Pharty Bb
I just published "7." of my story "MADUBIN GOBE!". https://my.w.tt/iVBD7rFeEbb
MADUBIN GOBE 7.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
....
Littafin kyauta ne.
....
"Nuratu?"
Da kyar ta buɗe idanunta da suka fara canza launi ta dubi Mami dake zaune gefenta bayan sun shigo gidan ta zube saman kujerun falon tayi kwanciyarta.
Hannu Mami ta saka ta kamo hannuwan Nuratu da ta bita da ido.
"Bana hana ki saka damuwa a ranki ba, bana son ciwon ki ya tashi dan Allah ki daure ki kawar da komai a ranki, ki duba halin da muka shiga dalilin haka, Nuratu in bana ganin dauriya tattare dake bana jin kwanciyar hankali a rayuwa ta, sai in ga har yanzu baki gama warkewa ba. Duk da nasan kina ƙoƙari, ki daure ki ƙara. "
Mami ta ƙarasa maganar cikin ƙarayar murya.
Murmushi Nuratu tayi ta damƙe hannun Maminta.
"Mami kai na yake ciwo, amma babu komai."
"Shikenan to tashi muje ganin babyn Hasiya, waya sani ma ko sabon miji na samu."
Mami tace tana dariya dan kawarwa Nuratu damuwarta.
Itama dariyar Nuratu tayi tana ƙoƙarin danne damuwarta, ta tambayi Mami.
"Sun koma gidane?"
"Eh muje can, in zaki zauna mata zuwa bayan suna sai ki ɗauki kaya."
To Nuratu tace ta miƙe ta shiga ɗakinta ta ɗauki kayanta cikin kits ƙarami ta fito suka fita.
...
Gidan har ya fara cika da mutane suka karɓi baby suna gani, babynta mace kyakkyawa fara tasha kayan sanyi farare. Bayan Mami ta miƙawa Nuratu babyn ta hana kowa karɓa.
Mami bata jima ba ta koma gida ganin su kansu sun isa kula da mai jego, ga Aunti Rahma ga Walida da Ameera mai bin ta ga Nuratu da Aunti Rukayya.
"Ki kula da ita Rahma dan Allah. Ki tabbatar tasha maganinta a kan lokaci."
Mami take faɗawa Aunti Rahma kafin ta wuce.
"Mami menene? Wani abun ya faru."
Aunti Rahma tace cikin damuwa.
"Kusan hakan ne, lafiyarta ƙalau ta dawo daga gidanki amma zuwanmu asibiti ya kusan dawo mana da aiki baya, ki kula da ita kar ku barta cikin damuwa."
"InshaAllah Mami komai zai wuce."
Aunti Rahma tace cikin tausayin ƙanwarta da wannan ƙaddara ta gifta a rayuwarta da nasu gaba ɗaya.
Tun da Mami ta tafi Rahma ta saka ido akan Nuratu har dare da ta lura ta kasa walwala gaba ɗaya ta zauna ta zuba jaririyar ido, Walida da Aunti Hasiya sai hira suke Ameera da Rukayya sun koma gida.
Da ido Aunti Hasiya ta nunawa Aunti Rahma Nuratu ta ɗaga mata kai alamar ta ganta.
"Ƙanwata!"
Aunti Rahma tace tana zama gefen Nuratu da ta juya a ɗan firgice ganin Aunti Rahma ne ya sata sauƙe ajiyar zuciya.
"Wa kike tunani? Yaya Al-ameen ko sauran samarin ki?"
Ɓata rai Nuratu tayi tana yamutse fuska.
"Babu kowa ciki. Ni fa ba samarina bane, dukkan su mutunci muke, kuma kun sani."
"Hakane kuma fa."
Aunti Rahma tace tana murmushi tare da ɗaga kai.
Turo baki Nuratu tayi ganin Aunti Rahma ta maida abin wasa.
"Tashi kiyi wanka ki kwanta, ga kuma can maganin ki yana jiranki."
