Skip to content

Solar system

Share |

Solar System, shi ne yankin sama da ya kunshi rana da duniyoyi har guda 9, wacce ɗaya daga cikin duniyoyin ita ce Ard da larabci, ko Earth da girkanci, kamar yadda aka sani a kimiyyance, inda ‘yan’adam da sauran dabbobi suke iya rayuwa.

Duniyoyin dai girma-girma ne kuma ko wacce tana da abubuwan da ta kunsa. Wasu duniyoyin na da duniyar wata ko watanni, kamar yadda duniyar mu ke da guda daya. Kewaye da duniya keyi wa rana, shi yake samar da chanjin yanayi. Mirginawar duniyar kuma shi yake kawo rana da dare.

Duniyoyi tara da suke tsarin solar system

Bayan rana, duniyoyi, da watanni, akwai kuma kananan duwatsun da suke yawo a sararin samaniya (meteorites). Su ne duwatsun da aka fi sani da wai ana jifan aljanu da su in sun je leken asiri a samaniya. In duwatsun suka shigo farfajiyar duniya, shi ne ake ganin su da daddare suna gudu a sama, wuta na ci a bayan su. Ana kiran su tauraruwa mai wutsiya (ko shooting stars a Turance).

Wasu duniyoyin za a iya ganin su da idanu, wasu kuma sai an sa abin hangen nesa. Za a iya ganin Mercury, Venus, Mars, Jupiter da Saturn da idanu saboda sun fi sauran duniyoyin haske. Za mu bi duniyoyin solar system don mu fahimci tsari da suke ciki. Duk duniyoyin da watanni yawancin su a dunkule suke kamar ƙwallo, kamar yadda hotunan kasa suka nuna.

Rana

Rana ita ce mafi girman halitta a solar system. Ita ce ginshiƙi, kuma ita ce tauraruwar da muke taƙama da ita. Ita ta riƙe gabadaya sauran duniyoyi guda taran da ƙarfin janta na girabiti (gravity). Su kuma duniyoyin guda tara suna yi mata ɗawafi. Idan duniya ta yi ɗawafi daga waje ɗaya zuwa ta dawo har wajen, shi ne shekara ɗaya ke nan ta duniyar. Abin da ke kawo dare da rana shi ne, ko wacce duniya, a yayin da take ɗawafin zagaye rana, tana kuma juyawa kamar yadda katantanwa take yi daga gabas zuwa yamma. Shi ya sa rana ke fitowa daga gabas ta faɗi a yamma.

Rana ta ninka duniyar ‘mu girma sau miliyan 1,300,000. Sannan kuma zafinta ya kai digiri 5,726 a kan ma’aunin Celsius. Haka nan rana kan yi kusufi

1. Mercury

Wannan ita ce duniyar da tafi kowacce kusanci da rana, sannan kuma ita ce ta biyu a wajen kankanta a cikin jerin duniyoyi tara bayan Pluto. Saboda kusanci da rana, shekara daya a Mercury kwanaki 88 ne na kwanan duniyar ɗan’adam, amma kuma rana ɗaya a Mercury kwana 59 ne na duniyar mu. Saboda haka yawanci sau ɗaya rana ke faduwa a shekarar Mercury. Watau mirginawarta a hankali take yi. Mercury ta kunshi karafuna ne ba kasa irin tamu ba. Sannan kuma zafinta na kai wa har digiri 427 a ma’aunin Celsius. Da sanyi kuma, tana kai wa digiri -173. Duniyar mu ta ninka girman Mercury sau 16.38.

Mercury, duniya mafi kusanci da rana kuma mafi zafi

2. Venus

Venus ita ce ta biyu a layin kusanci da rana, sannan ita ce ta fi kowacce duniya kusanci da tamu a girma. Shekara daya a Venus ya kama kwana 225 na duniyarmu. Amma kwana ɗaya a Venus kwanaki 117 ne na duniyarmu. Duniyar Venus ba ta juyawa da gudu kamar sauran duniyoyi. Doron ƙasar Venus tarin duwatsu ne masu aman wuta, saboda haka a iya bincike ba abin da zai iya rayuwa a doronta. Yadda bincike ya nuna doron duniyar Venus ana iya ganin Venus daga duniyarmu da idanuwa dab da faduwar rana a ko dab da fitowar ta.

3. Earth

Earth ce ta uku a layi, sannan kuma ita ce da duk wani abu mai rai da aka sani yana rayuwa a doronta ko cikin ta: ‘yan’adam, dabbobi, tsirrai. Earth na da wata guda ɗaya da ake kira moon. Shi ma ‘yar ƙaramar duniya ce da ƙarfin girabitin Earth ta riƙe shi a kusa da mu, kuma shi ma yana ɗawafi yana zagaye duniya. Nisa tsakanin su ya kai kilomita dubu 384,400. Tsakanin Earth da wata Abin da ya sa ake ganin tsaiwar wata kamar yankan farce a ranakun farkon watan musulunci shi ne Earth ce ta ke yi wa watan inuwa daga hasken rana.

Earth, duniya ta uku a jerin duniyoyin dake solar wacce halittu ke rayuwa a cikinta

Tsakanin duniyarmu da rana tafiyar kilomita 149,600,000 ce. Tsananin zafin da aka taɓa yi a duniyar an yi ne a sahara a Libya, inda zafin ya kai digiri 58; tsananin sanyi kuma ya kai digiri 88, a Antarctica, duk a ma’aunin Celsius.

