Rakumi yana ɗaya daga cikin manyan dabbobi marasa ƙaho wanda aka fi samun shi a cikin sahara mai zafi ta Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya. Saboda juriyar raƙumi da kuma daidaituwa da yanayin wasu wurare mafi tsanani a duniya baki ɗaya, ɗan’adam ya yi amfani da raƙumi dubban shekaru da suka wuce a matsayin dabbar hawa. Mutum zai iya jayayya cewa in ba don raƙumi ba, da wasu al’ummomi ba za su sami bunƙasa ba a wuraren da ba su da yanayi mai kyau.
Raƙumi ɗaya ne daga cikin manyan dabbobi masu shayarwa a doron ƙasa kuma ya dace da rayuwa a cikin jeji inda abinci da ruwa ba su da yawa, kuma yanayin zafi yana canjawa da sauri daga yini mai zafi zuwa dare mai sanyi. A da an taɓa samun su cikin walwala suna yawo a cikin hamadar Larabawa, amma yanzu sun ɓace daga daji sun yaɗu a duniya kuma suna da yawa.

Bayan taimakawa ga sufuri, rakuma a tarihi sun kasance wani ɓangare da ke samar da albarkatun nama da madara. Haka kuma raƙuma suna samar da nau’ikan gashin fata guda biyu waɗanda za a iya amfani da su, akwai na waje, mara nauyi da na ciki, mai laushi. Dukansu biyu suna da ban sha’awa saboda dalilai daban-daban, haka nan raƙumi yakan zubar da gashi a dabi’arsa.
Siffofi da bayyanar raƙuma
Kamar yadda aka ambata, raƙuma suna da nau’i biyu na gashin jikinsu, waɗanda ke aiki tare domin ba da kariya ga zafin rana da kuma ɗumi da sanyi a lokacin dare. Launi na gashin raƙumi ya bambanta daga launin hoda zuwa launin ruwan kasa.
Rakuma suna da wasu siffofin daidaituwa a muhallinsu domin nisantar yanayi mai tsanani a muhalli. Raƙuma suna da ɗan tsayin ƙafafu da ke samar da tazara da ƙasa. Haka kuma ƙirjinsu na a bayyane don kiyaye ciki daga ƙasa idan sun durkusa.
Hatta sassan jikinsu da ke taɓa ƙasa suna taimaka musu wajen samun kariya da tsira. Domin wani yanki da raƙuma ke zaune yana da dutse mai kaifi, ƙafafuwan raƙumi suna da ƙasusuwa masu kauri don kariya daga sara da raunuka. A wasu wuraren da ba su da wahala amma suna da yashi, raƙuma suna iya guje wa nutsewa a cikin yashi ta hanyar shimfiɗa ƙafafu masu kofato.
Idanun rakuma da hancinsu kuma an daidaita su don dacewa da busassun wurare. Dogayen gashin idanunsu masu lanƙwasa suna taimakawa wajen kawar da kura daga idanunsu, kuma hancinsu yana da siriri sosai don taimakawa wajen fitar da kura da tarkace.
Manyan raƙuma suna adana kitse ba ruwa ba, daga cikin abubuwan da suke iya amfani da su a matsayin abinci lokacin da abinci da ruwa ba sa samuwa. Wannan na ba wa raƙuma damar tafiya ta cikin yanayi mara kyau.
Raƙuma dabbobi ne masu ciki da yawa, suna da ciki daban-daban har guda uku waɗanda suka ƙware wajen adana sinadirai masu yawa gwargwadon iyawa domin tunkarar yanayi marar kyau.
Tarihin asalin halittar raƙumi
Kamar yadda asalin doki yake, an yi imanin cewa raƙuman farko sun samo asali ne a Arewacin Amurka kimanin shekaru miliyan 40 zuwa 50 da suka wuce. Girmansu bai fi girman zomo ba. A ƙarshe, sai su haɓaka kuma suka yi ƙaura zuwa yankin Eurasia. Rakumi nau’in Bactrian (mai tozo biyu) ya samo asali ne daga raƙumi mai tozo ɗaya, kimanin shekaru miliyan 1 da suka wuce.
Lokacin da raƙumi ya fara zama a gidaje, wato ya zama dabbar gida, batu ne da ake yin muhawara akai, amma kusan shekaru 5,000 da suka wuce, ‘yan’adam sun kasance suna amfani da raƙumi wajen taimaka wa jigilar kayayyaki da mutane daga wasu wuraren masu wahalar rayuwa a duniya.
