayajin komai idan har yasan ya faranta ma masoyiyarsa, so shike sa dangantakar zuci har za'a iya gani duk abunda masoyan zasuyi iri daya saboda zuciyoyinsu suna tare da juna.  
    • December 28, 2020
    • 8 person likes this
    • Jamila Abubakar Bello
      maman nana Tabbas hakane domin so yafi gaban haka
      • December 29, 2020
      • -
      • Report
  • Jamila Abubakar Bello
    Jamila Abubakar Bello → MARUBUTA:
    STRONG PEN WRITER'S (MANAZARTA)

    Hujja ta tara....  more
    STRONG PEN WRITER'S (MANAZARTA)

    Hujja ta tara.


    Sannan shi so yana ganin laifin masoyo, dan kuwa duk abunda za'a gaya ma mutun masoyinshi yayi to bai yarda, sannan kuma zai dunga jin haushin duk wanda yayi yunkurin gaya mashi abunda wannnan masoyin nashi yayi saboda tsakananin son da yake mashi.  
    • December 28, 2020
    • 8 person likes this
    • Jamila Abubakar Bello
      Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) Ai yar uwa wannan hujjar sau biyu kika kawota nake ga. Kin riga da kin fadeta a baya, har nake ce miki wannan ba masoyin gaskiya bane
      • December 28, 2020
      • -
      • Report
    • Jamila Abubakar Bello
      Jamila Abubakar Bello Banda netwk wlh nidai kawai yi nike dan yanzun ya barni naga comments ma
      • December 28, 2020
      • -
      • Report
View More
Loading ...

About

Personal Information

  • Cikakken Suna Jamila
  • Jinsi ko Nau'i Mace
  • Ranar Haihuwa August 8, 2020
  • Takaitaccen Bayani Ni marubuciyace Ina son mu karu da juna

Contact Address

  • Sunan Gari Kankia
  • Karamar Hukuma Kankia
  • Jaha Katsina
  • Kasa Nigeria

Abokai

  • Bakandamiya GORON JUMMA'A BA A YIN WUTRI BIYU A DARE DAYA Tambaya: Assalamu alaykum, Malam don Allah Malam amma naji wasu sunce wai idan mutum yayi wuturi a lokacin da ya yi sallan tarawi, toh wai idan zai yi nafila a cikin dare zai kara raka'a daya ya cika wuturin da ya yi da sallah tarawi. shine nake neman karin bayani plxx malam. Amsa: Wa alaikum assalam, Annabi S. A. W. yana cewa ba a wutiri biyu a dare daya, Na'am akwai malaman da suka faɗi siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon shafa'i, tun da wutiri daya ake yi a dare. Amma abin da yafi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama ,, wannan zai sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin Annabi S. A. W. yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare wutiri". Allah ne mafi sani. Amsawa: Dr Jamilu Zarewa 07/06/2017
  • Rahmatu Lawan Barka da jumma’a ‘yan uwa. Allah Ya sada mu alkhairan da ke cikinta!
  • Lawan Hello
  • Danladi Haruna *SAKAMAKON MUHAWARA* *RANAR MAGAJI DANBATTA (19/01/2021)* *KARAWA TA 55 FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 77 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI =76 *KARAWA TA 56 KARAMCI WRITERS ASSC.:- MAKI= 81 MARUBUTA KARE HAKKIN AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION:- MAKI= 80 #MuhawararBakandamiya2020
  • Mohammed Sani Hassan Forget OND, HND, BSc, MSc, & PhD, if you lack Islamic Knowledge you're still an illiterate👌
  • Bello Ahmadu Alkammawa Ita Wakar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da Marigayi Alhaji Musa Dankwairo ya yi ba ta tsaya ga Sarkin kawai ba, ta hada har da tsarin sarauta kasar, al'adunta, tarihinta da kuma mutanen dake ciki, wakar har tana sanya Kanawa farinciki ta hanyar sanin tarihin su da matsayin su a duniyar jiya da ta shekaranjiya da kuma a yau. Yaran dake tasowa a yau, za su san tarihin su ta saurara Wakar. Marubuta kuwa suna amfani da wakokin Hausa wajen rubuce rubuce musamman wadanda ke da nasaba da tarihi ko sarauta.
