Skip to content

Sheikh Ibrahim Maqari

Sheikh Maqari ya kammala digirinsa na farko a Al-Azhar a shekarar 1999 sannan ya yi digirinsa na uku a Jami’ar Bayero Kano a shekarar 2009. Ya yi karatu a faɗin Najeriya a matsayin Farfesa a fannin Larabci da Harsuna. Sheikh Maqari yana da litattafai da maƙalu da yawa da aka buga a cikin mujallu, kuma memba ne a Majalisar Musulmi a Najeriya, Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, kuma wanda ya kafa Cibiyar Bayar da Ilimi ta Tazkiyyah.

Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari, limamin Abuja.

Haihuwarsa da asalinsa

Ibrahim Ahmad Maqari, an haife shi a ranar 15 ga Satumba 1976. Malamin addinin Muslunci ne a Najeriya kuma wanda ya assasa Cibiyar Ilimi ta Tazkiyyah, da ke Abuja.

Kakansa wanda ya haifi mahaifinsa shi ne ya zo ƙasar Zariya daga garin Borno da niyyar neman ilmi, kuma bayan ya samu abin da yake so sai ya bukaci ya koma inda ya fito don ya cigaba da ilmantar da al’umma. Amma sai sarki Zazzau na wancan lokacin ya ce ai shi malamai ba sa zuwa garinsa su bar garin, don haka sai ya ba shi gida ya ci gaba da zama yana ilmantarwa.

Karatunsa da neman ilimi

Maqari ya fara tare da kammala karatunsa na firamare a garin Katsina bayan da aiki ya mayar da mahaifinsa can a shekarar 1987, daga nan kuma ya wuce Kwalejin Nazarin Larabci ta Jama’atu da ke Zariya domin yin karatunsa na sakandare. Digirinsa na farko ya yi shi ne a jami’ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira a shekarar 1999. A matsayinsa na dalibi a Al-Azhar, ya kasance kan gaba wajen haɗa ayyukan addini da aka tsara don samar da haɗin kai a tsakanin musulmi.

Ibrahim Maqari ya fara aikin koyarwa a jami’ar Ahmadu Bello, Zaria a 1999. A shekarar 2001 ya koma renon matashiyar Cibiyar Nazarin Cigaban Jama’atu Zariya sannan ya samu aiki a Kwalejin Ilimi ta Tarayya Zariya inda ya kuma samu Diploma a fannin Ilimi a shekarar 2004. A shekarar 2005 ya samu digiri na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A wani yanayi da ba a saba gani ba, ya kammala karatun digirin digirgir a cikin shekaru biyu a Jami’ar Bayero Kano, a shekarar 2009.

A 2006, saboda jajircewarsa da sadaukar da kai ga ci gaban Ilimin Larabci da Ilimin Addinin Musulunci a Najeriya, ya amince da tayin karantar da Harshen Larabci a Ngala, wani ƙauye mai nisa a kan iyaka a Jihar Borno. A shekarar 2010 ya dawo gida aka naɗa shi babban malami a jami’ar jihar Kaduna. Bayan shekara ɗaya Ibrahim Maqari ya koma Jami’ar Bayero Kano inda a yanzu yake zama Mataimakin Farfesa.

Duk da jajircewarsa a fagen karatu, an naɗa Maqari a matsayin mataimakin babban limamin masallacin ƙasa na Abuja a shekarar 2012. A matsayin mataimakin babban limamin yakan yi zirga-zirga a tsakanin Abuja, Zariya da Kano a kowane mako.

