Skip to content

Sunusi Lamido Sunusi

An haife Sarki Sanusi na II a ranar 31 ga Yuli, 1961 ɗa ga Muhammad Aminu Sanusi da Saudatu Anduwa Hussain. Sanusi ya fito ne daga zuriyar da ke da alaƙa da jinin sarauta masu hidimta wa jama’a. An samu limamai da alƙalai da dama a cikin magabatansa. Mahaifin Sanusi, wanda ya riƙe sarautar Chiroman Kano, ya kasance babban jami’in diflomasiyya na Najeriya.

Mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi na II

Nasabarsa

Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, ɗa ne ga Muhammadu Aminu Sanusi. Wanda shi kuma ɗa ne ga Marigayi Sarki Muhammadu Sanusi I, wato sarkin Kano na 54 (1953-1963). Ke nan, kakansa ya bar kujerar mulki lokacin yana shekara 2 da haihuwa. Shi kuma Sarki Muhammadu Sanusi na I ɗan ne ga Sarki Abdullahi Bayero, sarkin Kano na 54. Shi kuma ɗan Sarki Muhammadu Abbas, sarkin Kano na 51. Shi Kuma ɗan Sarki Abdullahi, sarkin Kano na 47. Shi kuma ɗan Sarki Ibrahim Dabo, sarkin Kano na 45.

Karatunsa

Mai Martaba Sarki, Muhammadu Sanusi II, ya yi karatunsa na firamare a makarantar St. Anne’s Catholic Primary School da ke Kakuri, Kaduna daga shekarar 1967 zuwa 1972. Daga nan kuma ya wuce zuwa makarantar sikandire ta King’s College da ke Lagas daga shekarar 1973 zuwa 1977. Bayan kammala karatunsa na sikandire ne ya samu nasarar shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digirinsa na farko a fannin tsimi da tanadi (Economics) a shekarar 1981. Ya kuma samu digirinsa na biyu shi ma a fannin tsimi da tanadi a wannan Jami’a ta Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1983.

Hakazalika a fannin ilimin addini ma ba a bar Mai Martaba Sarki, kuma malami a baya ba, saboda ya yi karatun addini mai zurfi. Ya yi karatun digiri a fannin Shari’ar Musulunci a Jami’ar ƙasa-da-ƙasa ta Afirka (African International University) da ke Khartum ɗin Sudan, inda ya yi karatu daga shekarar 1991 zuwa 1997.

Ayyukansa

Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, ya fara da aikin koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Ya zama malami a wannan jami’ar bayan gama karatun digirinsa na biyu. Ya kwashe shekara 2 yana koyarwa, daga shekarar 1983 zuwa 1985.

Ya bar aikin koyarwa a shekara ta 1985, sai ya koma aiki da wani kamfani mai zaman kansa mai suna Icon Limited reshen wasu bakuna biyu; Morgan Guaranty Trust Bank da ke New York ta ƙasar Amurka, da kuma Baring Brothers da ke London ta ƙasar Birtaniya.

A shekarar 1997, ya koma bankin haɗin kai; wato United Bank for Africa wanda aka fi sani da UBA, wanda ya shiga a matsayin General Manager na sashen bashi da kuma sarrafa hatsari (Credit and Risk Management Division). Ya yi aiki da wannan banki na har ya kai matsayin babban manaja a wannan fanni nasa.

A shekarar 2005, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya bar UBA ya koma First Bank. A wannan banki sai da ya riƙe muƙamin babban Manaja (MD) a shekarar 2009, muƙamin da ya zama shi ne ɗan Arewa na farko da ya fara riƙe shi tun daga lokacin da aka buɗe bankin a shekarar 1894.

A ranar ɗaya ga watan Yuli na shekarar 2009 (1st June, 2009), shugaban Najeriya Umaru Musa ‘Yar’aduwa mai rasuwa, ya yi masa muƙamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya.
Zamowarsa Sarki.

Bayan rasuwar marigayin sarkin Kano, Alhaji (Dr.) Ado Bayero, sai manyan ‘yan majalisar sarki; masu zaɓen sabon sarkin Kano suka tantance sunan Muhammadu Sanusi II, suka miƙa wa gwamnatin jahar Kano ƙarƙashin Engr. (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso. Zaɓen da ya samu amincewar gwamnatin jahar inda ta bayyana Muhammadu Sanusi II, a matsayin sabon sarkin Kano.

An cire shi daga mulki ranar 9 ga Maris na shekarar 2020. Gwamnan Kano da magoya bayansa sun zargi Sarki Sanusi da goyon bayan ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna.

A ranar Juma’a 24 ga watan Mayu, 2024 Sarki Muhammdu Sanusi II ya karɓi takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16.

Sarki Sunusi na II ya samu digirin girmamawar daga jami’o’i kamar haka:

  • Jami’ar Nsukka (University of Nsukka)
  • Jami’ar Bayero (Bayero University Kano)
  • Jami’ar jihar Jos (University of Jos)
  • Jami’ar Binin (University of Benin)
  • Jami’ar Maiduguri (University of Maiduguri)
  • Jami’ar jihar Benue (Benue State University)
  • Jami’ar Abuja (University of Abuja)
  • Jami’ar Oduduwa (Oduduwa University, Ile – Ife)
  • Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (Kano University of Science and Technology, Wudil)

Lambobin karramawa

  • Ya zama gwarzon Gwamnan Babban Bankin Najeriya na shekarun 2010, 2011 da 2013
  • Gwarzon Gwamnan Babban Bankin Duniya na shekarar 2011, Financial Times, London ce ta ba shi lambar yabon.
  • Haka kuma mai martaba ya zama gwarzon shekara ta mujallu da jaridu daban-daban na 2010, 2011 da 2013.
  • Mujallar TIME ta ayyana shi a jerin mutane masu karfin fada-a-ji a 2011
  • A 2013, Gidauniyar the Global Islamic Finance Awards ta ba shi lambar yabo kan bunkasa harkokin bankin Musdulunci a Najeriya.
  • An sanar da shi a matsayin Khalifar Tijjaniya a Najeriya a watan Maris ɗin 2021.
  • An kuma karrama Mai Martaba lambar girmamawa ta kasa ta (CON).

Rubuce-rubucen da ya yi

  • “Democracy, Rights and Islam: Theory, Epistemology and the Quest for Synthesis”, in Ibrahim, J. (ed), Sharia Penal and Family Laws in Nigeria and in the Muslim World: Rights Based Approach, Global Rights, 2004
  • “Shariacracy in Nigeria: The Intellectual Roots of Islamist Discourses”, in Osuntokun, A., Beyond Abacha: Companion Essays, Interconsult, Lagos, 2001
  • “Politics and Sharia in Northern Nigeria”, in Soares, B. F. and Otayek, R., Islam and Muslim Politics in Africa, Palgrave Macmillan, 2007
  • “The Shari’ah Debate and the Construction of a ‘Muslim’ and ‘Christian’ Identity in Northern Nigeria: A critical Perspective”, Paper, University of Bayreuth, July 11 & 12, 2003
  • tre-Dame at Jinja, Uganda, April, 2004
  • “The Hudood Punishments in Northern Nigeria: A Muslim Criticism”, Paper, Seminar of the West Africa Study Group, University College, London, January 17, 2003
  • “The Class Character of Religious Revival: Shari’ah and Ideology in Northern Nigeria” Paper, Second Essex graduate Conference in Political Theory, University of Essex, Colchester, May 4-5,
    2001
  • “Islam, Probity and Accountability: A Critical Essay in History, Philosophy and Law”, Paper, Nigerian Television Authority Channel 10 Annual Ramadhan Public Lecture, Nigerian law School, Lagos, December 3, 2003
  • “Institutional Framework of Zakat: Dimensions and Implications”, paper, Symposium on “Essentials for Building an Islamic Ummah” Katuru Road Mosque, Kaduna, Nigeria, December 2, 2000
  • “An Introduction to Islamic Insurance (Takaful)”, Paper, International Islamic Book fair, University of Lagos, Akoka, Lagos, Nigeria October 9, 2003
  • “Transparency and Probity in Nigeria: Confronting our Present with our Past”, Paper, Annual National Conference of the Federation of Muslim Women’s associations of Nigeria (FOMWAN), Maiduguri, Nigeria, August 27, 2004
  • “Kano Political economy: Reflections on a Crisis and its Resolution”, paper, “The Kano Debate”, Mambayya House, Kano, Nigeria, January 1, 2004
  • “Reforming the Nigerian Economy: Which Model? A Theoretical Critique of Nigerian Economic Policy from 1986-2004”, paper, 2nd Annual Trust Dialogue, Abuja Sheraton hotel, January 13, 2005.
  • “Issues in Restructuring Corporate Nigeria”, Paper, National Conference on the 1999 Constitution, Organized by Network for Justice and the Vision Trust Foundation, Kaduna, Nigeria, September 11-12, 1999
  • “Social Re-Orientation, Private-Public Policy Dialogue and Rebuilding Institutions”, paper, Kano Economic Summit, KAPEDI, Kano, April 25-27, 2006.

Manazarta

African Studies Centre: His highness Sanusi Lamido Sanusi. (n.d.). African Studies Centre.

BBC Hausa. (2014). Tarihin Mallam Sanusi Lamido Sanusi. 

His highness Sanusi Lamido Sanusi. (n.d.-c). His highness Sunusi lamido  African Studies Centre.

Central Bank of Nigeria | Home. (n.d.).

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page