  • Rahma kabir *SO SARTSE* © *Rahma Kabir Mrs MG* *Wattpad😗@rahmakabir *_Page 13._* Bukar ko da yaji labarin haihuwar Kaltume bai zo ba, sai ya kuma dulmiya cikin Maiduguri ya cigaba da rayuwar da ya ɗaukarwa kansa. Tun abin yana damun Mamman harya zo ya yakice shi a ransa ya cigaba da rayuwarsa tamkar bai da wani ɗan uwa a duniya. Kaltume na gama wankar arbain ƙanwar Kaala ta tafi gida, suka cigaba da rayuwar su gwanin sha'awa. Ɓangaren Alh. Zanna, asalinsa ya fito daga yankin ƙauyen Marte, kanuri ne ciki da bai, yana da mata Falmata da yaronsu guda Hafiz wanda yake da shekara huɗu a duniya, Zanna ya kasance manomi yana shuka kayan lanbu, a wani lokaci Allah ya jeho masa iftila'i gonarsa ya ƙone gaba ɗaya bai cire komai ba, tun daga lokacin ya shiga halin talauci sosai, hakan yasa wata rana ya shirya ya bar ƙauyensu ya shigo cikin birnin Maiduguri domin ya samawa kansa wani sana'a. Zuwansa da kwana uku ya samu aiki a gurin wanke motoci, da kyar suka ɗauke shi sai da ya haɗa da roko da magiya kafin suka amince. A washe gari ne Mamman ya kai motarsa gurin dan a wanke masa, aka yi sa'a Zanna shi ne ya wanke motar, Mamman ya kalleta shi cikin kulawa. "Ɗan uwa amma dai yau ne ka fara aiki a nan ko?" "Eh jiya na fara aiki" "Allah sarki, hala kai baƙo ne?" "Eh baƙo ne ni daga yankin Marte" "Amma meya baka sha'awa a wannan aikin? baka gudun sanyi ya kamaka saboda yawan amfani da ruwa" Idon Zanna ya kawo kwalla ya duba Mamman da kyau, kwata-kwata ba zai wuce sa'ansa ba, sai dai kuma daga ganin Mamman yana cikin rufin asirin Allah, saɓanin shi da an ganshi za a hango tsantsar talauci da ya yi masa katutu. "Kayi shuru" Cewar Mamman ya katse masa tunaninsa, Zanna ya nisa ya ce. "To na dai fara da wannan ɗin, kafin in samu wani aikin" "Kana da iyali?" "Eh ina da suka na baro su a kauye, yanzu a masallaci nake kwana kafin na samu matsuguni" "Allah sarki" Mamman ya ce sai ya ciro kuɗi ya miƙa masa. "Gobe in Allah ya kaimu da safe ka hau abin hawa ka ce ya kai ka Mamman Plaza, in ya sauke ka sai ka ce kana so a nuna naka office ɗin Mamman, za a kawo ka gurina sai mu yi magana" Cike da murna Zanna ya amsa kuɗin yana masa Nagode da Addu'a. Mamman ya yi murmushi ya shiga mota ya wuce gida. Washe gari kamar yadda suka yi magana haka Zanna ya tafi wurin Mamman, ya samu kyakkyawar tarba a gunsa, dan kafin su fara magana da Mamman, sai da ya sanya aka kawo masa abin karin kumallo ya ci ya ƙoshi kana Mamman ya yi masa bayani. "Sunana Mamman Bakura, wannan wurin mallakina ne, in ba damuwa zan ɗauke ka aiki a matsayin driver in ka iya tuƙi, sannan zaka riƙa zama a nan ofice ɗina kana taya ni wasu ayyuka da kuma kula da customers. Sannan kuma zan baka masauki a gidana, nan da mako guda ka je garinku ka ɗauka iyalinka" Nan take Zanna ya fashe da kukan murna ya rasa dame zai godewa Mamman, sai da ya yi mai isarsa kana ya sassauta kukansa ya shiga jero masa Addu'a da godiya. Mamman ya nuna masa babu komai, haka nan yaji ya taimaka masa saboda Allah, shi dai burinsa ya riƙe masa amana. A wannan rana haka suka yini a nan plaza, zuwa yamma Mamman ya ɗauki Zanna ya wuce da shi gurin wanke mota ya ɗauki kayansa ya yiwa masu gurin sallama, suka wuce gidan Mamman ya ba shi masauki a BQ. Wannan shi ne farkon haɗuwar Mamman da Zanna, a hankali suka shaƙu sosai, bayan mako guda Zanna yaje Marte ya ɗauko iylinsa, Falmata ba ƙaramin Murna ta yi ba suka yi sallama da dangi suka taho. Falmata ta shaƙu Kaltume kullun tana ɓangarenta tana taya ta aiki da renon Beena, cikin watanni shida sun shaƙu sosai kamar ƴan uwa. A wannan lokacin Zanna yasan wasu sirrika na Mamman saboda baya ɓoye masa komai dan ya ɗauke shi tamkar ɗan uwansa na jini, hatta labarin Bukar ya sani wanda a lokacin zuwansa biyu kuma duk suna haɗuwa, in ya zo bai wuce ya karɓi kuɗi wurin Mamman ya ƙara gaba, duk kansu sai dai su bi shi da addu'an shiriya. Mamman shi ne ya sanya Hafiz a makarantar boko da islamiya, yana jin yaron kamar ɗan cikinsa saboda tsantsar amanar da Zanna ya riƙe masa, yana jinsu tamkar ahali guda suka fito. Lokacin aikin hajji ta ya zo, haka Mamman ya biyawa kansa da Kaltume, a wurin Zanna ya bar duk kadarorinsa ya ba shi yaja ragamar kasuwancinsa har ya dawo saboda ya yaba da riƙon amanarsa, sannan Kaltume ta barwa Falmata riƙon Mubeena, lokacin tafiya ya yi, gaba ɗaya suka shiga mota suka tafi filin jirgi, haka suka yi ban kwana