Jamila Mustapha
Iskokai Sun Kori Shugaban Kasar Brazil Daga Fadar Gwamnati
Kwanaki 10 kacal bayan shi da iyalinsa sun koma fadar gwamnatin
kasar, shugaban Brazil Michel Temer ya tattara ina sa ina sa ya koma
fadar mataimakin shugaban kasa.
Ya bayyana dalilinsa da cewa akwai iskokai mara sa kyau a gidan. Ya
ce shi da matar sa da dan sa mai shekaru 7 ba sa iya barci da daddare
saboda wasu irin motsi motsi da suke ji, kuma tun da suka shiga fadar
gwamnatin, jikinsu bai gamsu da shi ba.
Fadar shugaban kasar wanda ake kira Alvadora Palace dai katafaren gida ne wanda ya kunshi abubuwan more rayuwa da dama.
Sai dai shugaban ya ce shi da iyalinsa sun fi sakewa a fadar
mataimakin shugaban kasar mai suna Jaburu Palace wanda ya fi kankanta.
Toh dama dai shugaban shi ne mataimaki kafin majalisar kasar ta tsige
tsohuwar shugaban kasar, Dilma Roussef a kwanan nan, kuma iyalinsa sun
riga sun saba da fadar ta Jaburu.