*Darasi Akan... more*MU KOYI... moreMustapha musa abu Aisha
*MU KOYI IBADA*
*Darasi Akan... more*MU KOYI IBADA*
*Darasi Akan Azumi*
FITOWA TA GOMA-(10)
*WADANSU ABUBUWAN DA YA KAMATA MAI AZUMI YA QARA NISANTARSU*
1-Mayar da dare ya zama rana.(Dogon hira)
2-Yin barci har lokacin salla ya wuce.
3-Almubazzaranci wajen cin abinci.
4-Tozartar da lokaci.
5-Yin sahur da wuri, kuma a koma a yi barci har lokacin sallar asuba ya wuce.
6-Qin yin sallar Tarawihi.
*ALLAH YA KEBE WATAN RAMADANA DA*
1-Mala’iku na roqa wa mai azumi gafara har ya yi buda baki.
2-Warin bakin mai azumi ya fi qamshin turaren miski a wajen Allah.
3-Ana Daure masu tsaurin kai daga cikin shedanu.
4-Ana bubbude kofofin Aljanna a kuma rufe kofofin wuta.
5-A cikin Ramadana ne daren Lailatul Qadri yake.
6-Ana gafarta wa mai azumi a qarshen ramadana
*UMRA A CIKIN WATAN RAMADANA*
Haqiqa umra tana daga cikin manya-manyan ayukka da ke da katafariyar lada mai yawa a wajen Allah musamman a cikin Ramadan.An samo hadisi daga Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda ya ce; Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
*(yin Umura a cikin ramadana yana daidai da kamar ka yi aikin Hajji tare da ni ne)*.
“wato tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”
@Bukhari da Muslim
TAHAJJUD/TARAWIHI
Tahajjud,Qiyamul-lail, Sallar Tarawihi dukkansu ma’anarsu daya,matukar dai a cikin watan Ramadan ne,Mutum ya yi sallar nafila a gida ya fi lada da ya yi ta a masallaci amma banda na watan Ramadan.
Sallar tarawihi a cikin azumi ka yi ta a cikin jam’i yafi da ka yi kai kadai a gida.Sayid Sabiq ya ce junhuru sun tafi kan cewa sallar tarawihi/Tahajjudi cikin jam’i
yafi lada da ka yi kai ka dai a gida.
@fiqhuSunnah.
Sheikh Zainudden Abdurrahaman ib Rajab al-Hambali ya ce:
*Malamai sun dogara ne da hadisin da ya nuna cewa duk wanda ya yi sallar dare tare da limani har ya gama za a rubuta mai ladan ya sallaci daren ne baki aya.
Shi kuwa Imam malik yana ganin ka yi a gida ya fi shi yasa ma yake yin nasa sallar Tarawihin/Tahajjudinsa a gida, dogaransa da maganar Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam da ya ke cewa; *(Mafificiyar sallar mutum wanda ya yi a gida sai dai in ta farilla ce)*wannan itace hujjarsa,su kuma Junhurun Malamai hujjar su ita
ce hadisin da ya ce; *(wanda ya yi sallar dare tare da limami har yagama za a rubuta mai ladan ya sallaci daren ne baki daya)*duba Muguni na ibn Qudamah 607/2 da Qiyamu Ramadan 19-20.
Imam Ahmad bn Hambal yana yin sallar Tarawihi ne a masallaci yana bin limami har sai angama sallah saboda ya sami ladan da Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya fada na ladan wanda yabi liman sallar dare har ya gama,Malamai dai sun rinjaya a kan yin sallar Tarawihi/Tahajjudi a masallaci ya fida lada da kayi kai kadai a gida, wallahu a’alam.
Arewa24 sunzo sun kawo cigaba mai girma ga Al'ummar Arewacin Nigeria tahanyar samar da damarmaki na ayyukanyi da kuma kara fito da wadansu biyayyun jarumai wadanda a yanzu tauraruwar su ke haskawa a fagen fina-finai amma abin takaici madadin agode... moreArewa24 sunzo sun kawo cigaba mai girma ga Al'ummar Arewacin Nigeria tahanyar samar da damarmaki na ayyukanyi da kuma kara fito da wadansu biyayyun jarumai wadanda a yanzu tauraruwar su ke haskawa a fagen fina-finai amma abin takaici madadin agode masu kawai sai wani shaci fadi akeyi akansu.
Mu masu kudin mu sam-sam basu iya yin investigating akan fannonin da suka shafi nishadi da technology ba domin samar da ayyukanyi ga matasa.
Nayi imani da Allah babu wani mai wata kwakkwarar hujja akan cewar kwangila aka basu. Ni idan naji ance kwangila aka basu abin sai ya bani mamaki da haushi da kuma dariya. less
Yusha'u Alhassan
Matan aure da 'yan mata miliyon 5.7 suke amfani da dabarar hana daukar ciki a Nijeriya
Wani Sabon Rahoto ya bayyana cewa matan aure da ‘yan Mata Miliyan 5.7 ne suka yi amfani da dabarar hana daukar ciki a... moreMatan... moreYusha'u Alhassan
Matan aure da 'yan mata miliyon 5.7 suke amfani da dabarar hana daukar ciki a Nijeriya
Wani Sabon Rahoto ya bayyana cewa matan aure da ‘yan Mata Miliyan 5.7 ne suka yi amfani da dabarar hana daukar ciki a... moreMatan aure da 'yan mata miliyon 5.7 suke amfani da dabarar hana daukar ciki a Nijeriya
Wani Sabon Rahoto ya bayyana cewa matan aure da ‘yan Mata Miliyan 5.7 ne suka yi amfani da dabarar hana daukar ciki a Najeriya.
Rahoton yace an hado bayanai ne daga shekarar 2012... less
Abdulwahab
*DUNIYA GIDAN WUCIN GADI CE.*
-
"Kada ka riƙi duniya gidan dauwamarka, a'a ita gidan wucin gadi ce, kada ka taɓa sakankance wa acikinta, domin lallai haƙiƙa kana tsaka da jin daɗinta zata yanke maka"
-
"Mai... moreAbdulwahab
*DUNIYA GIDAN WUCIN GADI CE.*
-
"Kada ka riƙi duniya gidan dauwamarka, a'a ita gidan wucin gadi ce, kada ka taɓa sakankance wa acikinta, domin lallai haƙiƙa kana tsaka da jin daɗinta zata yanke maka"
-
"Mai hankali... more*DUNIYA GIDAN WUCIN GADI CE.*
-
"Kada ka riƙi duniya gidan dauwamarka, a'a ita gidan wucin gadi ce, kada ka taɓa sakankance wa acikinta, domin lallai haƙiƙa kana tsaka da jin daɗinta zata yanke maka"
-
"Mai hankali shine wanda yake ƙoƙarin yawaita aiyukan alkhairi acikinta, sannan kuma ya taƙaita aiyukan saɓo acikinta"
-
"Dukkanin wasu matsal-tsalunka a nan duniyar, na wucin gadi ne, babbar masifar da zata baka tsoro itace masifar yin ido biyu da mala'iku bayan an binneka acikin rami alhalin kuma baka da kyawawan aiyuka, wacce zaka haɗu da ita a ranar lahira, baka sani ba shin zaka iya amsa tambayoyin mala'iku a lokacin da ka kwanta acikin ƙabarinka ko a'a, baka sani ba ko zaka iya amsa... less