Maishaq Muhammad
Assalamu Alaikum...
Barkanmu Da Wannan Lokaci Tare Fatan Alkhairi Ga Daukacin Ma’abota Wannan Manhaja Ta Bakandamiya, Allah Yasa Mu Karashe Yunin Wannan Lokaci Cikin Aminchi!
Mu'azzam: Mama, kin san akwai wani yaro da shima ya ce wai Uncle ya bashi timeKeeper.
Ni: Ikon Allah, toh tare kuke kaɗa ƙaraurawar ko?
Mu'azzam: A'a shi ko sau ɗaya bai taɓa kaɗawa ba, duk sadda ya fito, sai ya taras har na kaɗa.
Ban ɗauki magana serious ba, sai da aka kwana biyu.
Mu'azzam: Mama, ina yaron nan da na ce maki, ya ce shima timekeeper ne?
Ni: Eh na gane shi.
Mu'azzam: Toh yanzu duk inda ya ganni sai ya taɗe ni na faɗi, ko kuma ya dake ni.
Na yi shiru ina nazari, daga bisani na gano haushin bai taɓa kaɗa ƙaraurawa ne ba ya sa yake mashi haka.
Ni: bari in faɗa maka dalilin da ya sa yake maka haka, haushin bai taɓa kaɗa ƙaraurawa ne ba, yana son kaɗawa, kai kuma ka ƙi bari. Idan Allah ya kai mu Monday, ka yi zamanka, ka bar shi da ƙaraurawar.
Monday na yi, Mu'azzam ya yi yadda na ce, bayan sun dawo na tambaye shi, yau wa ya kaɗa ƙaraurawa?
Ya ce "Yaron ne", na ce ya dake ka a yau ɗin?, ya ce "A'a".
Na ce, toh ka riƙa bashi dama yana kaɗawa shima, tunda har yana so, idan ka yi haka ba zai sake dukan ka ba. Hakan kuma aka yi, ko kallon banza bai sake yi mashi ba.
Darasi: Yayin da ka fahimci kun haɗu a cikin son abu ɗaya kai da wani, toh kada ka sanya zalama a cikin abun, idan da hali ku yi tarayya aciki. Idan ka yi haka zaku zauna lafiya.
Idan kuwa ka sanya zalama, toh akwai yiwuwar ka haɗu da fushin ɗayan, domin wasu basu da... less