• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Shafin Farko
  • Mambobi
  • Zauruka
    • Browse Groups
  • Tambayoyi
  • Ra'ayoyi
    • Browse Polls
  • Makalu
    • Browse Entries
  • Bidiyoyi
    • Browse Videos
  • Sautuka
    • Nemo Sautuka
  • Hotuna
    • Browse Albums
    • Browse Photos
  • More
    • Kasuwa
      • Stores Home
      • Browse Stores
      • Browse Locations
      • Products Home
      • Browse Products
      • Products Pinboard
      • Categories
      • Browse Reviews
      • Wishlists
    • Sana'o'i
      • Browse Listings
    • Sanarwa
      • Bukukuwa Masu Zuwa
      • Past Events
  • Updates
  • About
  • Abokai(9)
  • Tambayoyi(1)

Updates

About

Personal Information

  • Suna Malam Dogo
  • Jinsi Na miji
  • Ranar Haihuwa January 1, 1960
  • Takaitaccen Bayani Ina so girkan arewa na 'kasar Najeriya

Contact Address

  • Sunan Gari Kasar waje
  • Karamar Hukuma Babu
  • Jaha Akwai
  • Kasa Germany

Abokai

  • Rahmatu Lawan Barkanmu da Jumma'a 'yanuwa. Allah Ya sada mu da albarkatun da ke cikinta!
  • Lawan Dalha Ya Allah Ka sada mu da alkhairan da ke cikin wannan rana; ka tsare mu daga sharri duniya da lahira. #JummaaMubarak
  • Imrana Abubakar Assalamu alaikum
  • Jamilu Abdulrahman Pls let your son/daughter know his/her genotype before he/she says yes to that handsome guy or to that beautiful lady whom he/she wishes to spend the rest of his/her life with... Genotype & It's Appropriate Suitor: AA + AA = Excellent AA + AS = Good AA + SS = Fair AS + AS = Bad AS + SS = Very Bad SS + SS = Extremely Bad (In fact, don't try it) #SickleCellAwareness 💉BLOOD GROUP COMPATIBILITY 💉 What’s Your Type and how common is it? O+ 1 in 3 37.4% (Most common) A+ 1 in 3 35.7% B+ 1 in 12 8.5% AB+ 1 in 29 3.4% O- 1 in 15 6.6% A- 1 in 16 6.3% B- 1 in 67 1.5% AB- 1 in 167 .6% (Rarest) Compatible Blood Types O- can receive O- O+ can receive O+, O- A- can receive A-, O- A+ can receive A+, A-, O+, O- B- can receive B-, O- B+ can receive B+, B-, O+, O- AB- can receive AB-, B-, A-, O- AB+ can receive AB+, AB-, B+, B-, A+, A-, O+, O- This is an important msg which can save a life! A life could be saved.... : Your Blood group also speaks about you. 🅰️(+) : Good leadership. 🅰️(-) : Hardworking. 🅱️(+) : Can Sacrifice for others and very ambitious, tolerance. 🅱️(-) : Non flexible, Selfish & Sadistic. 🅾️(+) : Born to help. 🅾️(-) : Narrow minded. 🆎(+) : Very difficult to understand. 🆎(-) : Sharp & Intelligent. What is ur blood group ? Try....It....share the Fantastic information.. EFFECT OF WATER 💐 We Know Water is important but never knew about the Special Times one has to drink it.. !! Did you ??? 💦 Drinking Water at the Right Time ⏰ Maximizes its effectiveness on the Human Body; 1⃣ 1 Glass of Water after waking up - 🕕⛅ helps to activate internal organs.. 2⃣ 1 Glass of Water 30 Minutes 🕧 before a Meal - helps digestion.. 3⃣ 1 Glass of Water before taking a Bath 🚿 - helps lower your blood pressure. 4⃣ 1 Glass of Water before going to Bed - 🕙 avoids Stroke or Heart Attack. 'When someone shares something of value with you and you benefit from it, You have a moral obligation to share it with others too.' So..., DO yours!
