Jibrin Adamu Rano
Na yaba da ƙoƙarin ki matuƙa 'yar'uwa. Don tun da muka fara muhawarar nan ban haɗu da wacce ta yi dagiyar ki ba. Muna yi miki fatan alkhairi da nasarori a rayuwa.
A Nijeriya, radiyo ta samu a shekarar 1933 da wani fasali na yada ayyukan da manufofin Turawan Mulki. 'RDS' ko 'Radio Diffusion Service' shi ne farkon abinda ya samar da gidajen radiyo... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Gabatarwa.
A Nijeriya, radiyo ta samu a shekarar 1933 da wani fasali na yada ayyukan da manufofin Turawan Mulki. 'RDS' ko 'Radio Diffusion Service' shi ne farkon abinda ya samar da gidajen radiyo sama da 200 yau a Nijeriya.
Zan... moreGabatarwa.
A Nijeriya, radiyo ta samu a shekarar 1933 da wani fasali na yada ayyukan da manufofin Turawan Mulki. 'RDS' ko 'Radio Diffusion Service' shi ne farkon abinda ya samar da gidajen radiyo sama da 200 yau a Nijeriya.
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani da radiyo ne a Nijeriya. Yayin da... moreHujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani da radiyo ne a Nijeriya. Yayin da gwamnati ta zo da wasu sababbin tsare-tsarenta wadanda take son su karade ko'ina, idan ta yi amfani da gidajen radiyo to mutane bakwai cikin goma da ke bibiyar labarai za su riski wannan sabon tsari, idan... less
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo.... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo. Misali a gidajen radiyo ne ake... moreHujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo. Misali a gidajen radiyo ne ake samun wasannin kwaikwayo wadanda kacokan gwamnati ce ke daukar nauyinsa domin isar da wani sako na musamman wanda zai amfani al'umma, kamar wasanni domin kawo karshen cutar foliyo ko tarin fuka ko zazzabin maleriya, uwa-uba kuma kariya daga kamuwa da... less
Jibrin Adamu RanoNa fahimci kin tsani talabijin, da alamu shi ya sa ba kya kallonta. Shi kuwa hukunci ba a yankewa bisa ra'ayi, abin da ka gani kake iya ɗorarwa.
WASAN KWAIKWAYO.
Ai daga sunan kawai kin san cikar fahimtarsa sai an kalla a talabijin, ba wai ji a rediyo... moreNa fahimci kin tsani talabijin, da alamu shi ya sa ba kya kallonta. Shi kuwa hukunci ba a yankewa bisa ra'ayi, abin da ka gani kake iya ɗorarwa.
WASAN KWAIKWAYO.
Ai daga sunan kawai kin san cikar fahimtarsa sai an kalla a talabijin, ba wai ji a rediyo ba. Wannan shi ya sa ita kanta gwamnatin a talabijin take ƙarfafa saka shi, don a can ne za a faɗaku ba rediyo ba.
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen yin shirye-shirye na fadakarwa da... moreHujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen yin shirye-shirye na fadakarwa da wayar da kai ga al'umma domin su fahimci illar da ke cikin toshe magudanan ruwa. A duba fa, gwamnati ba ta yi amfani da sojoji ko 'yan sanda ko wata hotiho wai ita talbijin ba, amma... less
Jibrin Adamu RanoKun bar bugun jaki, kun ɓige da bugun taiki. Ni fa abu ɗaya na ce, in da a ce gwamnati bata yi amfani da talabijin wajen nuna ainahin abin da ya faru ba, da babu wanda iya jin maganganun da kunne zai saka ya yarda kai tsaye.
Bayan na ga sanarwar a... moreKun bar bugun jaki, kun ɓige da bugun taiki. Ni fa abu ɗaya na ce, in da a ce gwamnati bata yi amfani da talabijin wajen nuna ainahin abin da ya faru ba, da babu wanda iya jin maganganun da kunne zai saka ya yarda kai tsaye.
Bayan na ga sanarwar a talabijin na ji babu daɗi sosai, har da safe nake ba wa abokaina labarin abin da na gani gwanin ban tausayi. To kamar yadda na faɗa wa abokaina, haka duk masu talabijin za su faɗa wa abokanan su na karkara da kuke da'awar cewa ba su da talabijin ko lantarkin da za su gani. less
Jibrin Adamu RanoNi fa magana ɗaya na yi, na ce muku na san lokacin da wannan matsalar ta faru.