Littafai da rubuce-rubucensa

Maqari ya yi wallafe-wallafe sama 20 a ciki jaridu kuma ya buga littattafai da yawansu ya kai arba’in. Akwai littafin da yake rubutawa yanzu wanda ya ƙunshi sababbin mas’aloli waɗanda za su ƙara kyautata fahimtar matasa almajirai ilimi da addinin Musulunci gabaɗaya a zamanin da muke ciki wanda ke cike da tahaddiyat. Wasu daga cikin littattafansa sun haɗa da:

  • A’alamus shi’eril muusahah
  • Azzahirat Alsalafiyyat
  • Attanaasu Bai Al Limtisasi wal’Intisasi
  • Alhawaa wabina’is Suratu shi’ri Yahya Annufaahki
  • Shi’iri Hubbul Ilaahy.

Zuwansa ƙasar Masar

Sheikh Ibrahim Maqari ya je kasar Masar karatu a daidai lokacin da ya buɗe makaranta a nan gida Najeriya. A ƙasar Masar babban guzirin da ya samu shi ne haduwarsa da babban malaminsa, abin alfaharinsa a dukkan fannonin karatu da rayuwarsa, wato Sheik Ibrahim Saleh al- Hussaini, kuma shugaban babbar majalisar Fatwa ta Najeriya.

Yawanci malamansa ba ‘yan Najeriya ba ne, sun zo daga ƙasashen Mauritania da Morocco, don haka ya yi amfani da wannan damar wajen ɗaukar wasu fannoni daga cikin ilmi daga hannun malaman.

Malamansa a nan gida Najeriya

  • Ya yi karatu gwargwado a gidan shahararren malami a garin Katsina Sheik Abba Abu.
  • Malam Tanimu Kusfa shahararren malamin fiqihu da sauran fannonin ilimi a garin Zariya.
  • Malam Bala Kusfa a garin Zariya, wanda kanen mahaifinsa ke ɗaukar shi yana kai shi zaurensa don sauraron karatun.

Majalisun da yake ciki

  • Mamba ne a Majalisar Musulmin Najeriya
  • Mamba ne a Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci
  • Shi ne wanda ya kafa Cibiyar Tazkiyah Educational Resource Center, Abuja
  • Shi ne wanda ya kafa Makarantun Tazkiyah mai yawan dalibai 8000.

Ya kasance memba a kwamitocin editoci da dama da suka haɗa da Jaridar Nigerian Association of Teachers of Arabic and Literature inda ya kasance memba tun 2003. Ibrahim Maqari ya gudanar da muhawara da laccoci da dama a duniya. Ya kuma halarci tarurrukan ƙasa da ƙasa da dama, tarukan ƙara wa juna sani. Yawancin laccoci nasa an naɗe su kuma ana rarraba su a cikin kafofin watsa labarai na bidiyo da DVD da kuma yanar gizo.

Haddar Al Kur’ani mai girma

Malamin yana da kimanin shekara 13 zuwa 14 ya yi haddar AlKur’ani mai girma a makarantar da aka buɗe mai suna Madarasatul Faidatul Islamiyya ta gidan Sheik Yahuza Zaria.

A wannan lokacin ne ya samu babban sauyi a rayuwarsa, bayan da mahaifinsa ya cire shi daga tsarin karatun boko bayan ya kammala makarantar sakandare ya mayar da shi makarantar da yake jagoranta da ake kira Jama’atu ‘College of Arabic and Islamic Studies’ kuma a lokacin ne ya muhimmantar da harshen Larabci musamman ilmin ginin ka’idar jimla da ake cewa ilmim nahawu.

Sheik Maqari Farfesa ne da ya koyar da Larabci a Jami’ar Bayero da ke Kano amma ya ritaya a 2020. Yana da aure da kuma ‘ya’ya.

Manazarta

BBC News Hausa. (2021a, February 5). Ku San Malamanku tare da Sheik Ibrahim Ahmad Maqari. BBC News Hausa.

Hamid, T. (n.d.). Books | Sheikh Ibrahim Maqary. 

Voice, M., & Voice, M. (2022, August 21). Know your Sheikh: Professor Ibrahim Ahmad Maqari | The Muslim Voice, Nigeria. The Muslim Voice, Nigeria | Journal of Nigerian Muslims.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page