Rahma kabir
*AKAN IDO NA*
Na
Rahma Kabir (Mrs MG)
Whattpad @rahmakabir
15
*Last free page*
Anty Amarya ta shiga tsananin rudani, ta rasa wani irin tunani zata fara, tana da tarin tambayoyi amma ba tada mai amsa mata. Koda Alhaji ya dawo ya kwanta tana jinsa har barci ya sake daukarsa tana jin saukar numfashinsa, hakan ne ya bata dama ta tashi zaune a hankali ta mike ta shiga bayi tayi fitsari kana ta dawo ta kwanta, da kyar barci ya dauke ta.
******
Washe gari.
Da safe bayan mutanan gidan sun kammala karin safe gaba daya, sai suka tattara suka koma falo saboda Alhaji yace zai yi magana dasu, ya kai dubansa ga Majaheed wanda yake sanye cikin blue din riga da bakin wando da alama ya gama shiryawa fita aiki kawai zai yi.
Kai Mujaheed ya zancen yarinyar nan daka kai station dinku?
Tana nan a hannunmu har yanzu bata bada wani bayani ba, ina ga nan da wasu kwanaki zan mikata kotu, sannan zamu yi bincike akan wanda suka yi silar kawota gidan nan.
Ayya ina ganin ba za ayi haka ba, ka sake ta kawai ta tafi tunda mu mun yarda da kaddara, duk kuma mai son ganin bayanmu Allah ba zai barshi ba koya kika ce Hajiya.
Yayi maganar yana duban Ummi.
Hakane Alhaji amma daka barshi yayi aikinsa dan amfanin naka yana waje kenan.
Ni kam nafi amincewa da arufe maganar, insha Allah asarar da muka yi zai dawo
Amma Baba ina ganin yin hakan kamar an kara mata wani karfi ne wanda nan gaba zata iya sakewa.
Mujaheed umarni na baka ka saketa ta tafi ba wai niman shawararka nake ba. Meye duniyar da har zamu tsaya muna zafafa abu.
Shikenan insha Allah zanyi yadda kace.
Yauwa, sannan batun Haj. Kausar shima ya kare tunda ita aiki ta dauketa bata san cewar da wani nufi ta shigo gidan nan ba, tsawon zaman dana yi da Kausar ban taba kamata da wani laifi mai muni ba, kun san dai halinta
Yayi maganar yana kallonta, Anty Amarya tayi murmushin yake ita kadai tasan halin da take ciki na rudani. Ummi taja guntun tsaki.
Ai ita dama bata laifi a gunka, waya sani ma ita ce tasaka kace a saki yarinyar
Babu ruwanta ganin damana ne yasa nace a saketa, kuma ai na isa da gidana na yanke hukunci, bana son irin wannan maganganun.
To ai shikenan Allah ya kyauta na gaba
Cewar Ummi tana kawar da kai gefe, nan Alhaji ya mike tare da yi musu sallama akan shi ya fita kasuwa, Anty Amarya ta bi bayansa dan yi masa rakiya kamar yadda ta saba kullun. Suna fita Mujaheed ya mike jiki a sanyaye Umminsu ta kalleshi cikin kulawa.
Sai dai kiyi hakuri da halin Babanku tunda ya riga ya yanke hukunci
Ai wlh wani lokacin lamarin Baba sai a hankali
Cewar Amina itama tana mikewa cike da jin haushi.
Kar na sake jin bakinki a nan kin san bana son raini, mahaifinmu ne ya isa ya zartad da duk hukuncin da yaso a gidansa kuma dole muyi masa biyayya, shiyasa kullun nake bambantaki da Aisha dan ta fiki hankali.
To to ni me nace ai gaskiya na fada
Tace tana turo baki sai ta wuce zuwa dakinsu da sauri dan karya kai mata hannu. Tsaki kawai yaja ya girgiza Kai.
Ummi ina zuwa
Ka fasa fitan kenan?
A'a zan yi wani abu ne
Yace yana haurawa sama, yana isa dakinsa ya kira station dinsu ya basu umarnin su dauko Saufyan su kawo shi gidansu yana jiransu.
Bayan minti goma sha biyar sai gasu sun karaso, Mujaheed ya fita zuwa farfajiyar gidan sai gasu sun shigo tare da Sufyan da suka sanyawa ankwa a hannu, ya yi baki ya rame jikinsa duk ciwuka gwanin tausayi, Mujaheed ya karasa gabansa ya kwance masa ankwan yace yaran aikinsa su jirashi, sai ya cewa Sufyan yabi bayansa, ba musu ya bishi suka isa dakin baki ya nuna masa wani daki yace ya shiga ciki yayi wanka, ba musu Sufyan ya shiga ciki dan yana bukatar yin wankan ko zaisa jikinsa ya rage yi masa tsami, yana shiga Mujaheed ya fito ya nufi dakinsa ya dauko wani shadda ash color daga cikin kayansa ya fito ya koma dakin bakin ya ajiyewa Sufyan a gefen gado ya zauna yana jiran ya fito. Ya dauki kimanin minti ashirin yana gasa jiki a cikin shawa, wannan ne karonsa na farko daya taba yin wanka a irin wannan bayi mai kyau na masu kudi, banda yana cikin halin tashin hankali da ba karamin kallo zai tsaya yasha a gidan ba, amma ina hankalinsa gaba daya yayi gida yana tunanin irin halin da mahaifiyarsa take ciki, ya maida kayansa ya fito sai yaci karo da Mujaheed suka hada ido ya sakar masa murmushi, kamar ba shi ne mara mutuncin nan ba da yasa aka yi masa dukan kawo wuka.
Ga wasu kaya na kawo maka ka sanya su dan wannan na jikinka sun baci sosai, in ka kammala ka fito ka karya.
Mujaheed yana gama fadar haka ya mike ya fice ba tare daya jira amsarsa ba, da kallo Sufyan ya bishi harya fice yana mamakin sauyawar da ya gani, haka dai ya zame kayan jikinsa ya sanya wannan da ya bashi, sun so suyi masa yawa da yake Mujaheed yanada tsayi shi kuma baida tsawo sosai sai dai kaurinsu zai zo daya, yana gama shiryawa ya fito ya samu an tsake masa center table da abinci, ya karasa ya zauna, Mujaheed ya mike yaja table din zuwa gaban Safyan.
Ka ci ka koshi amma kayi sauri dan zamu je asibiti a duba lafiyarka
Galala Sufyan ya kalle shi ya kasa yin shuru wannan karan, sai yace cikin raunin murya.
Dan Allah ka gaya min dalilin wannan sauyawar haka? Meyasa kake kokarin yimin kirki? me yake faruwa?
Babu komai sai alkhairi, bincikenmu ya tabbatar mana da ba kada laifi, kasantuwar ni na jawoka kazo garin, shiyasa nake son kyautata maka koda sau daya ne, kayi sauri ka kammala cin abincin lokaci na tafiya.
Sai ya fice ya barci, Sufyan bai kuma cewa komai ba ya dauki kofin tea da aka hada masa mai kauri ya fara sha yana kallon irin tagomashin da aka hada masa, wanda duk mugun cinsa sai ya barshi, soyayyar Irish da kwai, indomie wanda yaji kayan hadi, farfesun naman kaza, nan take ya hadiye wani yawu dan gaba daya yaji sha'awar yaci su duka, sai a lokacin bakin yunwar da yake ji ya taso masa, aiko haka ya saki ciki ya kwashi girki, harya nima mance a ina yake dan ba karamin yunwa yake ji ba, duk kuwa cinsa sai da ya hakura ya bar abincin. bayan ya kammala sai ga Mujaheed ya shigo yace masa suje, haka suka fito ya sashi a motar office dinsu shi kuma ya shiga nashi suka wuce asibitin murtala, sai driver din gidan shima ya bi bayansu dan cika umarnin Mujaheed.
Koda suka je likita ya duba Sufyan sosai ya rubuta masa Magani, sannan ya hada su da wata nurse suka wuce dakin dressing aka wanke masa ciwukan daya ji a jikinsa, bayan an gama masa suka siya magani sannan suka fito haraban asibitin, a nan Mujaheed ya sallami yaransa suka wuce, sai ya sanya Sufyan a motar gidansu ya mikawa driver kudi.
Wannan kasha mai dasu, sai sauran kaci abinci ka tabbatar kayi tuki a hankali, kuma ka kaishi har kofar gidansu, in dare yayi maka ka kwana gobe in Allah ya kai mu ka dawo.
To insha Allah nagode
Driver yace sai ya shiga motan, Mujaheed ya sunkuya windon baya in da Sufyan ke zaune ya mika masa kudi duba ashirin da wata leda wanda yake dauke da kayansa da wayarsa da kuma duk abinda yake nashi wanda suka cire masa lokacin da suka kai shi station.
Kayi hakuri da abinda ya faru, insha Allah yau zaka koma gida, ga kayanka nan, wannan kuma ka sha ruwa a hanya.
Nagode Allah ya saka da Alkhairi, sai dai ina son tambayarka labarin Mubeena.
Zata dawo itama insha Allah karka damu.
Sufyan zai kuma magana, Mujaheed ya daga masa hannu alamar baya son wani zance, sai ya umarci driver daya ja su wuce. Akan idonsa suka bar cikin asibitin kafin shima ya koma mota ya shiga ya tayar ya kama hanyar station dinsu, yana sauke wani irin murmushi wanda shi kadai ya barwa kansa sanin yinsa. Yana isa station dinsu yasa aka fito masa da Beena, ya tasa keyarta har zuwa wajen motarsa ya bude mata mazaunin baya ya ce ta shiga, ta kama marfin motar tana kallonsa.
Ina Sufyan? Bazan iya barin gurin nanba ba tare da shi ba
Na sallama shi ya tafi
Amsar daya bata kenan yaje mazaunin driver ya bude ya shiga, ganin babu wasa a fuskarsa shiyasa zuciyarta ta yarda da abinda yace sai ta shiga ta zauna, Mujaheed bai ji wani haushi ba danya kasance driver dinta, bazai iya jure ganinta a gaba kusa da shi ba shiyasa ya gwammaci ta zauna a baya ya jata. Suna fitowa yaran Alh. Maina suka shaida masa a waya cewar sun ga Mujaheed ya fito da wata mace a bayan mota, sai yayi musu umarnin su bisu a baya.
Mujaheed gidansu ya wuce da Beena, suna isa yayi parking ya karba key wajen mai gadi yace ta fito, ya tasa keyarta suka isa sashin ma'akaita har zuwa dakinta, ya bude ya fara shiga ta bishi a baya.
Ki kwashe duk kayan da kika san naki ne ina jiranki
Bata tanka shi ba ta shiga hada kayanta ta tusa a jaka, kana suka fito har zuwa harabar gidan, sai suka iske mutanen gidan cirko cirko sai kallonsu suke yi, Anty Amarya taji kamar ta jawo Mubeena ta boyeta a dakinta, gaba daya babu wanda ya iya magana, har sun gota su zata wuce Beena ta juyo ta kallesu tace cikin sanyin murya.
Labarin dana baku cewar daga kauye na fito ba gaskiya bane, hasalima ban taba yin rayuwa a kauye ba, shigata da kwalliyata duk shiri ne, asalin sunana Mubeena. Anty Amarya nagode da karamci, ba dan ke ba da ban kasance a cikin gidan nan ba.
Sai ta juya ta cigaba da tafiya, gaba dayansu sun kasa magana kamar babu wani halitta a gurin, sun tsorata sosai da zancenta, Anty Amarya kuwa taji kamar ta dakatar da ita dan tana so ta sanar mata asalin labarinta da dalilinta na zuwa gidan, akwai tarin tambayoyi data so Beena ta amsa mata su sai dai kash ba hali, Mujaheed kuwa wani bacin rai yaji yana taso masa, yana matukar jin zafin abinda mahaifinsa yasa shi yayi, sai dai bai da yadda yaso dole yayi masa biyayya, shiyasa har ya iya daukarta a motarsa suka zo gidansu ta kwashi kayanta ta kara gaba, sai dai akwai wani sirri daya barwa zuciyarsa wanda yake ganin me bullewa ce a gareshi, dan in har ya bar Beena ta tafi tofa taci bulus.
Akan idonsu ta fita daga gidan sai a sannan ne Ummi ta furta.
A gayas Allah ya mayar miki sharrinki
Su Inna Hauwa da sauran ma'aikatan gidan suka amsa da Amin. Mujaheed shine ya tare mata napep ya ciro dubu daya ya mika masa yace ya kaita duk inda take so. Sai ya tsaya ya kama karfen Napep din ya kalli Beena yana wani shu'umin murmushi, itama ta bishi da kallo cike da harara, haka ya saki karfen mai napep ya jata suka wuce shi kuma ya koma cikin gida.
Tunda suka kama hanya mai napep ya kula da wata bakar jeep tana binsu a baya, hakan yasa ya kara gudunsa dan su shiga cikin mutane ba tare daya sanar da Beena ba.
Koda suka shiga cikin mutane still jeep din na binsu harya isa hotel din data ce ya sauke ta, ya ciro canjin dari biyu ya bata tace ya barshi sai ta dauki kayanta ta shige ciki, mutane sai kallonta suke ganin jikinta duk datti ga ciwuka a fuskarta duk ta kubbura, haka ta ratsa ta wuce ko a jikinta, mai napep kuwa tuni ya bace ya tafi yana mai sauke numfashi zuciyarsa cike da sake saken ko meyasa wannan bakar jeep ke binsu. Su kuma ganin ta shiga hotel din suka tsaya daga nesa suka yi parking dan zaman jiran fitowarta.
Tana isa ta bude dakinta ta shiga ta kulle, ta shiga toilet ta yi wanka ta gasa jikinta sosai kana ta fito ta dauro alwala, zama tayi kan dadduma ta gabatar da sallah a zaune dan gaba daya jikinta babu karfin da zata iya tsayuwa, ga bakar yunwa tana ji, haka ta jima a zaune tana rama sallolin da ake binta, kana ta kira room service suka kawo mata abinci tea ne mai kauri da soyayyar plantain da kwai. Bata bukatar abu mai mauyi saboda ba zata iya ci ba, tana kammalawa ta sanya doguwar jallabiyarta ta gyara kayanta ta kwashe na gana mazgo ta mayar cikin trolley ta ninke jakar tasa a ciki, wannan lu'u lu'un daya zama dutse data gani a cikin kayanta ta sanya a aljihun trolley da nufin in sun isa wani rafi zata jefa a ciki. Cikin sauri sauri ta kammala shirinta saboda tayi matukar damuwa da halin data jefa Sufyan, ba zata iya kwana a kano ba dole ta bi bayansa dan sanin a halin da yake ciki. Ta sanya dogon hijab dinta ta rufe fuskarta da nikaf nan take tayi badda kama, taja trolley dinta ta fito ta rufe musu daki kana ta isa reception ta basu key ta wuce. Tana isa bakin gate ta samu napep ya sauke wani mutum sai kawai ta tare shi ta shiga tace masa ya kai ta kano line suka wuce. Bangaren yaran Alh. Maina kuwa suna nan a inda suka tsaya suna jiran fitowarta wanda harta fito ta wuce basu sani ba.
******
Gidan Alh. Nasir
Suna zaune a falo gaba daya, suna zancen askin da Shukura ta yiwa kanta, Abbansu shi kadai ne ya goyi bayanta da cewar.
Karku takurawa Autata, in dai gashi ne nan da wasu lokacin zai kara fitowa.
Ai dama kai baka ganin laifinta
Cewar Mami. Mustapha yace.
Ai bari Mami zan fadawa saurayinta cewar kwaikwaido zai aura
To kayi ta fada mana
Tace tana turo baki, sai duk suka sanya dariya. Shigowarsu Saifu ne ya dakatar da hirarsu, nan da nan Abba ya shiga natsuwarsa ya daga jarida ya rufe fuskarsa ya soma karatun dole, dan yana mugun jin kunyar hada ido da Aisha. Suka shigo ciki suka zauna sai suka gaishesu duk suka amsa, Abba dai da jarida a fuskarsa ya amsa, itama Aisha taji dadin haka dan bata son ganin fuskarsa saboda irin tsanar data ke masa, Saifu ma tunda yazo gidan ya kuda da Abbansa ya kasa sake jiki da shi suyi hira, shiyasa bai damu da shiga lamarinsa ba iyaka suka gaisa ya wadatar, yace.
Abba, Mami mu mun fito zamu tafi
Au komawar taku yau ne ko?
Cewar Mami
Insha Allahu yau ne har mun sanya kaya a mota,
To Allah ya tsare ya kaiku lafiya
Cewar Abba, Mami tace.
Zaku biya gidansu Aisha ko?
Ai tun jiya munyi sallama dasu wucewa kawai za muyi.
To Allah ya tsare.
Suka amsa da Ameen, kana suka mike su Mami suka rakosu har wajen mota Amma banda Abba, Shukura kamar zata yi kuka saboda taso ta bisu amma ba hali, suka shiga mota suka suna dagawa su Mami hannu har suka fita daga gidan suka kama hanya.
Bangaren Beena ma ta samu mota drop sun kama hanya, tafiyarta kusan lokaci guda ne dana su Saifullah.
*Ko me zai faruuu...?*
#Lastfreepage
#Rahmace
______________
Dan samun cigaban wannan labari da zakinsa hade da warwara ku biya cikin fara shi mai sauki N200. Ku tura ta wannan account number din.
0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access (Diamond) Bank.
In an biya a turo screen short din alert ta WhatsApp chart a Numberta 07036993733. Ko MTN card N200 ta wannan number 07036993733.
Insha Allah zan yi Adding mutum zuwa group d'in littafin.