Ban manta ba ina gida a zaune ina kallon talabijin na ga ana ta nuna irin ta'adin da ruwa ya yi musu.
Idan a rediyo za a faɗa, wa ye ma zai gane ainahin buƙatar taimakon da... moreNi fa magana ɗaya na yi, na ce muku na san lokacin da wannan matsalar ta faru.
Ban manta ba ina gida a zaune ina kallon talabijin na ga ana ta nuna irin ta'adin da ruwa ya yi musu.
Idan a rediyo za a faɗa, wa ye ma zai gane ainahin buƙatar taimakon da suke yi? Ai gani a talabijin ne ya jawo aka tausaya musu sosai suka samu wannan gudummawar.
Washegari da safe kuwa cikin alhini nake labarta wa abokaina irin asarar da waɗanda ambaliyar ta shaf. To idan ba ku sani ba ku sani, kamar yadda na ba wa abokaina labari, haka duk mai talabijin ɗin da ya kalla ya gamsu da gaske ne zai faɗa wa wanda bai kalla ba har zuwa kan 'yan karkarar da kuka ta haƙilon ba su da talabijin. less
Ai yanzu ci gaba ya zo, babu wani gidan talabijin da ba su da manhaja ta waya, wacce za ka sauke ka riƙa kallon labaransu. Ni ina da manhajar Arewa 24 wanda da shi na kalli Maryam Umar taku a tattaunawar da aka yi da ita ta ZOOM... moreAmrah (Takwarar 'ya ta)
Ai yanzu ci gaba ya zo, babu wani gidan talabijin da ba su da manhaja ta waya, wacce za ka sauke ka riƙa kallon labaransu. Ni ina da manhajar Arewa 24 wanda da shi na kalli Maryam Umar taku a tattaunawar da aka yi da ita ta ZOOM a arewa.
Don haka batun wai a ɗauke wuta kana kallo duk bai taso ba, ki dai sake wata makamar, wannan makamar ta ki ganyen iska kawai kika riƙe, kina sake masa nauyi faɗowa za ki yi.
Maryamerh AbdulKana yi kaman baka san tattalin arzikin najeriya ta yi qasa ba. Wa yake da datar kalle kalle a waya bayan ga sauki? Ana ta abinci ko ana ta data? Wai ni ko malam Jibrilla ko dai Gwamnatin nan ta masu kudi ne kawai da kake ta nanata telbijin, waya da... moreKana yi kaman baka san tattalin arzikin najeriya ta yi qasa ba. Wa yake da datar kalle kalle a waya bayan ga sauki? Ana ta abinci ko ana ta data? Wai ni ko malam Jibrilla ko dai Gwamnatin nan ta masu kudi ne kawai da kake ta nanata telbijin, waya da abubuwan da ba kan gado.
Da kake cewa masu talbijin ne suka gani kuma suka isar da sako ko suka bada labari, wannan magana taka karya ce, sanin kanka ne masu bada labarin da suka ji a gidan rediyo sun rinjayi masu badawa don sun gani a telbijin. Yoo yawanci masu kallon talbijin ‘yan birni ne da hira tsakaninsu ke musu wahala, kowa da wayarsa hannu ko an shiga kalle kallen televista. Amma mu mutanenmu kullum cikin zumunci da hira ake yi, in ba a bada labaran rediyo ba ma ai ka san zaman... less
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Rufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata kafar isar da sakon gwamnati wacce ta shallake radiyo, ko ma wacce kafa ce mu zube ta a faifai mu gani idan... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Rufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata kafar isar da sakon gwamnati wacce ta shallake radiyo, ko ma wacce kafa ce mu zube ta a faifai mu gani idan akwai riba. Ba domin hujjojina sun... moreRufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata...
Jibrin Adamu Rano
Abu na gaba da nake so ku kai hankalinku kai. A cikin ku ai akwai wacce ta samu nasarar zama zakarar BBC Hikayata ta bana. Shin ta murya Maryam ta zagaya duniya kowa ya gan ta ko kuwa ta bidiyo na talabijin da wayoyi?
Maryamerh AbdulArewa dai arewa dai, arewa kuma me alaqanta da sakon Gwamnati? Duk kallonka da arewa, yaushe ka ga sun sako sakon Gwamnati? Tambaya ta Allah da annabi kenan. Da kake maganar cancer, kafin cancer ta kama mutum biyu, ciwon ido ta kama mutum goma. Me zaka... moreArewa dai arewa dai, arewa kuma me alaqanta da sakon Gwamnati? Duk kallonka da arewa, yaushe ka ga sun sako sakon Gwamnati? Tambaya ta Allah da annabi kenan. Da kake maganar cancer, kafin cancer ta kama mutum biyu, ciwon ido ta kama mutum goma. Me zaka ce da wannan? Ko kwana zamu yi a nan, ina tabbatar maka bazan gaji da baka hujja kan hujja akan rediyo ta fi talbijin tura sakon Gwamnati ba, sannan ba zan...
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu;
Idan direbobi suka sheka da gudu kai ka ce da iska suke tsere! Ci-da-zuci yana d'aukar su a ga suna fera wuta tare da daukar kasadar kutsawa hannun da ba nasu ba (Overtaking), su a dole sai sun isa inda... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu;
Idan direbobi suka sheka da gudu kai ka ce da iska suke tsere! Ci-da-zuci yana d'aukar su a ga suna fera wuta tare da daukar kasadar kutsawa hannun da ba nasu ba (Overtaking), su a dole sai sun isa inda suka yi wa tsinke da wuri. A... moreHujja Ta Biyu;
Idan direbobi suka sheka da gudu kai ka ce da iska suke tsere! Ci-da-zuci yana d'aukar su a ga suna fera wuta tare da daukar kasadar kutsawa hannun da ba nasu ba (Overtaking), su a dole sai sun isa inda suka yi wa tsinke da wuri. A irin wannan gudun kuskure kadan za a yi shi... less
Rabiatu SK MashiSosai ma kuwa, wani direba da irin hakan ta taba faruwa dashi, garin saurin yayi accident mota tayi rugu-rugu shi dinma yasha jinya, ke kince bazai kara yarda yayi sauri ba balanta na tuqin ganganci, anma wallahi har yanzu tuqi yake da sauri kamar zai... moreSosai ma kuwa, wani direba da irin hakan ta taba faruwa dashi, garin saurin yayi accident mota tayi rugu-rugu shi dinma yasha jinya, ke kince bazai kara yarda yayi sauri ba balanta na tuqin ganganci, anma wallahi har yanzu tuqi yake da sauri kamar zai tashi sama, sannan ba ruwanshi da bin dokokin hanya, toh ina laifin gwamnati anan da ba itace zata mishi tuqin ba?
Maryamerh AbdulHanzari fa, idan da Gwamnati ne mai laifi da a garin Abuja baza a taba hatsari ba kenan. Amma kulli yaumin sai an yi hatsari, kuma kaf najeria babu inda ake da titina masu kyau, street light, tsagar hanyan nan fari, kai komai na tuki Gwamnati ta sa. Har... moreHanzari fa, idan da Gwamnati ne mai laifi da a garin Abuja baza a taba hatsari ba kenan. Amma kulli yaumin sai an yi hatsari, kuma kaf najeria babu inda ake da titina masu kyau, street light, tsagar hanyan nan fari, kai komai na tuki Gwamnati ta sa. Har yanzu Gwamnati ko? Don an renata komai sa a makala mata. Direbobi ne masu laifi babu shakka
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Direbobin zamani babu ruwansu da bincikar bukatun ababen hawansu, da sun tashi da safe sun cika cikinsu, sai su fita su shige gidan gaba su jefa wa mota makulli su garkama giya. Wannan halin ko-in-kula da... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Direbobin zamani babu ruwansu da bincikar bukatun ababen hawansu, da sun tashi da safe sun cika cikinsu, sai su fita su shige gidan gaba su jefa wa mota makulli su garkama giya. Wannan halin ko-in-kula da sakaci na direbobi suna janyo... moreHujja Ta Farko:
Direbobin zamani babu ruwansu da bincikar bukatun ababen hawansu, da sun tashi da safe sun cika cikinsu, sai su fita su shige gidan gaba su jefa wa mota makulli su garkama giya. Wannan halin ko-in-kula da sakaci na direbobi suna janyo... less
Maryamerh Abdul
Haka fa, daidaikun direbobi ne zaki ga da safe suna duba motar nasu, wanda wurin ruwa ya riga ya lalace ki ga an fara qiqarin qara masa ruwa. Abun fa ba dadi
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Direba! Ga ka mutum amma ka rike kambun mutuwa (sitiyari).