suna kuka kamar karsu rabu, bayan sun shiga jirgi ne su Zanna suka dawo gida. Tunda Bukar ya ji labarin tafiyar Yayansa Mamman Makka, sai ya shiga zuwa gidansa akai-akai, yana yiwa su Zanna iskanci kala-kala kuma sai ya ce dole sai ya ba shi kuɗi, haka dai Zanna yake haƙuri da shi kamar yadda yaga Mamman yana yi, sai ya ɗauki kuɗin ya ba shi dan a zauna lafiya, har Allah ya dawo dasu Mamman. Su Kaltume sun yi aiki hajji lafiya sun dawo gida cikin aminci, suka raba tsaraba ga mutane, kusan yawan tsarabansu daga na Mubeena sai na Hafiz, Kaltume kuwa duk tsarabarta na Mubeena ce, ta siya mata ɗan kunne na zinari ya kai kala uku, banda kayan sawa wanda har ta soma tafiya duk zata saka su. Danginsu duk suka zo yi musu barka da zuwa suka amsa nasu tsarabar suka tafi. Mamman ya ji shuru-shuru bai ga Bukar ba, sai hankalinsa ya tashi duk da yana da labarin zuwansa wurin Zanna lokacin basa nan, hakan yasa ya shiga cigiyarsa amma shuru ba labari, ƙarshe dole ya hukura ya cigaba da hidimominsa. Bayan dawowarsu Makka da wata uku ne, wata rana ƴan sanda suka zo gidan da safe suka yi sallama da Mamman, ko da ya fito suka gaisa, ɗaya daga cikin ƴan sandan ya shaida masa labarin cewar "An kama Bukar cikin ƴan fashi sun je gidan wani Alhaji sun kwashe masa kuɗi, sauƙin lamarin basu yi kisa ba, har an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar, to ana ɗan bibiyar lamarin nasu a kotu, shi ne ya bada labarinka ya ce mu zo mu gaya maka" Idon Mamman ya yi ja saboda tashin hankali. "Yanzu ni meye zan yi masa? tunda rayuwar daya zaɓarwa kansa kenan ni babu ruwana, dan haka zaku iya tafiya" "Haba Alhaji ka yi haƙuri mana, hannunka bai ruɓewa ka yar" Cewar ɗaya daga cikin ƴan sanda. "To me zan yi masa?" Cewar Mamman cike da takaici. "Taimakawa za ka yi, domin Allah da Annabi ya ke roƙon mu akan mu zo gunka ka ceci rayuwarsa, dan ya ce ya tuba ba zai sake ba. A yanzu dai an yanke belinsa miliyan uku kafin a fidda shi" "Tafdi jam, wallahi ba zan yi asarar kuɗina ba, ku ce masa zan taya shi da addu'a har Allah ya fito da shi" Daga haka bai kuma magana ba ya koma cikin gida cike da damuwa sosai. Haka ya labartawa su Zanna lamarin, Zanna ya sanya baki akan ya yi haƙuri ya bada kuɗin ya fidda shi, ƙila sanadin shiryuwansa ne ya zo. Mamman yaƙi sauraren maganar Zanna, a cewarsa in yaji wuya zai natsu ya gyara rayuwarsa, amma ba zai yi asarar kuɗinsa ba. ******* Kwanci tashi Mubeena ta shekara guda a duniya, ta yi wayo sosai tafiyarta ta yi kwari, ta yi mugun sabo da Falmata tamkar ita ce ta haifeta, saboda a lokacin Kaltume ta ƙara ɗaukar wani cikin hakan yasa ta yaye Mubeena, sai renonta ya zama yana gun Falmata. Wata rana Mamman ya shirya musu tafiya dan kai ziyara ƙauyensu, Kaltume ce a baya ita da Mubeena sai Mamman a gaba gefen Zanna yana tuƙasu. Haka suka je ƙauyensu suka sada zumunci, sai da suka yi tsawon kwana biyu kana suka kamo harya dawowa. Sun kusa shigowa gari mota ta kwacewa Zanna ya aukawa wata babban mota ta wuntsilasu gefen hanya, kafin zuwan Mutane Zanna ya fito da kyar yana jan jiki, kukan Mubeena ce yake ratsa dodon kunansa, cikin tashin hankali ya yi azama ya buɗe ƙofar baya, da kyar ya ciro ta ya aje ta a ƙasa nesa da motar, ya dawo ya jawo Alh. Mamman wanda jini ya wanke masa fuska yana fidda nishi da kya ya aje shi gefe, ya koma wurin Kaltume ya jawota ita ma ya ajeta gefen Mamman, a hankali Kaltume ta motsa hannunta ta kama na mijinta da ƙarfi, sai ta shiga yin nishi kamar mai naƙuda, jini ya fara fita ta kasanta nan take ya malale ƙasan wurin. Zanna ya matso gunta yana mata sannu, Kaltume tana son yin magana amma ta kasa, sai kawai ta nuna masa Mubeena da hannu, da gudu yaje ya ɗauketa ya kawota kusa da ita, sai ta kama hannun Mubeena. "Amana..." Kawai ta iya furtawa sai muryanta ya sarƙe hawaye masu ɗumi suna bin gefen fuskarta, Zanna ya fashe da kuka ya fara karanto mata kalmar Shahada, Kaltume ta soma amsawa a hankali, a haka motan road safety ta zo gurin suka kwashesu suka sanya a mota, Zanna yana rungume da Mubeena suka shiga motar, ya zauna gefen Mamman da bai san inda kansa yake ba, Kaltume kuwa tana ta jero kalmar Shahada, kafin su ƙarasa asibiti Allah ya yi mata cikawa. Wani irin kuka Zanna yake yi yana ambaton sunan Allah, hankali sa ya yi matuƙar tashi. A haka suka isa Babban asibitin Maiduguri, su duka aka shiga dasu emergency room, dai-dai lokacin ana kiran