Miƙewa Nuratu tayi ta shiga wanka, data fito ta saka kayan baccinta tasha maganinta kafin ta kwanta gefen baby. Wayarta ta ɗauka ta ƙira Dr Awwab tunawa da ya ƙirata ɗazu.
"Har na cire rai da ganin ƙiran ki Noor."
Dr Awwab ya amsa mata dashi bayan ya amsa sallamarta.
Murmushi Nuratu tayi.
"Ina Hanan? Ya aiki?"
"Lafiyar ta lau, tayi rigama ta gaji tayi bacci duk ta ishe ni in kawota gurin ki."
Har lokacin murmushi bai gushe saman fuskarta ba dan tana girmama Dr Awwab.
"Allah sarki My Baby, yaushe zaka kawo ta?"
"Duk lokacin da kike da free har Daddyn Hanan na son ganin ki ba ita ɗaya ba."
Shuru Nuratu tayi kamar ba zata amsa ba kafin ta sauƙe numfashi.
"Ni dai Hanan zan gani."
"Ni fa?"
Yace mata da sauri har ya bata dariya ta ɗan dara.
"In na samu time zan sanar da kai."
"Godiya muke ranki daɗe, ya jiki fatan babu wani matsalar?"
"Babu komai sai godiyar Allah."
"To allahamdulillahi haka ake so, Allah ƙara lafiya."
Ameen ta amsa dashi su kayi sallama ta kashe wayar tana kwanciya.
Tun tana jin hiransu Aunti Rahma da Hasiya har bacci ya ɗauketa.
"Tausayi take bani Aunti Rahma."
Aunti Hasiya tace tana kallon Nuratu dake bacci.
"Addu'a za muyi ta mata, Allah zai yaye mata komai."
"Hakane Allah kawo mata sauƙi."
Ameen Aunti Rahma ta amsa mata dashi tana shirin kwanciya ita ma dan ba zata koma gida ba ta bar yaranta da mai aikinta ta kula dasu, babansu yayi tafiya.
Gidan bai rabu da mutane ba har ranar suna Baby taci sunan kakarta ta wajen uba, dangin mijin Aunti Hasiya sun yi murna sun haɗa mata kayan goyo duk da haihuwa na biyu ne.
An yi taro lafiya an watse, ƙannenta sun zage sun mata aiki, Mami ma ta haɗa nata kayan ba laifi, Amma Jidda ma haka da ita ta tsaya kan komai. Haka Abban su ma ya aiko mata kuɗi masu yawa.
Washegarin Aunti Rahma da Rukayya da Walida da Ameera suka tattare komai suka gyara mata gida kafin su watse dan an nema mata dattijuwa da zata zauna mata.
***
Sati ɗaya da haka Nuratu suka fara final exam, ta maida hankali tana karatu sosai bangare ɗaya kuma tana ƙoƙarin ganin ta kawar da duk damuwar da yake damunta, ga maganinta da bata bari ya wuce ta tana sha akan lokaci.
Hakan yanama Mami daɗi ganin tana ƙoƙarin kauda komai a ranta ta maida hankali kan karatunta.
Sati biyu da kwanaki suka gama sai fatan samun sakamako mai kyau.
Agajiye lis ta dawo gidan cike da murnar yau ta kare exam ɗinta. Cikin falon ta shiga ganin wanda yake zaune ya sa murmushin fuskarta ya ɗan gushe ta ɗan haɗa fuska.
Shi ko ido kawai ya saka mata komai zai faru da Nuratu ba zai taɓa daina sonta ba, ba zata taɓa tashi daga Nuratun daya sani ba ta koma wata Nuratun da ƙaddara ta faɗa rayuwarta ba.
"Ƴan makaranta."
Yace mata ganin bata da niyar mishi magana.
"Ina wuni Yaya Al-ameen."
Ta faɗa ganin irin kallon da Mami ta watsa mata. Bata jira amsar shi ba ta wuce ɗakinta.