Rarrabawa da yaɗuwar raƙuma a sassan duniya
A tarihi rakumi zai yi yawo a cikin hamadar Arewacin Afirka, Gabas ta Tsakiya da kuma zuwa yankin Asiya har zuwa yammacin Indiya inda muhallan kan iya canjawa daga tarin ƙasa mai laushi zuwa yankunan duwatsu. A yau, ba a samun raƙuma a cikin daji suna dai wanzuwa ne a matsayin dabbobin gida a waɗannan yankuna kuma suna samar da damar sufuri da kuma muhimmin tushen abinci ga mutanen yankin.
Juriyar da suke da ita na tsawon lokaci ba tare da abinci da ruwa ba, tare da damar ɗaukar kaya masu nauyi ya taimaka wajen ba wa mutane damar ci gaba da ƙetara hamada. A halin yanzu, miliyoyin raƙuma na gida suna wanzuwa a cikin hamada kuma wani adadi mai yawa waɗanda za a iya samu a cikin hamadar tsakiyar Ostiraliya.
Nau’inkan rakuma
Rakumin bactrian (masu tozo biyu)
Ana samun wannan nau’in raƙuma a tsakiyar Asiya da kuma a yankin Bactria. Waɗannan raƙuma na gida ne. Yayin da mafi yawan rakuman da ake gani suna da tozo guda ɗaya ne, waɗannan da nau’in raƙuman daji kuwa masu tozo biyu ne. Waɗannan tozon suna da ƙanƙanta.
Dromedary/Raƙuman Larabci
Ana iya samun raƙuma masu tsini a Gabas ta Tsakiya, Kudancin Asiya, da Hamadar Sahara. An shigar da su Austaraliya ne kuma ana kiwata su a can. Suna cikin nau’ikan raƙuman gida. Su ne mafi tsayi a cikin raƙuma kuma ba su kasance a daji ba, sun wanzu kusan shekaru 2,000.
Wild bactrian camel
Raƙuman bactrian na daji suna cikin Mongoliya da yankunan arewa maso yammacin China. Irin wannan rakuma a zahiri na daji ne ba na gida ba. Wannan wani nau’i ne na daban daga raƙumi na Bactrian, kuma akwai kusan 1,000 da suka rage a duniya.
Ɗabi’u da salon rayuwar raƙuma
Rakuma suna rayuwa a busassun yankuna a cikin garken da zai iya ƙunsar raƙuma guda 40 wanda ya haɗa da mata tare da ƙananansu kuma namiji guda ɗaya ne ke jagorantar garken. A lokacin kiwo, mazan raƙuman da suka fi kowa girma suna kare matansu ta hanyar cizo, tofa da jingina ga kishiyoyinsu maza.
Rakuma suna hutawa ta hanyar kwanciya kuma suna yin haka ta hanyar lanƙwasa ƙafafunsu na gaba a ƙarƙashinsu, suna biye da baya. Haka kuma an san su suna tafiya a wata hanya ta daban da sauran dabbobi masu shayarwa, suna iya motsa ƙafafu biyu na hagu a tare sannan duka biyun dama don yin tafiya.
Domin a jurewa da sarrafa damshi mai mahimmanci a cikin irin wannan yanayi na mai tsanani, raƙuma suna da ƙarancin yin gumi, kaɗan ne idan aka kwatanta da girman jikinsu, wanda tare da haka sukan saki zafin jikinsu ya tashi a cikin zafin yanayin gari, hakan na nufin suna fitar ruwan jininsu ko gumi a hankali fiye da sauran manyan dabbobi masu shayarwa.
Tsarin haihuwa da rayuwar raƙuma
Rakuma na iya hayayyafa a lokacin da suke tsakanin shekaru uku zuwa hudu ga mata, da kuma maza masu shekaru biyar, yayin da mafi girma daga cikin mazan da ke da hakkin yin barbara da matan. Raƙuma mace da namiji suna samar da zafi a lokacin barbara wanda yawanci yakan wuce tsakanin Nuwamba da Maris. Bayan tsawon lokacin renon ciki wanda zai iya kaiwa har zuwa watanni goma sha uku, macen takan haifi ko dai ɗa ɗaya ko kuma tagwaye a wasu lokuta waɗanda nauyinsu ya kai 40kg a lokacin haihuwa.

A cikin sa’o’i takwas jaririn rakumi zai iya tsayawa sannan mahaifiyarsa ta shayar da shi har ya girma kuma ya kai minzalin mai cin gashin kansa. Raƙuma suna fara cin ciyawa tun suna tsakanin wata biyu zuwa uku kuma ana yaye su a lokacin da suka kai kusan watanni huɗu da haihuwa.