sallar Azahar. Likitoci sunata ƙoƙarin ceto ransu. Daya ɗaga cikin likitocin ne ya fito yana mai share gumi ya kamo hannun Zanna ya ce "Ka yi haƙuri, Matar tun a hanya ta rasu, shi kuka mai gidan mun samu nasarar dawowar numfashinsa. Allah ya jikanta da Rahma, zaka iya shiga ciki ga gansu" Yana faɗar haka ya wuce, Zanna ya ɗauki Mubeena da tun ɗazu take barci ya sabata a kafaɗa, ya shiga ɗakin a tsorace yana kuka ya hango Kaltume an rufe mata fuska, ga Mamman kwance magashiyyan yana fidda numfashi da kyar, ya isa bakin gadon Kaltume ya shiga jero mata addu'a yana tofa mata, ya ɗauki kimanin minti talatin a gunta. Daga bisani ya isa wurin gadon Mamman, a lokacin ya samu ya buɗe ido har yana ƙirƙiro wa Zanna murmushi, ya buɗe murya a wahalce ya soma magana. "Zanna kaga yadda lamarin Ubangiji ya kasance damu, ka yi haƙuri da nauyin da zai hau kanka. Ni Muhammad na danƙa maka amanar ƴata Mubeena ka zame mata ubu, uwa da dangi, don Allah karka barta ta yi kukan maraici, nasan kai mutum ne mai amana ina so ka ƙara akan na da dana sanka, kar ka yarda riƙon Mubeena ya koma wurin danginmu, kar ka yarda riƙon Mubeena ya koma hannun Bukar ko yasan in da kuke, ka nisanta kanku ga danginmu har sai Mubeena ta mallaki hankalinta, sai ka sanar da ita labarinmu ka kaita wurin ahalinmu. Don Allah ka bar in da muke ka gina sabuwar rayuwa ku kaɗai ba tare da sanin kowa ba, saboda ina son Mubeena ta yi rayuwar farin ciki da soyayyar iyaye, ka saida duk kadarorina ka gida sabuwar ruyuwa, ina so ka kasa dukiyata kashi huɗu ka ɗauki kashi ɗaya na baka halak malak, kashi uku kuma ka juyawa Mubeena har sai ta mallaki hankalinta sai ka danƙa mata dukiyarta. Nagode sosai Allah ya baka ikon riƙe amanarta" Sai ya juya kansa yana kallon Kaltume. "Allah ya jiƙanki Matata ya saka miki da gidan Aljanna Firdausi" Nan take muryarsa ya sarƙe, Zanna ya shiga karanta masa Kalmar shahada har Allah ya karɓi abinsa. A wannan lokacin kuka ya ɗaukewa Zanna, ya fita yaje ya dankawa wata nurse Mubeena ya kira likita ya zo ya duba Mamman, shima ya tabbatar masa daya ciki. Zanna ya fita ya tari abin hawa ya isa babban masallacin unguwarsu ya shaidawa limaminsu abin da ya faru, nan take aka tura mota zuwa asibiti aka ɗauki gawarsu Mamman zuwa gida. Falmata saboda firgici har suma ta yi, koda ta farfaɗo ta amsa Mubeena ta ƙanƙame ta a jikinta tana kuka kamar mahaukaciya, Hafiz duk da bayi da wayo yasan cewar babban abune ya faru a gidan nasu, kuka yake har muryansa yana dishewa. Kafin a ce kabo unguwar ya cika da al'umman annabi har cikin gidan, kafin sallar magrib aka yi musi sutura aka sadasu da gidansu na gaskiya. _Kullu nafsin za ikatul maut, Allah ka jikan duk wa'inda suka rigamu zuwa gidan gaskiya, kasa mu cika da Imani, Ameen._ Zuwa safiya danginsu duk sun hallara, sun ci kuka sosai. Har zuwa ranar bakwai Zanna bai fidda kwalla ba zuciyarsa ta bushe sai yawan ajiyar zuciya da yake yi, shi ne yake ta amsar gaisuwa, anyi addu'an bakwai an watse lafiya, wasu daga cikin danginsu suka zauna har sai anyi addu'an arba'in. A wannan zaman ne wasu daga cikin ƴan uwansu suka nuna maitarsu a fili cewar suna son su riƴe Mubeena da dukiyarta, har hakan ya kawo rikici tsakanin dangin Mamman dana Kaltume, Zanna shi dai na shi ido bai kuma yi masu musun ba zai bamu ba, face ma haƙuri daya basu da lallama akan su jira shi ya tattara dukiyarta gaba ɗaya ya basu, da wannan shawarar suka amince suka zauna lafiya. Bukar ya yi kuka kamar ransa zai fita lokacin daya ji labarin mutuwar ɗan uwansa da matarsa, duk yadda yaso ya fito an hana shi ƙarshe dole ya haƙura. Tun daga wannan lokacin ne ya watsar da duk shiriritarsa ya ƙuduri aniyar zai zama mutumin kirki in ya fito, zai yi aure ya riƙe Mubeena amana da dukiyarta. Abin da danginsu Mamman basu sani ba, Zanna ya tattara duniyar Mubeena duka ya buɗe sabon account ya kaimu banki, ya saida Mamman plazan da gidansa da suke ciki da motar da yake hawa, duk a haɗa kuɗin a asusun banki. Banki suka yiwa Zanna lissafin kuɗin gaba ɗaya, suka raba kashi huɗu, ya ɗauki kashi ɗaya na shi ya bar kashi uku a banki. Yaje can wata sabuwar unguwa kamar za a fita garin, ya siya gida a nan da kuɗinsa ɗaki ciki ɗai-ɗai har uku, sai bayi da kicin sai filin tsakar gida, ya yi komai cikin sirri, ya siya musu kayan ɗaki masu sauƙin kuɗi ya zuba, hatta abinci ya siya ya aje, dawowa kawai ya rage musu. Bayan anyi sadakar