Direba! Kana gudu bisa iska (tayoyi), makamashin wuta gefenka (fetur).
Kara wuta direba, Aljanna ta mai rabo... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Direba! Ga ka mutum amma ka rike kambun mutuwa (sitiyari).
Direba! Kana gudu bisa iska (tayoyi), makamashin wuta gefenka (fetur).
Kara wuta direba, Aljanna ta mai rabo ce!
Direba kenan... Me zai hana wadannan maganganu su hau kansa har ya ji kamar shi... moreDireba! Ga ka mutum amma ka rike kambun mutuwa (sitiyari).
Direba! Kana gudu bisa iska (tayoyi), makamashin wuta gefenka (fetur).
Kara wuta direba, Aljanna ta mai rabo ce!
Direba kenan... Me zai hana wadannan maganganu su hau kansa har ya ji kamar shi kadai ne bisa hanya a yayin da yake famfala gudu kamar wanda ya hau Dokin Iska Danfilinge?!
A yi mini afuwa na fara da sambatu ba tare da gaisuwa ba. Tsananin mamaki ne ya cika ni, jin har akwai masu tunanin wai laifin Gwamnati ne ke kawo yawaitar hatsari, ana neman a bar jaki a koma dukan taiki!
Masu girma alkalai, jagorori, abokan karafkiya, masu bibiya, ina nema mana amincin Allah Madaukakin Sarki. Sunana Amrah, daga kungiyar Nagarta. A karo na biyu na zo domin wakiltar kungiyata.
Tabbas direbobi ke da laifi a hatsarin da ke afkuwa a... less
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
Cikar kwari da ake yi wa motoci da fasinja ko kayan fasinjoji yana janyo a sami mummunan hatsari. Mota ce, watakil ma Baturen da ya yi ta kawai saboda a je cefane a dawo ne, amma sai a cusa mutane har a but,... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
Cikar kwari da ake yi wa motoci da fasinja ko kayan fasinjoji yana janyo a sami mummunan hatsari. Mota ce, watakil ma Baturen da ya yi ta kawai saboda a je cefane a dawo ne, amma sai a cusa mutane har a but, kafafu na reto, cikin motar kuwa... moreHujja Ta Uku:
Cikar kwari da ake yi wa motoci da fasinja ko kayan fasinjoji yana janyo a sami mummunan hatsari. Mota ce, watakil ma Baturen da ya yi ta kawai saboda a je cefane a dawo ne, amma sai a cusa mutane har a but, kafafu na reto, cikin motar kuwa an dora mutane wani... less
Rabiatu SK Mashi
Da naga wannan hujjar sai da nayi dariya, saboda tunawa da nayi da wani direba shima mai irin wannan zalamar daya taba tsayawa daukarmu😆
Rabiatu SK MashiMota cike da mutane, an maida kaya can sama an saka mutane a but, maza ne su hudu cikin but dinma wai ya tsaya d’aukarmu, ina zaku? Dakyar na iya fada mishi ina riqe dariyata, yana jin inda zamu yace to ku taho mu tafi, wallahi saboda dariyar data... moreMota cike da mutane, an maida kaya can sama an saka mutane a but, maza ne su hudu cikin but dinma wai ya tsaya d’aukarmu, ina zaku? Dakyar na iya fada mishi ina riqe dariyata, yana jin inda zamu yace to ku taho mu tafi, wallahi saboda dariyar data kamamu muka ma kasa haqura muga inda zai sakamu cikin wannan mota😆😆 daga cikinta har but mutane, ko saman ma cike da kaya, yaga yanda muke dariya kawai yaja motarshi ya qara gaba🤣🤣🤣.
Af! Ashe fa bakin abinda aka iyakance na lokaci yana tunkarowa, sai dai a yadda na shawo gangara da za a kyale ni to hujjoji yanzu ma aka fara; me aka yi da maza? In ji karya! Kodayake hakan ma na tabbata duk wanda ya karanta zai...