Duk fa ta gane take taken su musamman shi da yasha furta mata yana sonta kuma ta amince tun kafin ƙaddara ta faɗa rayuwarta. Babu wani ɗa namiji a rayuwarta yanzu ko zuciyarta da zata iya so har ta aura. Matsalar rayuwarta da damuwar da take ciki ma kaɗai ya isheta balle wani namiji da sanadin shi duk wani farin cikin rayuwarta ya tarwatse. Ta tsani duk maza in ka cire mutane ukun da take ganin mutuncinsu suka taimaka rayuwarta sai shi da take ganin girmansa matsayin Yayanta.
Babu aure a tsarin rayuwarta burinta tayi ta karatu ta gama ta samu aikin yi ta kula da maihaifiyar ta data sha wahala a kanta tun haihuwarta har girmanta, a dalilinta duk wani kadara nata ta siyar dan ta sama mata rayuwa mai kyau mai inganci, a dalilinta taƙi zaman aurenta, a dalilinta ta rabu da ƴaƴanta a dai-dai lokacin da suke buƙatar ta.
Kwanciya tayi ta ƙi fita tana jiran ya tafi.
....
"Bari in ƙirata ku gaisa."
"A'a Mami ki barta in ta gama ta fito babu matsala zan jira ta."
Yaya Al-ameen yace duk da yana son ganinta da sauri dan yana da gurin zuwa.
Mami bata jira mai yake faɗa ba ta shiga ɗakin Nuratu.
"Kin zo kin kwanta, kin san dai dan ke yake zuwa gidan nan."
Rai Nuratu ta ƙara haɗawa.
"Ni Mami kin san dai.."
"Na san me? Tashi dalla kije. Al-ameen ɗin ne zaki fara nuna hali. In bakya son sauran maza ai shi baya cikin su saboda ya nuna miki so da kauna duk da abinda ya faru bai gujeki ba."
"Kiyi hakuri Mami bari in je."
Nuratu tace ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta fita.
A falon ta sameshi zaune ta zauna tana sake gaishesa.
"Na takura miki ko na hanaki hutawa."
Kai Nuratu ta girgiza cike da kunya dan tana jin nauyin shi ita kanta bata san lokutan da take mishi haka ba. So take ya gane yanzu da baya ba ɗaya bane. Wannan wata Nuratu ce da duniyarta ta canza mata. Ba zata iya cigaba da soyayya dashi ba, ƙaddara ta hana hakan baya gani ne. Koma waye yanzu bata da lokacin ɓata mishi lokaci domin aure baya tsarin rayuwarta.
"Ƙanwata!"
Yaya Al-ameen ya ƙira ta ganin ta faɗa tunanin da baya so.
Murmushi yaƙe tayi tace.
"Na'am Yaya Al-ameen. Ya gida dasu Amma Jidda?"
"Lafiyarsu ƙalau, kina bani wahala ƙanwata har yanzu kin ƙi bani lokaci muyi magana. Karatu kullum shine uzirin ki, yanzu kuma gashi kuna exam in ma baku gama ba."
Kan Nuratu ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa bashi amsa dan yasha neman lokaci suyi maganar da bata da amsar shi.
"Ke nake saurara ƙanwata. Zan wuce wani guri nace bari in shigo miki in miki zuwa bazata."
"Za muyi magana ta waya ko WhatsApp."
Amsar da ta iya bashi dan neman mafita ma kanta.
Murmushi yayi yana miƙewa.
"Shikenan Allah yasa in ga canji, zan wuce sai munyi magana."
Itama miƙewa tayi tana bin bayan shi lokacin da ya nufi kofa.
"Nagode ka gaishe da Amma dasu Walida."
"Za suji."
Yace ya fita kafin ta koma falon ta samu Mami ta fito zata wuce ɗakinta Mami ta bata umarnin ta zauna za suyi magana.
Zama tayi ta san dai kullum maganar ɗaya ne ta bashi dama da ita kam bata jin zata iya haka.
