hajara yahaya
(¯'*•.¸,¤°´✿.。.😗քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Duk da kinyi nisa amman ban manta ki ba AISHA HAMZA (sweetheart) kinyi zarra wurin iya tsara comment😅😅 Allah ya bada sa'an jarabawa*
*Wannan shafin naku ne*
_my umma Sulaiman, Musmayya, Aisha Isma'il, mom eyman, and khadija mukhtar_
Ku ci gaba da antayo sharhi ina antayo typing 💃🏼💖 ummu Najma tana godiya❤️😍
06🧝🏻♀️
A hakan muka gama primary 2 muka shiga 3 amman wannan term ɗin saida Khamis yaje ya bada haƙuri ya faɗa musu matsala ta ban fara makaranta daga ajin da ya dace bane kuma ban shiga a kan lokaci ba tukunna suka yarda sukayi min promotion don na 45 nazo a cikin mu 48, ni kuwa ji nakeyi a raina ko banza na wuce mutum 3,
Duk lokacin da na tuna gida na tuna iyaye na zuciyata tana min ciwo, ina jin babu daɗi sosai a raina, nakan yi kuka idan na tuna halin da na barsu a ciki, baban mu yayi mazantaka tunda har ƙaddara masu muni ta faɗo ma yaran shi har biyu amman ya ci gaba da rayuwar shi normal, mahaifiyata kam na san har yanzu bata dawo dai_dai ba,
Wasa_wasa na shekara biyu da rabi a garin Yola banji daga iyaye na ba ko sau ɗaya, koma suna lafiya ko wani abun ya same su? Allah masani,
A makaranta kuma wannan term ɗin ba ƙaramin ƙoƙari nayi ba domin Khamis ya saka ɗaci, yace idan ban dage nayi karatu ba zai maidani gidan su yarima shiyasa na dage nazo na 39 na haye mutane har 6, lokacin da na kaao mishi result babu laifi yace na fara ƙoƙari amman idan har ina son zama tare da su to sai na ƙara ƙoƙari na fara zuwa na 1 ko na 2 a makaranta,
Nidai na san hakan ba zai taɓa yiwuwa ba amman na ƙara jajirce wa har na fara iya turanci irin su IS ME IS YOU,
dukda kasancewa ta shiru_shiru kuma mai sanyin hali amman ba shi yake hana ni faɗa da ƴan ajinmu ba, ban taɓa dambe ba amman ina iyakar ƙoƙari na wajen cacar baki, idan naga yarinya zata ƙure ni sai kawai na haɗe fuska nace mata "I AM MAD" na juya na bar qurin ina tafiyar ƙasaita ko babu komai na zage ta da turanci,
Yanzu haka na gama primary 4 da ƙyar, yau zamu je mu karɓo result ɗinmu ayi mana hutun azumi sai bayan Sallah zamu koma aunty Yusrah kuma ta kusan aihuwa shiyasa shekaran jiya mama ta gargaɗo ni nazo na taya ta zama ina rage mata wasu ayyukan,
Ohh ashe abinda ya kawoni kenan!!
Tashi nayi da sauri na naɗe darduman sallah na ajiye sannan nabi na bude labulayen parlorn har rana ta fito haske ya shigo na ɗauki tsintsiya na fara sharo ko wani kusurwa na gidan,
Ina gamawa ana kawo wutan lantarki, na dauki kettle ɗinta mai kaman buta na cika shi damm da ruwa sannan na jona na wankan mu na same ta a kitchen muka ƙarasa haɗa soyayyen doya da sauce sannan ta tafi haɗa ma Khamis ruwan wanka ni kuma na kama mopping,
Bayan mun gama breakfast, da sauri na shirya cikin uniform ɗina dark green and white, fuskata sai kyallin mai take na ɗauki jaka na na fita, a waje na samu mai napep ɗin da aka ɗauka yana kaimu makaranta ni da Jannat wanda take da shekara 3½ a yanzu, ta gama play class zata shiga nursery one bayan sallah, ya ɗauke ni muka biya gidan mama muka ɗauko ta tukunna muka wuce makaranta,
*****
"Alhamdulillah" Khamis ya furta lokacin da ya ajiye cup ɗin hannun shi ya gyara zaman hulan kanshi tare da kallon Yusrah yace "baby hanzarta mu tafi kada kiyi latti kinga yanzu har ƙarfe 8 harda minti 2" saboda shi da kanshi yake kaita makaranta, harƙoƙin kasuwancin ta da sauran abubuwa ne yace ta dinga bawa public transport saboda shima yana zuwa aiki ba ko yaushe yake available ba,
"Ayyah ban ƙoshi bane fah"
Sunkuyawa yayi yana leƙa fuskar ta da ta yamutse shi tana faman wurga loma yace "idan kika faɗi a test ɗin nan blame your stomach not me, tunda gashi ni na gama shiryawa jiran ki kawai nake amman da yanzu wani abu zai faru zaki ce, Abban Jannat ai laifin ka ne bamu tafi da wuri ba shiyasa ban samu nayi karatu ba" ya faɗa tare da lanƙwasa murya yana wani rausaya kai irin yanda take magana, "To kome ya faru babu ruwa na"
Murmushi tayi tace "ai karatun yanzu ba zaiyi min wahala ba 30 to 40 minutes yayi yawa na gama, a kwai wani abokin karatu na da sukayi magana da malamin yace yanzu zai raba mark ɗin test ɗin gida biyu ɗayan ya bamu assignment, harma ya fara min assignment ɗin mutumin yana da kirki wallahi, he is so kind"
Gyara zama Khamis yayi yana hararan ta, tana ganin haka ta tuntsure da dariya,
"Haba habiby sahibul ƙalbi, daga karatu fa sai aji babu abinda zai haɗa ni dashi bayan nan"
"To wannan yaba shi da kike yi a gaba na fa? Na menene?"