arbain, har lokacin danginsu Kaltume da Mamman sunƙi tafiya, suna jiran Zanna ya haɗo kuɗin gadon Mubeena. Cikin ikon Allah kuwa Mubeena bata yarda da kowa a cikinsu sai Falmata, hakan ya bawa Zanna damar ɗaukar yaran cikin dare ya fita dasu Falmata na biye da shi a baya, ko kayan su basu ɗauka ba sai na jikinsu, sai kuma akwatin da ya zuba gwala-gwalan Kaltume da hotunansu da kuma takardun banki da duk abin da ya shafi gadon Mubeena, shi kawai suka ɗauka suka bar gidan cikin dare misalin ƙarfe tara. Sai da suka yi safiya kusan na awa guda suka bar unguwar da kewayenta gaba ɗaya, kana suka tari mai taxi suka hau ya wuce dasu sabuwar unguwa, sai da suka yi tafiya na kusan hawa ɗaya da minti biyar kafin suka isa sabuwar unguwar, mai taxi ya sauke su bakin hanya suka ƙarasa da ƙafa, sai ƙarfe sha ɗaya da mintuna suka kai gidan, ko da suka isa kwanciya suka yi domin sun kwaso gajiya. Can cikin gari kuwa, ko da dangin suka wayi gari basu ga su Falmata ba sai basu nuna damuwarsu ba ganin akwai kayansu a gidan, hankalinsu bai tashi ba sai da aka kwana aka yini, basu ba labarinsu, zuwa yamma wanda ya siya gidan ya basu takardar notice, hankalinsu ya tashi suka bazama niman Zanna. Kwanan su biyu suna gantali daga ƙarshe suka gane cewar ya saida komai ya gudu ne, gaskiya yasha zagi a gunsu sosai wasu harda kukan bakin ciki suka yi suna tsinewa Zanna da Falmata. Haka suka ƙara kwanaki ganin ba sarki sai Allah, daga ƙarshe sai suka rabe kayan gidan harda nasu Falmata, kowa ya ja nasa suka bar gidan suka koma ƙauyensu. Haka lamarin ya ishe Bukar kamar labarin Hikaya, ya shiga tashin hankali sosai yana tunanin ko Zanna ya yi haka ne domin ya danne duniyar Mubeena. Hakan ne yasa ya ɗauki alwashin in ya fito sai ya nimo shi duk inda ya shiga, kuma sai ya raba shi da dukiyar ya dawo hannunsa ya kwace Mubeena. Ta mangaren Zanna sun kafa sabuwar rayuwa mai cike da aminci, Falmata ta riƙe Mubeena tamkar ita ce tahaifeta. Zanna ya buɗe shago a jikin gidansa yana saida kayan provision, hankalinsu ya kwanta Mubeena ta manta da wasu Iyayenta domin a yanzu ba tada Iyayen da suka wuce su Zanna. Haka rayuwa ya yi ta tafiya har tsawon shekaru uku, komai ya lafa an manta da rayuwarsu Mubeena, Zanna hatta garinsu yaƙi zuwa, dan yana ganin kamar ko danginsu Mamman zasu je can. A wannan lokacin Falmata ta ƙara haihuwar Hafsat harta she kara ɗaya a duniya, sun sanya Mubeena a makaranta mai tsada zuna zuwa da Hafiz, Falmata ke ɗawainiyar kaisu da ɗauko su, har zuwa lokacin Zanna bai taɓa dukiyar Mubeena ba. Ana haka ne ya haɗu da wani mutum a unguwarsu yana fita ƙasashen afrika yana saro atamfofi a can, da haka Zanna ya soma binsa suka ƙulla abota mai tsafta, Alhaji Umaru ya koyar da Zanna yadda ake kasuwanci, ganin haka yasa Zanna ya sanar da shi cewar yana da kadarorinsa na gado a ƙauye, yana so ya saida ya buɗe katon guri don bunƙasa kasuwancinsa, Zanna ya ɓoye gaskiyar labarin dan har yanzu bai yarda da wani ba da har zai gaya masa gaskiyar dukiyar na Mubeena ce. Alh. Umaru ya ba shi shawara da ya samu fili ya gida shaguna ya zuba haya, sauran sai ya sanya kayansa a ciki yana bada sari, da wannan sharawan Zanna ya ɗibo kaso biyu a dukiyar Mubeena ya siya fili a bakin hanya ya gina shaguna bakwai, ya riƙe biyu yaba zuba atamfofi da kayan pan senigal yana saidasu akan sari, duk bisa jagorancin Alh. Umaru. *******   ***    ******* *Bayan shekara biyu* Bukar ya kammala zaman gidan yari na shekara biyar cif, ko da ya fito ƙauyensu ya nufa ya samu labarin duk abin da ya faru, kwanan sa biyu ya dawo cikin birni cike sa baƙin ciki, a wannan lokacin ya ɗau aniyar zama mutumin kirki dan cika ƙudurin Mamman, sai kawai ya yake shawarar ya tafi garin Kano. Zuwansa da wata guda Allah ya haɗa shi da wani Alh. Aminu, ya ɗauke shi aiki a kamfaninsa na haɗa yoghurt, cikin ƙanƙanin lokaci Bukar ya samu karɓuwa sosai a gurin, ya tsaya tayin dana ya koya aiki mai kyau ana biyansa duk wata yana tara kuɗinsa. *****       ****** *Bayan shekara biyu* Bukar ya kware sosai ya iya aiki kuma kuɗinsa sun taru da yawa, a nan ya sanar da Alh. Umaru zai koma garinsu ya kafa nashi gurin, Alhajin bai ji daɗi ba amma ba zai tauye shi ba tunda ya koya aikin, burinsa duk yaransa da suka yi aiki ƙarƙashinsa su kafa nasu gurin, hakan yasa ya ɗauki kuɗi masu tsoka ya ba Bukar kyauta, ya yi murna sosai da godiya ya kama kansa bayan ya yi sallama da