An haifi Sheikh Dakta Ahmad Bamba a shekarar 1940, sannan ya taso a garin Alabar A.E.B ko Nguwan Gonjawa, a Jihar Kumasi ta ƙasar Ghana. Mahaifinsa shi ne, Muhammad Ibrahim Bamba iyayensa mata su ne, Hajia Khadijah (Mama Adizatu) and Hajia Fatima (Mama Hajia), su kuma sun kasance ‘ya’ya ne a wajen Mama Gyamata. Ita kuma Gyamata ta kasance ‘ya a wajen shahararren malamin addini sannan dattijo na farko a unguwar Gonja ta jihar Kumasi. Wato Marigayi Mallam Sani.

Dangin Sheikh Dakta Bamba
Sheikh Dakta Ahmad Bamba mutum ne mai ƙan-ƙan da kai kuma abin girmamawa. Shi ya sa ma ya zama abin so ga kowa. An haife shi ne a babban gida, inda yake da ƙanne da yayye masu yawa.
Yayyensa da ƙanne maza sun haɗa da Malam Adam Bamba Sufi, Sheikh Aminu Bamba, Alhaji Abdul Aziz Bamba, Malam Saidu Bamba, Alhaji Ishak, Alhaji Salu Bamba, Alhaji Mahmoud, Alhaji Farouk, Alhaji Wasiu, Sheikh Suleman Bamba, Alhaji Adam, Alhaji Usama, Alhaji Sadiku, Alhaji Hashiru Hamburg, da sauransu.
Yayye da ƙannensa mata su ne Hajia Awuraba, Hajia Kande, Hajia Baida, Mma Muhamdiyya, Hajia Iya, Hajiya Aunty Bamba, Hajiya Zulai, Hajia Safura Bamba, Hajiya Amatu Khalid, Hajia Barkisu, Hajiya Abbatu da sauransu.
A cewar ‘yan uwan Dakta Ahmad Bamba, Alhaji Isshaku da Alhaji Salu Bamba, Alhaji Kassimu ya damƙa amanar Rubama a hannun Hajia Fatima (Mahaifiyar Dakta Ahmad Bamba). Bayan ta karɓi amanar ne, sai ta ce: “Ina fatan za ta kasance mata ga Ahmad Bamba”. Alhamdulillahi kuma sai Allah ya amsa addu’arta.
Karatunsa
Ya fara karatun darusan ilimin addinin Musulunci a Wataniyya a ƙarƙashin sanannen Sufin nan, wato Alhaji Baba Al-Waiz, 2anda aka fi sani da Babal-Waiz a Kantudu.
Ya yi saukar Ƙur’ani mai girma a ƙarƙashin koyarwar mahaifinsa a Masallacin Kakan Kakansa wanda yake a garin Afia Kobi. Daga nan sai ya ci gaba da zurfafa iliminsa a fannin hukunce-hukuncen shari’a (Fiqihu). Inda ya fara da littafin Al-Ishmawiy wanda yake ɗauka a gaban Mallam Amadu Langonto. Daga nan kuma ya koma gaban babban malamin da ya jaddada Sunnah a Kumasi, Sheikh Abdul Samad Habibullah.
Abokan karatunsa sun haɗa da: Mallam Imrana Musa, tsohon limamin masallacin Ashanti. Sai tsohon Halifan Wataniyya, Mallam Muntari. Sai sarkin limaman garin Dagomba, Alhaji Lawal na Baba Abbas wanda aka fi sani da Alhaji Nuhu Abbas. Sannan akwai Mallam Zakari Alhaji Nuhu na Kotokoli. Sannan Ustaz Umar, Sarkin limaman garin Yadiga da kuma irin su Mallam Muhammad Danraz da Mallam Dan Azumi, da sauransu.
Sheikh Dakta Ahmad Bamba ya kasance ɗaya daga cikin manyan ɗalibai ga babban malamin addinin Islamar nan na Jami’ar musulunci ta Madina, Sheikh Hamad Bin Muhammad Al-Ansari. Sannan ya bar tarihi mai girma a lokacin rayuwarsa a matsayin ɗalibin jami’ar.