"Cewa kawai nayi he is kind, that's all"
"Shi wannan soooo ɗin da kika faɗa kafin kind ɗin kuma a dalilin me kika saka shi ciki?"
Dariya kawai tayi dan ta lura yau niman magana ya tashi dashi,
"Menene na tada hankali my love? Ka manta akwai shaidan ka a jiki na ne? Babu wanda ya isa ya raɓe ni idan yaga wannan, ka dai ci gaba da mana addu'a Allah ya raba mu lafiya"
Ƙayataccen murmushi ya sake saman fiskar sa tare da faɗin "Amin, amarya kuma uwar gidan Abban Jannat, my rich wife yarinya ƴar kasuwa, daga ke ba ƙari"
"Haka dai ko yaushe kuke faɗa amman halin ku maza sai a hankali, idan kaso ka ƙaro auren ka bazan hana ka ba"
"Oh ke baki kishi na kenan ko? Shikkenan daman kuwa naga wata yarinya ƴar fara ta unguwan ku kinga muna gama gina gidan mu sai mu tare da sabuwar A......"
Bai ƙarasa ba Yusrah ta katse shi da bala'in da bata san daga ina yazo mata ba,
"Kada yarinya ta kuskura wallahi, zan yanka wuyan ƴar mutane idan ta kuskura ta shigo gida na, gwanda ma kada ku fara"
"Yi haƙuri aunty Yusrah" ya faɗa tare da zabga tagumi yana kallon ta, yanda tayi kicin_kicin lokaci ɗaya ya nemi ɗan murmushin da take masa ya rasa,
Ƙaramin tsaki taja taci gaba da cin abincin ta wanda yana kyautata zaton plate na uku kenan,
"kefa yanzu abincin runduna kike ci, ba zaki saka ma baby na rashin lafiya ba kuwa?"
Bata amsa shi ba dan ya gama bata haushi, mafarkin ta bai wuce mijinta ya mallaki gidan kanshi su koma rayuwan su a ciki da ƴan ƴaƴanta ba amman gashi yana son shigo mata da wani zance daban,
Saida ta gama sannan ta tattara wurin ta saka hijab ɗinta ta lanƙaya handbad ɗinta ta ƙaraso inda yake tsaye fuska a tamke tace "muje" bai nuna damuwa da canjin yanayin ta kaman yanda taso yayi ba, ya miƙe tare da sauƙe rigan shi ta baya ya ɗauki key ɗin mitar shi yayi gaba,
Har zai fita daga parlorn ta kira shi ya juyo yana kallon ta,
"Daman nace ka barshi kawai ka wuce wurin aikin ka kada na ɓata maka lokaci, akwai wani aboki na ɗan ajinmu zai zo ya ɗauke ni mu tafi"
Girgiza kai Khamis yayi yana dariya, wato abinda ya faɗa mata ne take so ta rama, Allah sarki baya mai wucewa da a lokacin ne ta faɗa mishi wannan maganar da ya daɗe da haɗa kanta da bango ko cikin jikin ta bazai dame shi ba,
Kusanto ta ya fara yi yana gwada ta da key ɗin hannun shi still yana dariya yace
"You are trying me ko? Allah idan kika yi Wasa makarantar nan sai a fasa shi, daga yau kin bar zuwa"
Murmushi tayi wanda ya bayyana haƙwaran ta gudun kada ta takalo ma kanta fitina ta riƙo hannun shi suka nufi hanyar waje tana faɗin "Allah ya huci zuciyar angon Yusrah, ba ma za'ayi hakan ba"
**********
Sallama yayi da buɗaɗiyar murya, mutanen ɗakin suka amsa tare da bashi izini kafin ya shigo, tsugunawa yayi suka gaisa da mahaifiyar Zayyad kafin ya samu kujera ya zauna yana masa sannu da jiki,
Yafi 20 minutes zaune ba tare da yace komai ba yana jiran ta fita ta basu wuri amman ko kallon inda yake bata yi ta maida hankalin ta kan wayar hannun ta dukda kunnuwan ta yana muradin sauraron abinda zasu tattauna a kai don tunda taga Sulaiman ya shigo da sanyin safiya ta san a kwai matsala,
sannan ta fara gajiya da irin takurawan da yake yi ma Zayyad yana saka shi ɗaga hankalin shi kan matsalar da bata kai ta kawo ba, ta gaji da sanya shi damuwa da yake yi ko wani lokaci ya maida shi matsoraci kuma rago, ya saka ya dawo kaman mace kullum yana ƙunshe a ɗaki,
Tsawon shekara da shekaru yake ɓoye shi a gida, ya hana shi yin abokai ya hana shi yin ƴammata, bata son ko bayi son yayi aure bane a rayuwan shi gaba ɗaya, dan taurin kai da rawan kai da samaruka suke yi idan sunzo gaɓar girma duk Sulaiman ya daƙushe na Zayyad, ita yanzu abin ya fara isan ta, ta jure shekara da shekaru amman hanzu da abu yazo bakin gaɓa bata jin zata ci gaba da haƙuri daman ance aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, yanzu kam tana son sama ma ɗanta ƴanci,
Ganin bata da niyyan basu wuri kuma ba zai iya ce mata ta fita ba yasa ya tashi daga mazaunin shi ya ƙarasa bedside drawe ya tura lamp ɗin dake kai ya zauna yana kallon shi na wasu ƴan daƙiƙu,
Tun kafin yayi wani abu Zayyad ya tsorata a zuciyan shi yana addu'ar Allah yasa ba tsintan abin nan Sulaiman yayi ba, don a daren shekaran jiya Sulthana ne ta hana shi nema da tazo da kalan nata iya shegen,
Bai ƙarasa tunani ba Sulaiman ya saka hannu cikin aljihun jamfan shi ya ciro wata ƙaramar container fari ya miƙa ma Zayyad tare da faɗin
"Wannan abun kaje nema ko?"
Kame_kame Zayyad ya fara dan yasan idan yayi ƙarya tabbas Sulaiman zai gane,
Bai gama laluɓo abinda zai faɗa ba ya jefa mishi wani tambayar
"Yaya akayi kayi sake ka rasa shi?"
"Babban yaya ban san ya zame daga aljihu na bane kum...."
"Me ya fitar da kai wurin a lokacin, kuma mai ya haɗa ka da Sulthana cikin dare? Baka guje ma kanka fitina ko??"
Ba abin mamaki bane don ya san da duka wa'innan abubuwan bayan bayi wurin kuma babu camera dake ɗauka amman yana da munafukai masu barci da ido ɗaya,
Zayyad ya buɗe baki mahaifiyar shi tayi saurin saka bakin ta ciki, daman daman da take nema kenan wanda zatayi mishi complain ɗin abubuwan da yake yi,
"Haba Sulaiman, ka sassauta ma al'amarin nan dan Allah da wanne ɗaya kake so yaji? Halin da yake ciki ko kuma tuhumar da kake mishi?"
A dake kaman yanda yake magana da kowa yace "Aunty Amarya maganin matsalar nake son kawowa baki ɗaya, dan Allah ku tausaya min, shekaru biyu kaɗai tunda na lura ku baku son Zayyad ya samu kason shi to ni ina so, ina mafarkin ganin ya mallaki wani muhimmin abu a duniya saboda yayi farin ciki nan gaba ya samu yayi murmushin da baiyi shi lokacin baya ba, kuma insha Allah duk inda maganin matsalar Zayyad yake sai naje na samo shi"
Da faɗan haka ya wurga mishi containern ya fita,
Tsaki aunty Amarya tayi ta dubi Zayyad da ya sadda kanshi ƙasa kaman mai shirin kuka tace "kayi haƙuri Zayd nasan an takura maka amman ka ƙara haƙuri insha Allah wata rana komai zai zamo kaman ba'ayi ba, zamu fita daga ƙangin sulaiman"
"A'a aunty, abunda babban yaya yake yi shine dai-dai, duk laifi na ne da bani kiyaye dokokin da yake shimfiɗa min wanda zai kaimu ga nasara..........🤦🏻♀️
_Ayi manage, muna tsakiyar gasa ne a kuma taya mu adduan nasara Please_
#vote
#share
#comment