  • Yusha'u Alhassan Sirrin ƴaƴan kankana da ɓawonta ga ma’aurata Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matukar amfani ga bil'adama. Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuka ga jikin bil'adama. Masana sun bayyana Kankana da ƴaƴan itaciyar mai matukar amfani ga rayuwar bil'adama, don sindarai da ke cikinta na Vitamins da Minerals da Antioxidants da kuma Calories. Kankana na da nau'ika biyar: akwai mai ƴaƴa da mara ƴaƴa, akwai mai kalar ruwan dorawa da dan karami kore da mai kama da lemun zaƙi. Sai dai a galibin kasashen Afirka irin Najeriya koriyar kankana mai ƴaƴan itatuwa aka fi sani. Kashi 92 cikin 100 na kankana ruwa ne zalla, don haka mai yawaita shanta ba shi da matsalar ƙarancin ruwa a jiki, musamman lokacin zafi, in ji Maijidda Badamasi Burji da ke da ƙwarewa a ilimin abinci mai gina jiki. Ga wasu abubuwa 9 da ƙwararru ke cewa kankana na iya a jikin dan Adam: Kara ruwa a jiki Rashin shan ruwa na illa sosai ga jikin dan adam, hakan yasa ake yawaita jan hankali mutane kan alfannu shan ruwa domin inganta lafiyar jiki. Sai dai shan ƴaƴan itatuwa irin kankana wanda kashi 92 cikin 100 ruwa ne zalla zai maye gurbi bukatar da ake da ita na yawaita shan ruwa. Sannan kankana baya ga ruwa akwai sinadarin Fiber a jikinta, don haka shan ta tamkar anci abinci ne mai matukar inganci wanda ke kunshe da galibin sinadarin da jiki ke bukata. Sinadarin Vitamins da Minerals A cikin jeren kayan marmari ko itatuwa, Kankana ita ce wacce ke da karanci sinadarin calories. Calories din da ke jikinta bai kai na ƴaƴan itatuwa da ake ganin kwata-kwata basu da zaki ba, danginsu inibi. Kofi guda na ruwan kankana na kunshe da sinadaran Vitamin C da A da Potassium da Magnesium da Vitamis B1 da B5 da B6. Kariya daga daji ko Cancer Shanruwan kankana ma yana da amfani Daga cikin sindaran da ake samu a jikin kankana akwai masu bada kariya daga wasu nau'ikan ciwon daji ko cancer. Bincike ya nuna cewa masu yawaita shan kankana masu fiye kamuwa da cancer ciki ba. Kariya daga ciwon zuciya Ƙwararu sun sha cewa ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen hallaka mutane a duniya baki ɗaya. Sai dai an lura akwai nau'in cimakar da ke taƙaita bugun zuciya da shanyewar barin jiki ta hanyar rage kamuwa da hawan-jini da rage kitse a jiki. Sinadarai da dama a jikin kankana na iya samar da waraka da taimaka wajen yaƙi da wadanan cututtuka. Garkuwa da kuzari Kankana na bai wa jiki garkuwa, sannan yana taimakawa da sinadarin da ke taimawa halittar da suke yaki da cututtuka da kuma samun wakara daga ciwo ko rauni, sannan tana maganin kasala da sa kuzari Ƙwarin Ido Shan kankana na kara ƙwarin ido da kariya daga kamuwa daga wasu cutuka ido masu lahani ko kai wa ga makanta. Mutanen da ke yawaita shan kankana ko ɗiga ruwanta a ido kan tsufa da idanunsu a cewar ƙwararu Kumburin gabobi Sinadarin citrulline, da ke jikin kankana, na rage kumburin gabobi. Sannan ana amfani da shi a hada magunguna kara ƙwarin gabobi da cutukan da ake samu saboda yawaita zama ko kin motsa jiki. Hakazalika yawaita shan kankana da bada kariya daga kamuwa da Basir. Gyara fata da gashi Vitamins A da C na cikin kankana na da muhimmanci sosai wajen baiwa jiki sinadarin collagen da ke sa fata laushi da kyau da gyara gashi da kwari Taimaka wa wajen narkewar abinci Kankana da kunshe da ruwa sosai don haka shanta na taimaka wajen narkewar abinci. Yawaita shanta na hana cushewar ciki da bai wa jiki dama sarafa abinci da narkewarta cikin dan kankanin lokaci. Ko ku san sirrin ƴaƴan kankana? Watakil kana/kina cikin mutanen da ke zub da ƴaƴan kankana wajen shanta - ko tsameta kafin ayi amfani ko sarafa kankana. To ga wasu bayanai masu muhimmanci da muka tattara da ka iya taimaka mu ku wajen sauya ra'ayi kan ƴaƴan kankana a tattaunawarmu da Maijidda Yahaya. Ƴaƴan kankana na da sirika sosai da ba kowa ya san da su ba, suna kunshe da sinadarin Zinc da Magnesium da Potassium da Iron da dai sauransu. Ƴaƴan kankana na bai wa jiki garkuwa da matsalar ciwon zuciya da hana ko warkar da ciwon suga da inganta jima'i. Ga karin alfannunsa ga jikin dan adam 1. Yana sa kuzari 2. Inganta jima'i ko saduwa 3. Gyara maniyin maza musamman masu matsalar haihuwa 4. Inganta lafiyar kwakwalwa 5. Kwarin kashi 6. Garkuwar jiki 7. Warkar da Ciwon suga nau'i na biyu ko Diabtes type 2 a Turance 8. Ƴaƴan kankana na gyara gashi ga mace 9. Gyara fatar jiki 10. Lafiyar zuciya Yadda ake sarafa ƴaƴan kankana Kana iya taunewa hade da kankana, ko a shanyata ta bushe ko a soyata sama sama. Duk yada mutum ya sarafata zai ji dadinta. Ɓawon kankana -Boyayyar sirri da akasari ba a san da shi ba Na san galibin mutane idan ana shan kankana zub da ɓawonta ake yi ko a shanye jiki a ɓare bayan a zubar. To kamar dai ƴar'uwarta gurji, ita ma kankana kyanta a shanye komai har da ɓawonta da galibin lokuta ake ganin an watsar a cikin shara, a cewar ƙwararu. Ga wasu dalilai da ka iya sa ki/ka gamsu da waɗanan bayanan 1.Tana kara gamsuwa wajen kwanciya. To amma fa kankana ba maganin karin kuzari ba ce, sai dai wani bincike ya nuna cewa za ta iya taimakawa maza wajen magance matsalar saurin kawowa. Tasirinta wajen kara karfin maza yana zuwa ne daga sinadarin amino da ke jikin ɓawonta. Wani binciken ya nuna cewa sinadarin L-citrulline da ke cikin kankana zai iya taimakawa wajen inganta yanayin karfin maza ba tare da wasu illoli da ake samu a magungunan karfin maza ba. Hazalika ga mata ɓawan kankana na taimaka musu wajen karin ni'ima musamman idan aka markadata cikin madara, in ji Maijidda Yahaya kwarariya kan abinci masu gina jiki. 2. Inganta maka kuzari Za kuma ta iya inganta maka kuzari bayan kara nishadi a gado, domin sinadarin ruwan citrulline zai iya taimakawa wajen kara kuzari yayin motsa jiki. 3. Maganin hawan jini Idan likita ya ce akwai bukatar jininki ya yi kasa, to gwada cin kankana baki dayanta - har da ɓawonta. Binciken masana ya nuna cewa shan kankana na taimakawa manya da tsoffi musamman masu ƙiba yin maganin hawan jini. Wata dabarar jin dadin kankana kamar yadda ƙwararru a fanin abinci mai gina jiki ke cewa, shi ne a sanyata a firij don ta yi sanyi a yankata sala-sala a shanye baki daya. 4. Tana kunshe da Sinadarin Fiber Wani alfannun kankana ga jiki shi ne tana ƙunshe da sinadarin Fiber sosai da ke taimakawa matuka wajen kariya daga cututuka, rage kitsen jiki ko suga, da kuma cimma buri ga masu son rage kiba. Karin haske Wani karin haske da shawarwarin ƙwararru kan shan kankana shi ne mutum na iya bare ɓawonta ya yanka sala-sala sannan ya barbade da yaji, ma'ana a yi kwadonta ga wadanda cin ɓawon zai yi wa wahala.
  • Jannat Qurratul-ayn BAHAGUWAR RAYUWA. NA QURRATUL-AYN. NWA® SHA TAKWAS. MAINA.     "Fad'i dukkan sharad'inka a shirye nake domin cika maka su ko da kuwa fansar raina ne, indai zaka amince da bukata ta". Tsaraki ya yi gajeriyar dariya kafin ya sake daidaita tsayuwarsa yakai dubansa fuskar Dan Zabuwa a karo na kusan hudu, kafin ya fara magana da fadin. "Tabbas zan amince da Manya ya auri Mairamu idan har zaka dawo da kambun tsarafi gare ni, zan yarda na sadaukar da fansar gaba idan har ka amince ka damka kambun sarautar ahalin mu guda biyu a hannuna, wanda kakanmu ya kwace daga hannun Mahaifina, zan yarda da auren ne kawai idan ya kasance ka durkusar da karfi da iko na Manya, idan har ka aminta da wadan nan sharadin to shirye nake ko yanzu basai anjiba ba ko gobe a daura wannan aure". Dan zabuwa ya zubawa Tsaraki idanuwa tsayin wasu dakikai yana nazartar gaskiyar al'amarin daya zo masa da su wanda bai yi tunanin hakan daga Tsaraki ba, domin abin da ya bukata abubuwa ne masu matukar wahala, amma da ya tuna da gudan jininsa tilo daya tal a duniya mafi soyuwa a gareshi sai ya ji a shirye yake ya sadaukar da komai daya mallaka domin samun lafiyarsa, dago kai ya yi yakai dubansa ga Tsaraki wanda shima kallon nasa yake yi fuskarsa fal murmushi domin yasan ko babu komai ya yi abin da zai wulakantar da Dan Zabuwa a kauyen Maina, shi kuwa Dan Zabuwa ba tare da sake nazartar yanayin Tsaraki ba ya cigaba da fadin. "Zan baka dukkan abin da ka ambata, amma akan sharadi guda daya". "Ina jinka". "Sai idan ka yi alkawari da kambun tsafi ba zaka cutar dani da yarona ba*. "Na yi alkwari, kuma kasan nasan girman alkawari zan rike kalmar da yakininta, bazan canja abin da na fada ba". "Shi kenan zuwa daren yau ka zo gidana zan baka dukkan abin da ka bukata" "An gama" Da ga haka suka yi sallama kowa ya yi hanyarsa, Tsaraki cike da dumbin farin ciki da murnar cin galaba akan Dan Zabuwa, Dan Zabuwa kuwa abin duniya ya yi masa yawa, yana ganin zai aikata babban kuskure ne zunubi mai girma, amma idan ya tuna lafiyar yaronsa sai ya ji a ransa hakan ba komai ba ne. KANO. WASHE GARI.   Bayan ta idar sallar asuba tana zaune kan abin sallar tana addu'o'inta, saboda sabo da tashi a gidan su Salima, har ta soma zame mata jiki, bacci ne ya sace ta anan inda take zaune, kamar daga sama taji yo tashin bugun kofar dakin nata, firgigit ta farka tare da murje ido ta nufi bakin kofar da fad'in.   "Waye ne?". "Hafsy ce". Ta bata amsa a daidai sanda ta bude kofar, da murmushi suka dubi juna Ishatu na fad'in. "Bismillah shigo mana". Hafsy ta sanya kai cikin dakin tana mai cigaba da fad'in. "Kin jini shiru sai yanzu Allah ya yi dawowar mu, kai amma dakin naki ya yi kyau wallahi". Ta kare maganar tana mai ajiye manyan ledojin data shigo da su kafin ta nemi gefan katifa ta zauna, ta sake duban Ishatu dake tsaye tana binta da kallon mamakin jin cewar tun daren jiya sai yanzu ta dawo.   "Ishatu lafiya kuwa?". Ishatu ta dawo daga duniyar tunanin da murmushi shimfide saman fuskarta kafin ta ce.   "Kenan ba gida kika kwana ba?". Hafsy ta yi dariya ba tare da ta bata amsa ba ta cigaba da magana. "Kin ga duba cikin waccan karamar locker akwai plate da sauran kayayyaki kitchen dauko nan mu yi breakfast dan wallahi da yunwa na dawo, wannan shegiyar dinner a bushe basu tanadi abincin kirki ba sai kayan shaye-shaye na banza". Ita dai Ishatu tuni ta dauko mata abin da ta bukata ba tare da ta damu da son jin inda zancen nata ya nufa ba, ta ajiye mata kayan a gabanta tana cewa. "Yunwa tun yanzu Hafsy?". Baki sake Hafsyn ke dubanta da mamaki kafin ta daga kai takai dubanta jikin bangon dakin inda agogo yake kafe lokaci guda ta dawo da kallonta ga Ishatu da fadin. "Kika san yanzu karfe nawa?". Sai lokacin Ishatu takai dubanta wajen agogon karfe tara har da wani mintuna lokacin, Ishatu ta zaro ido da fadin. "Ikon Allah ashe bacci na yi sosai haka?". Hafsy ta girgiza kai da murmushi ba tare da ta sake magana ba, ta cigaba da juye musu kayan makulashe kala-kala wanda Kamal ya biya ya siya Mata, saboda mitar yunwa data cika shi da ita suna hanya.    "Ya kamata a ce an kawo miki kayan tea fa? Babu wanda ya shigo wajenki ne?". "Aa Aunty ta shigo tun jiya da dare". "Ok may be ina jin ta yi aike kina bacci, dan nasan ba zata bari a tashe ki ba". "Ai tana da kirki Aunty sosai". Hafsy ta gimtse dariyar dake shirin kufce mata jin maganar da Ishatu ta yi akan Aunty har tana shirin kwarewa a daidai sanda takai cokali bakinta dauke da farfesun kayan jiki, a jiye cokalin ta yi tare da yafito Ishatu da hannu ta zaunar da ita gefanta da fadin. "Zan gaya miki wani abu a game da zaman gidan nan amma kafin nan na tambayeki abu daya zuwa biyu, idan kin ga dacewar ki sanar da ni ina maraba da hakan, idan kuma abin ya kasance sirri ne a gareki to kibar abin a cikin ranki". Ishatu ta gyada kai alamun ta gamsu da batun nata, Hafsy ta zubawa Ishatu nata naman a dayan plate din tana mai cigaba da cewa.     "Mene dalilin da ya fito dake daga gida, sannan kuma kin shiryawa zama a cikin gidan nan?". Ishatu ta yi shiru tsayin wasu dakiku tana nazari da tunanin amsar da zata bata, kafin ta yankewa kanta hukuncin sanar da Hafsy wani abu a dangane da ita, nan dai ta fara bata labarin zuwanta gidansu Salima da shiga dakinta da ake yi da yanda aka yi ta baro gidan, Hafsy ta girgiza kai kafin ta ce.   "To ni a ganina nan din ma da kika zo duk kanwar ja ce, amma kafin na ce wani abu bani amsata ta biyu". Ishatu ta gyara zama kafin ta cigaba da magana. "A shirye nake na cigaba da zama anan, domin idan har nabar nan bansan inda zan nufa ba". Hafsy ta girgiza kai da murmushi kwance saman fuskarta, kafin ta kama hannun Ishatu ta rike a cikin nata ta dubeta da kulawa kafin ta ce. "Kinsan abin da zan fada miki da zaman gidan nan? Babu ruwanki da shiga harkar da bata shafeki ba, haka kuma duk wacce ke nemanki da rigima ki bawa banza ajiyarta, Aunty na son girma da iko, ki girmamata ki yabeta a gabanta, idan kin bi wannan zaki zauna kafiya kalau da kowa cikin gidan nan, sannan kuma a labarin da kika bani kamar kin boyemin abubuwa da dama, amma karki damu kanki nasan may be sirrinki ne, nasan kuma akwai lokacin da zaki yarda dani ki sanar dani, Bismillah muci abinci". Tana kaiwa nan ta cigaba da cin abincinta, haka itama Shatun, amma a gefe guda tana mamakin saukin kai irin na Hafsy da yanda ta dauki rayuwa ba komai ba, tafiyar da rayuwarta take yi hankalinta kwance, alamun babu abin da yake damunta a fadin duniya, a haka suka kammala karyawa Ishatu ta kwashe kwanukan ta wanke kafin ta dawo ta nemi inda ya tashi ta zauna tana kallon Hafsy dake ta faman latse-latsen waya data gaji ta shiga daukar selfie har tana sanya Ishatu ta matso sunyi hotuna sosai masu kyau da yake wayar iPhone  11 ce ga kyau ga fidda hotuna masu kyau, Ishatu ta dubi Hafsy dake gyara kwanciya da shirin bacci tana fadin.    "Na tambayeki mana Hafsy?". "Allah yasa na sani ina jinki". Ta karashe maganar tana hamma alamun baccin take ji sosai, Ishatu ta gyara zama sosai kafin ta ce. "Wai dan Allah mene Bariki ne? Kuma suwaye kadangarun Bariki kamar yanda na ji jiya suna maganar anan waje?". Hafsy ta mike zaune tare da murje gidonta daga baccin dake fizgarta, ta kafe Ishatu da manyan idanuwanta sosai take yi mata kallon mamaki.    