Sannan ya yi karatunsa na boko a wani gari mai suna Roman Hills a Kumasi. Inda ya fito da sakamako mai kyau.
Ayyukan da gwagwarmayar sana’a
Bayan neman ilimin da yake, Dakta Ahmad Muhammad Bamba ya koyi ɗinkin kaya daga Mallam Awudu, wanda shi ma abokin karatun nasu ne. Sannan bugu da ƙari, ya yi sana’ar kiwon shanu wanda ya koya a wajen Mallam Muntari wanda shi kuma mahaifinsa sana’arsa ita ce sayar da shanu a mayankar garin Kumasi.
Duk da kasancewar ya tsunduma cikin sana’o’i daban-daban, wannan bai saka shi yin wasarere da harkar neman iliminsa ba, har sai da ya tattara tarin ilimi mai yawa daga wajen Sheikh Abdul Samad da wajen wasu Malamai Misrawa waɗanda gwamnatinsu ta ɗauki nauyinsu su zo garin Kumasi domin su buɗe wata makaranta mai suna Markaz Al-Sharif, inda za a dinga koyarwa kyauta.
Sheikh Bamba masanin hadisi ne
Jami’ar Musulunci ta Madina da kuma Jami’ar Bayero ta Kano dukkansu sun ayyana Dakta Ahmad Bamba a matsayin babban masanin hadisai. Wannan shi ne mafarin zaman shehin a Jihar Kano a Nijeriya. Inda ya zauna a matsayin Malamin jami’a kuma Malamin addini tun a lokacin shekarun Alif ɗari tara da tamanin har zuwa lokacin rasuwarsa.
Sheikh Dakta Ahmad tsohon malamin jami’a ne da ya koyar a Jami’ar Bayaro ta Kano. Ya koyar a tsangayar Ilimin Islama sannan ya ci-gaba da karantar da mutane ta hanyar wa’azi da littatafan Hadisai a Masallacin Jami’ar daga baya kuma ya koma Masallacin ƙashin kansa mai suna Darul Hadith da ke Kano, a Unguwar Tudun Yola. Inda yake limami kuma shugaba.
Sheikh Dakta Ahmad Bamba ya sadaukar da dukkan rayuwarsa wajen bautar Allah da hidima ga mutane. A cewar Dakta Umar Sani Rjiyar Lemo, idan ka ɗebe ƙoƙarin Sheikh Mahmoud Gumi, Dakta Ahmad Bamba shi ne masani Hadisi na farko wanda ya kammala cikakken sharhi a kan dukkan littatafan sahihan hadisai guda shida mai suna Kutub al-Sittah a Larabce su ne:
- Sahih al-Bukhari
- Sahih Muslim
- Sunan Abu Dawood
- Sunan al-Tirmidhi
- Sunan al-Nasa’i/al-Mujtaba
- Sunan ibn Majah.
Duk da nauyin shekarunsa da suka kai 82, kishin Dakta Ahmad na yaɗa addinin Musulunci bai ragu ba. Ya ƙara ƙara nuna shakuwa da makarantarsa fiye da kowane waje.
Marigayin ya samu zarafin fassara sanannen littafin Hadisin nan, Muwaɗɗa Malik, zuwa harshen Hausa. Aikin da ake ɗauka a matsayin mafi kyawun da aka yi a cikin ‘yan lokutan baya-baya nan.
Ya shafe shekara 24 marigayin Malamin yana karantar da Kutub as-Sittah, littafai guda shida da ke ɗauke da tarin Hadisai (maganun ko ayyukan Annabi Muhammad (SAW) wanda malaman Musulunci guda shida suka haɗa, lamarin da ya ce ba a taba yin shi a Kano ba.
Halaye da ɗabi’unsa
Ɗaya daga cikin halayensa na musamman shi ne sauƙin rayuwarsa, shi ya sa duk shekarun da ya yi a masallacin BUK ba limami ba ne, ya bi kuma ba ya sha’awar a bi shi a lokacin sallar jam’i.