duk mutanen kamfanin. Bukar kafin ya bar Kano sai da ya siya duk injinan da suke amfani dasu wajen haɗa yoghurt ɗin, da duk kayan aiki ya barsu a nan, kafin ya tattara ya koma Maiduguri ya samu wani ƙaramin gida ya kama hayansa, sai ya koma Kano ya kwaso kayansa da ya siya ya zo ya kafa su a gidan, ya samu yara matasa ya karantar dasu komai ya fara yin yoghurt na shi na kansa, a hankali ya amsu a wurin mutane, da kaɗan-kaɗan ya bunƙasa sosai. ******   ***   ******* *Bayan shekara uku* Zanna ya zama babban Alhaji duk sun sauya kamar ba su taɓa shan wata wahala ba a duniya, a wannan lokacin ne Zanna ya buɗe katafaren kamfani wanda ya sanya masa M&B cosmetics & perfumes Nigeria limited. Ma'anar M&B shi ne Mamman Bakura, hakanan yaji sha'awar sanya sunan Mahaifin Mubeena. Wannan kamfanin ya karɓu sosai domin har daga garuruwa suna zuwa suna sarar kaya, suna yin duk kayan kwalliyar kama daga power kala-kala, jan baki, gazal, mascara, da sauran kayan kwalliya, duk kuma suna ɗauke da tambarin M&B jikin ko wani kaya. Ɓangaren turaruka ma haka, kama daga na jiki, kaya, hatta su humra da turaren tsinke dana wuta duk suna saida nasu na kamfanin, sai kuma wasu turaruka da suke kawosu daga ƙasashen waje, sai dai sunfi kawo irin na ƙasar Makka da ƙasar Sudan. Duk wani turare da kake nima in dai ka zo kamfanin M&B zaka samu. A wannan lokacin Baba Zanna ya sauya musu gida zuwa new GRA, ya siya motar hawa da kuma motar su Mami wanda za a riƙa kai su Mubeena makaranta. *********     ********* *Bayan shekaru da yawa* Ɓangaren Bukar ya gina kamfaninsa na yoghurt mai suna AB yoghurt. Yana bayar da sari ga ƴan kasuwa birni dana ƙauye. Duk wannan buɗi daya samu yana nan yana bincike akan inda Zanna na ɓoye, kuma har zuwa lokacin bai samu bayanin komai a kansu ba. Har malaman tsubbu yasa suka yi masa bincike, sun ba shi tabbacin zasu haɗu amma lokaci bai yi ba. A wannan lokacin Bukar ya yi aure harya haifi yara biyu, Nabeela da Anwar har sun tasa suna primary school. Sai kuma halin da ya ɗauka na niman mata, tun Matar bata sani ba har ya fito fili, haka dai ta cigaba da zama da shi tana haƙuri. ****** Mubeena da Fanna sun kammala secondary har zasu shiga university, kawancensu ya samo asali tun primary da aka sanya Fanna suka shaƙu sosai, duk inda Beena take Fanna tana wurin har zuwa girmansu suna tare, wanda suka yi alwashin yin karatu tare komai ɗaya. Sun samu admission a nan university of Maiduguri, duk iyayensu suka yi musu register suka fara zuwa, kwas ɗinsu ɗaya Mass com. Mubeena ta tashi cikin gata wanda bata taɓa sanin cewa basu Baba bane suka haifeta ba, su kuma su Baba sun cigaba da riƙe maganar har zuwa lokacin da zai aurar da Mubeena kafin zai faɗa mata gaskiyar asalinta.             ***** Su Beena suna 200level, wata rana ruwa ya tare Fanna a makaranta lokacin Yaya Hafiz ya ɗauki Beena sun wuce gida, da ruwan ya ɗauke Fanna ta fito ya fara takawa a hanya kafin ta samu a abin hawa, Alh. Bukar ya biyo ta hanyar Allah ya haɗa shi da Fanna yana ganinta ransa ya biya, sai ya tsaya dan ya latsa yaji ko ƴar hannu ce, suka gaisa ya nima zai rage mata hanya ba musu ta amince dama ta soma gajiya da tafiyar sai ta shiga motar, Alh. Bukar ya shiga janta da hira, cikin dabara ya shigar da bayanin yana sonta, Fanna ba jan aji ta amince a cewarta ta samu saurayin siyan kati, dan ita dama mace ce mai san ƙarya da harkan wayewa, sai dai duk samarin da take dasu ba wasu basu kuɗi bane shiyasa take haƙuri dasu a haka. Tun daga wannan lokacin Alhaji ya shiga kashe mata kuɗi ya siya mata babbar waya, nan da nan Fanna ta yi clean ta faso gari, lokacin da take bawa Mubeena labarin Alh. Bukar da irin hidimar da yake mata, Mubeena faɗa ta yi mata da nasiha akan tabi duniya a hankali, tun daga lokacin Fanna ta daina gaya nata komai, ko zata bata labari sama-sama take faɗa mata. A haka ne Alhaji Bukar ya buɗe wa Fanna ido, shi ne mutum na farko daya fara keta mata haddi, a ranar Fanna tasha kuka, Alh. Bukar ya ce mata ba wani abu bane ya nuna mata tabbacin zai aureta, hakan yasa ta saki jiki suka cigaba da rayuwar shashanci yana kashe mata kuɗi. Wata rana ya zo ɗaukar Fanna a makaranta lokacin ita kuma Beena ba a zo ɗaukarta ba, a nan Fanna ta jata zuwa wurin Alh. Bukar dan su gaisa, yana ganin Mubeena gabansa ya faɗi domin ya hango tsantsar kamarta da ɗan uwansa Mamman sai dai ita tanada haske, bakinsa har yana rawa wurin tambayar Fanna sunanta, ba wani ja ta gaya masa sunanta Mubeena Zanna. Gaban Bukar ya faɗi ras, ya lashe lebensa na ƙasa ya saki wani shu'umin murmushi, abin da ya daɗe yana nima shekara da shekara yau ya yi katari da shi. 