Abincin raƙuma da ganimarsu
Rakumi a fasahance dabba ce daga cikin herbivorous, wato abincinsu ba ganyayyaki da ciyayi ba ne, kamar yadda aka sani suna tauna ƙashi da cin nama don cike gurbi a tsarin abincinsu. Wata karin siffa da ta dace da rayuwa a cikin jeji ita ce rarrabuwa, leɓe mai ɗauke da fata mai gashi wanda ke taimaka musu wajen cin tsirrai masu kauri da ƙaya waɗanda sauran dabbobi ke gujewa. Haka kuma an san raƙuma da cin shuke-shuken da ke da yawan sinadarin gishiri wanda kuma hakan ke nuna cewa ba a samun gasar cin wannan nau’in abinci daga sauran dabbobi.
Wani abu mai ban mamaki game da Rakuma shi ne damar da suke da ita wajen adana sinadaran abincinsu da ruwan sha a matsayin kitse a cikin tozonsu, wanda ke nuna suna da isasshen kuzari lokacin da abinci da ruwa suka yi karanci. Rakuma na iya rasa kusan kashi 40% na nauyin jikinsu kafin su sake cika kansu kuma da zarar an sami ramin ruwa ko lungu, za su iya sha kusan galan 40 na ruwa cikin kankanin lokaci.
Mahara da barazanar da raƙuma ke fuskanta
Kodayake a yanzu babu raƙuma a cikin daji, yanayin girman raƙumi yana da tasiri ta fuskar ƙayyadaddun mafarauta. Zaki da Damisa sun kasance mafi yawan mafarautansu; duk da haka, kasancewar raƙuma suna zaune a cikin maƙiya da yankuna masu haɗari inda za a iya samun manya-manyan dabbobi ‘yan ƙalilan masu cin nama yana nufin ba za a riƙa farautar su akai-akai kamar sauran dabbobi masu kofato ba.
Kodayake mutane fara kiwon su ko ajiye su a gida fiye da shekaru 5,000 da suka wuce, da sun daɗe suna farautarsu domin namansu da fatunsu. A halin yanzu dai babu rakuma a cikin daji, yawancinsu suna gida, kuma ana samun mafi yawansu a Arewacin Afirka zuwa Yammacin Asiya.
Abubuwan ban sha’awa game da raƙuma
Raƙuma ba kawai ƙaƙƙarfan dabbobi ba ne, dabbobin jeji ne domin suna iya rayuwa ba tare da ruwa ba har na tsawon watanni 10 muddin sun sami abinci, amma yanayin tafiyarsu a hankali yana nufin suna iya yin tafiya mai nisa (wani lokaci fiye da kilomita 30) a cikin kwana ɗaya, yayin da suke iya ɗaukar kayan da zai iya wuce kilogiram 200.
Kamar yadda yake ga wasu dabbobin gida, yanzu akwai nau’ikan raƙuma daban-daban waɗanda suka samo asali daga ire-iren raƙuma masu tozo na Bactrian don samar da ɗaiɗaikunsu waɗanda ko dai sun fi girma da ƙarfi don amfani da su a matsayin dabbobi masu hidima ko kuma suna da sauri. Ba kamar sauran dabbobi masu shayarwa ba, raƙuma suna da nau’ikan jajayen ƙwayoyin jini na musamman waɗanda ke ba da damar jini ya ci gaba da gudana a hankali lokacin da dabbar ta bushe kuma jinin ya yi kauri.
Dangantakar raƙuma da mutane
A tarihi an yi amfani da raƙuma na dubban shekaru ta fuskoki biyu don jigilar kayayyaki a cikin hamada da kuma kyakkyawan tushen samuwar madara da nama. Haka nan ana iya amfani da gashinsu don yin sutura da sauran su. Kamar sauran dabbobin gida, yanzu akwai nau’o’in raƙuma da yawa
Kariya da kulawa da raƙuma
Kamar yadda aka bayyana a halin yanzu babu raƙuma a daji sun ƙare, sun zaje a matsayin dabbobin gida yawancinsu, tare da ƙiyasin da ya kai adadin miliyan 20. A cikin shekarun 1800s, an shigo da raƙuma na farko zuwa Ostiraliya don a yi amfani da su wajen taimaka wa mutane shiga wurare a hamada. Tun daga wannan lokacin kuma da yawa sun biyo baya wanda ya kai ga samun ɗimbin raƙuma masu ƙarfi waɗanda maiyuwa sun kai miliyan 1 da ke yawo a cikin saharar tsakiyar Ostiraliya.
Manazarta
Frame, & W, L. H. a. G. (2025, March 1). Camel | Description, Humps, Food, Types, adaptations, & Facts. Encyclopedia Britannica.
NATURE, PBS. (2020, September 17). Camel Fact Sheet | Blog | Nature | PBS. Nature. .
Vedantu, & Vedantu. (2025, February 26). Facts about Camel. VEDANTU.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.