"Mai yasa kike bawa yaron nan wahala ne Nuratu, kina ganin dai shekarunsa sun kai aure har sun wuce shekara talatin da biyu, dalilin ki har yanzu ya kasa hakura yana binki kina mishi wulaƙanci."
Idanun Nuratu cike da hawaye take duban Mami data haɗa rai.
"To ni kam Mami na nuna mishi bana so ya yake so in mishi."
"Auren ne ba za kiyi ba?"
Kai Nuratu ta ɗaga hawayema zuba saman kuncinta.
"Babu aure cikin tsarin rayuwata Mami, ba zan yi ba."
"Saboda abin da ya faru?"
Mami ta tambayeta itama da dauriya take ganin hawaye saman fuskar ƴartan da tasan dole in ta tuna abinda ya faru da ita sai ta zubar da hawaye balle kuma maganar aure.
Ajiyar zuciya ta sauƙe.
"Ba zan miki dole ba Nuratu, amma duk da abinda ya faru aure shine mutuncin ki, ki cire komai a ranki ki cigaba da rumgumar Ƙaddarar ki. Shi Al-ameen ɗin ya san abin da ya faru kuma ya yarda a haka zai aure ki to ki godewa Allah, kiyi ta addu'o'i in da alheri tsakanin ku Allah tabbatar muku in kuma babu Allah muku canji mai alheri. Share hawayen ki Noori."
Murmushi Nuratu tayi jin maganar Mami na ƙarshe dan ta kwantar mata da hankali. Nasiha ta mata kamar kullum dan yadda da ƙaddara duk da itama Mami dauriya take. Sai lokacin Nuratu taji nutsuwa ta samu cin abinci taci ta wuce ɗakinta ta kwanta dan jiran ƙiran sallar magriba.
Yaya Muhammad Al-ameen shi ya fara nuna mata menene so, ɗa namiji da ta fara saka sonshi cikin zuciyarta da rayuwar ta. Har yanzu tana son shi tana kaunar shi amma Ƙaddarar da ba zata iya goge shi ba ya rabata dashi. Ba auren shi ne ba za tayi ba abinda zata tarar gaba take tunani, balle bata tsammanin danginshi zasu barshi ya auri mace irinta, duk da Amma Jidda ta nuna itama tana son auren su.
Tunani ta faɗa na abinda ya wuce.
***
Shekaru biyu kenan da gama makarantar su Rahma da Hasiya suka shiga makarantar gaba da sakandare dan ci gaba. Suna aji biyu a lokacin samari suka dame su dan son aura ganin haka Alhaji Mamman ya ce su fitar da mazajen aure. A ciki suka zaɓa ko wanne ya turo aka saka ranar auren su.
Daga lokacin Alhaji Mamman ya fara shirin aurar da yaranshi, kaya ya musu na gani na faɗa dan arziki shi sai bunƙasa yake.
Mami sai a bakin Amma Jidda taji da yaranta, dan su Rahma har gidanta suka kawo samarin da zasu aura suka gaisheta. Ta yaba da tarbiyyarsu dukkansu biyu ta musu addu'a da samun zaman lafiya.
Lokacin Rukayya tana ajin ƙarshe na sakandare, Walida da Nuratu suna aji biyu. Muhsin yana aji ɗaya a digiri nashi. Amma Jidda ta sake haihuwar ƴa mace Ameera.
Biki saura sati yan uwa daga Gombe sun zo dangin Alhaji Mamman haka Amma Jidda tayi nata gayyar dan wasu ma sun ɗauka itace mahaifiyarsu.
Anan Amma Jidda ta samu Mami ta roƙeta ta bar Nuratu ta zo gidan dan ayi biki da ita dan ta ɗinka mata har anko na aure da dinner party.
Mami bata so ba amma ganin itama Nuratu tana so ta barta akan ranar wuni maza ta dawo dan tana guje mata haɗuwa da Abban ta gudun wulaƙanci ko zagi. Amma Jidda itama ta san nufin Mami dan haka ta mata alƙawarin ba abinda zai faru.
Nuratu a gidan Alhaji Mamman.
Like.
Comments.
Share.