Maryam Umar → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
'A hungry man is an angry man.' A Hausance kuma sai mu ce zafin rai da saurin jin haushi sai mai yunwa (talaka kenan). Rashin fahimta kadan ya hau haushi, bare kuma ya hadu da mutumin da bai san me... moreMaryam Umar → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
'A hungry man is an angry man.' A Hausance kuma sai mu ce zafin rai da saurin jin haushi sai mai yunwa (talaka kenan). Rashin fahimta kadan ya hau haushi, bare kuma ya hadu da mutumin da bai san me duniya take ciki ba (saurayi).... moreHujja Ta Uku:
'A hungry man is an angry man.' A Hausance kuma sai mu ce zafin rai da saurin jin haushi sai mai yunwa (talaka kenan). Rashin fahimta kadan ya hau haushi, bare kuma ya hadu da mutumin da bai san me duniya take ciki ba (saurayi). Shi saurayi a kullum yana jin ba ke ba ce autar mata don... less
Pharty BBAi wallahi saurayi marar kwaɓo ya fara miki bala'i daga cewa megida kawo kuɗi za'a saya kaza sai kinji kin gwammace baki tambaya ba ko ba kiyi auren ba.\nTo me amfanin haka aure kullum cike da dana sani.\nYi aure in da za kiji dadi a lallaɓa ki ana... moreAi wallahi saurayi marar kwaɓo ya fara miki bala'i daga cewa megida kawo kuɗi za'a saya kaza sai kinji kin gwammace baki tambaya ba ko ba kiyi auren ba.\nTo me amfanin haka aure kullum cike da dana sani.\nYi aure in da za kiji dadi a lallaɓa ki ana tambayar My Dear menene kike buƙata ba sai ke kin buɗe baki kin tambaya ba wanda za'a biyoki da faɗa wani lokaci da zagin cin mutuncin.
Maryam Umar → MARUBUTA:
Kammalawa:
Kudi masu mayar da kurma mai ji su mayar da makaho mai gani. Ke ba iya nan ba sukan mayar da tsoho yaro iya adadin shekarun da kike son ganinsa. Mai kudi, iccen kabari kowa ka hau ba zai taso ba.
Wane makahon... moreMaryam Umar → MARUBUTA:
Kammalawa:
Kudi masu mayar da kurma mai ji su mayar da makaho mai gani. Ke ba iya nan ba sukan mayar da tsoho yaro iya adadin shekarun da kike son ganinsa. Mai kudi, iccen kabari kowa ka hau ba zai taso ba.
Wane makahon tunanin zai sa ki zabi bakin ciki... moreKammalawa:
Kudi masu mayar da kurma mai ji su mayar da makaho mai gani....
Pharty BB
Tabbas maganganun ki dutse ne. Mun gamsu mun yarda mun amince auren tsoho mai kuɗi yafi marar saurayi marar kwaɓo.\n\nYo Annabi ma ya lissafo cikin abubuwan da ake dubawa in za'a yi aure ciki har da ARZIKI. To yar uwa ina zaki da kayan taƙaici (Talauci).
Maryam Umar → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Duk abinda babba ya hango, yaro ko ya hau dutsen dala ba zai hango ba. Kamala da hangen nesa na dattijo ko kusa ba za a hada da na saurayi ba, balle an hada da kudi maganin zaman duniya. Yarinta da karkataccen... moreMaryam Umar → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Duk abinda babba ya hango, yaro ko ya hau dutsen dala ba zai hango ba. Kamala da hangen nesa na dattijo ko kusa ba za a hada da na saurayi ba, balle an hada da kudi maganin zaman duniya. Yarinta da karkataccen ra’ayi irin na... moreHujja Ta Biyu:
Duk abinda babba ya hango, yaro ko ya hau dutsen dala ba zai hango ba. Kamala da hangen nesa na dattijo ko kusa ba za a hada da na saurayi ba, balle an hada da kudi maganin zaman duniya. Yarinta da karkataccen ra’ayi irin na ‘ya mace idan ta auri dattijo, uzuri yake mata, ba kamar saurayi da ke jin kanshi na yawo sararin samaniya ba. Tafiyar biri a rairai yaro ba zai iya ba!
Shirme,... less
Pharty BBDa kin auri saurayi marar kwabo an ci wata ɗaya da aure Gara ya ƙare sai ki ji an fara jin tace nace. Daga nan babu ke babu kwanciyar hankali balle jin daɗin aure ko cin daɗi. Tuni kina yarinya zaki fara kwamatsewa ki tsofe.\n\nAmma mai akwai fa ai... moreDa kin auri saurayi marar kwabo an ci wata ɗaya da aure Gara ya ƙare sai ki ji an fara jin tace nace. Daga nan babu ke babu kwanciyar hankali balle jin daɗin aure ko cin daɗi. Tuni kina yarinya zaki fara kwamatsewa ki tsofe.\n\nAmma mai akwai fa ai ke da babu kunyi hannun riga domin tun kafin Gara ya ƙare ya sayo ya jibga miki, babu batun maigida babu abu kaza babu kaza. Sai kin zaɓa kin dafa ko a dafa a kawo miki.
Maryam Umar → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Tabbas kika auri tsoho kin gama samun kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa. Tazarar da ke tsakanin talaka da mai kudi kamar sararin samaniya da k'asa ne. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da k'asa. Ki ci... moreMaryam Umar → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Tabbas kika auri tsoho kin gama samun kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa. Tazarar da ke tsakanin talaka da mai kudi kamar sararin samaniya da k'asa ne. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da k'asa. Ki ci ki kwanta a bi ki da tambayar hajiya me... moreHujja Ta Farko:
Tabbas kika auri tsoho kin gama samun kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa. Tazarar da ke tsakanin talaka da mai kudi kamar sararin samaniya da k'asa ne. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da k'asa. Ki ci ki kwanta a bi ki da tambayar hajiya me za a dafa? Da Dare Alhaji ya shigo da kazarsa da madara mai sanyi, safiya ta waye ya shinshina miki naira a hanci tare da tambayar tikitin wace kasa kike so? A bata miki rai ki kalli gabanki ga gwal halaliyanki, kudu fankacecen... less
Pharty BB
To Annabi yace a guji talauci wa zai zo talauci?\n\nKo kun manta da wannan addu'a Allahumma inni as'aluka ilman nafi'a wa ruzƙhan ɗayyiba.\nCewa yayi kudi mai amfani ba talauci ba.\nTo taya mutum zai so talauci abinda yake hana rayuwar ɗan Adam cigaba.
Maryam Umar → MARUBUTA:
Gabatarwa:
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai. Masu girma alkalai, jagorori, abokan fafatawa, masu bibiya, ina nema mana amincin Allah. Sunana Maryam Umar wakiliyar Nagarta writers.
Hakika auren mai kudi dattijo ya fi... moreMaryam Umar → MARUBUTA:
Gabatarwa:
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai. Masu girma alkalai, jagorori, abokan fafatawa, masu bibiya, ina nema mana amincin Allah. Sunana Maryam Umar wakiliyar Nagarta writers.
Hakika auren mai kudi dattijo ya fi dacewa da mace fiye da auren... moreGabatarwa:
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai. Masu girma alkalai, jagorori, abokan fafatawa, masu bibiya, ina nema mana amincin Allah. Sunana Maryam Umar wakiliyar Nagarta writers.
Hakika auren mai kudi dattijo ya fi dacewa da mace fiye da auren matashi mara kwabo.
Aure!
Wannan kalma ce da takan girgiza kowanne dan Adam ta tsirar da wani tsiro a can tsakiyar tsokar da ke tsakanin kirji.
Wasu kan fada idonsu da kwalli(arziki) wasu kuwa rashin sa'a ke... less
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
KAMMALAWA:
Taƙaitattun kalmomi sun yi ƙaranci wajen wanzar da tarin hujjojin da ke gare ni, sai dai bin ƙa'ida da tsayawa a tsakanin layukan da aka shata min ya sa ni dakatawa a nan.
Hadiza Abdullahi Aliyu
Mun gamsu kam,satar amsa laifin dalibai ne,rashin fahimtar darasi ba zai ba dalibi lasisin ya saci amsa ba,yawan faduwar dalibai a jarabawa shi ke nuna rashin fahimtar darasin dalibai ba wai satar amsa ba.
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Wasu dalibai suna ganin cewa maki a takarda shi ne mafi sahihancin ilmin da aka fi bukata; wato dai daliban halarar 'Wanda ya ci, shi ya iya!' Sai su dogara da satar jarabawa a matsayin wata... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Wasu dalibai suna ganin cewa maki a takarda shi ne mafi sahihancin ilmin da aka fi bukata; wato dai daliban halarar 'Wanda ya ci, shi ya iya!' Sai su dogara da satar jarabawa a matsayin wata madafa wadda za ta sa a gane lallai... moreHujja Ta Biyu:
Wasu dalibai suna ganin cewa maki a takarda shi ne mafi sahihancin ilmin da aka fi bukata; wato dai daliban halarar 'Wanda ya ci, shi ya iya!' Sai su dogara da satar jarabawa a matsayin wata madafa wadda za ta sa a gane lallai sun iya. Zuciyar irin wadannan daliban ta kekashe ba ta jin fus! Su dai koyaushe suna jiran lokacin jarabawa ya yi su tanadi 'yan takardu a yi 'yan-mitsi-mitsi, wai maganin mantuwa. Dalibin da ya auri wannan dabi'a ba zai... less
Hadiza Abdullahi AliyuRabi da yawansu fa masu wannan tunani basa ko tsayawa su koyi darasi basa attending lectures sai lokacin jarabawa su je su siyo takardun karatu ko su ari na abokan karatunsu suyi photocopy kuma fa ba wai dan su karanta ba,dan ko sun karanta ba zasu... moreRabi da yawansu fa masu wannan tunani basa ko tsayawa su koyi darasi basa attending lectures sai lokacin jarabawa su je su siyo takardun karatu ko su ari na abokan karatunsu suyi photocopy kuma fa ba wai dan su karanta ba,dan ko sun karanta ba zasu fahimta ba,kuma sun ma dauki karatun a b'ata lokaci gwara kawai su shiga da takardun su kwasa ,ko kuma su maqalewa wayanda suka san sun karantu domin su kwasa daga wurinsu.
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
Rashin yarda da kai da gudun a ce an muzanta na taka muhimmiyar rawa wurin yawaitar satar amsa. Malamin da zai koyar, ya yi gwaji har sau biyu (C.A) sannan ya yi maimaicin karatu (Revision), ta ya za a dora... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
Rashin yarda da kai da gudun a ce an muzanta na taka muhimmiyar rawa wurin yawaitar satar amsa. Malamin da zai koyar, ya yi gwaji har sau biyu (C.A) sannan ya yi maimaicin karatu (Revision), ta ya za a dora laifin satar amsa a kanshi?... moreHujja Ta Uku:
Rashin yarda da kai da gudun a...
Oum NassMalama wannan musalin naki ba shi da alaƙa da malami domin ɗalibi duk inda ya kai da shara da ƙwarewa a satar amsa ya tafi kenan. Anan kin yi magana ne akan yanda ɗalibai suka sauya akalar amsar 'yar uwarsu ɗaliba, kinga wannan misalin ba shi da... moreMalama wannan musalin naki ba shi da alaƙa da malami domin ɗalibi duk inda ya kai da shara da ƙwarewa a satar amsa ya tafi kenan. Anan kin yi magana ne akan yanda ɗalibai suka sauya akalar amsar 'yar uwarsu ɗaliba, kinga wannan misalin ba shi da alaƙa da na malami, a tunani wannan cuta ce ta kai-da-kai ga ɗalibai. Ba wai hakkin...
Oum NassHakan ba ya iyuwa Ruƙayya, idan yaro bai san komi ba aka kai shi makaranta to za a mayar da shi ajin sabbin yara ne irin sa. Amma ɗalibin da bai san komi ba ko an bashi ma satar amsar me zai rubuta tunda kina magana aka bai san komi ba? Zai yi tafiyar... moreHakan ba ya iyuwa Ruƙayya, idan yaro bai san komi ba aka kai shi makaranta to za a mayar da shi ajin sabbin yara ne irin sa. Amma ɗalibin da bai san komi ba ko an bashi ma satar amsar me zai rubuta tunda kina magana aka bai san komi ba? Zai yi tafiyar tsutsa ne ko kuwa ta maciji a takardarsa da sunan satar amsa?