Abdullahi Arzika Jaredi
Haihuwar jinjirin watan Jumada Sani, 1442.
BismilLāhir Rahmānir Rahīm
Wal qamara qaddarnāhu manāzila hattā āda kal urjūnil qadīm.
SadaqalLāhul Azīm.
Haihuwar jinjirin watan Jumada Sani 1442 zai auku ne karfe 6:00am agogon Nigeria a safiyar Laraba 13 ga January, 2021.
Kusan abinda ya faru wata 2 baya a haihuwar jinjirin watan Rabi'us Sani, 1442 shine ne zai kuma aukuwa. Haihuwar kusan lokaci daya ne don qarfe 6:08am na safe agogon Nigeria aka haifi jinjirin watan Rabi'us Sani, 1442.
A yau Laraba 13 ga January, 2021 ita ce 29 ga Jumuda Ula, 1442 a Nigeria.
Zuwa faduwar rana sannan jinjirin watan ya yi kusan awa 12 da haihuwa a Nigeria.
Saboda haka awa 12 da haihuwa, jinjirin watan ba zai ganu da idon dan adam ko da na'urar hangen nesa a Nigeria ba amma duk da haka za'a fita duban watan don bin qa'idar da shari'ar musulunci ta ajiye cewar duk 29 ga wata a fita duban wata.
Idan Allah Ya nufa ba'a samu rahoton ganin wata a Nigeria ba to Mai Alfarma Sultan zai zartar da kashegari Alhamis 14 ga January, 2021 ya zama 30 ga watan Jumada Ula, 1442 sai Juma'a 15 ga January, 2021 ya zama 1 ga watan Jumada Sani, 1442.
Su kuma Qasa Mai Tsarki ta Saudi Arabia kowa ya san ba sa bin qa'ida ta shari'ar Musulunci wajen duban wata suna bin lissafin kalandar Ummul Qura ne wadda ta ce idan haihuwar jinjirin wata ya auku kafin faduwar rana sannan kuma rana ta riga wata faduwa to kashegari kawai ita ce 1 ga wata. Shi isa watam da ya wuce a post dina na kamawar jinjirin watan Jumada Ula, 1442 na ce za su birkita mana lissafi a Jumada Sani.
A Saudi Arabia haihuwar jinjirin watan Jumada Sani 1442 zai auku ne karfe 8:00am agogon Saudia a safiyar Laraba 13 ga January, 2021.
Suma yau ne 29 ga Jumada Ula, 1442. Lissafinsu daidai da na Nigeria ne. Yau da Maghriba a sannan jinjirin watan yayi kusan awa 10 kenan da haihuwa a Saudia.
Jinjirin watan kuma zai fadi ne bayan faduwar rana da minti 17 a garin Makkatul Mukarramah.
Awa 12 da haihuwa ma wata ba zai ganu a Nigeria ba balle Saudia masu awa 10 amma tunda an cika qa'idar lissafin kalandar Ummul qura na rana ta riga wata faduwa, to automatically gobe
Alhamis 14 ga January, 2021 ita ce 1 ga watan Jumada Sani, 1442 a Saudi Arabia.
Nigeria kuma sai mun bi qa'idar shariar musulunci mun jíra rahoton ganin wata idan an gani yau din kuma Fadar Mai Alfarma Sultan ta tabbatar da ganin muma gobe sai ya zama 1 ga watan Jumada Sani amma dai da kamar wuya.
Watan Rajab,1442 idan Allah Ya kaimu lissafin zai kuma daidaita tsakanin masu bin shari'a na duban wata da masu bin lissafin kalanda.
Allah kuma Ya sa Saudia su daina amfani da lissafin kalandar Ummul Qura wanda shima da kamar wuya amma Wallahi da duk wani rudani da sabani na ganin wata a duniya an daina.
Azumin bana ga dukkan alamu Saudia za su rigamu dauka amma Qaramar Sallah rana daya za ayi ta kusan ko ina a duniya.
Babbar Sallah, 1442 ma Dole a samu sabani da rudani muddin Saudia lissafin kalanda za su bi domin ranar da za su hau Arfah mu kuma sai kashegari ce za ta zama 9 ga watan Zulhajji a Nigeria. Dole sai Mai Alfarma Sultan ya sanya mun qara kwana 1 a lissafinmu na Zulhajji, 1442 domin samun daidaito da ranar Arfah.
Allah Ya sa mu dace
*
**
***
Abdullahi Hamza Bayero