'Wato Zanna ka riƙe Mubeena da dukiyarta tamkar kaine ka haifeta ko? baka sanar da ita labarin iyayenta ba, ka sanya tana amfani da sunanka' Duk zancen zuci ya yi, a fili kuma ya kalli Mubeena suka gaisa, a haka ne Hafiz ya zo ɗaukarta Mubeena ta yi musu sallama ta wuce. Fanna ta shiga motar suka wuce, a hanya ne Bukar ya yi ta tambayar Fanna labarin Mubeena cikin dabara, ita kuma ta ba shi labarin duk abin da ta sani nata. Tun daga wannan lokacin ya fara binciken Zanna da duk abin da yake ciki ba tare da ya sani ba, a wannan lokacin baya buƙatar Mubeena ta san labarinta ya fi ƙaunar dukiyarta fiye da ita, shiyasa ya ɗauki alwashin ya kasheta daga baya sai ya tunkari Zanna, ya san zuwa lokacin dole ya danƙa masa dukiyar Mubeena tunda ta riga ta mutu, shi sai ya ci gadon. Da wannan gurɓatacciyar shawarar ya soma haɗa plan yadda zai kashe Mubeena, ya ɓoye komai a ransa, hatta Fanna bai nuna mata ya san Mubeena ba suka cigaba da harkansu. Ɓangaren Alh. Zanna kuwa, hankalinsa kwance yake gudanar da rayuwarsa, ya ɗauki son duniya ya aza akan Mubeena, ƙiri-ƙiri yake nuna banbaci a kan yaransa kuma Mubeena yarinya ce mai biyayya, domin sunyi wa yaran tarbiyya mai kyau, zuwa girmansu ne Mami ta saki komai a cewarta sun mallaki hankalinsu ba zasu lalace ba. Yadda Baba yake nuna mugun so ga Beena shi ne ya hura wutar ƙiyayyar Mubeena a zuciyar Hafsat, har wata ran Mami take shigar mata tana jin zafin bambancin da Baba ke nunawa, sai dai takan yi ƙoƙarin danne zuciyarta gudun kar ranta ya ɓaci a gurinsa, dan duk lokacin data kawo masa ƙorafin haka, kaca-kaca yake mata ya tunatar da ita asalinsu da kum matsayinsu, sannan arzikin Mubeena suke ci. _Wannan shi ne asalin tushen labarin, wanda son da Mubeena take yiwa Mansoor ya yi sanadin tono asirin da ke ɓoye_ _Cigaban Labarin..._ *Rahma ce*
  • Hafsat Rano
  • Balkisu Musa Galadanchi
  • Safiyya Huguma
  • Kamala Minna ME YA SA...? Na kasa fahimtar cukumurɗar nan, lamarin yana raunata min lissafi sosai. Akwai mazaje da yawa da suke yiwa mace kallo wata maras tunani da lissafi a cikin rayuwarta. Bata da iko ko alfarma a fannin a yi shawara da ita,ko a zauna da ita cikin wani zance ko lamari da ya jirkice ake neman mafita. Sai kaji ana cewa bata da lissafi ko shawarar da za ta bayar har anyi amfani dashi, domin bata san kanta ba, shiririta kawai zata yiwa mutane. Ba abin takaici da ciwon rai, sai Mazaje da suke yiwa matansu kalar fahimtar nan, sai ka ji namiji na cewa ba zai nemi shawara da matarsa ba, mace ce ita kanta bata san kanta ba shiririta za ta yi masa. Na kasa fahimtar tunanin mazajen nan. Shin mace ita ba mutum bane ko kuwa bata da zuciya da kwanyar da za ta yi tunani da ita ce?. Shin namiji ne kawai mai hangen nesa da sanin ya kamata ko ya ya? Na kasa fahimtar gangan ɗin nan. Lissafin mace da namiji na sani ba ɗaya bane na amshi Farillar nan. Amma mai yasa ba za ake yi musu adalci ba wajan ba su dama a cikin neman mafita? wannan tauye haƙƙi ne da mai da mace ta ji a ranta ita ba wata bace hakan kuma damuwa ce da ke sanya ciwuka masu girma a zuciyar mace. Don Allah ake adalci Kamar yadda ake ganin mace bata cancanta da lissafin neman mafita ba, to haka shima namiji. Akwai mazajen da tunaninsu in aka sanya shi a sikile wallahi Allah ko an amshe shi a matsayi mafita faɗuwa za ayi warwas macen da aka raina sai ka ga ita nata da aka mai kallon hadarin kaji ya yi amfani. Kalmar Wasu Mazan da wasu matan ya kamata ace ana ado dashi wajan yanke hukunci ba wai ayi jam'u wanjan faɗin MATA ba hakan rashin adalci ne. Matarka fa sirrin kace duk yadda za kayi saɓa-ta juya-ta sunanta ba zai taɓa canzawa a sirrinka ba. Ya kamata ake adalci. An san ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, don haka ake saka kalmar 'Wasu' a duk abinda za ayi in har ana son adalci. Zama kayi nazari da tunanin wani duhu da ka shiga tare da iyalinka ba karamar shakuwa da girmamawa da sanya zukatan iyalan naka alfahari hakan ke yi ba, don Allah ake duba ana saran bakin gatari. Ɗiya mace daraja ce da ita, girma ne da ita, in ka kira mace duk mara lissafi kana da uwa fa ita a wani mataki zaka ajje ta?🤔 Allah ya kyauta. KamalaMinna.
  • Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) *AHALINA* *Na* *Aishan Umma* *???????? ZAMAN AMANA WRITER'S (Z.A.W)* https://www.facebook.com/ZAMAN-AMANA-Writers-FANS-311893699485963/ 2019 1 Cike da zumud'in yau zasu zauna da mahaifansu ababen alfaharinsu suka tashi daga bacci, sakamakon yau babu makaranta. A gaggauce Fahat yayi wanka yasa Aida ma taje tayi sannan yayiwa sauran k'annensa guda biyu, duk suka shirya sannan suka fito. Fahat ne yayi saurin shiga kitchen dan anan ya jiyo motsin Amminsu, har k'asa ya tsuguna ya gaisheta, suma sauran k'annensa da suka shigo kitchen d'in yadda suka ga d'an uwansu yayi hakan sukayi, ta amsa cike da fara'a had'i da kulawa, duk seda ta shafa kawunansu tana mai karanta musu addu'ar da Annabi Sallalahu alaihi wa sallam yake karantawa Hassan da Hussaini (u'izukuma bi kalimatillahi tammat min kulli shaid'anin wa hamma, wa min kullu ainin lamma). Tana matuk'ar son yaranta, sosai take k'aunarsu, har wani lokacin takanyi tunanin Kodai mutuwa zatayi ta barsu ne?. Fahat ne ya katse mata tunaninta ta hanyar cewa "Ammi bari naje na gaida Abbu na dawo na tayaki da wani abin mana se mufi yin sauri". "A'a d'an albarka jeka ku gaisa d'in daga nan kuje ku gyara d'akunanku tukunna ni na k'arasa wannan" cewar Ammi Kafewa yayi yace "ai tunda babu school yau to zan tayaki aiki insha Allah, Habibtyna ina k'aunarki, bana son naga kina gajiya da yawa. Mene amfanin Allah ya baki ni amma na gagara taimaka miki, gaskiya inde kina so na samu lada ki bari na tayaki kinji Ammi na?" Tayi murmushi had'e da shafa kanshi tace "na amince to yaron kirki, kaida kake namiji kaine me son shiga kitchen ita kam Aida ko a jikinta, yanzu ko nace tazo muyinma se raina ya kusan b'aci, ban san inda ta koyi k'uiya ba. Allah ya raya mana ku, ya tsareku ya kare ku, Allah yayi muku albarka ya kareku dukkan sharri, ina alfahari da samunku masoya na sanyin idaniyata." Daga haka ya je ya gaida mahaifinsu, se gashi ya dawo tare da Aida suka ci gaba da aikinsu suna hirarsu ta tsakanin uwa da yaranta. A haka ta dad'a samu tayi ta yi musu nasiha akan halin rayuwa. Su ko su Sa'eed da Alim suna can wajen mahaifinnasu suna tayashi hira sakamakon weekend baya zuwa ko ina. A haka suma suka kammala aikinsu suka fito da komai suka jere a dinning area, kowa kuma ya hallara akayi bismillah aka fara cin abinci cikin ladabi. Haka rayuwar gidan take tafiya cikin aminci gashi dai ba wani me kud'i bane me gidan sedai rufin asirin Allah da kuma wadatar zuci, amma zuciyar mutanen gidan tana cike da k'aunar juna da kuma tausayawa. Iyayen suna k'ok'arin ganin sun bawa yaransu tarbiyya daidai gwargwardo, haka ma yaran suna biyayya ga iyayen nasu, duk kuwa da irin soyayyar da suke nuna musu hakan besa raini ya shiga tsakaninsu ba. Rayuwar gidan abar sha'awa ce ga duk wanda ya gani sedai san barka. Alhaji Nasir Aliyu (Abbu) shine mahaifinsu Fahat, se mahaifiyarsu Maryam, sunyi aure tsawon shekara goma sha bakwai kenan a yanzu. Allah ya azurtasu da yara hud'u Fahat shine babba wanda yake da shekara goma sha shida, se Aida take bi masa ita kuma tana da shekara goma sha d'aya, se Sa'eed me shekara bakwai, sannan auta Alim me shekara hud'u a duniya. A yanzu haka Fahat yana SS 2 a makaranta sannan yayi saukar Al Qur'an tun yana shekara sha hud'u yanzu hadda yake, ita kuma Aida tana Pri. 6 itama takai kusan izifi 30 a Al Qur'an, Sa'eed yana Pri. 2 yana uzifi 10 a Al Qur'an, se auta Alim yana Nur. 2 shi kuma izifi biyu a Al Qur'an Kwatsam wata ranar Juma'a bayan su Fahat sun tafi makaranta wani irin ciwon ciki ya taso Ammi a gaba, da k'yar ta iya lalubar wayarta ta kira Abbu ta sanar masa, cikin tashin hankali shima ya baro office domin yaga meke damunta har haka?, dan tabbas duk ciwon da Maryam zata bud'e baki ta fad'a harta kira a waya ba k'aramin ciwo bane. Da hanzari ya shiga d'akin ganin halin da take cikine ya sashi fita nemo mota dan baze iya d'aukarta a babur ba cikin wannan halin. Allah sarki Ammi! Allah ya baki lafiya ???? *Aishan Umma* ??????????????
Previous
Next

Zauruka

  • MANAZARTAA WRITERS ASSOCIATION
    s
    masu aiki da ilimi da sanin ya kamata
Previous
Next
© 2021 Bakandamiya  -  About  -  Terms  -  Privacy  -  Talla  -  Support  -  Contact  -  Mobile Site
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram