Ko a lokacin da ba a shiga irin kuncin rayuwar da ake fuskanta a yanzu ba, akwai wadanda al’adarsu ce kullum su yi korafi.
A lokacin da aka tambaye su da lokacin da ba a tambaye su ba, kullum a cikin kuka suke. Wasu na yin haka ne saboda neman a ta...
Jamila Mustapha Hujjojin Cin Hanci Da Rashawa Akan Babachir Lawan
Wani rahotan bincike da aka mika ga kwamitin da shugaban kasa ya kafa akan binciken zarge zargen da ake yi wa sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawan ya nuna yadda sakataren ya bata hannun sa dumu... moreHujjojin Cin Hanci Da Rashawa Akan Babachir Lawan
Wani rahotan bincike da aka mika ga kwamitin da shugaban kasa ya kafa akan binciken zarge zargen da ake yi wa sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawan ya nuna yadda sakataren ya bata hannun sa dumu dumu da cin hanci da rashawa da keta dokokin kasa.
A karkashin shugabancin Lawan, hukumar farfado da yankin Arewa Maso Gabas da rikicin Boko Haram ya lalata PINE ya rikide ya koma wani nau’i da kasuwancin zalunci, inda kusan gaba daya kudaden da aka warewa yankin ke shiga aljihun wasu kamfanoni da shi Babachir Lawan.
Rahotan ya bayyana yadda Lawan ya baiwa wadannan kanfanoni kwangiloli duk da cewa ba su cacanta ba, da yadda kamfanonin suka raba kason su na kudaden kwangilar da shi.
Rahotan wanda majalisa ta aika wa kwamitin ya kunshi takardun banki da ke nuna yadda biliyoyin Nairori suka dinga shiga asusun Lawan da na kamfanin sa mai suna Rholavision Engineering LTD.
Bayan da suka karbi Kudaden kwangilar, akalla kamfanoni biyar ne suka biya kudaden da adadinsu ya kai Naira Miliyan 450 cikin asusun bankin Rholavision na Eco Bank mai lamba 182001809, wanda ya ke mallakin Babachir Lawan da kuma asusu mai dauke da sunan sa a bankin Diamond mai lamba 0003004417.
Banda wadannan, akwai wasu asusunan banki guda 13 da ke dauke da lambar BVN na Lawan.
Tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 29, 2016 da 20 ga watan Afrilun 2016, Kamfanin Josmon Technologies Limited ya aika Nairan miliyan 317 zuwa asusun bankin Rholavision bayan ya samu kwantiragin Naira Miliyan 530.6 na cire ciyayi a jahar Yobe daga hukumar ta PINE.
Haka kuma an baiwa kamfanin Rholavision din kan shi kwantiragi duk da cewa Babachir, wanda ya mallaki Kamfanin ma’aikacin gwamnati ne, kuma hakan ya sabawa dokokin Nijeriya.
Bugu da kari, a ranar 8 ga watan Agustan 2016, kamfanin JMT Global Technologies Ltd ya aika Naira miliyan 30 daga asusun bankin sa na Zenith Bank mai lamba 114357188 zuwa asusun bankin Rholavision.
Hakan ya faru ne bayan kamfanin ya samu kwantiragi guda 8 na gyare gyare a jahar adamawa akan Naira miliyan 199.4.
Kamfanin Messrs Adamawa Boreholes and Drilling Companies Ltd kuwa Naira miliyan 18 suka tura asusun Kamfanin Babachir bayan sun samu kwantiragin naira milyan 54.8 na gyaran ajujuwa guda 7 a Yeskule Girls Secondary School, danke Michika, a jahar Adamawa.
Kamfanin Barde Brothers Multi-Services Limited shi ma kwantiragin Naira miliyan 145 ya samu na gyaren ajujuwa, a ciki ya aika miliyan 71 zuwa asusun kamfanin Babachir.
Rahotan ya bayyana cewa akalla kanfanoni 39 ne suka samu kwantiragi kala kala daga hukumar ta PINE, amma a gaba daya kwantiragin da aka bayar an saba wani sashe na dokar kasa.
Yayin da wannan badakala ke wakana, fiye da yara dubu 400 ne a yankin arewa maso gabas ke fuskantar matsanciyar yunwa, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana.
A yanzu haka dai Babachir na fuskantar dakatarwa daga mukaminsa na sakataren gwamnatin tarayya yayin da kwamitin da aka kafa ke ci gaba da gudanar da bincike.
Kwamitin ya kunshi mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Babagana Mungonu da Ministan Shari’a Abubakar Malami.
Jamila Mustapha Iskokai Sun Kori Shugaban Kasar Brazil Daga Fadar Gwamnati
Kwanaki 10 kacal bayan shi da iyalinsa sun koma fadar gwamnatin
kasar, shugaban Brazil Michel Temer ya tattara ina sa ina sa ya koma ... moreIskokai Sun Kori Shugaban Kasar Brazil Daga Fadar Gwamnati
Kwanaki 10 kacal bayan shi da iyalinsa sun koma fadar gwamnatin
kasar, shugaban Brazil Michel Temer ya tattara ina sa ina sa ya koma
fadar mataimakin shugaban kasa.