'Baya ga haka kuma bata zubi ga mutanen kauye bare ta kirata bakauya, kuma tasan a kauye ma yanzu yaro da babba babu wanda zai ce baisan me kalmar bariki take nufi ba amma da mamaki' Hafsy ta gyara zama tare da fara yi mata bayani daya bayan daya ta cigaba da fad'in. "Aunty zata yi alfahari da ke ne idan kin fita kin nemo mai yi Miki hidima  tare da ita, haka kuma zata kaunace ki fiye da kowa idan farashinki ya haura na sauran matan dake gidan nan, ni nasan zaki yi kasuwa matukar kika waye a wannan harkar, sannan kuma kinsan wani abu?". Ishatu ta girgiza kai alamu a'a. "Na ji mamaki da kika tambaye ni game da abin da ake nufi da bariki, dama wai ba BARIKI KIKA FITO BA?". Ishatu ta girgiza kai alamun zancen Hafsy ba haka bane. "Shi yasa dama na tambayeki idan kin shiryawa zama anan domin babu macen da Aunty ke ciyarta da ita abanza matukar ba zata fita ta nema ba sunanta sorry, ki yi tunanin mafita Ishatu zan taimake ki da yardar Allah kin ji?". Hafsy ta koma takwanta tabar Ishatu nan zaune zuciyarta cike da sake-sake kala-kala na neman mafita akan tudun data taka a yanzu, wanda tana ganin har kusan gara zamanta a gidan su Salima akan hanyar da rayuwarta take shirin bi yanzu, ko kusa ko da wasa bata fatan sake kazanta kanta domin Allah ya nufa ta tsabtacu akan addininta, tunani sosai take yi tare da neman mafita kamar yanda Hafsyn ta fada mata. Ku BIYO Ni..! Fiddausi Salisu Aliyu (QURRATUL-AYN).
  • Aminu Umar
  • Surajo Yau
  • Yusuf lawal Yusuf ADDU'A TAKOBIN MUMINI 05 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya kasance idan ya ga jinjirin wata yana cewa: "الله أكبر، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺃَﻫِﻠَّﻪُ ﻋﻠَﻴْﻨَﺎ ﺑِﺎﻷَﻣْﻦِ ﻭﺍﻹِﻳﻤَﺎﻥِ، ﻭَﺍﻟﺴَّﻼﻣَﺔِ ﻭﺍﻹِﺳْﻼﻡِ، لما تحب وترضى، ﺭَبنا ﻭﺭَﺑُّﻚَ ﺍﻟﻠَّﻪ". 📚ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ (٣/١٥٧) "Allahu Akbar, Allahumma Ahillahu Alaina Bil-Amni Wal-Iman, Was-Salamati Wal-Islam, Lima Tuhibbu Rabbuna Wa Tarda, Rabbuna Wa Rabbukallah". 📚 Tirmizi (3/157) Ma'ana: "Allah ne mafi Girma, Ya Allah! Ka sanya tsayuwarsa a garemu ta zamo kwanciyar hankali ce, da imani, da aminci, da musulunci, da kuma gamokatar da abin da ka ke so Ya Ubangijinmu, kuma ka ke yadda da shi, Ubangijinmu da Ubangijinka (ya kai wannan jinjirin wata!) shi ne Allah". Allah ya sa mu dace 1st Muharram, 1442H. (21/08/2020). ✍️ Yusuf Lawal Yusuf
Previous
Next

Tambayoyi

  • July 21, 2019 9:31 AM BST
    in the topic Tarihin shigowar boko kasar Hausa in the forum Al'adun Hausawa
    To, Malam akwai irin littafi guda biyu. Na farko dai littattafan addini. Sun shiga ?asar Hausa tare da zuwan addinin musulmanci wato tare da zuwan larabawa. Na biyu fa akwai littattafan da ake rubuta da ba?a??en turawa. An fara rubuta su a shekara 1854. Sunan wannan littafi "Polyglotta africana" na Sigismund Klle. A wannan littafi ake samun kalmomin hausa. Cikin 1885 an wallafa "Magana Hausa" na James Frederic Schn. Akwai tatsunyoyi da karim magana da sauransun da ya rubuta a harshen Hausa a ciki. Cikin 1934 Muhammad Bello Kagora ya rubuto littafi (novel) "Gandoki". Shi ne farkon novel ?in da aka rubuta a harshen Hausa. Shi ke nan.
Previous
Next
© 2021 Bakandamiya  -  About Us  -  Terms  -  Privacy  -  Advertise  -  Support  -  Stock Photos  -  Contact Us  -  Mobile Apps
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram
Create New Content
  • Kasuwa
Add Link