Dakta Ahmad ya bayar da gudunmawa sosai wajen yaɗa Sunna ( koyarwar Musulunci) tun a farkon shekarun 1990.
Duk da ƙalubalen da Malam ya fuskanta a lokacin da yake malami a BUK ya tsaya tsayin daka kan abin da ya yi imani da shi.
Mutuwarsa
Dakta Ahmad Bamba ya rasu yana da shekaru 82 a ranar Juma’a 7 ga watan Janairu 2022, a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH). Ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya 30 da jikoki da dama.
Yadda aka yi jana’izarsa
Dubban jama’a daga sassa daban-daban na ciki da wajen Kano ne suka halarci sallar jana’izar marigayin malamin ƙarƙashin jagorancin babban limamin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Sheikh Abubakar Jibril, a babban masallacin marigayi Dakta Ahmad Bamba BUK, Darul Hadith, da ke Tudun Yola, kusa da gidansa, a cikin birnin Kano.
An binne gawar marigayi Dakta Ahmad BUK a maƙabartar Ɗandolo da ke kusa da unguwar Kabuga-Tal’udu a cikin birnin Kano.
Yabon da jama’a suka yi masa
Jama’a da dama da suka haɗa da malaman addinin Islama sun bayyana rasuwar marigayi Dakta Ahmad a matsayin wani ƙaton giɓi da zai yi wuyar cikewa.
Fitaccen malamin addinin Musulunci na Sashen Shari’ar Musulunci na Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo, ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗaukacin al’ummar Musulmi. ”Wannan babban rashi ne ga kowa ba wai a Kano ko Najeriya kaɗai ba har ma da sauran kasashen duniya, Dakta Ahmad BUK babban malami ne, mutum ne mai faɗin gaskiya, mutane sun ci gajiyar koyarwarsa tsawon shekaru.”
Ɗaya daga cikin ɗaliban marigayin malam Hafiz Abubakar Rogo wanda yake tare da malamin sama da shekaru 30, kuma ɗaya daga cikin limaman masallacin Darul Hadith, ya ce, ”Rasuwar Dakta Ahmad ba ta misaltuwa da kowace irin mutuwa domin duniyar addinin Musulunci ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun malamai.”
Mutuwar tasa ta dawo da tunanin abin da ya faɗa a karatunsa na ƙarshe ƙasa da mako guda kafin rasuwarsa. Karatun darasin hadisin ya gudana ne a ranakun Asabar da Lahadi a tsohuwar harabar Jami’ar Bayero Kano (BUK) tsawon shekaru da dama sannan aka koma Tudun Yola lokacin da ya gina Masallacin Juma’a a can.
A cikin wani faifan bidiyo na darasin ƙarshe da malam ya gabatar, an jiyo shi yana shaida wa mahalarta ɗaukar karatun a masallacin cewa ba za a yi karatu a mako mai zuwa ba. Ya ce shi da mutanen da suke zuwa domin ɗaukar darasi suna buƙatar su huta. Yayin da wani daga cikin taron ya tuna masa cewa darasin ranar shi ne na 100 a cikin littafin Sharhus Sunnah, littafin Hadisin da yake koyarwa. An hango marigayin yana girgiza kai a faifan bidiyon yana nuna mamakinsa.
Wani makusancin marigayi mai suna Alhaji Ibrahim Gerawa, ya tabbatar da abin da aka gani a faifan bidiyon, inda ya ce, ”Marigayi Dakta Ahmad ya bayyana cewa ba za a yi karatu a mako mai zuwa don haka ɗalibai su tafi hutu”. Wannan shi ne gani na ƙarshe da suka yi masa a raye.
Manazarta
Abdulraheem, B. (2022, January 8). Dr Ahmad Muhammad Bamba: A scholar that history will not forget – Radio Nigeria Kaduna English.
BBC News Hausa. (2022a, January 7). Sheikh Ahmad Bamba, ’Kala Haddasana, na Kano ya BBC Hausa News
Daily Trust. (2022a, January 11). Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, a tribute. Daily Trust.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.