Ya bayyana dalilinsa da cewa akwai iskokai mara sa kyau a gidan. Ya
ce shi da matar sa da dan sa mai shekaru 7 ba sa iya barci da daddare
saboda wasu irin motsi motsi da suke ji, kuma tun da suka shiga fadar
gwamnatin, jikinsu bai gamsu da shi ba.
Fadar shugaban kasar wanda ake kira Alvadora Palace dai katafaren gida ne wanda ya kunshi abubuwan more rayuwa da dama.
Sai dai shugaban ya ce shi da iyalinsa sun fi sakewa a fadar
mataimakin shugaban kasar mai suna Jaburu Palace wanda ya fi kankanta.
Toh dama dai shugaban shi ne mataimaki kafin majalisar kasar ta tsige
tsohuwar shugaban kasar, Dilma Roussef a kwanan nan, kuma iyalinsa sun
riga sun saba da fadar ta Jaburu. less
Jamila Mustapha Tsohon Shugaban Hukumar NNPC, Adrew Yakubu Ya Kai EFCC Kotu
Andrew Yakubu, tsohon shugaban kamfanin mai na (NNPC) ya maka hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) a gaban kotu, in da ya ke bukatar biyan sa diyyar kudi kimanin... moreTsohon Shugaban Hukumar NNPC, Adrew Yakubu Ya Kai EFCC Kotu
Andrew Yakubu, tsohon shugaban kamfanin mai na (NNPC) ya maka hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) a gaban kotu, in da ya ke bukatar biyan sa diyyar kudi kimanin naira N1,000,000,000, a dalilin cewa hukumar ta ci zarafinsa.
Ya na kuma bukatar kotu ta hana hukumar ci gaba da gudanar da duk wani bincike akan sa.
Yakubu ya gabatar da karar ne a wata babbar kotu da ke Abuja, wadda ta sanya ranar 9 ga watan nan domin sauraron karar. less
March 8, 2017
Jamila Mustapha Mukaddashin Shugaban Kasa ‘Farfesa Yemi Osibanjo’ Ya Cika Shekaru 60 A Duniya
A yau ne Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya cika shekaru 60 a Duniya.
Yan Nijeriya da dama sun nuna farin cikin su na zagayowar ranar haihuwar sa a yayin... moreMukaddashin Shugaban Kasa ‘Farfesa Yemi Osibanjo’ Ya Cika Shekaru 60 A Duniya
A yau ne Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya cika shekaru 60 a Duniya.
Yan Nijeriya da dama sun nuna farin cikin su na zagayowar ranar haihuwar sa a yayin da ya samu sakonni masu dunbun yawa ta shafin sa na twitter daga ‘yan Nijeriya tare da yi masa addu’ar Allah ya taya shi rikon kwaryan da yakeyi tun bayan tafiyar shugaba Buhari a tsakiyar watan Junairu
March 8, 2017
Jamila Mustapha Bayan Shekaru 17, An Kaddamar Da Sabuwar Samfurin Nokia 3310
Wayar Nokia 3310 waya ce da ta karbu a wajen mutane sosai a shekarun baya a sakamakon karkon da da kuma rike... moreBayan Shekaru 17, An Kaddamar Da Sabuwar Samfurin Nokia 3310
Wayar Nokia 3310 waya ce da ta karbu a wajen mutane sosai a shekarun baya a sakamakon karkon da da kuma rike caji.
Wayar wadda aka kaddamar a karon farko a shekarar 2000 yanzu haka za ta dawo kasuwanni bayan da aka yi mata kwaskwarima.
An kaddamar da wayar ne a babban taron wayoyi na duniya (Mobile World Congress) da aka gudanar a garin Barcelona a ranar Lahadin da ta gabata.
Ita dai sabuwar samfurin wayar Nokia 3310 an kera ta ne ta yadda za ta iya kaiwa kwanaki talatin kafin cajinta ya ‘kare, kuma za ta iya amfani da yanar gizo, sai dai ba komai mutum zai iya yi da ita ba idan akayi la’akari da sabbin wayoyin zamani da ake amfani da su.
Za a sayar da sabuwar Nokia 3310 akan Euro 49, wanda ake kyautata tsammanin mutane za su iya sayen wayar su yi amfani da ita a matsayin waya ta biyu.
Za a fara sayar da wayar a Nahiyar Turai kafin watan Yunin wannan shekarar. less
Wata rana an Tambayi Annabi {S.A.W} cewa mene ne ''HAKURI''?
Sai Annabi (S.A.W)... moreMENENE HAKURI?
Wata rana an Tambayi Annabi {S.A.W} cewa mene ne ''HAKURI''?
Sai Annabi (S.A.W) yace:
(1) Juriya kan bakin ciki.
(2) Yin raha ga makiyi.
(3) Barin mummunan zato.
(4) Cire girman kai.
(5) Karbar uzuri a gurin da kasan babu
gaskiya.
(6) Hakuri a inda kake da karfin
ramawa.
(7) Yafiya ga wanda ya cuce ka.
(8) Kyautatawa ga wanda ya kyautata maka.