4. Mars

Mars ce ta hudu a layi sannan kuma ita ce ta uku a mafi kankanta bayan Pluto da Mercury. Kasar Mars jajir take cike da tsaunika da duwatsu, shi ya sa ake ce mata “Jar Duniya.” A siffa ta fi kowacce duniya kamance da Earth saboda ana hadari, kuma an samu shaidar wataƙila wata halittar za ta iya rayuwa a ciki saboda akwai birbishin Oxygen, iskar da abubuwa masu rai suke shaƙa a Earth. Mars na da watanni guda biyu a sama suna mata ɗawafi.

Mars

Shekara daya a Mars kwana 687 ne na Earth, amma kuma kwana ɗaya, awa 24 ne da minti 39 — kusan daidai da mu. In za ka auna girman Earth da Mars, za a iya saka Mars kusan 9 a cikin Earth. Yanayin zafin Mars ya kama digiri 23 da zafi, -125 kuma da sanyi, duk a ma’aunin Celsius. Nisa tsakanin Mars da rana tafiyar kilomita miliyan 227,900,000 ce.

5. Jupiter

Jupiter ita ce duniya ta biyar a jerin, sannan kuma ita ce mafi girma a duka cikin guda taran. Earth guda 1,321 za su iya shigewa cikin Jupiter tsaf. Watannin Jupiter guda 69 ne suke mata ɗawafi. Amma waɗanda suka fi kowanne girma su ne Ganymede, Callisto, Io da Europa. Jupiter gabad’ɗayanta curin iskar Hydrogen ne a siffar ƙarfe (da turanci ana ce mata Gas Giant).

Jupiter, duniya mafi girma a jerin duniyoyin solar system

Shekara ɗaya a Jupiter shekaru 12 ne na Earth, amma kuma kwana ɗaya, awa 10 ne kacal. Jupiter ba a zafi ko kaɗan. Yanayin sanyin ya fara ne daga digiri -145 a ma’aunin Celcius zuwa abin da yai gaba. Nisa tsakanin Jupiter da rana tafiyar kilomita miliyan 778,500,000 ce.

6. Saturn

Saturn ce ke bin Jupiter a layi da kuma a girma. Earth 764 na iya shiga cikin Saturn. Watannin ta a kalla 62 ne, amma waɗanda suka fi girma su ne Titan, Enceladus, Iapetus, Rhea, Mimas, Tethys da Dione. Abin mamaki ga siffar Saturn shi ne tana da kuma wasu dauwatsu da suke yi mata kawanya kamar zobe.

Saturn ke bin Jupiter a girma

Kamar Jupiter, saman Saturn ma ba a zafi. Sanyi ya fara ne daga aƙalla digiri -175. Sannan ita ma ana ce mata Gas Giant saboda tarin sinadaran iskokin su Hydrogen da Ammonia, da sauran su, ne suka haɗa ta. Nisan Saturn zuwa rana kilomita biliyan 1,429,000,000 ne. Shekara daya a Saturn ya kama shekaru 29 da rabi na Earth. Kwana ɗaya a Saturn ya kama awa 10 da minti 40.

Uranus

Uranus ita ce ke bin Saturn a layi da kuma girma. Za a iya sa Earth 63 a cikin ta. Watannin ta guda 27 ne, amma waɗanda suka fi girma su ne Miranda, Titania, Ariel, Umbriel da Oberon. Kamar sauran duniyoyin da suka zo kafin ita, ita ma ba a zafi. Duniya na ƙara nisa daga rana tana ƙara sanyi. Sanyin Uranus ya fara daga aƙalla digiri -216 zuwa abin da ya yi gaba. Ita ma curin iska ne kamar Saturn da Jupiter, amma komai a ƙanƙare yake. Saboda haka ake ce mata Ice Giant a Turance. Shi ya sa za a gan ta shuɗiya a hoton kasa.

Nisan ta zuwa rana kilomita biliyan 2, 871, 000, 000 ne. Shekara ɗaya a Uranus ya kama shekaru 84 da kusan wata 4. Rana ɗaya kuma ya tashi awa 17 da minti 14.

8. Neptune

Neptune ita ce mai bin Uranus a girma da kuma a nisa daga rana. Ta ninka Earth girma sau 58. Watanninta guda 14 ne, amma waɗanda suka fi girma su ne Triton, Nereid da Proteus. Sanyin ta ya fara daga digiri -214. Kuma ita ma a ƙanƙare take kamar Uranus. Shekara daya a Neptune ya kama shekaru 164 da watanni 5. Sannan kwana ɗaya ya kama awanni 16 da minti 6. Nisan ta daga rana kilomita biliyan 4,498,000,000 ne.

9. Pluto

Pluto ita ce ta ƙarshe a cikin jerin. Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin guda taran da aka lissafo. Earth ta fi Pluto girma sau kusan 157.

Duniyoyi tara da ke wa rana ɗawafi.

A shekarar 2006, masana sun cire Pluto daga jerin duniyoyi saboda ƙanƙantarta da kuma cewa ba ta cika sharuɗan zama cikakkiyar duniya ba. An samu wasu duniyoyin irin ta a kusa da ita waɗanda su ma duk a ƙanƙare suke.

Sharuɗan abu ya zama duniya:

  1. Ya zamanto duniyar na zagaye rana/tauraruwa.
  2. Ya zamanto ƙarfin girabitin/fizgarta ya sa bavta layi ko tangaɗi a cikin system ɗin.
  3. Ya zamanto babu wani abu a kusa da ita da ya kai ta girma.
  4. Sai kanana, da ake kira wata, ko satellite ‘

Pluto ta cika sharuɗan 1 da 2, amma ba ta cika na uku ba. Saboda haka masana suka cire ta daga cikin jerin duniyoyi.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading